Tag: addini

  • Nazari A Kan Tasirin Watsi Da Littattafan Hadisi A Cikin Addini Da Al’umma

    Nazari A Kan Tasirin Watsi Da Littattafan Hadisi A Cikin Addini Da Al’umma

    Gabatarwa

    A zamanin nan, wani sabon rikicin addini ya taso a wasu sassan Arewancin Najeriya game da asalin Aƙida da kuma tushen ilimin addini. Wasu mutane waɗanda ba su da zurfin ilimi a fannin ʿUlūm al-Ḥadith (ilimin hadisi) ko ʿUlum al-Din (ilimin addini) — suna kiran Musulmi da cewa su dogara da Alƙur’ani kaɗai, su watsar da Hadisi saboda suna ganin wasu hadisai “sun taɓa mutuncin Annabi ﷺ.

    ” Wannan ra’ayi, duk da cewa yana iya kama da tsoron Allah a zahiri, yana da matuƙar hatsari ta fuskar aƙida, ɗabi’a, da zamantakewa. Addinin Musulunci ya ginu ne a kan Alƙur’ani da Sunnah, waɗanda ba za a iya raba su ba. Watsi da Hadisi yana lalata asalin Musulunci kuma zai haifar da ruɗani da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.

    Alƙur’ani kansa ya umarci Musulmai da su bi Annabi ﷺ: ‘Kuma abin da Manzon Allah ya ba ku ku karɓa, abin da kuma ya hana ku ku guje masa.’ (Surat al-Ḥashr 59:7). Wannan aya ta tabbatar da cewa Sunnah ita ce tushe na shari’a da imani bayan Alƙur’ani. Annabi ﷺ ya ce: ‘An ba ni Alƙur’ani da wani abu makamancin sa tare da shi.’ (Sunan Abu Dawud, 4604). Wanda ya ƙi Hadisi, tamkar ya ƙi wani ɓangare na wahayi ne, yana kuma rushe tsarin Shari’a, ɗabi’a, da aƙida gaba ɗaya.

    A tarihi, ƙungiyoyin da ke ƙin Hadisi (Qur’aniyyah) sun taɓa fitowa a lokuta daban-daban. Dalilansu yawanci jahilci ne game da hanyoyin binciken hadisi, ko tasirin ra’ayoyin Turawa masu son lalata Musulunci. A yankin Arewacin Najeriya, wannan aƙida tana samun gindin zama musamman a wajen masu jahilci, ko masu son farin jini a idon jama’a. Suna ɗauka cewa ƙin Hadisi na kare mutuncin Annabi ﷺ, alhali kuwa hakan yana goge tarihin koyarwarsa da kyawawan halayensa.

    Mummunan Tasiri da Illolin Ra’ayin Watsi da Hadisi

    1.1 Lalata Imani da Shari’a — Ba tare da Hadisi ba, ba za a iya fahimtar Musulunci daidai ba. Hanyoyin Sallah, Zakka, Azumi, da Hajji duk daga Hadisi ake koyonsu. Rashin bin Hadisi yana kaiwa ga lalacewar ibada da rushewar addini.

    1.2 Rage Darajar Annabi ﷺ — Wanda ya ƙi Hadisi yana rage matsayin Annabi ﷺ a matsayin Manzo. Wannan yana saɓawa kalmar Allah da ta ce: ‘Bai yi magana daga son zuciyarsa ba, abin da yake furtawa wahayi ne da aka yi masa.’ (Surat an-Najm 53:3–4). Saboda haka, ƙin Hadisi yana nufin shakku cikin wahayi, wanda yana iya kai wa ga kufr al-juhūd.

    1.3 Rarrabuwar Kawuna da Ƙungiyoyi — Idan aka watsar da Hadisi, kowa zai fassara Alƙur’ani yadda ransa yake so. Wannan zai haifar da rarrabuwar ra’ayi da ƙungiyoyi masu saɓa wa juna. (Surat al-An‘ām 6:159)

    1.4 Raguwar Hankali da Ɗabi’a — Hadisi na ƙunshe da koyarwar ɗabi’a da halayen Annabi ﷺ. Idan aka watsar da shi, al’umma za ta rasa shugabancin ɗabi’a, za a samu ruɗani da raunin ruhi.

