Tag: mace

  • Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana wata mata mai juna biyu ta je ɗibar ruwa a bakin rafi. Bayan ta cika tulunta da ruwa, sai ta kasa ɗauka saboda cikinta ya girma sai nishi take yi, abin tausayi. Kuma ga shi ita kaɗai ce ƙwal a wurin.

    Haka ta haƙura ta zauna. Can sai ga wani mutum ya taho, sai ta dube shi ta ce: “Malam don girman Allah ka ɗora ni mana.” Sai yace shi ba zai ɗora ta ba sai dai idan za ta yi masa wani alkawari. Mai ciki ta dube shi ta ce: “Na mene ne?” Shi ko ya kaɗa baki yace: “Idan kin haihu, in namiji ne to abokina ne, idan kuma mace ce, to matar ɗana ce.

    ” Da jin wannan sharaɗi sai ta yarda. Ya ɗauki tulu ya ɗora mata ta kama hanya ta tafi gida. Da ta je gida sai ta yi wa mijinta bayanin yadda suka yi da mutumin. Da yake mijinta mai sauƙin kai ne, sai ya ce: “To shi ke nan, Allah ya sauke ki lafiya.

    ”Bayan ’yan kwanaki sai mutumin ya zagayo gidan matar, suka gaisa. Ya nuna mata ɗansa suka yi sallama ya koma gida. Bayan wata ɗaya sai matar ta haifi ’ya mace, amma jikinta na jaki ne. Da mutumin ya ga haka sai ya yi halin dattaku ya ce: “To shi kenan tun da an yi alƙawari ai sai an cika.

    ”Sai ya kira ɗansa aka ɗaura musu aure da yarinyar ya kai ta gidansu. Yaro ya zauna da mace mai jikin jaki, ya ɗaure ta a gida. Amma duk sanda ya tafi gona idan ya dawo gida sai ya tarar an yi masa shara, an dafa masa abinci an kuma kai masa ruwan wanka bayan ɗaki.

    Kullum haka, sai abin ya fara ba shi tsoro tun da ba kowa a gidan. Rannan sai ya je ya sami babansa ya gaya masa, amma sai baban ya ƙi kula shi sai ya kore shi. To da ma yaron yana mutunci da wata tsohuwa maƙwabciyarsa dangarsu ɗaya. Sai wata rana ya zauna a gindin bishiya, yana tunanin abin mamakin da ke samunsa.

    Da tsohuwar ta gan shi a zaune haka, sai ta kira shi ta ce: “Ɗanyaro me ke damunka ne?” Shi ko sai ya kwashe labari ya bai wa wannan tsohuwa. To da ma ashe tsohuwa tana ganin duk abin da yarinya take yi idan ya tafi gona. Watau rikiɗa take yi ta koma kyakkyawar budurwa, ta shiga yi masa waƙa, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, ta dafa abinci, ta ɗebo ruwa a rijiya ta kai masa banɗaki.

    Duk bayanta gama kafin ya dawo sai ta mayar da jikinta na jaka, ta ɗaure kanta a turke.
    Da tsohuwa ta gama bai wa yaron labarin abin da take gani sai ta shawarce shi da cewa gobe ya kwashi kayan aiki kamar zai tafi gona, idan ya kama hanya sai ya ratse a hanya, ya zagayo gidanta.

    Bayan sun gama shirya zancensu, sai ya koma gida yana mamaki, ya shiga ɗaki ya kwanta. Da gari ya waye sai ya saka kayan aiki ya ɗauki fartanyarsa ya kama hanyar gona. Bayan ya tafi ya yi nisa sai ya ratse cikin ciyawa, ya zagayo ta gidan tsohuwa, ya same ta a ɗaki.

    Daga nan sai suka ɓuya suka shiga leƙen yarinyar. Jim kaɗan sai suka ga ta rikiɗa ta koma kyakkyawar mace, ta fara waƙa ta kama shara da sauran ayyukan gida, ta shirya miya, ta dafa abinci, ta zuba nasa, ta kai masa ruwan wanka banɗaki. A daidai lokacin da ta fito daga bayan gida sai mijinta ya tsallaka danga ya dira a gabanta.

