Tag: sauro

  • Sauro Yana Gani Ne Da Iskar Da Muke Fitarwa (Co2)

    Sauro Yana Gani Ne Da Iskar Da Muke Fitarwa (Co2)

    Kamar yanda ɗan Adam yake son launin kore domin ingantuwar lafiyar ganinsa, shi kuma sauro ya fi son duhu saboda baƙar kala ta fi karɓar yanayin zafi yayin da farar kala take mai da yanayin zafin. Misali: idan ka saka baƙaƙen kaya za ka ji gaba ɗaya jikinka yana gumi yayin da kuma idan ka saka fararen kaya za ka ga ko da rana ta doke ka ba za ka ji gumi sosai ba.

    Tunda sauro yana da na’urar jin zafi nan take yake amfani da wannan damar wajen farmakar mutumin da yake sanye da baƙaƙen kaya, yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa za ka ga sauro yana ta sunturi a saman gashin mutum saboda launin gashin baƙi ne.

    Duk da cewar sauro ba ya amfani da haske wajen ganin abu kamar mutane, amma launi yana taimaka masa bisa la’akari da launin baƙi yana janyo zafin yanayi wanda yake faruwa silar kaɗuwar iska wadda dama da iskar da muke fitarwa ta Carbon dioxide (CO2) yake ganin abu.

    Wani mai ilimin sanin ƙwari (entomologist) da ke jami’ar Florida a Vero Beach da ke ƙasar Amurka yace “Sauro yana dogara da gani ne wajen zaƙulo abin farautarsa, abubuwa masu duhu kamar irinsu: baƙaƙen kaya, blue ko ja kan saka ƙwari saurin gano abu”

    Ganin wannan hikima da Allah Azza wa jallah ya tsarawa wannan halitta ta sauro ne ya sa masu ilimin fasaha (technologist) suka kwaikwaya wajen fitar da na’urar gano abinda ya shamakance idon mutum, misali: ‘yan sanda suna iya gano adadin masu laifi yayin da suka shiga maɓoya ta hanyar amfani da hular kwano mai ɗauke da binoculars mai amfani da hasken ultraviolet light, wannan cigaba ne a tarihin ɗan Adam, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allaah Azza wa jallah wanda ba ya kwaikwayon halitta a matsayinSa na gwanin iya halitta.

    Masana ilimi da suke a jami’ar Alaska ta Amurka sun ce halittar sauro ta zarce sama da shekaru miliyan 226. Amma mu a matsayinmu na musulmai sai dai mu ce “wallahu ta’ala a’alam” 

    Domin karanta adadin idanun sauro danna nan

    Danna nan don karanta cikakken littafin

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Shin Sauro Yana Yaɗa Cutar HIV/AIDS?

    Shin Sauro Yana Yaɗa Cutar HIV/AIDS?

    Mun san da cewar macen sauro tana da saliva wato miyau, sannan tana da allurai har guda 6 waɗanda da su take aikin zuƙar jinin mutum, guda 4 tana amfani da su ne wajen huda fatar mutum yayin da guda 2 ɗin kuma suke ɗauke da wani “pipe” da ake kira da “tube” wanda 1 magudanar miyau ne 1 kuma magudanar da jinin mutum yake bi ne yana komawa jikin sauron wannan ɗaya daga cikin dalilai ne da yasa ba sa iya yaɗa cutar HIV ko da sun ɗauko ta daga mai ƙanjamau ɗin, kamar yanda Professor Wayne Crans da ke jami’ar Rutgers ya sanar da manema labarai

    Dalili na 2 kuma shi ne: ƙwayar cutar HIV ba ta replicating ma’ana yaɗuwa a cikin hanjin sauro ko da ya yi ƙoƙarin yaɗa ta ga wanda ba shi da cutar, nan da nan Allah yake kiyaye bayinSa cutar take breaking down wato nan take take mutuwa. Ga mutane, cutar HIV tana nannaɗewa ne ga T-cells hakan yakan saka ta yaɗuwa amma a cikin sauro kuwa babu T-cells don haka cutar ba za ta iya tsallakawa zuwa miyau ɗin sauro ba.

