Tag: yadda ake

  • Tarihin Sarkin Musulmi Muhammad Bello

    Tarihin Sarkin Musulmi Muhammad Bello

    Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ɗa ne ga Shehu Usmanu bn Fodiyo, kuma yana daga cikin fitattun almajiransa, waziransa, sannan daga ƙarshe magajinsa. Mutum ne mai tarin ilimi, jarumta, hazaƙa da fasaha, kuma marubuci ne mai zurfin tunani. Tarihi ya tabbatar da cewa jarumtar Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ta bayyana ƙwarai, domin shi ne ya jagoranci yaƙin da aka kwace birnin Alƙalawa, cibiyar Daular Gobir.

    Ya shiga har cikin fadar sarki, ya fatattaki jama’ar Sarki Yunfa, kuma a wannan yaƙi ne aka kashe sarkin. Haka kuma, ya halarci yaƙe-yaƙen jihadin Shehu Usmanu bn Fodiyo sama da arba’in, yana daga cikin ginshiƙan da suka ɗora jihadin bisa ƙafafunsa.

    An haife Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo tun kafin fara kiran Shehu Usmanu bn Fodiyo. Tare da shi aka fara kiran, tare da shi aka yi hijira, tare da shi aka aiwatar da jihadi, sannan daga ƙarshe shi ne ya kafa birnin Sakkwato, inda ya gina wa Shehu gida da masallaci wanda daga baya ya zama cibiyar Daular Musulunci ta Sakkwato.

    Wannan ya nuna irin rawar da ya taka tun daga matakin farko har zuwa kafuwar daula. Muhammadu Ballo ɗa ne ga Shehu Usmanu bn Fodiye, mahaifiyarsa kuma ita ce Hauwa’u. An haife shi a ranar Laraba, cikin watan Zilƙa’ada na shekarar 1195 hijira, a Gidan Shehu na Ɗagel.

    Wannan na nufin an haife shi shekaru bakwai bayan fara kiran Shehu, wanda ya fara ne a shekarar 1188 hijira. Sunansa Muhammad, yayin da laƙabinsa Ballo, kalma ce ta Bafilatani wadda ke nufin mataimaki, kamar yadda Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana a tsokacinsa kan littafin Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur.

    Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya taso cikin kyakkyawar tarbiyya a hannun mahaifinsa, Shehu Usmanu bn Fodiye, wanda shi ne malaminsa na farko. A hannunsa ya fara karatun Alƙur’ani da sauran ilimomin wajibi. Daga baya ya koma hannun baffansa Abdullahi bn Fodiye, ƙanin Shehu kuma almajirinsa, wanda ya zurfafa masa ilimin harshen Larabci tun daga ilimin harshe, nahawu, sarfu, balaga da sauran rassa na ilimi.

    Haka kuma, ya yi karatu a hannun Shehi Muhammadu Nur az-Zaman, inda ya koyi fassarar Alƙur’ani, ilimin Usuluddin, ilimin Haƙiƙa da sauran manyan ilimomi. Ya ci gaba da neman ilimi ba tare da kasala ba har ya zama babban malami mai cikakken basira. An rawaito cewa ya karanta littattafai sama da dubu ashirin da ɗari uku, ko ma fiye da haka, abin da ke nuna zurfin neman iliminsa da himmarsa.

    Bayan rasuwar Shehu Usmanu bn Fodiyo, Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya zama halifa a daren da Shehu ya rasu. Musulmi suka yi masa mubaya’a a gidan Malam Shafa, inda ɗan’uwansa Muhammadu Sambo ya fara yi masa mubaya’a. Da zamowarsa halifa, jihadi bai tsaya ba, sai dai ya ci gaba da ƙarfi da tsari.

    A watan Rajab na shekarar farko da halifancinsa, wasu daga cikin jama’ar Zamfara suka yi ridda, abin da ya sa Sarkin Musulmi ya jagoranci runduna zuwa Burmi, inda aka yi yaƙi mai tsanani har aka samu nasara. Haka kuma, a watan Zulƙa’ada, Malam Abdussalam ya kauce ya haɗa kai da kafirai, sai Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya fuskance su da yaƙi, har ya ci Kware a ƙarshen watan Safar.

    Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya yi yaƙe-yaƙe da Kadaye, Gunki Ganƙa, Kalambaina da Dakarawa. Haka nan ya doke rundunar haɗaka ta Sarkin Gobir Ali tare da Auzinawa na Azbin da Abaru ya jagoranta, inda ya fatattake su har suka tsere. Ya kuma yi yaƙi da rundunar haɗaka ta Zamfara da Bauchi, da wata runduna da ta tattara mayaƙa daga Katsina, Gobir, Azbin da Maraɗi.

    Dukkan waɗannan yaƙe-yaƙe sun ƙare da nasara. An ƙiyasta cewa Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya gudanar da yaƙe-yaƙe sama da arba’in da bakwai, abin da ya tabbatar da jajircewarsa wajen kare daular Musulunci da ya gada.

    A ƙarshe, Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya rasu a gidansa da ke Wurno, gidan da yake amfani da shi wajen keɓewa domin ibada da kusanci ga Allah, wato ribaɗ. Ya rasu a ranar Alhamis da yamma, cikin shekarar 1253 hijira. Kalmominsa na ƙarshe su ne: La ilaha illa Allah, Muhammadu Rasulullah.

    An yi jana’izarsa bisa Sunna, sannan aka binne shi a wannan gida kamar yadda ya yi wasiyya. Tarihi ya bar shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan Daular Sakkwato, malami, jarumi, shugaba kuma abin koyi ga al’umma.

    Danna nan don karanta Tarihin Kafuwar Ƙasar Kuwait

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ciwon Kunne Yake

    Yadda Ciwon Kunne Yake

    Da farko shi kunne kanshi an kasa shi ɓari uku (3) :

    1- Outer Ear (Wajen Kunne).

    2- Middle Ear (Tsakiyar Kunne)

    3- Inna Ear (Cikin Kunne)

    Kuma kowannen su zai iya samun matsala amman mafi yawan ciwon kunne da mutane suke complaining a kai Middle Ear ne (Ciwon tsakiyar kunne Wanda a turance a Kira da (Otitis Media).

    ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE (OTITIS MEDIA)?

    Yana daga cikin abubuwan da suke kawo ciwon tsakiyar kunne:

    1- Kwayar cututtuka kamar su:

        a- Bacteria

        b- Virus

        c- Fungi

    Amma mafi yawa Bakteriya ne, waɗannan ƙwayoyin cututtukan yawanci suna samun hanyar shiga ne ta maƙogoro zuwa tsakiyar kunne. (Akwai hanyar da ta haɗa su dama).

    2- Ana samun ciwon kunne ta dalilin shigar wani abu kamar ɓurɓushin ƙura , Gashin mage da sauransu (Allergies).

    ALAMUN CIWON TSAKIYAR KUNNE:

    1- Mutum zai ji kamar wani abu ya cika masa kunne.

    2- Rashin ji sosai

    3- Zubar da ruwa a kunne

    4- Jin zafi a cikin kunne.

    5- Ƙaikayi da ji kamar ana masa kiɗa

    6- Zazzaɓi da ciwon kai.

    MENENE ALAƘAR MURA DA CIWON KUNNE:

    Gaskiya akwai alaƙa tsakanin mura da ciwon kunne, mafi yawan mura yana kama hanci da maƙogoro kuma idan ba ku manta ba mun ce akwai hanyar da ta haɗa tsakanin maƙogoro da hanci da kuma tsakiyar kunne .

    Kamar yadda muka ce ƙwayoyin cutar Bakteriya, da virus da fungi da kuma ɓuɓushin ƙura su suke kawo ciwon kunne. To waɗannan ƙwayoyin cutar su suke kawo mura kuma suna samun hanyar shiga kunne ta wannan hanyar da ta haɗa tsakanin maƙoro, hanci da kunne.

    SHIN ƊIGAWA KUNNEN MAN ZAITUN YANA MAGANIN CIWON KUNNE :

    Kuskure ne ɗiga wa kunne man zaitun, ba ma man zaitun ba ko maganin ciwon kunne irin su Gentamycin bai kamata a ɗigawa kunne ba, in ba da izinin likita ba. Dalili shi ne wani lokocin ana samun hujewan dodon kunne (Rupture of earwax) lokocin da ake ciwon kunne to kowanne irin abu idan ya wuce can ciki zai iya kawo matsala.

    MAGANIN CIWON KUNNE :

    Tabbas duk wani ciwon kunne da ƙwayoyin cutar bakteriya ta kawo su ana amfani da ANTIBIOTICS wajen treatment, hakanan wanda aka samu ta dalilin ɓurɓushin ƙura ana amfani da ANTIHISTAMINES.

    GARGAƊI:

    Da yawa daga cikin mutane idan kunnensu yana ciwo kawai zuwa suke chemist a wanke musu kunne. Bincike ya nuna akwai sinadarai guda goma a tsakiyar kunne wanda aikinsu shi ne hana wasu ƙwayoyin cuta na bakteriya da makamantan su girma da shiga cikin kunne,  a garin wanke dauɗar kunne idan aka wanke waɗannan sinadaran to daga nan an buɗewa ƙwayoyin cuta ƙofa ne. Shi wannan wankin kunnen yana da ƙaidoji.

    WASU ZA KA GA SUNA YAWAN ƘWAƘULE KUNNE:

    Amfanin “dauɗar kunne” da illar ƙwaƙwale ta.

    “Dauɗar kunne” wani ruwa ne mai ɗan danƙo da dodon kunne ke samarwa domin bai wa kunne kariya, saɓanin yadda Bahaushe ke cewa “dauɗar kunne” ce . Saboda haka “dauɗar kunne” ba dauɗar ƙazanta ba ce, face wata hanya ce da kunne ke samar wa kansa kariya daga baƙin abubuwa da ka iya shigowa daga waje. 

    Allah da ikonsa, kamar yadda kunne ne ke samar da wannan “dauɗar kunne”, haka nan kunnen ke da ikon yashe wannan “dauɗa” da kansa. Daga cikin amfanin “dauɗar kunne” akwai:

    1. Cafke dukkan nau’in ƙura, ƙasa, ƙwari ko yayi kafin su kai ga cikin kunne.
    1. Kashe ƙwayoyin cutar Bakteriya, da sauransu.

    Saboda haka kada ka yi amfani da waɗannan abubuwa don ƙwaƙwale dauɗar kunne:

    1. Magogin kunne wato ‘cotton bud’ a turance.
    1. Tsinken tsintsiya
    2. Mirfin biro
    1. Kan ashana
    1. Gashin kaza, da makamantansu.

    Sanya waɗannan abubuwa cikin kunne don ƙwaƙwalo “dauɗar kunne” na da haɗarin:

    1. Ƙara cusa “dauɗar” zuwa can cikin kunne.
    2. Karairaya gasun cikin kwararon kunne, wanda suke amfani wajen kare kunne daga baƙin abubuwa daga waje.
    3. Cusa irin waɗannan abubuwa na da haɗarin shigar da ƙwayoyin cuta cikin kunne.
    4. Raunata gangan kunne yayin da irin waɗannan abubuwa suka zarme cikin kunne.
    5. Shafe ko manne “dauɗar kunnen” a kwararon kunne.

    Haka nan, zira waɗannan abubuwa cikin kunne don susa ko ƙwaƙwalo “dauɗar” akai-akai zai share kwararon kunne, kuma share ƙwararon kunnen na nufin share kariyar da Allah ya shirya wa kunne.

    Saboda haka, dukkan baƙin abubuwa na iya kutsa kai cikin kunne kai tsaye. Kada ka ɗauki ɗabi’ar sa magogin kunne cikin kunne don goge “dauɗar kunne” kullum. 

    SHAWARA: Tuntuɓi likitan kunne (ENT DR.) da zarar ka fara jin wani baƙon yanayi a kunnenka, ko neman shawarwari kan tsabtace kunne daga “dauɗar kunnen”.

    Danna nan don karanta Yadda Hukuncin Tsotsar Al’aura Yake A Likitance

    Edita@rumasau-kallamu

  • Cin Zarafin Ƙananun Yara Da Kariya A Bisa Haka

    Cin Zarafin Ƙananun Yara Da Kariya A Bisa Haka

    GABATARWA

    ‘Child maltreatment’:- Cin zarafin ƙananun yara na nufin cutarwa ko wofantarwa da ake yi wa yara ‘ƴan ƙasa da shekaru 18. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da cewa a duk faɗin duniya, kimanin yara biliyan 1 ne suka fuskanci cutarwa ta taɓuwar lafiyar jiki, ko ta ɓangaren jima’i ko kuma ta ɓangaren damuwa mai jiɓi da ƙwaƙwalwa.

    Wannan na nufin, rabin yara masu shekaru 2-17 da ke rayuwa a wannan duniyar tamu sun haɗu da wancan tasgaron. Lallai wannan abin tashin hankali ne. Don haka ne yake da matuƙar muhimmanci a gare mu manya mu ɗauki mataki a game da shi.

    Kawar da cutarwa da wofantarwar da ake yi wa yara haƙƙi ne da ya shafi al’umma baki ɗaya, saboda haka ya kamata a ce mutane daga rukunan al’umma mabambanta sun fahimci matsalolin da ke tattare da cutar da ƙananun yara tare da ɗaukar matakai don daƙile aukuwar hakan.