    Sai kawai ta razana za ta rikiɗa sai ya kama hannunta ya fara yi mata waƙa yana roƙon ta. Da ta ji waƙarsa sai ta fara kuka tana roƙon ya yafe mata. Shi kenan suka yi zamansu cikin daɗi suka ci gaba da more rayuwarsu cikin ƙauna da farin ciki. Dan kan ɓarya, ba domin Gizo ba da na sheƙa muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Alkawari kaya ne, in an sauke sai a huta.
    • Tsintar dami a kala.
    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Warin Gaban Mace Da Yake Nuna Matsala

    Warin Gaban Mace Da Yake Nuna Matsala

    1. Idan mace ta rinƙa jin gaban ta yana ɗoyin warin kifi, to wannan yana nuni da ƙananun ƙwayoyin halittar bacteria masu haɗari sun rinjayi masu amfanin dake gaban mace. Ƙarin alamu sun haɗa da fitar farin ruwa, jin zafi wajen yin fitsari da kuma ƙaiƙayi saman gaban mace. Awani ɓangaren kuma idan mace tana jin warin kifi ga gaban ta haɗe da fitar tsanwa ko ɗorowan ruwa jin zafin fitsari da kuma ƙaiƙayi to wannan yana nuna alamaun trochomoniasis cutar da ake ɗauka ta hanyar saduwa.

    2. Idan kuma mace najin wari a gabanta kamar ana gasa bread wanda ya ƙone haɗe da fitar wani abu ta gaba kamar dussa-dussar cukui da matsanancin ƙaiƙayi a cikin matunci da wajen matunci to wannan alamu ne da ke nuna akwai (YEAST INFECTION)

    3. Idan mace tana jin mugun ɗoyi wanda ke haɗe da zazzaɓi ,matsanancin ciwon mara da kuma jin zafi yayin saduwa to wannan alamu ne da ke nuni da mace na da PID.

    4. In wari kamar warin cukui wanda ba kasafai ake samun shi ba. Shi wannan yana da nasaba da kamar macen da ke da yeast infection ta haɗu da irin sinadaran da ake shafawa ga gaba kafin saduwa ko macen da ke trichomoniasis a saka condom wajen saduwa da ita.

    WARIN GABAN MACE DA ZAI IYA ZAMA BA MATSALA BA

    1. Wari kamar na ruɓaɓɓen abinci ga gaban mace in dai ba wasu alamun ƙaiƙayin , wari ƙarni ko ƙuraje Gaba, ko kumburin gaba, to wani lokaci ba matsala ba ne. Wannan yana da nasaba da macen da take barin panties ga jikin su na tsawon wuni lokaci ba a canza ba. Hakan na da nasaba da haɗuwar kamar tsohon jini, ƙwayoyin bacteria da aka halitta ga gaban mace don wani amfani da kuma cakuɗuwar su da ruwan da ke fita ga gaban mace ga panties ɗin ta.

    2. Jin wari kamar na man bleaching lokacin saduwa na da nasaba da abinda aka yi amfani da shi don taushi ga gaban mace lokacin saduwa ko kuma hanyar kariya kamar amfani da condom.

    3. Jin wari kamar na muski yana da nasaba da idan mace ta yi wani aiki mai yawa sai gabanta ya fitar da zufa mai wari kamar na muski.

    4. Jin wari kamar na wani abu mai zaƙi yana da nasaba da abubuwan da mace ke ci ko sha. Idan abubuwan da mace ke ci sun shafi ababe masu zaƙi to za ta rinƙa jin shi ga gabanta sakamakon zufar jiki. Shi yasa wasu matan ke yawan shan abarba da sauran fruits.

    Don karanta Zinariyar Awa Ga Jariranmu danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tusar Gaban Mace(Queening Vaginal Gas)

    Tusar Gaban Mace(Queening Vaginal Gas)

    Tusar gaban mace:

    Itace fitar da wani iska musamman lokocin jima’i da mijinta, ko idan tayi wani motsin sai taji gabanta yana fitar da wani iska harda kara kamar tusa.

    Dalilan Da Suke Kawo Wannan Tusar Gaban Sun Hada Da:
    1. Pelvic floor weakness: Sakewar naman cikin farji, idan naman cikin farjin mace ya saki baya iya rike abu yakan kawo wannan matsala.
    2. Infection: Shigar kwayar cuta bangaren da ya shafi  mafitsara shima yakan haifar da wannan matsala.
    3. Feminine hygiene products: chuse-chusen kayan mata, da wasu sabulai marasa asali domin sarƙake farji ko matse shi yakan haifar da wannan matsalar.
    4. Inserting an object in the vagina: tura wani abun da ba muhallin sa ba zuwa cikin farji yakan kawo wannan matsalar.
    5. Menopause: Wasu matan suna fuskantar wannan matsalar idan lokocin dauke jinin al’adar su yayi, shekaru arba’in da biyar zuwa sama.
    6. Vaginal Fistulas: Wannan idan akan samu tazara ko wata ƙofar tsakanin hanyoyin da ta hada farji, mafitsara da wajen kashi akan samu wannan matsalar.
    Sai Kuma Wasu Hallayar Mu Da Take Taimaka Wajen Kawo Wannan Matsalar:
    • Zama a kasa cikin AC ba wando kuma a kan tiles.
    • Yawo ba takalmi musammanma a AC kuma kan tiles.
    • Ƙwanciya ki kunna fanka kuma ba wando a jikinki.
    • Rashin yin tsarki da ruwan zafi.
    • Rashin yin tsarki bayan gama jima’i. Wato barin sparm ya kwana a jikinki ba tare da yin tsarki ba.
    • Yawan yin maganin mata ba gaira ba dalili.
    • Rashin iya positioning na kwanciyar aure da miji.
    • Zama da fant guda daya tun daga safe har dare sai kaga mace ta bar fant tun safe har dare yana jikinta tsaban qazanta.