    Wannan ikon Allah ne kam, domin kuwa ban manta da hadisin nan da ke cikin Sahihul Bukhari ba wanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace “Idan alfasha ta yi yawa a ban ƙasa to sababbin cututtuka da ba ku san su ba za su yawaita”, a nan Allah cikin ikonSa ya kiyaye wasu mutanen daga kamuwa da cutar ƙanjamau ta hanyar cizon sauro wanda suke zuƙowa daga masu ƙanjamau cutar da aka fi samu silar alfasha duk da dai ana samu ta ɓangaren amfani  da reza ko kuma allurar da take ɗauke da jinin mai cutar, wannan duk tsantsar lissafi ne na Allah Azza wajallah wanda dama shi ne “AL-HASIBU” mai lissafa kuma Mai ƙididdige abu. Allahu Akbar !

    A likitance ma ko da a ce sauro zai yaɗa cutar HIV to sai an samu cizon sauraye sama da miliyan 10 kafin a samu guda 1 da zai iya saka cutar, a kintace, masu cutar HIV ba sa ɗauke da unit 10 na cutar. A haɗarance kuma, ko da zaka hadiye sauro ko kuma make shi da hannu hakan ba zai sa ka kamu da cutar HIV ɗin a jikin sauron ba, hakan na nufin sauro ba shi da isasshen jinin mai ƙanjamau da har mutane suke tunanin zai iya yaɗa shi ga mara ƙanjamau ba.

    Suna ƙyanƙyashi ‘ya’yansu ne ta hanyoyi 4

    Na farko haihuwar ƙwayayen (eggs) daga nan kuma cikin ikon Allah da hikimarSa sai ƙwan ya koma abinda ake kira da larva (za su yi kama da caterpillar ko kuma ɗan mitsisin kifi) daga nan kuma sai pupa (kamar tsutsa) sai kuma su zama adult, sai Allah Azza wajallah ya ba su ikon buɗe fika-fikansu sai su fara tashi su zama sauro.

    Namijin sauro yana kai kwanaki 10 kafin ya mutu amma macen takan share kwanaki 42 zuwa 56 kafin mutuwarta. Bambancin adadin kwanakinsu kuwa yana da alaƙa da ɗawainiyar da macen take na ɗaukar nauyin ƙyanƙyashe ƙwayayenta.

    Ko da jininka ko babu Allah Azza wajallah yana ba wa sauro tsawon a ƙalla rayuwar sati 2 zuwa 3, ba wai dole sai da jini suka ta’allaƙa su rayu ba kamar yanda wasu suke tunani ba.

    A kowanne kwana 3 macen sauro take zuba ƙwayayenta akan ruwa, musamman ma ruwan kwata, ba abin mamaki ba ne kenan idan ya zamana sauro ya yawaita a kwatocin unguwanni da mutane marasa tsafta.

    Don karanta littafin sauro halittar Allah mai ban al’ajabi danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Sauro Halittar Allah Mai Ban Al’ajabi

    Sauro Halittar Allah Mai Ban Al’ajabi

    Yayin da ɗan Adam yake da idanu guda 2 domin gani, shin ko ka san da cewar sauro yana da idanu sama da guda 100 masu suna mini eyes kuma kowanne guda 1 a cikinsa shi ma akwai sama da guda 100 da ake kira da lenses, kuma kowanne da irin aikinsa ?

    Dalilin hakan ne yasa ba za ka iya kashe shi farat ɗaya ba ko da kuwan ka biyo ta bayansa. Irin wannan dalilinne yasa aka kwaikwayi idon sauron ta hanyar qirqiro CCTV camera, drones, motoci masu tuqa kansu da kansu da ake kirada self driving cars, dadai sauransu. Allahu Akbar !

    Shin ko kun san da cewar macen sauro ce take cijo ba wai namijin ba ?

    Shi aikin namijin shi ne: ya sadaukar da rayuwarsa ta hanyar jan hankalin mutum domin macen (wato matarsa) ta samu damar zuƙar jinin da za ta samar da isassun ƙwayayen da za ta ƙyanƙyashe ta yanda za a ƙara samun wasu ‘ya’yan sauron, kenan hakan yana nufin ta cikin jininmu suke samun ƙwayayensu, wanda a ƙalla macen sauro tana ƙyanƙyashe ƙwayaye guda 100 zuwa 200 a lokaci ɗaya, Allahu Akbar !