    BAYANAI NA GASKIYA GAME DA CIN ZARAFIN YARA

    Bisa haƙƙaƙewar ƙungiyar ISPCAN (International Society for the Prevention of Child Abuse and Neglect), hujjoji na ƙara ƙamari masu nuni da cewar wofantarwa gami da cutarwar da ake yi wa ƙananun yara ne silar aukuwar rabin matsalolin da al’ummar mu ke fuskanta a halin yanzu.

    Cin zarafin ƙananun yara laifi ne, kuma saɓa dokar kundin tsarin mulkin Nigeria ne, kamar yadda yazo a;- Chapter 21: Offences against morality”  Criminal Code Act, Chapter 77, Laws of the Federation of Nigeria 1990. Retrieved 2 April 2016.

    Haka nan, rahoton binciken ƙasashen duniya ya bayyana cewa kusan a duk yara 4 masu shekaru tsakanin 2-4, ana samun yara 3 waɗanda suka fuskanci azabtarwa ta jiki da/ko cusa musu damuwa daga ɓangaren iyaye ko masu reno, haka kuma ana samun a duk  mace 1 a cikin mata 5, da namiji 1 a cikin maza 13 cewa sun miƙa koken an ci zarafin su ta ɓangaren jima’i a lokacin da suke yara.

    MATSALOLIN DA CIN ZARAFIN ƘANANUN YARA KE HAIFARWA A YANKUNAN MU

    Matsalolin da cin zarafin yara ƙananu ke haifarwa suna da tarin yawa, kamar yadda a baya muka kawo rahoton binciken ƙungiyar WHO cewa kusan rabin matsalolin al’ummar mu na da tushe ne daga cin zarafin ƙananun yara, wanda hakan ke nuni da cewa matsawar za mu tashi tsaye wajen kawar da waɗannan matsaloli to kuwa tabbas yawaitar rashin zama lafiya da ƙananun laifuffuka har ma da manya za su ragu matuƙa a garuruwan mu.

    NAU’IKAN CIN ZARAFI

    Nau’ikan kashi huɗu ne, amma suna da rukunai ko yanayai da dama.

    1. Cin zarafin yaro ta hanyar cutar da lafiyarsa

    2. Cin zarafin yaro ta hanyar jima’i. Wannan ya danganci wasa ko cusa wa yaro wani abu na al’aura ko makamancin sa a al’aurar sa, da kuma ɗaukar hoton al’aurar ko sanya yaro yin wasa da ita.

    3. Cin zarafin yaro ta hanyar cusa masa damuwa

    4. Wofantarwa; watau rashin sauke wani nauyi na yaro da ya rataya a kan wani mutum.

    YADDA ZA A KAWO ƘARSHEN CIN ZARAFIN ƘANANUN YARA

    YA KAMATA MU SOMA MAGANTUWA: Cin zarafin ƙananun yara kan faru cikin sirri, don haka muna da buƙatar samar da kyakkyawar hanyar jan ra’ayin al’ummar mu su soma magantuwa a kai domin wannan batu ne wanda mutane ba kasafai suke jin daɗin tattauna shi ba.

    Don haka muna da buƙatar sanya abubuwa da dama domin gina ‘shingayen kariya’ (safety nets) a cikin mazaɓun mu.

    Matakan bi domin kare cin zarafi su ne:-

    1. Ilimantar da al’umma

    A. Koyawa alummar mu alamomi na kai tsaye da suke nuni da cin zarafi ga ƙananun yara.

    B. Ilimantar da Malamai

    Malamai kan iya zamowa bangon samun rabauta jallin-jal wajen kawar da cin zarafin ƙananun yara idan har ya kasance malaman sun fahimci abin sosai tare kuma da ba su tallafi na musamman.

    C. Ilimantar da Yara

    Ƙananun yara ba su da buƙatar sanin cikakken bayani game da cin zarafi, to amma akwai buƙatar koyar da su sauƙaƙan dokokin kare kai daga haɗuwa da cin zarafi, misali ya kamata a koyar da yara cewa :-

    -Babu wanda zai kasance yana cutar da ni

    -Babu wanda zai taɓa min al’aura

    -Babu wanda zai ɗauki hoton al’aura ta.

    – Idan ina da wata matsala, zan sanar da ita ga wani na

    -Kada na bar duk wata cutarwa da wani ke yi mini a matsayin sirri musamman wadda ta shafi taɓa al’aura ta.

    -Na sanar da wani/wata idan wani na ƙoƙarin haiƙe mini

    2. DOKOKI

    Wajibi ne masu zartar da dokoki su samar da doka mai ƙwari da hukunci mai raɗaɗi ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin ƙananun yara. Wannan shi ne babban mashimfiɗi da za mu samar domin kawar da duk wata barazana mai fuskantar manyan gobe.

