Tag: Allura

  • Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Akwai jita-jitar cewa an kammala gwaji ko kuma ana kan hanya wajen samar da allurar hana haihuwa ga maza. Wannan gaskiya ne cewa ana gudanar da bincike, amma har yanzu babu wata allura da aka amince da ita a duniya domin yin tazarar haihuwa ga maza.

    Wasu daga cikin alluran da aka fi duba yiwuwar yin amfani da su, sun haɗa da:

    1. Reversible Inhibition of Sperm Under Guidance (RISUG) a Indiya, wacce ta ƙunshi ɗura ruwan magani mai maiƙo a cikin bututun ajiyar maniyyi (injecting gel into vas deferens). Amma har yanzu wannan dabarar ba ta samu amincewa daga hukumomin lafiya na duniya ba.

    2. Allurar sinadarin testosterone da progestin wacce take hana samar da ruwa da ‘ya’yan maniyyi. A shekarar 2016, wani bincike na hukumar kula da lafiya ta duniya (World Health Organization – WHO) ya dakatar da yin wannan gwajin saboda zai haifar illolin da suka haɗa da fushi, baƙin ciki, taɓin hankali, da matsalar ƙarancin sha’awa ga maza, illolin da suka fi na alluran tazarar haihuwa na mata muni.

    MATAKAN SAMAR DA MAGANI (STAGES OF DRUG DEVELOPMENT)

    Domin fahimtar dalilin da yasa ba a samu nasarar fitar da alluran tazarar haihuwa na maza ba, ya kamata a fahimci matakai guda shida waɗanda ake bi kafin a ƙirƙiro magani har ya fita kasuwa:

    1. Gwajin yin amfani da maganin a cikin ɗakin gwaje-gwajen kimiyya da dabba (discovery and preclinical lab testing using guinea pigs) – Ana yin sa ne don a fahimci ingancinsa da yadda yake aiki, amma a jikin dabba.

    2. Gwaji a mataki na farko (Phase I Trials) – A jikin mutane kaɗan, wato marasa yawa, don tabbatar da ingancinsa a kan lafiyar mutanen.

    3. Gwaji a mataki na biyu (Phase II Trials) – Ana yin gwajin ne ga mutane masu buƙata don a duba inganci da illolinsa a jikinsu.

    4. Gwaji a mataki na uku (Phase III Trials) – Gwaji mai faɗi ta hanyar ƙara yawan jama’ar da za a yi gwajin a kansu don tantance amfanin maganin da illolinsa a jikinsu.

    5. Amincewa daga hukumomin lafiya (Regulatory review and approval) – Hukumomi, kamar NAFDAC a Nigeria ko FDA a America, za su bayar da sanarwar amincewa da maganin a hukumance, domin mutane su cigaba da yin amfani da shi.

    6. Bibiya bayan an fara amfani da maganin (Post marketing surveillance) – Don cigaba da sa ido a kan illolinsa.

    Yawancin alluran tazarar haihuwa na maza da ake ƙoƙarin ƙirƙirowa suna kasa samun nasarar gwajin ne tun a mataki na biyu ko na uku saboda mummunan sakamakon da suke nunawa ga lafiyar maza, ko rashin daidaiton sakamakon (inconsistent test results).

    DALILIN DA YASA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA NA MATA SUKA FI DACEWA DA JIKIN MATAN (REASONS THAT FEMALE INJECTABLE.CONTRACEPTIVES REMAIN MORE SUITABLE)

    1. Jikin mace ya fi sauƙin sarrafa sinadaran estrogen da progesterone, saboda tsarin al’ada na halittar jikin mace yana aiki da sinadaran estrogen da progesterone ɗin ne, wanda ake iya kwaikwayon su cikin sauƙi da magunguna. Allurar tazarar haihuwa ta mata tana hana mace yin ovulation cikin sauƙi da aminci, kuma illolinta sun daɗe ana yin nazari a kansu, kuma ana iya sarrafa su.

    2. A jikin namiji kuwa, ana samar da miliyoyin ‘ya’yan maniyyi a kullum, waɗanda in har za a yi amfani da allurai na tazarar haihuwa domin rage yawansu, to, hakan yana nufin sai dai a dakatar da samar da su gaba ɗaya, wannan abu ne mai wahala da hatsari.