    1.5 Wulaƙanta Malaman Addini — Wa’azin irin wannan yana sa mutane su raina manyan malamai kamar Imam al-Bukhari, Muslim, da Ahmad ibn Hanbal. Wannan yana haifar da girman kai da rashin girmama ilimi.

    1.6 Tasirin Ra’ayoyin Yammacin Duniya — Yawancin masu ƙin Hadisi a yau suna bin hujjojin Turawa masu son cire Musulunci daga ikon Annabi ﷺ.

    A yankin Arewacin Najeriya, irin wannan ra’ayi yana jawo: ruɗani ga matasa; rashin haɗin kai a al’umma; rage girmamawa ga malamai; lalacewar tsarin karatun addini; da kuma rikicewar shugabanci.

    Gargadin Annabi ﷺ

    Annabi ﷺ ya yi gargaɗi da cewa: ‘Wani lokaci zai zo inda mutum zai zauna a kan gadonsa yana cewa: “Mu bi Alƙur’ani kaɗai; abin da muka samu halal a cikinsa, za mu ɗauka halal; abin da muka samu haram, za mu ɗauka haram.

    ” Lallai abin da Manzon Allah ya hana, kamar abin da Allah Ya hana ne.’ (Sunan Abu Dawud, 4604). Wannan Hadisi yana bayanin halin da ake ciki a yau kuma yana nuna cewa wannan tunani alama ce ta karkacewa daga hanyar gaskiya.

    Watsi da Hadisi ba ƙaramin kuskure ba ne hatsari ne ga asalin Musulunci. Yana rushe ginshiƙin Shari’a, yana wulaƙanta ikon Annabi ﷺ, kuma yana buɗe ƙofa ga ruɗani, sekularizm, da rarrabuwar kai.

    Don haka wajibi ne a ƙarfafa ilimi da fahimta mai kyau game da Hadisi, gina girmamawa ga malamai, da yin da’wah mai ilmantarwa don gyara wannan kuskuren. Wanda ya watsar da Hadisi, ya watsar da Annabi ﷺ. Alƙur’ani saƙo ne daga Allah, Sunnah kuma ita ce aikace-aikacen sa. Addinin Musulunci ba zai rayu sai da biyunsu tare.

    Rubutu da nazari: Huzaifa Mukhtar Muhammad

    Dalibin ilimi

    Karanta Manufar Rayuwar Duniya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addinin Mutanen Ƙasar Hausa

    Addinin Mutanen Ƙasar Hausa

    Hanyar bauta wa wani abu wanda mutum yake tsammanin shi ne zai biya masa bukatun rayuwar yau da kullum shi ne addini. Addinin farko na mutanen ƙasar Hausa shi ne addinin gargajiya, wato tsafi ta hanyar bautar iskoki ko mutanen ɓoye da kuma bori da camfi.

    Irin wannan addini ya faru ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka ƙaga wa kansu ta bautar waɗansu abubuwa don cimma biyan buƙatunsu na rayuwa. Wannan hanyar bauta ta daɗe ƙwarai a dukkan sassan duniya ba ƙasar Hausa kawai ba. Mutanen da suka fara zama a duniya ne suka ƙirƙiro ta, daga nan sai abin ya zama al’ada ga sauran ƙabilun da suke biye da su har ya zo ga Hausawa.

    A sakamakon shigowar addini Musulunci cikin ƙasar Hausa da kuma karɓar sa da mafi yawancin Hausawa suka yi, irin wannan addini ya sami rauni. Amma duk da haka ba a bar yin wasu abubuwa waɗanda suka danganci addinin gargajiya na Hausawa ba. Don kuwa za a ga yana yin tasiri a kan wasu al’amuran da suka shafi rayuwar wasu Hausawa ta yau da kullum.

    Idan muka waiwaya muka duba yadda al’ummar Hausawa suka gudanar da addininsu na gargajiya, za mu ga ba wai suna sassaƙa wani gunki ne suna bauta masa ba, a a, suna yin bautarsu ne ta hanyar yin tsafi. Bauta ta hanyar tsafi tana nufin bauta wa wani iska da aka ɗauka yana zaune a wani wuri na daban. Ire-iren wuraren da aka ɗauka iskoki suna zama sun haɗa da wata kwankwamar dutsi ko cikin wata sarƙaƙƙiya ko wurin wata tsohuwar bishiya, irinsu kuka da tsamiya da marke da dai sauransu.

    Misali, a Kano an bauta wa iska Tsumburbura wanda aka ɗauka ya zauna a Dutsen Dala, Kainafara-Arnan Birchi suna bauta wa iska Ɗantalle wanda suka ce yana zaune a cikin Dutsin Birchi. Arnan Kwatarkwashi kuma suna bauta wa Ƙunƙurutu wanda suka ɗauka yana cikin Dutsin Kwatarkwashi, arnan Sauna kuma suna bautar Magiro.

    Haka kuma a duwatsun Kufena ta Zariya mazaunan farko a wannan wuri sun ɗauka akwai wasu iskoki da suke zaune a wannan wuri. Saboda suna biya masu buƙatunsu shi ya sa suke bauta masu. A ƙasar Katsina ma akwai wasu arna da suke bautar Magiro a Safana da Ɗan-musa da Ƙanƙara da Dutsin-ma wanda suka ce yana zama a wurin tsamiya mai sarƙaƙƙiya da duhu, kuma ba mai iya zuwa wurin da yake sai masu yi masa hidima

    Bayan addinin gargajiya sai addinin Musulunci wanda addini ne da Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko ta hannun Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) don ya zama hanyar shiriya ga al’ummomin duniya, ya kuma zama hanya madaidaiciya a gare su. Wannan kuwa ya faru ne a cikin shekara ta 610 Miladiyya.

    Addinin Musulunci ne ya biyo bayan addinin Kirista wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko ta hannun Annabi Isa, Allah ya ƙara yarda da shi. An sami shekaru ɗari shida a tsakanin waɗannan addinai (Ibrahim, 1982:63 da Gusau, 2005:18-19). Ba kamar sauran addinan da suka gabace shi ba, addinin Musulunci an aiko da shi zuwa ga dukkan al’ummomin duniya don ya zama hanyar shiriya ga kowa.

    Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya fara da kiran ‘yan’uwansa zuri’ar Banu Hashim don su karɓi wannan addini. Wasu suka karɓa wasu kuwa suka ƙi. Sannu a hankali yana wa’azi shi da waɗanda suka fara ba shi goyon baya, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sai da dukkan ƙasashen Larabawa suka amshi addinin Musulunci.

    Wannan ne ya sa aka kafa Ƙungiyar Al’ummar Musulmi wadda take da cibiya a Birnin Madina, Annabi shi ne shugaban wannan al’umma. Dukkan abin da zai zartar, sai ya yi shawara da sahabbansa. Wajen tafiyar da wannan al’umma ba a nuna ƙabilanci ko fifiko a tsakanin jama’ar da suke cikinta. Abin da ta sa gaba shi ne haɗin kai da son juna da nuna ‘yan’uwantaka a tsakanin Musulmi. Babban tsarin mulkin wannan al’umma shi ne shari’ar Musulunci. Kafin Annabi ya yi ƙaura, ya bar wa al’ummar Musulmi Alƙur’ani mai tsarki da kuma Hadisai don su yi masu jagora dangane da addininsu (Ibrahim, 1982:63).

    Manyan shika – shikan addinin Musulunci biyar ne:

    • Shaidawa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) bawansa ne kuma manzonsa ne.
    • Tsayar da salla.
    • Bayar da zakka.
    • Yin azumin watan Ramalana.
    • Ziyartar ɗakin Allah don yin aikin Hajji ga wanda ya sami iko.

    Bayan ƙaurar Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) da kuma zaɓaɓɓun halifofi huɗu da suka biyo bayansa. An sami wasu daga cikin sahabbai da wasu malamai da suka biyo bayansu, sun kawo hanyoyin da suke ganin ya dace a riƙa yin aikace-aikacen addini don samun sakamako mai kyau a duniya da lahira. Wannan ne ya sa aka sami ɗariƙu da ƙungiyoyin addini mabambanta masu yawa waɗanda suke da magoya baya a ko’ina.

    Daga cikin ire-iren waɗannan ɗariƙu akwai Ƙadiriyya da Tijjaniyya da dai sauransu da dama. Haka kuma akwai ƙungiyoyin addini waɗanda suka haɗa da Ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa Iƙamatus Sunna wato Ƙungiyar Kawar da Bidi’a da Tsayar da Sunna. Akwai kuma Ƙungiyar ‘Yan’uwa Musulmi (Shi’a). Waɗannan ɗariƙu na Ƙadiriyya da Tijjaniya suna da magoya baya sosai a cikin ƙasar Hausa. Haka su ma waɗannan ƙungiyoyi suna da nasu magoya baya a sassa daban-daban na ƙasar Hausa (Ibrahim, 1982:98-99, ‘Yanɗaki, 1997:46-50 da Suleman, 1997: 58-59).

    Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU ya wallafa WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

    MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Addinin Bahaushe

    Addinin Bahaushe

    Kafin zuwan addinin Musulunci yammacin Afrika,  Bahaushe na addinin gargajiya, wasu na bautar iskokai,  wasu mutum-mutumin itace, ko dodo, ko rana, ko ruwa  da dabbobi (Malumfashi, 2008 & Adamu, 1997). Amma  a yau, yawancin Hausawa Musulmai ne, a kan sami  tsirarun Kiristoti da masu addinin gargajiya (NNPC,  2007).

    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
  • Yadda ake Yiwa Jarirai Hudubar Haihuwa

    Yadda ake Yiwa Jarirai Hudubar Haihuwa

    Akwai hanyoyin biyu da za a iya yiwa jarirai huduba wanda suka tabbata a suna bisa tsarin addinin musulunci kamar haka:

    Hanya ta farko.

    Yana daga cikin abin da yatabbata a sunna idan aka haifi jariri sai mahaifinsa ko wani wanda mahaifin sa ya wakilta,ya dauki jaririn ya kara bakin sa adaidai kunnen sa na dama,ya kira sallah, yadda ake kiran sallah da kalmomi guda (19) kamar haka:

    Idan da maimaici kenan,ko guda (17) idan babu maimaici kenan,ga misali na guda (19)

    “Allahu Akbar Allahu Akbar, Allahu Akbar Allahu Akbar,

    Ashhadu an Laa iLaaha illal Laah, ashhadu an Laa iLaaha illal Laah

    Ashhadu anna muhammudur rasulul Laah ashhadu anna muhammadan rasulul Laah,

    Hayya alal Salah hayya alal Salah

    Hayya alal falah, Hayya alal falah

    Allahu Akbar Allahu Akbar,

    Laa iLaaha illal Laah.”

    Sannan ya kara bakin sa a daidai kunnen sa na hagu,nanma sai ya tayar da iqama kamar haka

    “Allahu Akbar Allahu Akbar

    Ashhadu an Laa iLaaha illal Laah,

    Ashhadu anna muhammadan rasulul Laah

    Hayya alal salaati, Hayya alal Salah,

    Qad qaamatus salaatu, qad qaamatus salah,

    Allahu Akbar Allahu Akbar

    Laa iLaaha illal Laah.”

    Sannan sai yace sunan ka wane,kamar misali sunan ka/ki (Ahamad ko Zainab).
    Toh kuma daga nan Idan mahaifin yana so sai yayiwa yaron (tahaniki) abin nufi da (tahaniki)shine kasa dabino a bakin ka idan ka gatsa shi sai a sakawa jariri a bakin sa kafin a bashi wani abinci, amma ba hakan yana nufin uwa baza tabashi ruwan nono mai kauri kalar rawaya da ake kira daKushi da harshen hausa ba.

    Zata bashi idan jariri na bukata sannan sai a bashi dabinon da aka gatsa ya tsotsi ruwan wannan shima yana cikin abinda akewa jariri da zaran an haife shi.

    Hanya ta biyu:

    Za ayiwa jariri (tahaniki) idan mahaifin sa naso sannan yace sunan wane, misali yacewa jaririn sunan ko sunan ki(Ahamad ko Zainab) ba tare da yin kiran sallah a kunnen dama da tayar da iqama a kunnen hagu ba.

    Domin karanta yadda zakai tarbiyar yaro danna nan 

  • Tarbiyyar Addini

    Tarbiyyar Addini

    Duk da muhimmancin samun mutum daga iyaye masu addini, wannan ba zai wadatar ga barin yi masa tarbiyya irin ta addini ba. Ita tarbiyya gini ce a kan harsashin da iyaye suka kafa, ta zamowar su masu addini.

    Kodayake tarbiyya (idan aka dace) za ta iya gyara mutumin da bai gaji halin addini daga iyayensa ba, amma mafi yawan lokaci, tarbiyya ga wanda ya gaji halin addini ta fi sauƙi da tasiri. Saboda haka wajibi ne ga mai shirin yin aure mace ko namiji ya fi bayar da muhimmanci ga siffar addini a wurin wanda zai aura fiye da kowace irin siffa daban. Sai dai idan halin addini ya haɗu da sauran halaye, ko siffofi, kamar kyawun halitta da dukiya ko dangi da sauran su, to haka ya fi kyau, idan kuma aka sami dukkan siffofi sun haɗu, sai dai babu addini shi kaɗai to abu ya ɓaci, lallai ne a nemi mai addini.
    Sannan kuma ita kanta tarbiyyar addini ba za ta yiwu cikin sauƙi ba, idan mahaifa ba masu addini ne ba,  domin su ne masu tarbiyya na farko, yana da kyau mu san cewa ita tarbiyyar addini ana fara yi wa yaro ita tun kafin a haife shi, ta hanyar aiwatar da ladubban da addini ya tanadar wa miji da mata, waɗanda idan suka bi su, babu shakka, albarkar yin haka za ta shafi ɗan da za su haifa. Haka kuma, ba za ta samu ba daga mahaifa bin tsarin rayuwar Yahudu da Nasara, waɗanda ba ruwansu da addini. Misalin Manzo Allah (Sallallahu alaihi wassallam )ya ce: “Idan mutum zai kusanci iyalinsa ya yi addu’a ya roƙi Allah Ya kiyaye su (Shi da matar) daga shaiɗan, kuma ya nesantar da shaiɗan daga abin da za su Haifa”.Manzo Allah (Sallallahu alaihi wassallam ) yace : “idan aka samu yin hakan kafin kusanta, Allah zai kare shi daga Shaiɗan”.
    Lallai babu shakka, irin wannan ɗa an fara yi masa tarbiyya ta addini tun kafin a sami cikinsa.
    Haka idan ana maganar tarbiyyar addini, lallai ne a tsaya a kan batun karutu, domin shi ne tushen tarbiyya, don haka kowace irin makarantar da yaro zai shiga, ya kamata a tabbata makaranta ce wanda ta ƙunshi koyar da karatu tare da koyar da tarbiyyar addinin Musulunci, kamar yadda Allah Ya saukar kuma ManzoSa (Sallallahu alaihi wassallam ) ya isar. Haka kuma abokin karatu yaro ko abokin hirarsa, shirarsa, shirye-shiryen talabijin da na rediyo da rikoda da na’ura mai ƙwawalwa ( computer) duka lallai ne ya yi masa jagora don ya yi amfani da abin da zai haɓaka tarbiyyars  ba wanda zai rusa ta ba. Idan aka yi wa mutum haka babu shakka an taimake shi, domin zai iya cin jarrabawarsa cikin sauƙi. Kuma zai gagari abokan gabarsa (shaiɗan da ruɗin duniya da son zuciya).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yanayi Mai Tsafta danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Yake Son sa. wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Wane Suna Ake Kiran Manzon Allah(S.A.W)

    Wane Suna Ake Kiran Manzon Allah(S.A.W)

    Wane suna ake kiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kafin zuwan annabta: 

    Sunan da ake kiran Manzon Allah (s.a.w) da shi kafin zuwan annabta shi ne

    1.Al-Amin(mai gaskiya).

    Domin sanin wace ce kakar Manzon Allah danna nan