    Karanta Waƙa Mai Taken Rabbi Kare Min Mijina

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Ɗan Achaɓa

    Waƙa Mai Taken Ɗan Achaɓa

    1. Salamu Alaikumu barka da yanzu,
    Gaishe ku nake da fatan za ku karɓa.
    2. Batu zan yo da fatan za ku so shi,
    A kan goganku wato Ɗan Acaɓa.
    3. Mutum mai taimakon jama’a a kullum,
    Cikin sanyi da rana har da raɓa.
    4. Da yin asuba ka leƙo za ka gan shi,
    Da rana haka dare kwai Ɗan Acaɓa.
    5. Idan tafiya ta kama za ka yi ta,
    Cikin sauri ka nemo Ɗan Acaɓa.
    6. Wuri in ya zamo nisa da titi,
    Shigar sa mutum guda ne Ɗan Acaɓa.
    7. Idan hanya ta zam mai “go slow” ce,
    Idan sauri kake ɗau Ɗan Acaɓa.
    8. Shi ne zai kai ka kai gararin gabanka,
    Ya mai da ka idan haka nan ka zaɓa.
    9. Mutum ɗaya har biyu ɗauka yake yi,
    Ya kai ya zube ya juyo Ɗan Acaɓa.
    10. Tsananin sanyi ba ya hana ɗan acaɓa,
    Tsakar rana ruwan sama za ya caɓa.
    11. Akan jinga da shi a biya shi mako,
    Ko ko a wata in ya cika sai ya karɓa.
    12. Kamar yara ya kai su ga makaranta,
    Uba ko wuri na aiki ba shi saɓa.
    13. Wannan su ne wasu daga fa’idoji,
    Na wannan taliki mai yin acaɓa.
    14. Akwai kuma aibuka jingim gare shi,
    A muninsu da wari sun fi jaɓa.
    15. Masifar son kuɗi Jimina kira shi,
    Kai ya fi makauniya nema a caɓa.
    16. Bai ɗau rai nasa komai ba bare ma,
    Na fasinjansa goga Ɗan Acaɓa.
    17. Tafiyar hauka da ganganci gare shi,
    Dukan runtsi ya je sai ya laɓaɓa.
    18. Sanin doka ta hanya ba ruwansa,
    “Shiga a haka” yake yi Ɗan Acavɓa.
    19. Shigarsa kwana ƙafa tai za ya harba,
    Siginar ya ciccire domin a kwaɓa.
    20. Mota ƙarama da bas har gingimari,
     Ratsa su yake gaba-gaɗi mai acaɓa.
    21. Burinsa kawai ya kai fasinja nasa,
    Ya karɓi kuɗin ya ɗau wani mai acaɓa.
    22. Idan ya yi ma karo babur ya lotse,
    Taron dangi suke maka ‘yan acaɓa.
    23. “Ɗan uwa namu ka cuta ba mu yarda,
    Biya za kai asara ba mu karɓa!
    24. “Domin ba nasa ne ba wanga babur,
    “Waninsa ka mallaka shi ko acaɓa.”
    25. Ɗaruwwan famfamai kullum ka samu,
    Biyansa balas a nan ne za a saɓa.
    26. Tun kan ranar yake ta cika ya batse,
    Ganin ƙyashi yake yi Ɗan Acaɓa.
    27. “Mutum na zaune ni ko ga ni rana,
    Ina nema shi ko sai dai ya karɓa!
    28. “Tsananin sanyin Disamba duk a kaina,
    Ya ƙare ni ka yin aikin acaɓa.
    29. “Wannan ɗanyen hukunci ba ni yarda,
    Kura a buga kuɗin gardi ya karɓa!!”
    30. Da ya ɗan fara zowa sai ya noƙe,
    Ku ɗaura burum-burum ho Ɗan Acaɓa!
    31. Ya ɗauke wuta wata har sai ya shuɗe,
    Bai zo da balas ba goga mai Acaɓa!
    32. Idan ko an yi sa’a zai ta kai wa,
    Zuwa wasu ‘yan watanni ba shi saɓa.
    33. Daga nan babur yakan ce ya yi tsufa,
    A sayar a sayo wani don yai Acaɓa.
    34. Idan har ka ƙiya wani za ya nema,
    Ya aje ma naka sabo za ya karɓa.
    35. Ka nemi sayar da shi in an taya ma,
    Abin ba kyau gumi za kai ta sharɓa.
    36. Wannan halinsu kenan aksarinsu,
    Marasa kishi na zuci ‘yan a kwaɓa.
    37. Amma fa akwai nagartattu cikinsu,
    Da ke neman halal hanyar acaɓa.
    38. Tuƙin nutsuwa sanin doka ta hanya,
    Abin da ka ba shi duk shi za ya karɓa.
    39. Ba ya wasa da kai haƙƙi na babur,
    Wurin mai shi amintaccen acaɓa.
    40. Albarka Rabbana kan sa wa wannan,
    Cikin samun da zai hanyar Acaɓa.
    41. Idan ka tashi neman Ɗan acaɓa,
    Mutum mai hankali nutsuwa ka zaɓa.
    42. Guji mai karkacewa in ya zauna,
    Ya sa hana-salla ɗan gararin acaɓa.
    43. Idonai ya rufe da baƙin gilashi,
    Danja ko ta tsayar shi za ya raɓa.
    44. Takensu irin waɗannan “Sai ka kai shi!”
    “Ko ba rai!” za ya amsa Ɗan Acaɓa.
    45. Muna roƙon ka Allah taimake mu,
    Ka sa gyara cikin sana’ar Acaɓa.
    46. Gwamnati dole ta yo wani agaji kai,
    Domin samun rage haɗuran acaɓa.
    47. Haka su ma masu babur kar su ba da,
    Sai ga mai nutsuwa da zai aikin Acaɓa.
    48. A nan zan dakata sai an jimanku,
    Salamu Alaikumu har Ɗan Acaɓa.
    49. Muhammadu Nasiru G. Ahmadu ne,
    Ya yo waƙar bayanin Ɗan Acaɓa.
    50. Baiti Ashirin biyu daɗa goma kansu,
    Hamsin ke nan a kan sana’ar Acaɓa.
    Alhamdu Lillah.
    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Alƙawari Kaya
    Edita@rumasau-kallamu
  • Waƙa Mai Taken Alƙawari Kaya

    Waƙa Mai Taken Alƙawari Kaya

    1. Sunanka farko ya Allah,

    Tsira amincinka Allah,

    Ƙara su gun Manzon Allah,

    Shi munka burin mui kalla,

    Ko da cikinsa mafarkinmu.

     

    1. Yau damuwa ce ke raina,

    Bisa batu da muke raina,

    Cikin darenmu ko rana,

    Son rai gare mu abin ƙauna,

    Kan dukkanin harkokinmu.

    1. Cika shi alƙawari sunna,

    Ga dukka manya da ƙanana,

    Saɓa shi ko aikin ɓarna,

    Da Rabbi sarki ya yi hana,

    Ga duk maza har matanmu.

    1. Muna barin sa umarnin nan,

    Na Rabbana da ya yo ɗin nan,

    Ayar cikin Qur’anin nan,

    “Ku zam cika alƙawarin nan,

    Don za a tambayi shi” gun mu.

     

    1. “Ya muminai shin mis sa ne,

    Kuke batu” a tsaye zaune,

    “Da ba ku yin sa a aiki ne?”

    Faɗin Ta’ala sarki ne,

    Gare mu kan hali namu.

     

    1. Abin takaici mun ƙyale,

    Wannan umarni sai hole,

    Ran tambaya ba ma kalle,

    Halinmu ba kyawu walle,

    Don babu alƙawari gunmu.

     

    1. Alƙawari in mun ɗauka,

    Na lokaci kan duk harka,

    Ko yin wani aiki gun ka,

    Ni kam gaske nake ɗauka,

    Amma cikawa bai samu.

     

    1. Murna muke in mun saɓa,

    Muna ganin ai mun caɓa,

    Har jinjina muka zam karɓa,

    Kuka ya dace mui sharɓa,

    Don ya  ƙazanta aikinmu.

     

    1. Ga ‘yan siyasa ko ado ne,

    Suna ganin mai sauƙi ne,

    Hanyar zuwa ga muradi ne,

    Bayan guba mai halaka ne,

    Gare su har umma tamu.

     

    1. Babu dalilin saɓawa,

    Sai don mugunta aikawa,

    Nuna isa ko burgewa,

    Ko sakaci ga mutuntawa,

    Da munka yi bisa zatinmu.

     

    1. Ƙarfe goma ka ce zan zo,

    Ko ko ka ce wa wane ya zo,

    Ba kai shiri goman ta zo,

    Sai uzuri ba yin ƙwazo,

    Ba ka nadama ko damu.

     

    1. Ka ce wa yaro bar kuka,

    Abu kaza ne zan ba ka,

    Alƙawari ne ka ɗauka,

    Amma ka saɓa wa ɗanka,

    Ka muna tarbiyyar ɗanmu.

     

    1. Wannan fa mugun hali ne,

    Amma gare mu abin so ne,

    Da takamar mun burge ne,

    Bayan ko laifi babba ne,

    Za ai hisabin sa kanmu.

     

    1. Bai zam cikar addini ba,

    Bai zam shi halin kirki ba,

    Bai zam abin tunƙaho ba,

    Bai zam cika ga kamala ba,

    Saba wa alkawari namu.

     

    1. In ka tsananta ga cikawa,

    Ka ƙyamaci a yi saɓawa,

    Wai ka yi halin Turawa,

    Halinka na da tsanantawa,

    Don ka ƙi mugun halinmu.

     

    1. Faɗa a cika dattaku ne,

    Ko da ko mai yin yaro ne,

    Ko a ina mai ƙima ne,

    Abin a ba wa aminci ne,

    Mai martaba gun sarkinmu.

     

    1. Da mu ya dace ai koyi.

    Ya zam gare mu abin ya yi,

    A zahiri da cikin rayi,

    Mun bar Nasara kaɗai ke yi,

    Mun zaɓi ɗaukar son ranmu.

     

    1. Wannan abin jin kunya ne,

    Gare mu babban aibu ne,

    Abin ragewar ƙima ne,

    Da za mu taru mu gaggane,

    Da sun yi kyau harkokinmu.

     

    1. Tsari rashin sa ka damun mu,

    Na lokutan harkokinmu,

    Loto abin banza gunmu,

    Shi ne ko ai rayo tamu,

    In ya wuce bai komen mu.

     

    1. Faɗa a saɓa laifi ne,

    Loto a sauya aibu ne,

    Warware zance nakasa ne,

    Kin cika kawari sabo ne,

    Mu zam cire shi a halinmu.

     

    1. Shi alƙawar ai kaya ne,

    Bisa ga kai nannauya ne,

    Kula da shi imani ne,

    Cika shi aikin lada ne,

    Mai nauyaya mizaninmu.

     

    1. Allah ya ba mu dukan dace,

    Mu’amalarmu ta zam tsafce,

    Ta zam gudana dinance,

    Yara su koya su gwanance,

    Su zam du’a’i bayanmu.

     

    1. Nan zan tsaya na ciyo burki,

    Tabara ba mu yawan ɗauki,

    Mu tabbata a halin kirki,

    Kullum bisa dukka mataki,

    Na rayuwa har ƙarshenmu.

     

    1. Mai tsara waƙar Nasir ne

    Ahmad rarrauna ne,

    Gare mu mai yin addu’a ne,

    Bisa ga kyautata hali ne,

    A dukka alƙawarorinmu.

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙar Neman Mafita Da Riba Babba

    Waƙar Neman Mafita Da Riba Babba

    1. Allah sarki ne mai yawaita

    Falala da tsari da kyauta

    Bismillah zan karanta

    Waƙar mafita da riba

    2. Zamanin nan ya ƙazanta

    Lamurra duk sun jirwanta

    Ayyuka da halin mugunta

    Ga cin amana bai tsaya ba.

    3.  Garkuwa don kuɗi da sata

    Ga yawan fyaɗe da ƙeta

    Ga rashin ladabin ‘yammata

    Duk ba zai mana mafita ba.

    4. Tur da sauyi maras nagarta

    Mai ɗorawa mutum kurumta

    Ayyukan sharri ko mugunta

    Mance Allah ba zai mana ƙa’ida ba

     

    5. Son kuɗi duk ya tsananta

    Burin kowa ya huta

    Da kuɗi mata da mota

    Babu cas, ko as dat ta’abba.

     

    6. Shi yasa ayyukan mugunta

    Munana, masu raba zumunta

    Ayyuka na rashin aminta

    Sun yawaita ba ma huta ba.

     

    7. Ga uwa ta saida ɗanta

    Ga uba ya haiƙewa ‘ƴar ta

    Ga ɗa yay fansa da wauta

    Ya subhanallahi ka tsare mu gaba

     

    8. Ran Hanan dai ya salwanta

    Malaminta ya ha’inta

    Ya aikata abin mugunta

    Aikin sa gareshi babu riba

     

    9. Aisha mai kasshe kanta

    Wani jami’i shi yai lahanta

    Cin zarafi mai muni na mata

    A zamanin nan ana yi ba da ƙa’ida ba

     

    10. Shugabanni da halin mugunta

    An sa talaka yana ragaita

    Daɗin haraji, tsada, duk an azabta

    Janye tallafin mai ba abu ne mai kyau ba

     

    11. Masu tsafi kun ƙazanta

    Masu caca kuna da wauta

    Luɗu da cin zali duk sun haramta

    Wanda duk bai bi Allah ba ba zai zauna lafiya ba

     

    12. Yau fasadi ya inganta

    Mai bin shaiɗan zai kafirta

    Ayyukan sa duk sun muzanta

    Annabin Allah ya hane mu da cin riba

     

    13. Masu shirka sun yawaita

    Masu kiran haram saboda wauta

    Ayyukan gaskiya ya ƙaranta

    Lalle masifa a duniya ba ta gushe ba

     

    14. A yau ƙarya ita ce mai tsafta

    Wasu ma sun ƙware a kanta

    Samun kuɗin su shi ne mafitta

    Ai kuwa hakan ba abu ne mai kyau ba

    15. Aikin ‘yan ta’adda ya ƙazanta

    Zubar jini a yankin mu ya yawaita

    Asalinsu akwai cin hanci da ƙeta

    Jami’ai masu cin amana ƙarshensu ba zai yi kyau ba

     

    16. ‘Ƴan siyasa ya kuke ta

    Yaudarar talaka da sata

    Kun hana arziƙi ya wadata

    Kawunan ku kuke so ba talaka mai wahala ba

     

    17. Ya kamata fa mu fahimta

    Arziƙi ko da ya tsananta

    Ko talauci in ya rabanta

    Ga bawa ƙaddara ce wadda ba a guje ba

     

    18. Tun gabannin yin halitta

    Rabbuna Allah ya hukunta

    Arziƙin ɗa, bawa ko jarrabta

    Duk abinda mutum zai yi ba zai keta ƙa’ida ba

     

    19. Yanzu menene mafitta?

    Ga zukata sun firgitta

    Rashin natsuwa ya yawaita

    Duk abinda mutum zai yi ba zai sake ba

     

    20. Fahimtata a rayuwa ta

    Sai mun sauya jigon nagarta

    Sai mun rage raɗaɗen masu jinta

    Sai muso juna da alheri banda gaba

     

    21. Jama’ar mu akwai nagarta

    A basu ilimi shi na fahimta

    Zai kawar da talauci mai kanta

    Duk mai aiki da hikima ba zai sha wuya ba

     

    22. Ilimi mai sa nagarta

    Mai gyara ayyuka da fahimta

    Jahilci kuwa idan ya yi kanta

    Dole ayyukan jama’a ba za su yi kyau ba

     

    23. Tarbiyya ko mafi inganta

    Turbar Islama binta

    Ba fasadi babu cuta

    Komai aka mayar ga Allah ba zai zama mai wuya ba

     

    24. Ladabi abu mai kyau ga mata

    Rufe tsiraicin su za su kuɓuta

    Bin iyaye da magabata

    Barin fariya, yin ɗagawa abu ne ba mai kyau ga lahira ba

     

    25. A koyar da yara jarumta

    Aiki tuƙuru shi ne za a huta

    Lalaci, sakaci ko sata

    Ayyuka ne haramtattu da ba za a yi su da ƙa’ida ba.