    ILLOLIN DA ZA SU IYA BIYO BAYAN AMFANI DA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA GA NAMIJI (POTENTIAL REGRETS AND CONSEQUENCES OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Idan aka gaggauta yin amfani da su ba tare da yin cikakken bincike ba, to, ana iya fuskantar matsaloli kamar:

    1. Matsalar rashin haihuwa ta dindindin (permanent infertility) – Saboda hana samar da ‘ya’yan maniyyi na dogon lokaci yana iya lalata ƙwayar haihuwa har abada.

    2. Taɓarɓarewar hankali da rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (mood disorders and hormonal imbalances) – Hakan yana iya haddasa damuwa, fushi da cututtukan zuciya.

    3. Ƙarin hatsari ga dangantakar aure – Mace tana iya ɗaukan cewa an ɗauki matakin hana haihuwa alhali namiji yana fama da illoli ko ya manta. Daga nan sai ciki ya samu ba tare da an shirya masa ba.

    Wani bincike da aka wallafa a “The Journal of Clinical Endocrinology & Metabolism” ya nuna cewa yin amfani da sinadaran testosterone da progestin yana iya aikin samar da tazarar haihuwa ga maza, amma yana haddasa hawan jini, lalacewar hanta, da hauhawar kitse (cholesterol).

    SHAWARA GA YAN’UWANA MATA

    Ya kamata mu kasance cikin shiri da fahimta. Duk da cewa alhakin yin tazarar haihuwa ya rataya ga maza suma, yana da muhimmanci mu san cewa jikin mace ne yafi dacewa da irin waɗannan magunguna, tunda an ɗauki dogon lokaci ana yin nazarin su kuma an riga an tabbatar da ingancinsu.

    Idan aka gaggauta yin amfani da alluran tazarar haihuwa na maza ba tare da cikakken bincike da tabbatar da ingancinsu ba, to, duniya za ta yi nadama kamar yadda aka yi da wasu magunguna a tarihi.

    Har zuwa lokacin da aka samu cikakken gwaji da tabbatar da ingancinsu, alluran tazarar haihuwa na mata su ne mafi aminci da sahihanci.

    Danna nan don karanta Rashin Kawowar Mace A Lokacin Jima’i (ANORGASMIA)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Allurar Da Ake Yi A Jijiya Da Allurar Da Ake Yi A Tsoka (INTRAVENOUS AND INTRAMUSCULAR INJECTION)

    Allurar Da Ake Yi A Jijiya Da Allurar Da Ake Yi A Tsoka (INTRAVENOUS AND INTRAMUSCULAR INJECTION)

    A likitance, yin allura shi ne a ɗurawa maras lafiya ruwan magani a jikinsa. Ana yin allura ne ta hanyar amfani da tsinken allura mai siririn rami a tsakiyarsa tare da tsini a ƙarshensa, wanda ake kira “hypodermic needle”. Ita kuma kwalbar da ke ɗauke da ruwan maganin ana kiranta “”vial”, ko ”phial”, ko “flacon”. Shi kuwa zungurun roba mai ɗauke da ruwan maganin da ake zuƙowa, ana kiransa “syringe”.

    Akwai nau’ukan tsinken allura masu yawa waɗanda ake yin amfani da su a asibiti. Sun rabu zuwa mayan rabe-rabe kamar haka:

    1. Tsinken allurar da ake tsirawa a cikin tsoka (intramuscular hypodermic needle): Ana amfani da shi ne domin ɗura ruwan magani a cikin tsokar jikin mutum. Girmansa (gauge) yakan kama daga 20g zuwa 29g. Tsawonsa (length) yakan kama daga 13mm zuwa 16mm.

    2. Tsinken allurar da ake tsirawa a tsakanin shimfiɗar fata da fata (intradermal hypodermic needle): Ana amfani da shi ne domin ɗura ruwan magani a shimfiɗar fatar jiki ta sama (epidermis) da shimfidar fatar jiki ta kusa da tsoka (dermis). An fi yin amfani da shi wajen auna bijirewar fata (skin allergies). Girmanta (gauge) yakan kama daga 25g zuwa 30g. Tsawonsa (length) yakan kama daga 8mm zuwa 13mm.