    Sannan yana dakyau mace ko namiji ya karanta bayanin mu akan Cututtuka Da Ake Dauka Ta Jima’i

    Hanyoyin Samun Sauki Ko Waraka:
    • Ayi ƙoƙori zuwa asibity domin ganin likita wanda ya ƙware a bangaren abinda ya shafi mahaifa (Gynaecologist)
    • A kiyaye dukkanin abinda zai kawo wannan ji matsalar.
    • Adinga yin exercise lokoci bayan lokoci domin naman farji ya samu ƙarfi.

    Domin karanta Ciwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure) Danna nan

  • Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

    Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

    PID: wata cuta ce wacce ta ke addabar ɓangaren da ta shafi mahaifar mace, mutane da dama a Nahiyan Afirka suna fama da wannan ciwon.

    Wasu ƙwayoyin cututtuka né, idan sun samu sun shiga mahaifar mace (uterus, fallopian Tubs, ovaries ) sai su haifar da Cutan PID.

    Daga cikin alomaminta akwai:


    1- Ciwon ƙasan cibi (ciwon mara).
    2- fitar da ruwa mai wari a gaban mace.
    3- Ganin jini a gaban mace musamman lokacin jima’i da bayan jima’i.
    4- Zafi lokacin jima’i.
    5- Zazzaɓi da jin sanyi.
    6- Zafi lokacin fitsari ko wahalar fitsari.
    7- Ƙaiƙayin gaba.
    8- Rashin daidaitawar jinin haila.
    9- Tashin zuciya
    10- Ciwo lokacin jima’i
    11- Ciwon baya.

    Hanyoyin da ake ɗaukar wannan ciwon sun haɗa da:


    1- Jima’i da namiji mai ɗauke da cutar gonorrhea ko clymadia.
    2- Amfani da kayan karɓar haihuwa waɗanda ba su da tsafta.
    3- Yawan kai ɗan yatsa cikin farji.
    4- Amfani ni da wando (fant) wanda mai ɗauke da wannan cutar ta yi amfani da shi.
    5- Rashin amfani da condom lokacin jima’i.
    6- Yawan tsaftace gaba da sabulu musamman masu ɗauke da sinadaran kashe ƙwayoyin cuta.
    7- Yawan amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta irin su: Ampiclox da muka dabi’untu da shan su kullum.

    PID idan ba a magance shi da wuri ba, yana sabbaba waɗannan matsalolin kamar haka:


    1-Rashin haihuwa
    2-Zaman ciki wajen mahaifa(entopic pregnancy).
    3-Yakan kawo ɓari (abotion ko Miscarriage)
    4-Ciwon mara da baya mara jin magani.

    Hanyoyin kariya daga waɗannan cututtuka sun haɗa da:


    1- Amfani da Condom lokacin jima’i, yana rage yaɗuwar PID kashi 95%.
    2- Mace ta tsaya a kan namiji guda ɗaya, kuma a tabbata an yi gwaji kafin saduwa ko sun yi aure.
    3- A kiyaye yawan saka hannu a farji.
    4- A tsaftace wandon sakawa musamman pant, kuma a kiyaye amfani da pant na wata.
    5- A dinga tsaftace kayan karɓar haihuwa da kuma wanke ciki.

    Wannan ciwo na PID yana da magani idan aka bi hanyoyi masu kyau:

    1- Da Zarar mace ta ga alamun da muka lissafa a sama, ta gaggauta zuwa asibiti

    Daga nan likita zai yi gwaje-gwajen da ya kamata a yi, an tabbatar an gano matsalar, sannan a bada magani.

    2- Idan kina da miji shi ma, ya kamata ya je a gwada shi; a ba ku magani tare.

    3- Daga nan sai a ƙaurecewa jima’i sai likita ya tabbatar muku kun warke.

    GARGAƊI

    Idan mace tana tare da wannan cutar kuma ta yi shiru ta zauna saboda kunya ko makamancin haka, yakan jawo mata matsala a mahaifarta, daga nan za ta fara somawa da matsalar zubar da ciki (miscarriage) zaman ciki wajen mahaifa (Ectopic pregnancy) ko kuma rashin ɗaukar ciki gabaki ɗaya. karanta yadda jinin Haila yake ko Yadda ake gwajin juna biyu

    Lafiya Uwar Jiki.