     

    26. Mu kalli Japan, Sin da Kolkata

    Matasa na fafutika, kai hatta

    Yara ƙananu da mata

    Kowa na son ceton ƙasarsa ba cutar da ita ba

     

    27. Neman halak abu ne mai tsafta

    Mai gyara ƙasa da zukata

    Idan zukata suka ladabta

    Ayyukan bayi da dama ba za su ƙetare ƙa’ida ba

     

    28. Wajibi zalinci ya huta

    Adalci shi ake buƙata

    Tsayar da haddi ga masu gata

    Matsawar kuɗi suka rinjayi adalci ba za mu zauna lafiya ba

     

    29. Ya Allah ka ba mu mafitta

    Ya Rahmanu sarkin Nagarta

    Ya man iza da aka fa ajibta

    Ya Laɗifu ka yaye mana  rashin aminci da gaba

     

    30. Ni Sadiq Gwarzo na yawaita

    Damuwa shi yasa na rubuta

    Waƙar ina kewa da buƙata

    Ina adduar samun tsira da rabo babba.

    ALHAMDULLAHI

    Karanta Tarihin Garin Rimin Gado

    Edita@rumasau-kallamu

  • Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya 2025

    Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya 2025

    Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ya gudana cikin nasara a ranar 31/12/2025 a ɗakin taro na Manpower Development Institute da ke garin Dutse jihar Jigawa, inda ya haɗa marubuta, manazarta, malamai, ‘yan jaridu, ɗalibai, da wakilan gwamnatoci daga sassa daban-daban na Nijeriya da maƙwabtanta.

    Taron ya ƙara jaddada muhimmancin rubutun Hausa a ƙarni na 21, musamman a fuskokin tsaro, tattalin arziki, al’adu, da ci gaban al’umma.

    Muhimman Abubuwan Da Aka Tattauna A Wajen Taron:

    1. Ƙalubalen Tsaro da Al’adar Karatu: An jaddada cewa duk da ƙalubalen rashin tsaro, akwai babbar matsala ta raguwar al’adar karatu musamman a tsakanin matasa, wadda ke buƙatar tsayuwar daka. An ba da shawarar a fara gyara tunani tun daga makarantu, ta hanyar kafa kulob-kulob na karatu da al’adu, tare da gayyatar marubuta su riƙa yi wa ɗalibai bita kan muhimmancin rubutu da karanta littattafai.

    Sai kuma yadda za a yi amfani da fasahar AI domin gina rubutu mai inganci da kuma sauƙaƙawa marubuta da amfanin hakan ta fuskar tsaro da tattalin arziƙi.

    2. Zaurukan Tattaunawa (Panels):

    “Rubutun Zube na Hausa a Onlayin: Ina aka dosa?” inda masana suka tattauna muhimmanci da ƙalubalen rubuce-rubucen onlayin, musamman matsalar rubutun batsa.

    “Marubuta Mata a Jiya da Yau: Ina aka dosa?”

    “Rubutun Gajerun Labaran Hausa: Ina aka fito? Ina ake? Ina aka dosa?”

    “Tattaunawar waƙoƙin Hausa.”

    “Rubutun Hausa a wajen ƙasar Hausa”

    Waɗannan zauruka sun samar da ilimi mai zurfi da gogewa wadda ke da wahalar samuwa a wuri guda.

    3. Halarta da Wakilci: Taron ya samu halartar marubuta sama da 250 daga faɗin Nijeriya, tare da wakilcin gwamnatocin Arewa musamman Kano, Katsina da Jigawa. Haka kuma, an samu baƙi daga ƙasashen Togo, Kamaru, Senagal da kuma ƙasar Nijar.

    An bayar da kyaututtuka ga manyan baƙi na musamman da kuma marubutan da suka samu nasara a gasar da aka shirya don taron.

    Ga wasu daga cikin hotunan taron

    Kammalawa

    Taron ya tabbatar da cewa rubutun Hausa ginshiƙi ne na gina tunani, tsaro, da tattalin arziki, kuma dole ne a ƙara ƙaimi wajen farfaɗo da al’adar karatu da rubutu, musamman a tsakanin matasa. An amince da ɗaukar darussa daga ƙalubalen da aka fuskanta domin ƙara inganta taruka na gaba.

    Danna nan don karanta Taron Makon Hausa FCE Bichi 23 Oktoba 2025

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Rabbi Kare Min Mijina

    Waƙa Mai Taken Rabbi Kare Min Mijina

    Rabbi kare min mijina

    Abin kirana farin ciki na

     

    1. Ni ina sonsa sahibina

    Shi nake so nake wa ƙauna

    Shi yake sanya murmushi na

    Shi yake yaayen fushi na

    Shi nake yi wa kwalliya ta

    Ina adon gyara fuskata

    Na sanya kwallin idaniyata

    Na fesa ƙamshi ga suttura ta….

    Rabbi kare min mijina!!!

    Rabbi amsa min kira na!!!

    Rabbi kare min mijina!!!

     

    2. Ni a guna sam bai da tamka

    Duk sirrikana shi za su riska

    Da nay fushi, in ya zo na sauka

    Hidimtakarsa ke sani kuka

    Ya abin so farin cikina

    Na mallaka maka dukka kaina

    Ina ƙaunar ka dare da Rana

    Ina yawan sonka sahibiyna…

    Abin kirana farin ciki naaaa!!!

    Rabbi kare min mijinaaa

    Abin kirana farin ciki naaa

     

    3. Yau da kullum na ayyukansa

    Hawa da sauka a lamurransa

    Yana cikin sauke haƙƙunan sa

    Yana yawan bani lokacin sa

    Shi ya sanya nake ta son sa

    Ina ta Rama don ambaton sa

    Ina shirin kare lafiyar sa

    Ina nufin na zama garkuwar sa…

    Haba masoyi ka ceci raina!!!

    Rabbi amsa min kira na!!!

    Rabbi kare min mijina!!!

     

    4. Son ka ya keta zuciya ta

    Yayi cafkar idaniya ta

    Yana ta yawo a jijiya ta

    Son ka shineee Rayuwa ta

    Zan biyayya a lamuranka

    Zan yi tamkar Sa ɗakar ka

    Zan duƙursawa zantukan ka

    Za ni girmama ‘ƴan uwan ka…

    Ni ina sonka ya miji na..