    3. Tsinken allurar da ake tsirawa a tsakanin shimfiɗar kitse da fata (subcutaneous hypodermic needle): Ana amfani da shi ne domin ɗura ruwan magani a tsakanin fatar jiki da tsoka. An fi amfani da shi a allurar ciwon sugar (diabetes). Girmansa (gauge) yakan kama daga 25g zuwa 30g. Tsawonsa (length) yakan kama daga 4mm zuwa 8mm.

    4. Tsinken allurar da ake tsirawa ta jijiyar jini (intravenous hypodermic needle): Ana amfani da shi ne domin ɗura ruwan magani kai-tsaye a cikin jijiyar jini. Girmansa (gauge) yakan kama daga 20g zuwa 25g. Tsawonsa (length) yakan kama daga 4mm zuwa 6mm.

    Sa’annan akwai nau’ukan zungurun ruwan allura (syringe) masu yawa waɗanda ake yin amfani da su a asibiti. Sun rabu zuwa mayan rabe-rabe kamar haka:

    1. Zungurun ruwan allurar da ake tsirawa a cikin tsoka (intramuscular syringe): Ana amfani da shi ne domin ɗura ruwan magani a cikin tsokar jikin mutum. Girmansa (gauge) yakan kama daga 21g zuwa 22g. Tsawonsa (length) yakan kama daga 1 inch zuwa 1.5 inches.

    2. Zungurun ruwan allurar tsoka (IM syringe): An fi yin amfani da shi wajen allurar riga-kafi (vaccines). Girmansa (gauge) yakan kama daga 21g zuwa 23g. Tsawonsa (length) yakan kama daga 1 inch zuwa 1.5 inches.

    3. Zungurun ruwan allurar da ake tsirawa a tsakanin shimfidar kitse da fata (subcutaneous syringe): Ana amfani da da shi a allurar ciwon sugar (diabetes). Girmansa (gauge) yakan kama daga 25g zuwa 27g. Tsawonsa (length) yakan kama daga 5 inches zuwa 8 inches.
    Likita yana yanke shawarar zaɓen irin allurar da za a yi wa maras lafita ne bisa la’akari da abubuwa masu yawa, kamar yanayin maganin, nau’in rashin lafiyar, halin da maras lafiyan yake ciki, shekarun maras lafiya, sauri ko rashin saurin da ake buƙata wajen tasirin maganin, da sauransu.

    YIN ALLURA A JIJIYAR JINI (INTRAVENOUS INJECTION)

    Allurar jijiyar jini, wacce ake taƙaita sunanta da IV, ana yin ta ne idan likita ya ga akwai buƙatar samun tasirin maganin cikin gaugawa (immediate response to medication). Don haka, idan aka yi allurar IV, to, an kaucewa dogon lokacin fara aikin allurar. Ma’ana, za ta shiga cikin jini kai-tsaye ta fara aiki. Idan za a yi wa mutum ƙarin jini (blood transfusion) ko ƙarin ruwa (rehydration theraphy), to, a jijiya ake sanya allurar. Yawanci allurar jijiya ana yin ta a hannu ne.

    Matsaloli (complications) da ake samu idan aka yi kuskuren allurar IV su ne; kumburin jijiya (phlebitis), shigar maganin cikin tsoka (infiltration), toshewar jijiya (embolism). Kura-kuran IV da ke kawo waɗannan abubuwan su ne tsira allurar ba daidai ba (wrong angle needle insertion), rashin tsabtace wurin allurar (non-sterilization of injection site), yin amfani da tsohuwar allura (use of dirty needle), ɗura ruwan magani fiye da kima (medication overdose), amfani da ruwan maganin da bai dace ba (wrong use of medication), da sauransu.

    YIN ALLURA A CIKIN TSOKA (INTRAVENOUS INJECTION)

    Allurar tsoka, wacce ake taƙaita sunanta da IM, ana yin ta ne idan likita ya ga babu buƙatar samun tasirin maganin cikin gaugawa (non-immediate response to medication). Ma’ana, ana buƙatar maganin ya je cikin hanta kafin ya dawon cikin jini, kuma ya riƙa yin aiki kaɗan-kaɗan na dogon lokaci. An fi yin alluar IM wajen riga-kafi (vaccines), ko kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics), ko kashe raɗaɗi (pain relief).

    Idan za a yi allurar IM, ana tsira allurar ne a tsaye ba tare da karkacewa ba (90-degree angle), sa’annan a ɗura ruwan maganin a cikin tsoka. Matsaloli (complications) da ake samu idan aka yi kuskuren allurar IM su ne, kamuwa da ƙwayoyin cuta (infection), jin zafi (pain), zubar jini (bleeding), taruwar gunya (abscess), da sauransu. Kurakuran IM da ke kawo wadannan abubuwan sune dura ruwan magani da sauri (injection at once), taɓo ƙashi (hitting a bone), taɓo jijiya (hitting a vein), rashin tsabtace wurin allurar (non-sterilization of injection site).

    RUWAN MAGANIN ALLURAR JIJIYA (MEDICATIONS FOR IV INJECTION)

    Ruwan maganin allurar jijiya suna da yawa. Kaɗan daga cikinsu su ne:

    a. Maganin ƙarin ruwan jiki, kamar normal saline, lactated Ringer’s solution, da dextrose solutions.

    b. Maganin ciwon cancer (chemotherapy drugs).

    c. Maganin kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics), kamar penicillin, cephalosporins, fluoroquinolones, da vancomycin.

    d. Ƙarin jini (blood transfusions), kamar packed red blood cells, platelet concentrates, da fresh frozen plasma.

    e. Maganin ciwon zuciya (heart disease), kamar nitroglycerin, beta-blockers, da anti-arrhythmics.

    RUWAN MAGANIN ALLURAR TSOKA (MEDICATIONS FOR IM INJECTION)

    Ruwan maganin allurar jijiya suna da yawa. Kaɗan daga cikinsu su ne:

    a. Maganin riga-kafin mura (influenza vaccine), kamar afluria quadrivalent, flulaval quadravalent, da fluzone intradermal quadrivalent.
    b. Maganin riga-kafin tetanus (tetanus vaccine), kamar tetanus toxoid vaccine ko tetanus immunoglobulin.

    c. Maganin kashe raɗaɗi (pain relievers), kamar morphine, fentanyl, non-steroidal anti-inflammatory drugs (NSAIDs), da corticosteroids.

    d. Maganin kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics), kamar penicillin, cephalosporins, da aminoglycosides.

    e. Maganin ƙara jini (transfusions), kamar vitamin B-12 shots, Iron supplements ko erythropoietin-stimulating agents (ESA).

    Daga ƙarshe, ya kamata mu fahimci cewa na rubuta wannan maƙalar ne domin wayar da kan masu neman sanin makamar aikin allura, ba za a fahimci ainihin yadda al’amuran allura suke ba, sai an je makaranta, kuma an lizimci yin nazarin littattfan pharmacology. Allah ya taimaka, amin.

    Danna nan don karanta Magance Laulayin Da Magungunan Tazarar Haihuwa Suke Haddasawa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Post Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura}

    Post Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura}

    Abubuwan Suke Sa Hakan

    • Babban abinda yake kawo hakan shine fata ko Kuma garkuwar jikin mutum saboda bakon yanayi data tsinci kanta aciki dalilin karfen allurar kokuma ruwan allurar musamman allurar rigakafi wato vaccines. 
    • Wasu kuma allergic reaction ne yasa hakan 
    • Wasu kuma rashin bin ka’idar allura yayin gabatar da ita ga ma aikacin lafiya da kuma marah lafiya misali (wasu matan sai suce a musu a zaninsu) ga ma’aikaci kuma rashin gwarewa wajen jan allurar hakan zai jawo bakin allurar a baci, da dai sauransu
    Alamomin Sun Haɗa Da
    • Zafi in an taba gun 
    • Kumburi agun (swelling)
    • Kaikayin wajen allurar
    • Zafi (pain) 
    • Wajen zai yi ja (redness) 
    • kuraje 
    Abunda  Mutum Zaiyi Wajan Yadaina Ciwo Sune Kamar Haka

    Mutane dayawa hakan yana warkewane batare da sunsha komai ba dakanshi yake tafiya amma in yakai kwana biyu 

    Karanta Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether

    • Mutum yanemi kankara yasa agun na tsawon mintina 10 zuwa 15
    • In kuma yana zafi sosai sai a sha maganin rage radadi 
    • Amfani da lidocaine skin cream
    Abu Na Ƙarshe Kuma Sshine Inhar Alamomin Suka Hada Da :
    • Taruwar jini a wajen allurar
    • Matsanaicin zafin wajen allurar 
    • Matsainaicin ƙaiƙayi

    Ko kuma ya kai kimanin sati daya  sai mutum ya garzaya asibiti mafi kusa domin tantancewa dakuma daukar mataki so inaga bawani abun ɗa ga hankali bane in anbarshi ma insha Allah within 2day’s zai warke da kanshi  

    Domin karanta amsar wannan tambayar Ina Bada Nono Amma Baya Isar Jaririna, Ko Kuwa Ba Maiƙo Danna nan 

  • Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether

    Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether

    1) Ba’a ba yarda allurar nan ga mace mai cikin da bai wuce wata 3 ba.

    (2) Ba’a ba yarda allurar nan hade da Erythromycin lokaci daya.

    (3) Duk wanda bai da isashshen jini ajiki ba zai yi anfani da Artemether ba.

    (4) Shin ko kasan ba’a ba yarda Allurar Artemether ga mata masu shayarwa da sunan magance uncomplicated malaria bincike ya nuna matukar ana so sai anyi anfani da ita to dole a tsayar da bayar da nono din.

    (5) Maganin daya kunshi Artemether an samoshi ne daga wani ganyen itaciya mai suna shrub artemesia annua.

    Domin karanta bayani a kan malaria in pregnancy ko zubar jinin haila sosai fiye da ƙima wato “Rushing” [heavy bleeding] ko dalilin da ina bada nono amma baya isar jaririna, ko kuwa ba maiƙo danna wannan koren rubutun 

    Domin karanta bayani akan Noristerat (Norist) Danna nan 

  • Noristerat (Norist)

    Noristerat (Norist)

    (Allurar tazarar haihuwa ce wacce take dauke da sinadarin progesterone kadai kuma tana zuwa da nauyin milligrams dari biyu (200mg))

    Wannan alurar ana yinta ko wacce bayan sati takwas (8weeks) domin tazarar haihuwa (ba hana haihuwa ba) musamman ga wadanda ke da kananan shekaru masu buƙatar allurar tazarar haihuwa kamar me haihuwa 2 ko 3 wadda acikin magungunan tazarar haihuwa norist tanada saukin sha’ani kuma bata bada matsala idan aka bi dakokinta.

    Da zarar ranar da aka daina amfani da allurar norist ana kyeutata zato mace zata iya samun juna biyu.

    Wannan allurar idan aka fara amfani da ita tana zuwa da wasu canji ga wasu matan ba dukka ba kamar yadda ko wacce magani tana da nata side effects din.

    Domin karanta bayani akan Vaginal Infection Danna nan 

    Daga cikin canji da ake samu akwai:
    • Rikicewar al’ada 
    • Rashin ganin al’ada
    • Ganin gudaje gudaje lokocin al’ada.
    • Ciwon Kai
    • Tashin zuciya
    • Kara jiki
    • Hajijiya
    Masu wannan matsalar baikamata sufara amfani da allurar norist ba
    • Ciwon daji na mama
    • Mace mai juna biyu
    • Masu hawan jini
    • Masu wankan jego
    • Masu matsalar zubar da jini.

    Kamar yadda mukai magana a baya idan aka ga wadannan alamomin lokocin amfani da maganin planning ayi gaggawar zuwa asibiti:

    •  Ciwon kai mai tsanani
    •  Gani dishi dishi 
    •  Rashin ji sosai
    •  Ido yazama yellow
    •  Kaikayin jiki
    •  Kumburin kafafuwa
    •  Daukewar numfashi
    Abinda ma’aurata yakamata su sani shine:

    Ga kadan daga cikin amfanin daukan matakin tazarar haihuwa da zaran an haihu:

    • Yana hana mata samun cikin da ba’a shirye shi ba har tsawon wata shida bayan haihuwa
    • Yana hana samun ciki idan har an sami wadan nan abubuwa uku da aka fada a sama
    • Bashi da illa
    • Hanya ce mai sauki bata buƙatar magani.
    • Yana samar da lokaci ga ma’aurata wajen zaben wata hanyar idan har wannan bata yi aiki ba.

    Domin karanta bayani akan Ƙurjin Farji Danna nan