    Allah mai yanda ya so !

    Yayin da ya zamana Allah SWT ya halicce mu da zuciya guda 1, shin ko kun san da cewar sauro yana da zuciya har guda 3 ?

    Akwai left ventricle akwai right ventricle sannan kuma akwai central ventricle kuma cikin ikon Allah, kowacce da irin aikin da take yi a jikin sauron.

    Sauro ita ce halittar da ta fi kowacce halitta yawan kashe ɗan Adam ta hanyar saka masa cutar Malaria, Zika da kuma West Nile. A ƙalla da akwai ire-iren sauraye a duniya sama da 3,500 waɗanda suke satar jinin dabbobi kama daga mijizai, kifaye da kuma mutane domin su samar da ƙwayayensu.

    Sauro na iya ganin mutum a cikin mosquito net ba tare da wani shamaki na bango ba, a maimakon mu da muke amfani da haske domin gani, shi kuma sauro yana amfani da iskar Carbon dioxide ne wadda yakan iya shaƙar numfashinka daga nisan ƙafa 150, hakan ke ba su damar gano blood group ɗinka, wanda in dai bai yi daidai da nasu ba, ba za su sha jinin ba, Allahu Akbar !

    To ya akai muka san wannan ilimin ?

    Allah cikin ikonSa ya ba wa Professor Jeffery Riffel (Malamin Biology a Jami’ar Washington ta Amurka) ikon gano ɗabi’un sauro da kuma yanda sauron yake tunani. Lokacin da ya buɗe ƙoƙon kan sauron wanda ake kira da cuticle ya ga ƙwaƙwalwar sauron, kamar yanda ya zanatawa manema labarai. Sun gano hakan ne bayan shafe shekaru sama da 12 shi da abokan aikinsa (team).

    Shin ko kun san sauro yana kaɗa fika-fikansa sau 1000 a cikin second 1?

    Yayin da macen sauro take sokawa fatar mutum allurai 6 da suke a bakinta, a lokacin ne namijin sauro yake jan hankalin mutum don aikin macen ya kammala ba tare da mutum ya farga ba. Duk da cewar ma kafin ka ji zafin cizon sai an ɗauki ‘yan sakwanni saboda allurar sedative da take tsirawa fata domin kashe zafin cizon, yayin da aikin ya kammala ita kuma ta riga ta bar fatar a lokacin ne zafin cizon zai fara tasiri akan fatar mutum, yayin da ka kai duka kuma tuni ta daɗe da tsotsar adadin jinin da take buƙata. Allahu Akbar !

    Wannan duk ba abin mamaki ba ne domin kuwa idan muka koma cikin littafin Allah SWT, Al-Qur’ani mai girma to zamu tabbatarda cewar ikon Allah ya wuce duk yanda ‘yar ƙaramar ƙwaƙwalwarmu take tunani. Allah SWT yace a cikin Suratul Baqara ayata 26 “Innallaha layastahyi anydriba, masalamma ba’udatan fama fauƙaha” ma’ana “Lalle ne, Allah ba ya jin kunyar ya buga misali kowanne iri ne, SAURO, da binda yake bisa gare shi”. To a nan tunda ka ji misalin sauro ya fito a cikin Qurani kai ka san yana da abubuwan al’ajabi kam.

    Wannan kaɗan daga cikin bayani ne akan halittar sauro, ɗaya daga cikin ziliyoyin halittun Allah SWT, duk Allah ya ba wa masu ilimin kimiyya wannan damar ne domin su gane ayoyinsa da suke sararin sama’uddunya da kuma kan duniyarmu ta Ard da muke rayuwa

    Muna roƙon Allah ya ƙara mana imani da kuma jin tsoronsa, ya tabbatar da mu akan bin sunnar ma’aiki ya raba mu da bidi’a ya nesanta mu daga azabar wuta sannan kuma ya saka mu a AljannarSa don RahamarSa ba don halinmu ba.

    Domin karanta cikakken littafin danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu