Tag: Awo

  • Abubuwan Da Ke Sa Mace Ta Riƙa Jin Alamun  Juna Biyu

    Abubuwan Da Ke Sa Mace Ta Riƙa Jin Alamun  Juna Biyu

    Haƙiƙa mata da yawa suna ƙorafi akan jin alamun juna biyu amma idan sun yi awo ko gwaji sakamakon ya nuna babu cikin. Abubuwa masu yawa suna iya haifar da wannan yanayin. Amma bisa nazarin da na yi, muhimman abubuwan da suke kawo shi su ne:

    1. Dalili na farko shi ne hasashen samun juna biyu wanda ake kira “phantom pregnancy” ko kuma “pseudocyesis”. Shi yanayi ne wanda yake sanya mace ta riƙa ji ko ganin dukkan alamomin samuwar juna biyu, kamar rashin zuwan jinin al’ada a lokacin da ya saba zuwa mata (missed period), ko zazzaɓin safe (morning sickness), ko ciwon nono (breast tenderness), ko tashin zuciya (nausea), ko yawan gajiya (fatigue), ko motsi irin na jariri a ciki (fetal-like movement), da sauransu.

     Duk da waɗannan alamomin, idan mace ta yi awon ciki sakamakon zai nuna cewa babu cikin. Babban abinda yake haddasa shi shi ne tsananin kwaɗayi da zaƙuwar samun juna biyu. Ma’ana, idan mace ta ƙosa ta samu juna biyu, to, ƙosawar za ta sanya jikinta ya fara zubo da sinadarai daban-daban irin waɗanda suke zuba a jikin mai juna biyu, daga nan sai dukkan alamun juna biyun su tabbata a gareta.

    1. Dalili na biyu shi ne idan halittun jikin mace masu alaƙa da haihuwa (reproductive organs) suka kamu da rashin lafiya, to, za ta riƙa jin alamun juna biyu. Misali, idan tana da matsalolin mahaifa (uterine disorders), ko rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (hormonal imbalance), ko matsalolin nono (breast disorders), ko matsalolin jakunkunan ruwan sinadarai (hormonal gland disorders), da sauransu.
    1. Dalili na uku shi ne juna biyun sinadarai (chemical pregnancy). Wannan yana faruwa ne idan mace ta yi ɓarin ƙaramin ciki (early pregnancy miscarriage). To, mai yiwuwa ne ta riƙa jin alamun juna biyu bayan ta yi ɓarin, domin jikinta ya fara samar da ruwan sinadarin human chorionic gonadotropin (hCG). Tasirin sinadarin zai ci gaba da haifar mata da alamun juna biyu bayan ta yi ɓarin, sai a hankali zai daina.
    1. Dalili na huɗu shi ne samuwar cikin bayan mahaifa (ectopic pregnancy). Idan ƙyanƙyasasshen ƙwan haihuwa ya maƙale a jikin bututun fallopian tube, maimakon a cikin mahaifa, to, mace za ta riƙa jin alamun juna biyu, amma ko da ta yi awon ciki sakamakon zai nuna cewa babu cikin, saboda yawan sinadarin hCG da jikinta yake samarwa ba shi da yawan da zai nuna cewa akwai cikin.
    1. Dalili na biyar shi ne yawan amfani da magungunan gargajiya da na bature ba bisa ka’ida ba. Yin hakan zai rikirkita jikin mace, har ta riƙa jin alamun juna biyu alhalin kuma ba ta da shi, domin ko an yi awon ciki sakamakon zai nuna cewa babu.

    A taƙaice, idan mace tana ji ko ganin alamun juna biyu amma awon ciki ya nuna babu, to, a binciki waɗannan abubuwan da na lissafa a sama.

    Waɗannan ƙari ne akan abubuwan da ‘yan-uwa suka faɗa na amfani da magungunan tazarar haihuwa, molar pregnancy, da sauransu. Allah SWT ya kawo ciki da goyo mai amfani, amin.

    Domin Karanata Amfanin Aya Wajen Samar Da Lafiya A Jiki danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

       

  • Awon Juna Biyu

    Awon Juna Biyu

    Awon ciki shi ne gwaji wanda ake yi a lokacin da mace take jin alamu a jikinta kamar ta sami juna biyu. Sakamakon awon shi ne yake tabbatar da gaskiya ko akasin abinda take hasashe. Idan sakamakon ya nuna tabbaci (positive), to, shikenan juna biyu ya tabbata. Idan kuma ya nuna rashin tabbaci (negative), to, juna biyu bai tabbata ba.

    RABE-RABEN AWON JUNA BIYU 

    Awon juna biyu ya rabu zuwa manyan gidaje guda biyu:

    1. Na fitsari (urine test)
    1. Na jini (blood test)

    Amma bayan waɗannan gwaje-gwajen, ana yin wasu, sai dai su ba na tattabatar da shigar juna biyu ba ne, a a na bibiyar halin da juna biyun yake ciki ne bayan an tabbatar da shi. Waɗannan sun haɗa da gwajin hoto na ciki (ultrasound scan) da kuma na jini kamar rhesus factor domin gane ko akwai protein a ƙwayoyin jinin mace, chorionic villus sampling (CVS) da amniocentesis domin gane ko jariri yana da nakasa, glucose test domin gane yiwuwar ciwon sugar, group B streptococcus test domin gane ko uwa tana ɗauke da ƙwayoyin cutar da zata iya sanya ma jaririnta a lokacin haihuwa, da sauransu.

    AWON JUNA BIYU NA FITSARI

    Ana amfani ne da wani tsinke wanda ake kira “strip”, kuma akwai shi na kamfanoni da yawa kamar First Response Early Result, Clinical Guard GCH Pregnancy Test Strip, Clear Blue Rapid Detection, Early@Home Pregnancy Test Strip, Wondfo Pregnancy Test Strip, da sauransu.

    A jikin tsinken akwai sinadarai da ake kira “immunochemical reagents” masu tantance ko akwai sinadaran human chorionic gonadotropin (hCG) a cikin fitsarin. Jikin mace zai fara samar da sinadarin hCG a cikin jininta da zarar ’ya’yan maniyyin namiji (sperm cells) sun ƙyanƙyashe ƙwan haihuwarta (ovum) kuma ƙwanƙyasasshen ƙwan ya maƙale a cikin mahaifa. Don haka idan aka tsoma tsinken strip a fitsarinta zai canza launi, ko ya nuna layi biyu, ko ya nuna alamar tarawa (+).

    Domin samun kyakkyawan sakamako, ana buƙatar a yi amfani da fitsarin farko na safe. Sa’annan kada a sha ruwa da yawa domin fitsarin ya yi kauri (concentrated). Idan akwai hCG a fitsarin, to, zai nuna sakamako cikin minti 5 zuwa 10, ya danganta da kamfanin da ya yi tsinken. Kuma an fi buƙatar yin test ɗin kwana 7 zuwa 14 da gama al’ada. Idan kuma tsinken bai canza ba, to, babu juna biyu kenan.

    Abubuwan da suke sanya a yi awon fitsari kuma a rasa ganin sakamako mai kyau duk da mace tana jin alamun ciki sun haɗa da lalacewar tsinken strip ɗin (expired strip), rashin isasshen fitsari a lokacin da aka yi test ɗin, ko fitsarin da ya haɗu da ruwa (diluted urine). Yawancin mata sun fi son awon juna biyu na fitsari saboda sauƙin kuɗinsa da kuma rashin ɗaukar lokaci kafin a ga sakamako.

    AWON JUNA BIYU NA JINI

    Ana yin sa ne a ɗakin bincike na kimiyya (laboratory). Shi ma abinda ake dubawa a cikin jinin shi ne sinadarin hCG. Wannan awon ya fi tabbas saboda komi ƙanƙantar sinadarin ana iya ganinsa.

    SHIN SAKAMAKON AWON FITSARI DA NA JINI ZA SU IYA NUNA ƘARYA?

    Allah (SwT) da Manzonsa (SAW) su kaɗai ne ba su kuskure. Don haka mai yiwuwa ne shi ma sakamakon awon juna biyu ya nuna kuskure. Amma kashi 99 bisa ɗari (99%) na awon juna biyu, fitsari ko jini, suna ba da sakamako daidai. Sai dai idan an yi kuskure wajen yinsu, ko kuma wanda ya yi bai fahimci yadda ake yi ba. 

    SHAWARA

    Idan kina shakkun  sakamakon awon fitsari, to, a sake yi bayan wani lokaci, haka kuma idan na jini ne, ko kuma a canza wurin awon. Allah yasa mu gama haife-haife lafiya, Allah ya ba mu zuriyya ɗayyiba, amin. 

    Danna nan don karanta yanda ake amfani da na’urar gwajin ciki (juna biyu)

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu