Tag: maza

  • Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Akwai jita-jitar cewa an kammala gwaji ko kuma ana kan hanya wajen samar da allurar hana haihuwa ga maza. Wannan gaskiya ne cewa ana gudanar da bincike, amma har yanzu babu wata allura da aka amince da ita a duniya domin yin tazarar haihuwa ga maza.

    Wasu daga cikin alluran da aka fi duba yiwuwar yin amfani da su, sun haɗa da:

    1. Reversible Inhibition of Sperm Under Guidance (RISUG) a Indiya, wacce ta ƙunshi ɗura ruwan magani mai maiƙo a cikin bututun ajiyar maniyyi (injecting gel into vas deferens). Amma har yanzu wannan dabarar ba ta samu amincewa daga hukumomin lafiya na duniya ba.

    2. Allurar sinadarin testosterone da progestin wacce take hana samar da ruwa da ‘ya’yan maniyyi. A shekarar 2016, wani bincike na hukumar kula da lafiya ta duniya (World Health Organization – WHO) ya dakatar da yin wannan gwajin saboda zai haifar illolin da suka haɗa da fushi, baƙin ciki, taɓin hankali, da matsalar ƙarancin sha’awa ga maza, illolin da suka fi na alluran tazarar haihuwa na mata muni.

    MATAKAN SAMAR DA MAGANI (STAGES OF DRUG DEVELOPMENT)

    Domin fahimtar dalilin da yasa ba a samu nasarar fitar da alluran tazarar haihuwa na maza ba, ya kamata a fahimci matakai guda shida waɗanda ake bi kafin a ƙirƙiro magani har ya fita kasuwa:

    1. Gwajin yin amfani da maganin a cikin ɗakin gwaje-gwajen kimiyya da dabba (discovery and preclinical lab testing using guinea pigs) – Ana yin sa ne don a fahimci ingancinsa da yadda yake aiki, amma a jikin dabba.

    2. Gwaji a mataki na farko (Phase I Trials) – A jikin mutane kaɗan, wato marasa yawa, don tabbatar da ingancinsa a kan lafiyar mutanen.

    3. Gwaji a mataki na biyu (Phase II Trials) – Ana yin gwajin ne ga mutane masu buƙata don a duba inganci da illolinsa a jikinsu.

    4. Gwaji a mataki na uku (Phase III Trials) – Gwaji mai faɗi ta hanyar ƙara yawan jama’ar da za a yi gwajin a kansu don tantance amfanin maganin da illolinsa a jikinsu.

    5. Amincewa daga hukumomin lafiya (Regulatory review and approval) – Hukumomi, kamar NAFDAC a Nigeria ko FDA a America, za su bayar da sanarwar amincewa da maganin a hukumance, domin mutane su cigaba da yin amfani da shi.

    6. Bibiya bayan an fara amfani da maganin (Post marketing surveillance) – Don cigaba da sa ido a kan illolinsa.

    Yawancin alluran tazarar haihuwa na maza da ake ƙoƙarin ƙirƙirowa suna kasa samun nasarar gwajin ne tun a mataki na biyu ko na uku saboda mummunan sakamakon da suke nunawa ga lafiyar maza, ko rashin daidaiton sakamakon (inconsistent test results).

    DALILIN DA YASA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA NA MATA SUKA FI DACEWA DA JIKIN MATAN (REASONS THAT FEMALE INJECTABLE.CONTRACEPTIVES REMAIN MORE SUITABLE)

    1. Jikin mace ya fi sauƙin sarrafa sinadaran estrogen da progesterone, saboda tsarin al’ada na halittar jikin mace yana aiki da sinadaran estrogen da progesterone ɗin ne, wanda ake iya kwaikwayon su cikin sauƙi da magunguna. Allurar tazarar haihuwa ta mata tana hana mace yin ovulation cikin sauƙi da aminci, kuma illolinta sun daɗe ana yin nazari a kansu, kuma ana iya sarrafa su.

    2. A jikin namiji kuwa, ana samar da miliyoyin ‘ya’yan maniyyi a kullum, waɗanda in har za a yi amfani da allurai na tazarar haihuwa domin rage yawansu, to, hakan yana nufin sai dai a dakatar da samar da su gaba ɗaya, wannan abu ne mai wahala da hatsari.

    ILLOLIN DA ZA SU IYA BIYO BAYAN AMFANI DA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA GA NAMIJI (POTENTIAL REGRETS AND CONSEQUENCES OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Idan aka gaggauta yin amfani da su ba tare da yin cikakken bincike ba, to, ana iya fuskantar matsaloli kamar:

    1. Matsalar rashin haihuwa ta dindindin (permanent infertility) – Saboda hana samar da ‘ya’yan maniyyi na dogon lokaci yana iya lalata ƙwayar haihuwa har abada.

    2. Taɓarɓarewar hankali da rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (mood disorders and hormonal imbalances) – Hakan yana iya haddasa damuwa, fushi da cututtukan zuciya.

    3. Ƙarin hatsari ga dangantakar aure – Mace tana iya ɗaukan cewa an ɗauki matakin hana haihuwa alhali namiji yana fama da illoli ko ya manta. Daga nan sai ciki ya samu ba tare da an shirya masa ba.

    Wani bincike da aka wallafa a “The Journal of Clinical Endocrinology & Metabolism” ya nuna cewa yin amfani da sinadaran testosterone da progestin yana iya aikin samar da tazarar haihuwa ga maza, amma yana haddasa hawan jini, lalacewar hanta, da hauhawar kitse (cholesterol).

    SHAWARA GA YAN’UWANA MATA

    Ya kamata mu kasance cikin shiri da fahimta. Duk da cewa alhakin yin tazarar haihuwa ya rataya ga maza suma, yana da muhimmanci mu san cewa jikin mace ne yafi dacewa da irin waɗannan magunguna, tunda an ɗauki dogon lokaci ana yin nazarin su kuma an riga an tabbatar da ingancinsu.

    Idan aka gaggauta yin amfani da alluran tazarar haihuwa na maza ba tare da cikakken bincike da tabbatar da ingancinsu ba, to, duniya za ta yi nadama kamar yadda aka yi da wasu magunguna a tarihi.

    Har zuwa lokacin da aka samu cikakken gwaji da tabbatar da ingancinsu, alluran tazarar haihuwa na mata su ne mafi aminci da sahihanci.

    Danna nan don karanta Rashin Kawowar Mace A Lokacin Jima’i (ANORGASMIA)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Amfani Da Kuma Illar Magungunan Ƙara Ƙarfin Maza (MALE SEX ENHANCEMENT SUPPLEMENTS)

    Amfani Da Kuma Illar Magungunan Ƙara Ƙarfin Maza (MALE SEX ENHANCEMENT SUPPLEMENTS)

    Tabbas saduwar aure a tsakanin namiji da mace tana da matuƙar muhimmanci a zamantakewar aure. Duk da kasancewar ba ita kaɗai ba ce ta ke samar da morewar zaman aure. Saduwa ita ce a kan gaba.

    Wannan yana nufin cewa ko da mace tana da ladabi da biyayya, iya magana, iya girki, iya kwarkwasa, iya kwalliya, tsabta da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkan su ba su kai muhimmancin saduwa ba a wurin mijinta.

    Haka nan kuma, ko da namiji yana da ƙoƙarin samar wa matarsa da abinci da abin sha, sutura, wurin zama, kiwon lafiya, tsare mutunci, tausayawa, kyautatawa da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkansu ba su kai muhimmancin saduwa ba a wurin matarsa. Bisa wannan dalilin ne maza su ke jajircewa wajen ganin cewa sun gamsar da matansu ta fuskar jima’i.

    ABIN DA AKE NUFI DA GAMSAR DA JUNA WAJEN SADUWAR AURE (SEXUAL SATISFACTION)

    Masana a fannin lafiya (medical health), da na addinin Musulunci (Islamic clerics), da na halayyar ɗan-adam (psychologists) sun kai sun komo ga me da ma’anar gamsar da juna a wurin saduwar aure. Amma duk bayanansu sun tattara ne a kan cewa ma’anarsa ita ce, “A samu natsuwar da za ta gusar da duk wata sha’awa bayan an gama saduwar, sai kuma wani lokaci idan buƙatar hakan ta taso”.

    Da wannan ne wasu da yawa daga cikin mazajenmu su ke ɗaukar cewa mutum ba zai iya gamsar da iyalinsa ba sai:

    1. Idan yana da al’aura mai kauri, ko tsawo, ko kuma duka biyun.
    2. Idan yana daɗewa wajen saduwa.

    Hakan ne ya bai wa wasu kamfanoni masu sarrafa magungunan Bature, da kuma masu maganin gargajiya damar samar da magunguna iri-iri waɗanda aka ce suna bai wa namiji ƙarfin gamsar da iyalinsa yadda ya kamata. Abin ya yi yawa sosai, ta yadda masu waɗannan magunguna suka cika chemists, da kasuwanni, tituna, da tashoshin mota suna cin karensu babu babbaka.

    RABE-RABEN MAGUNGUNAN BATURE NA ƘARA KARFIN NAMIJI

    Magungunan sun kasu kamar haka:

    1. Kwayoyi (drugs): waɗannan su ne magungunan da ake sha da baki, kuma suna da yawa. Sun haɗa da Viagra, VigRX Nitric Oxide , TestRX, GenF20 Plus, Semenax, ProSolution Plus, VigRX Plus, Extenze, da sauransu.
    2. Mayuka (creams): waɗannan su ne magungunan da ake shafawa. Su ma suna da yawa, kamar Maxman Delay Sex Cream, Viamax Maximum Gel, TITAN Gel, Doc Johnson Power Plus Delay Cream, Man1 Oil Penile Health Cream, Lavenda Massage Oil, da sauransu.
    3. Allura (injection): waɗannan su ne magungunan da ake yin allura da su. Su ma suna da yawa, kamar Papaverine, Prostaglandin E1 (PGE1), Phentolamine, Alprostadil, Trimix, da sauransu.
    4. Tiyata (surgery): wannan ita ce aikin yanka mazakuta da ake yi a ɗakin tiyata domin a ƙara mata tsawo ko kauri (penile augmentation surgery) ta hanyar sanya wata roba mai kama da jijiyoyin mazakuta (medical grade silicone). An fi yinta a ƙasashen Turawa, kuma tana da tsada sosai.
    5. Jiƙe-jiƙen magungunan gargajiya (herbal concoctions): wannan shi ne ya fi yawa a cikin al’umarmu. Su ma akwai na sha akwai kuma na shafawa. Masu ilmin kimiyya ba su cika yarda da tsabtar waɗannan magungunan ba, haka kuma ba su yarda da sahihancin ƙa’idar amfani da su ba (dosage).

    TASIRIN MAGUNGUNAN ƘARA ƘARFIN NAMIJI

    Masu amfani da waɗannan magunguna suna ganin tasirinsu. Hakan ba ya rasa nasaba da abubuwan da ake haɗa su da shi, kamar ginkgo biloba, ginseng, DHEA, horny goat weed, fenugreek, maca da sauransu. Wasu chemicals ne wasu kuma ana tatso su ne daga tsirrai, sa’annan suna sanya ƙaruwar zubar sinadarai (hormones) a cikin jiki ne. Amma a gaskiya sakamakon binciken kimiyya da yawa ya tabbatar da cewa daɗewa ana amfani da su yana haifar da illa ga lafiyar mutum. Bayan wannan kuma, idan jikin mutum ya saba da su, to, zai yi wahala ya iya saduwa da matarsa in bai yi amfani da su ba. Assha! Ka ga kenan matsala ta auku.

    SIRRIN GAMSAR DA MACE WAJEN SADUWAR AURE

    Alqur’ani mai girma ya gama mana komai, domin ya sanar da mu yadda za a gamsar da mata wurin saduwa:

    نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا لِأَنْفُسِكُمْ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ مُلَاقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ

    “Matanku gonakinku ne, ku shiga gonakinku ta yadda ku ke buƙata, kuma ku yi wasanni da su (a lokacin da za ku sadu da su)”, Baqarah: 223.

    Kenan idan mutum ya yi wasanin motsa sha’awa sosai kafin ya fara saduwa da iyalinsa, to, insha-Allahu zai gamsar da ita. Wasu suna yin kuskuren fahimtar cewa daɗewa ana saduwa shi ne kwazo da burgewa. A likitance wannan ba gaskiya ba ne, domin ana so ne saduwa ta zama daga minti 3 zuwa 17. Idan ta kai minti 20, to, ta yi yawa domin za ta iya sanya ni’imar matar ta ɗauke, daga nan sai ta fara jin zafi, ƙila ma a yi mata rauni. Amma a lura ba wai ina nufin dole kada a wuce abinda na faɗa ba ne, domin wani yana iya yin minti 60 ma ba tare da matar ta tsawwala ba.

    MENE NE ABIN YI?

    1. Matsalar ƙanƙancewar gaba gaskiya ce. Idan mutum yana da ita, to, ya kamata ya tuntuɓi likita, domin a ɗora shi a kan maganin da ya dace, maimakon saye da kuma amfani da magunguna barkatai, waɗanda idan illarsu ta taso, bai san yadda zai magance ta ba.
    2. Idan ba ya zama dole ba, kada ka saba ma madam da daɗewa ana saduwa, domin idan ka daina daɗewa daga baya, to, akwai matsala fa.
    3. Ka ƙarfafa wasanni kafin ka fara, kamar yadda Alƙur’ani ya yi umarni.

    WalLahu A’lam

    Domin karanta yadda ake gyara soyayya ko Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki ko yadda ake wa maigida lokacin al’ada