Tag: Maganin Tashin Zuciya

  • Tashin Zuciya (Nausea)

    Tashin Zuciya (Nausea)

     Jin rashin gamsuwa da zaƙuwa wajen jin alamar mutum kamar zai yi amai.

    Dalilan Da Ke Kawo Tashin Zuciya

    Za a iya samun tashin zuciya a sakamakon wata cuta ko wani yanayi da jikin ɗan Adam ka iya samu (conditions)

    Motion Sickness: Yanayi da ka iya haifar da cutar a sakamakon tafiya a abin hawa.

     Misali

    • Tashin zuciya (Nausea)
    • Rashin samun balance
    • Amai (Vomiting)

    Concussion: Samun rauni a ƙwaƙwalwa sakamakon duka ko naushi (blow) a kai ko girgiza kai ba bisa ƙa’ida ba

    Misali

    •    Tashin zuciya (Nausea)
    • Amai (Vomiting)
    • Akan iya rasa human memory

    Alcohol Abuse: Yanayin ko salon shaye-shaye ba bisa ƙa’ida ba.

    Misali

    • Tashin zuciya (Nausea)
    • Amai (Vomiting)
    • Craving ko physical defence

    Morning sickness: Inda aka fi raja’a da kuma ba da sunan tashin zuciya kacokan shi ne zargin ko samun juna biyu.

    Halaiyar Mu Da Ke Kawo Mana Tashin Zuciya
    • Shan magunguna na ƙwaya daban-daban ba tare da an ci abinci ba.
    • Yawan cin abinci a cika ciki tab.
    • Ƙarancin cin abinci a zauna da yunwa.
    • Yawan ƙwanƙwaɗar barasa ko shaye-shaye.
    • Tsintar kai a yanayin tafiya a jirgi ko mota.
    Hanyoyin Kare Kai Daga Tashin Zuciya
    • Samar da wadatarciyyar iska a abin hawa jirgi ko mota.
    • Cin abinci akan lokaci ko ƙa’ida ba tare da ci kaɗan ba ko cikawa.
    • Rage cin abinci me maiƙo yayin karyawa zuwa ɗagawar rana.
    • A yawaita karyawa da (dry food) busashen abinci kamar biscuit cabin.
    • Kada a zura hannu a baki don kakaro mai.
    • Samun hutawa da wadataccen bacci sannan a guji cin abinci me ɓata ciki.
    • Kai ziyara asibiti dan bambance me ke kawo tashin zuciya, da ɗora mutum a kan hanyar da ta dace na shawarwari ko magani.

    Domin karanta Illolin Shan Ampiclox Ba Bisa Ƙa’ida Ba Danna nan

    Edita; RMK