    Rabbi kare min mijina

    Abin kira na Farin cikina 

     

    5. Shi ne mijina farin ciki na

    Shi ne yake gyara laifuka na

    Shi ne yake saita lammura na

    Shi ne yake ɓoye kuskure na

    Bautar sa Bautar Ubangiji ne

    Fushin sa wannan abin gudu ne

    Ka ɓata rai ko na yo kure ne

    Haba masoyi, rashin sani ne..

    Ka ceci raina, ya kai mijina!!!

    Ni ina son masoyiyata

    Son ki ke mulka zuciya ta.

    haƙƙin mallaka @Sadiq Tukur Gwarzo

    Danna nan don karanta Tarihin Garin Rimin Gado

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Hukuncin Tsotsar Al’aura Yake A Likitance

    Yadda Hukuncin Tsotsar Al’aura Yake A Likitance

    A LIKITANCE MEYE HUKUNCIN MAI TSOTSAR FARJI YAYIN SADUWA ??

    • Shin haɗiye maniyyi na da illa ga lafiya?

    • Sannan shafa maniyyin da mata kan yi a fuskar su shin da gaske ne yana maganin ƙuraje da sa kyawun fuska?

    Bismillahir rahamanir rahim. Ko kusa ban nufaci wasa da wannan post ɗin ba, ban kuma yi shi don wata manufa ta daban mara kyau ba. Hasali ma wannan al’amari ne da ke faruwa koyaushe a yanzu, ya zama ruwan dare. Don haka ku biyo ni………..

    Tsotsar farji wannan ɗabi’a ce da mafi yawan ma’aurata da ma wanda ba ma’auratan ba ke yi, suna jin sun fi samun gamsuwa in suka haɗa da hakan a yayin ibadar aure ko ma ga maneman mata waɗanda muke addu’ar Allah ya shirya su su yi aure su daina.

    Dole ne a matsayina na musulma na waiwayi hukuncin hakan a musulunce, wanda kuma a bisa bibiyar jawabai na malamai da tambaya ga masana ilimi Babu Haramci a kan hakan.

    Toh sai dai mu a likitance akwai wani rukuni na wasu abubuwa da muke kallo a matsayin larurorin ɗan Adam na halayya ta fannin (Behavioral medicine) da manyan masana suka fitar da jadawalinsu a matsayin larurorin saduwa da muke kira (Paraphilic Disorder) wanda wani sashin da suka fitar ya shafi wannan.

    Toh amma ba zan iya zayyano su yanzu ba don taƙaita yawan rubutun sai zuwa gobe in Allah ya nufa zan kawo muku larurorin domin idan dame irinsu toh ya sani yana buƙatar ya dena ko kuma in ya gaza to sai ya nemi kulawar likitocin halayya wato Psychiatrists.

    Kai tsaye kamar yadda musulunci bai haramta ba mu ma a likitance ba wani sanannen binkice da na yi karo da shi da ya nuna illa game da hakan ƙarara. Sai dai ma wasu alfanu da masana suka yi ƙoƙarin fitarwa kamar inda suke cewa hakan daidai ne da shan maganin ciwon jiki domin rage raɗaɗin ciwo wato (Anti inflammatory).

    Toh sai dai ba komai muke gudu da irin hakan ba illa kar a yi hakan har sai an tabbatar da lafiyar juna musamman in ba matarka ba ce domin akwai cuttukan da ke biyo maniyyi ko maziyyi kamar ƙwayoyin cutar ƙanjamau, Ciwon hanta, Herpes virus, da sauransu. 

    Idan babu ko ɗaya matarka ce, toh abu na biyu da muke gudu shi ne: Kar mutum ya je yasa ma matar ƙwayoyin infection musamman bacteria da akan samu tattare cikin bakin mu ta sanadiyyar ragowar abincin da mukan ci ya mammaƙale mana a haƙora inda suke biyo miyau su taho…..

    Ko kuma shi ɗin ya sha dattin vaginal bacterial flora ya zo yana fama da ciwon ciki domin wasu matan suna da ƙarancin tsafta. Idan har ya kasance mijin ba mai kula da tsaftar haƙora ba ne koyaushe to lallai zai iya sa mata waɗannan ƙwayoyin infections ɗin na bacteria daga cikin bakin sa.

    Kuma kar jin haka yasa mutum yace yanxu to duk sanda za su yi mu’amullar aure sannan zai dinga brush domin samun damar yin abinda suka saba. A a tun minti 20 zuwa 30 ake so a yi brush saboda maganganun da za ku dinga yi zai sa bacteria ɗin da ka wanke su bi numfashi su fice.

    Haka ko abinci a ƙa’ida ba wai daga kammala brush ya kamata a ci ba. An so kuma sai kamar bayan minti 45 da yin brush sannan za ka ci komai ko yin abinda aka saba saboda haka ga masu wannan lallai suke tabbatar da tsaftar bakunan su kodayaushe sannan su kiyaye hakan.

    Sannan Kuma ga kai ma namijin idan mace ba mai tsaftace gabanta yarda ya kamata ba ne kai ma za ka iya ɗibar ƙwayoyin cututtukan musamman yadda wasu kan haɗiye miyau ɗin yayin wannan artabu, za su iya fuskantar ciwon ciki da sauran ‘yan matsaloli amma dai tabbatar da cikakkiyar tsafta ita ce maganin komai, ake shaving a kan lokaci. 

    Ga masu ganin ƙuraje bayan sun yi shaving to abunda za su dinga yi kafin su yi shaving ɗin da kamar minti 10—zuwa—5 su sami ruwan ɗumi su dinga zama a ciki wajan ya jiƙa su kuma su dinga canza reza duk sanda za su yi a kuma daina sa ƙarfi ana kartar fatar gun, in ana haka ba za a samu ƙuraje bayan shaving.

    MU SANI

    Tsotsar farji still a tsari na cikakkiyar tsafta wannan ba ya ciki saboda in dai mutum na da cikakken ilimin yadda mu’amular auren ya kamata ta kasance to ba sai ma an kai ga irin wannan ba, sai dai da yake kowa da yanayin yadda Allah ya halicce shi da tsarin sa. Amma azzakarin namiji ya fi zamowa abun tsotsa mara matsala 90% fiye da farji, saboda nan depot ce.

    GA BATUN SHAN MANIYYI 

    Ni dai har a safiyar yau na yi binkice na kuma karanta littafai na cutuka da dama ban ga inda aka fidda wani ciwo da hakan ke haddasawa ba. Kamar yadda na faɗa muku sai ma ƙoƙarin bayanin anti inflammatory effect da yake da shi. Don haka in dai an yadda da lafiyar juna babu wani ciwo na hanta ko ƙanjamau da za a iya ɗauka, shi kenan.

    GA BATUN SHAFA MANIYYI A FUSKA

    Har yau dai ba binciken masanan da ya tabbatar da hakan na maganin ƙuraje to amma in ma ya yin ba abun mamaki ba ne duba da irin sinadaren da ya ƙunsa, kuma an ji da yawa matan da suka yi hakan na nuna gamsuwar su 99% kan hakan cewar akwai biyan buƙata.

    SHAWARA DAGA GARENI NA LIKITA

    1) A tabbatar da tsaftar al’aura a kodayaushe ba sai in ana shirin saduwa ba.

    2) Maza a dinga canza boxer a ƙalla sau 4 a sati, mata a dinga canza pant a ƙalla sau 10 ko 14 a sati. Sau biyu kullum.

    3) A matsayinki na mace ki guji matsi tare da cushe-cushen abubuwa a farji da sunan tsuke kai, domin ba fa bola ba ce ke, kina kashe vaginal PH ɗinki.

    4) Aski duka mazan da matan a ƙalla duk kwana 30 zuwa 40.

    5) Rashin tsafta in ya haɗu da infection ko kuna yin wannan ba za ku ji daɗin saduwa ba, don haka ake tsarki da ruwan ɗumi ga duk wanda ya sami dama.

    6) Ga mata ku dena wanke farji da sabulu ku sani farji na wanke kansa da kansa shi yasa wani lokacin za ku ji abu me yauƙi me haske na futowa wannan ba infection ba ne aiki ne na Bowmans Gland… wanke ku ya yi.

    7) A dinga ƙoƙarin gwada wani Pose ɗin kada kullum a ce wannan tsotsen sai an yi shi… in ya yi yawa to fa zai zama da larura kamar yadda a gobe in Allah yaso za ku ji abubuwan da suke larura.

    8) A kuma riƙa motsa jiki.

    Allah yasa mu dace. Ameen.

    Karanta Yadda Danya (Molluscum Contagiosum) Take

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi

    Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi

    1. Muna godiya ga jalla sarki Rahimuna,
    Da ya horace mana halittunsa bai ɗaya.
    2. Ya fifita ɗan Adam bisa dukka talikai,
    Na kogi tudu da masu tashi samaniya.

    3. Salati gurin Muhamman da ya zamo,
    Mai jinƙai da tausayi ga kowa a duniya.
    4. Salamu Alaikumu zumaina ina kuke?
    Batu zan yi kan hali na zulmu ga khalƙiya.
    5. Dabbobi nake nufi da tsuntsaye wanda ke,
    Zaman rayuwa cikinmu yamma da safiya.
    6. Allah ya huwace su gare mu mu mallaka,
    Mu turke mu garkace nau’i ne na dukiya.
    7. Wasunsu kayanmu munka lafta bisa nasu,
    Mai nauyi su kai wuri mai nisa na nahiya.

    8. Wasunsu Allahu ya ce mu ci su ne,
    Mu yanka da sunansa a gyare mu sha miya.
    9. Wasunsu har gonaki mukan sa su ayyuka,
    Na noma da huɗa duk buƙatunmu sun biya.
    10. Wasunsu don sha’awa muke kiwatar su ne,
    Ganin su ke ba mu jin nishaɗi a zuciya.
    11. Wasunsu girman jikinsu ya zarce tambaya,
    Wane namu har wa yau sun fi mu ƙarfin tsiya.
    12. Misali ɗau Raƙumi da Sa har da sha bugu,
    Da doki ya ‘yan uwa mu zam yin tunaniya.

    13. Allah ya hore mana muna sarrafa su duk,
    Ta duk yadda munka so muna masu fariya.
    14. Amanar su Rabbi ya aje gun mu mun shina,
    Domin jin daɗi namu mu bauce shi shi ɗaya.
    15. Abin ban takaici shi ne yadda muke musu,
    Mugunta da cin zali da dukan bulaliya!
    16. Ina mai sakin dabba kiwon Allah ya isa?
    A ran lahira wallahi kai za a tambaya.
    17. Ina mai aje kare da kyanwa wuri nasa,
    Ya kasa ciyar da su sai dai sui ta shan wuya?

    18. Ina mai lafta wa jaki kaya niƙi-niƙi,
    Ya daure yana tafe amma ga dukan tsiya?!
    19. Ina mai barin yara su kamo tsuntsu da ma,
    Sarkin-ƙwai domin wasa da su ba shi tausaya?
    20. Ina masu ragaita da dabba don su sayar,
    Ba ci sai galabaita ga zafi na shamsiya?
    21. Ina masu taskace ta dabba su killace,
    Ba ci ba fita ta nemi nata a rariya?
    22. Ina mai zama ƙoto kare na zaman suɗi,
    Farko ya hana shi ga bugu babu zanbiya?

    23. Ashe ba mu yin tsai mu tuna duk halittuka,
    Na Allah ne mu da su don Allah mu tausaya.
    24. Mu bar zaluntar dabba da tsuntsu da ƙwaruka,
    Allah za ya tambaye mu ranar hisabiya.
    25. Dukkansu rai ne da su jin daɗi suke biɗa,
    Kamar mu da ‘yancin rayuwa har da wataya.
    26. Idan ka aje dabba ka cishe ta kowashe,
    Ruwa mai kyawu ba ta a kwano kwatarniya.
    27. Lallai kar ka cuce ta da duka ko razani,
    Ko kyara da zagi in ka yo su tana jiya.

    28. Idan kai mai kiwo ne yawansu ya kai zuwa,
    Nisabin zakka ka fid da ta banda noƙiya.
    29. Manzo ya hana wahal da dabba a lokacin,
    Yanka ta ka zam wasa wuƙa kar ta sha wuya.
    30. Bayanin na nan a “Arba’una” da mun biya,
    Hadisi na sha bakwai ku duba shi bai ɗaya.
    31. Amma fa ku san kashe kunama halal yake,
    Da ɓera ɓarawon nan Hankaka Macijiya.
    32. Kare mai hauka a kar shi Kura da ma Tsaka,
    A duk inda an gan su kashe su halaliya.

    33. Don Allah mu tausaya wa dabba a kowashe,
    Mu ma sai Allah ya tausaye mu ran tambaya.
    34. Kiwo sai an haƙuri don Allah mu tausasa,
    Ku san babu hankali ga dabba haiwaniya.
    35. Abin duk da ka ciyar da dabba ai sadaka,
    Ake ba ka ladanta mu zam yin rigeniya.
    36. A nan zan tsaya da wagga waƙa ya ‘yan uwa,
    Ya Allah ka yafe mu kurenmu gaba ɗaya.
    37. Sunana Muhammad Nasiru G. ɗan Ahmadu,
    Kano birnin Dabo masu mota da Saniya.
    38. Fa’ulun Mafa’ilun fa’ulun Mafa’ilun,
    Ma’aunin Ɗawilu ke da waƙar da na biya.

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.
    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Haƙƙin Maƙwabci

    Edita@rumasau-kallamu