Tag: Adabi

  • Juyin -Juya Hali A Rubuce-rubucen Littattafan Adabi

    Juyin -Juya Hali A Rubuce-rubucen Littattafan Adabi

    Duk da cewa maza su suka. fara rubuce tun 1933 Mukhtar (2004). Amma wacce ta fara Rubuta ƙagaggen Labari na Hausa ita ce Hafsatu Abdulwaheed, Abdalla Uba Adamu (2024). Mace ta farko ‘Yar Arewa da fara rubuce-rubuce a Hausa da Fulatanci ita ce Dadasare Abdullahi Uwargidan Dr. R M. East takan taimaka wa Maigidanta Jaumisare (R.M. East) da labaran da akan saka a Jaridar Gaskiya Ta fi Kwabo da kuma tace labaran. Dadasare (2019)

    Waɗannan su ne wasu daga cikin talife-talifen wannan marubuciya wacce babu shakka ta yi namijin ƙoƙari a wannan nau’i na Adabin na tailfin Hausa da Fultanci. Bayan sai ita Zuwaira Isa wacce ta rubuta ƙagaggen littafi a 1972 sannan tana ‘yar makaranta a Rikkos can jos amma ba a buga ba sai daga baya, mai suna Ɗaki Ba Ya Tashi Jinka Ya Zauna.

    Ya iso kasuwar ta Kano tun 1992, to sai bayan shekaru uku ne wato a 1995 littafin Bilkisu ya fara bayyana kamar yadda aka gani a jerin littattafan nata, a sama. Ita kuma Bilkisu it ace ta fara rubuta littafai masu na Hausa, kimanin guda ashirin cikin shekaru uku zuwa huɗu.

    Littattafan zuwaira Isa Danlami Jos sun haɗa har da:

    • Zuwaira Isa daki Ya Tashi Jinka Ta Zauna (1992) Gaskiya corporation Ltd.Zaria.
    • Zuwaira Isa Labarin So (1995) littafi na 1-3 City Publishers Jakara, Kano.
    • Zuwaira Isa Sants in Soyayya (1996) littafi na 1-3 city Business Centre Daneji, Kano.
    • Zuwaira Isa  kissar Mata (1996) City Publishers Goron Dutse Road Jakara,Kano.
    • Zuwaira Isa  Wahala Siraxin Masoya (1997) Sauqi Bookshop and Publishing Company Sabon Gari,Kano.
    • Zuwaira Isa  ‘Ya’ya Mata (1999) littafi na 1-3 M Square Telecomm,Zoo Road, Kano.

    Sauran littattafan wannan marubuciya da muka ji labarinsu amma ba su zo hannuna ba har lokacin da zan buga wannan littafi sun haɗa har da:-

    • Zuwaira Isa  A Lallaɓa Auren Zamani
    • Zuwaira Isa  Mowar Mata
    • Zuwaira Isa  Ƙwarya Ta Bi Ƙwarya
    • Zuwaira Isa  Kara Da Kiyashi
    • Zuwaira Isa  A Ci Duniya Da Tsinke
    • Zuwaira Isa  Duniya Labari, Ciwon ƙauna, ƙishirwar Bege (d.s.)

    Bayan waɗannan, mata marubuta, daga cikin maza kuma waɗanda suka fi fice kamar yadda wallafe-wallafe ya nuna akwai Nazir Adam Salih da kuma Ado Ahmad Gidan Dabino. Wasu daga cikin littattafan Nazir Adam Salih sun haɗa da:-

    • Nazir Adam Salih  Me Ya Fi Kuxi? Kamnas Publishers, Kano.
    • Nazir Adam Salih  Kibiyar Ajali littafi na 1-2 (1996) City Business Centre Daneji, Kano.
    • Nazir Adam Salih  Naira Da Kwabo littafi na 1-2 (1998) Jet Age Publishers Kano.
    • Nazir Adam Salih Birnin Sarauniya (1998) Qamnas Publishers Kano.
    • Nazir Adam Salih Ta Leƙo Ta Koma (b. kw.) Qamnas Publishers Kano.
    • Nazir Adam Salih Mutuwar Kasko (1999) Layeet Printers Kano.
    • Nazir Adam Salih  Aljani Ya Taka Wuta (2000) Jet Age Printers Kano.
    • Nazir Adam Salih A Ci Bulus (b. kw.)
    • Nazir Adam Salih  Kudi Da Maciji (b. kw.)
    • Nazir Adam Salih  Damisar Takarda (2000) Jet age Printers Kano.

    Amma shi Ado Ahmed Gidan Dabino shi ma ya taka muhimmiyar rawa a cikin wannan nau’in adabi inda littattafansa suka fito kamar haka:-

    • In Da So Da Ƙauna (1991) Gidan Dabino Ado Ahmed  Publishers, Kano.
    • Masoyin Zamani I (1993) Gidan Dabino Publishers, Kano.
    • Wani Hanin Ga Allah (1994) Gidan Dabino Publishers, Kano.
    • Kaico! (1996) Gidan Dabino Publishers, Kano.
    • Duniya Sai Sannu (1997) Gidan Dabino Publishers, Kano. Mukhtar (2004)

    Adabin Kasuwar Kano

    To amma a cikin shekarar 1984 wata al’adar rubuce-rubuce ta ƙagaggun littattafai ta kunno kai wadda aka sa wa suna Adabin Kasuwar Kano, a Turance “Kano Market Literature”. An sami wani jigo na soyayya inda ya yi tasiri sosai da sosai a cikin wannan adabin. Daga cikin waɗanda suka share fage akwai irin su littafin;

    • Rabin Raina littafi na ɗaya(1984) na Talatu Wada Ahmed
    • Soyayya Gamon Jini (1986) na Ibrahim Hamza Abdullahi
    • In Da Rai (1987) na Idris Imam
    • Budurwar Zuciya (1987) na Balaraba Ramat Yakubu
    • Kogin Soyayya (1988) na A.M. Zahraddeen
    •  Idan So Cuta Ne (1989) na Yusuf M. Adamu.

    (Duba muƙalar Yusuf M. Adamu 1996).

    Bayan wannan an sami mace a karon farko wacce ta yi fice a cikin rubutun adabi na Hausa inda ta rubuta ƙagaggun littattafai a ƙalla sama da guda ashirin (20) a cikin shekaru huɗu rak. Wannan kuwa ita ce uwargida Bilkisu Salisu Ahmed Funtuwa, wadda kafin ta yi aure ake kira Bilkisu Ibrahim. Nabature Funtuwa.

    Ita dai wannan marubuciya ta yi fice a kan waɗannan rubuce-rubuce ba ma kawai tsakanin mata ba, hatta cikin mazan ma na wannan nau’in adabin babu wanda ya kamo ta. Binciken da muka yi, ya nuna cewa. Makaranta littattafan wannan nau’in adabin har bincikawa sukan yi ko sabon littafinta ya fito su yi maza su karanta don kada wani ya ba su labarinsa. Kaɗan daga cikin irin waɗannan rubuce-rubuce nata sun haɗa har da:-

    • Bilkisu S.A.F Allura Cikin Ruwa, (1995) Gidan Dabino Publishers Kano, Nijeriya.
    • Bilkisu S.A.F Sirrin Ɓoye littafi na 1-2 (1996) City Publishers Jakara Kano, Nigeria
    • Bilkisu S.A.F Wa Ya San Gobe littafi na 1-3 (1996) City Pulishers Jakara Kano, Nijeriya.
    • Bilkisu S.A.F Ƙarya Fure Take, littafi na 1-2 (1996) Nabila Surayya Bookshop.
    • Bilkisu S.A.F Gaskiya Na Mafaɗinta littafi na 1-2 (1997) Printed
    • Bilkisu S.A.F Kyan Ɗan Maciji littafi na 1-2 (1997) Printed
    • Bilkisu S.A.F In Da kwaɗayi littafi na 1-2 (1998).
    • Bilkisu S.A.F Ki Yarda Da Ni (b. kw) littafi na 1-2
    • Bilkisu S.A.F Sa’adatu Sa’ar Mata (b. kw)
    • Bilkisu S.A.F Maryamu (1999) littafi na 1-2
    • Bilkisu S.A.F Mugun Zama (1999) littafi na 1-2 Anti Bilki Bookshop Kano
    • Bilkisu S.A.F Kowa Ya Raina Tsaiwar Wata (1999) littafi nal-2 Anti Bilki Bookshop Kano.

    Kammalawa

    A taƙaice, takardar wata tafarki ce a fagen adabin Hausa, musamman ta fuskar rubuce-rubucen da suka shafi tarbiyya da gyaran halaye. Saboda haka Littattafan ƙagaggun Labari ba wai labaran soyayya kawai suke ba, har ila yau suna nuna irin rawar da adabi ke takawa wajen sauya tunani da ɗabi’a.

    A matsayin shawara, akwai buƙatar a ci gaba da nazarin irin waɗannan marubuta domin fahimtar tasirin rubuce-rubucen Hausa wajen gina tarbiyyar matasa da inganta al’ummar Hausawa gaba ɗaya. Duk waɗannan suna jan kunne ne da a tarbiyyantar da mutune su yi aiki da tarbiyya a cikin mu’amalarsu da mutane.

    Ana cusa tarbiyya wajen horar da mutane ko ilimantar da su, ko ta hanyar rubutu, domin a gano kaifin hankalin mai karatu idan da buƙatar gyara a gyara maka ko a cusa musu labarai na ban tausayi ko na jin ƙai ko ta hanyar yi musu tarbiyyar ta ta hanyar gargajiya misali Karin Magana da Tatsuniya ko kuma ta hanyar gaya musu wani labari mai daɗi na baka ko a rubutaccen ƙagaggen labari wanda kuma shi ne muka yi magana kai.

    Wanann bayanin an ciro shi ne daga muƙalar da aka gabatar a taron makon Hausa wanda ya gabata a Ranar 24 ga wata Oktoba 2025 a Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Bichi.

    Danna nan don karanta Samuwar Rubutun Ajami

    Edita@rumasau-kallamu

  • Sharhin Wasu Littattafan Adabin Kasuwar Kano

    Sharhin Wasu Littattafan Adabin Kasuwar Kano

    A wannan babi an yi ƙoƙari na yin sharhin wasu daga cikin litattafan Adabin Kasuwar Kano. Sai dai da yake littattafan da yawa an taƙaita ne ga zaɓo wasu daga cikin zangunan da littattafan suka wanzu na rayuwar wannan adabi. Kamar yadda aka bayyana a baya a  wannan aiki, akwai zanguna huɗu na samar da littattafai na Adabin Kasuwar Kano.

    An bi waɗannan zanguna ne aka zaɓo littafi ɗaiɗaya waɗanda suka haɗa da; Rabin Raina da So Jinin Jiki da  Ina Son Sa Haka da kuma Mace Mutum. Amma sharhin da za a yi wa littattafan ya ta’allaƙa ne a kan jigo da salo kawai.

    Masana da dama suna kallon salo ta fuskoki daban-daban. Salo dai kamar yadda Cuddon (1977) ya ce ‘salo wata hanya ce da marubuci ke bi domin ya ɓarji guminsa a rubutun zube ko waƙa domin isar da saƙonsa cikin sauƙi. Salo hanya ce da marubuci ko mawallafi ke rattaba abubuwa cikin harshe mai burgewa ko kuma domin ya inganta wallafarsa.

    Ke nan irin yadda marubuci yake zaɓar kalmomi da yadda yake amfani da adon harshe da kuma yadda yake tsara zancensa da tsarin tsawon jimlolinsa, kai, har da ma yadda yake amfani da sakin layi da dai duk sauran hanyoyin da ya bi domin fiddo da tsara batu mai burgewa shi ne salonsa.

    Ɗangambo (2007:35) da yake ƙoƙarin fitar da ma`anar salo cewa ya yi ‘ba wani abu ba ne salo face zaɓi cikin rubutu ko furuci. Sai dai ba dole ne a same shi cikin kowane rubutu ko furucin ba’. Haka nan Yahya (2001:2) cewa ya yi ‘ salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya ƙwarzanta ko ya bayyana,’ ya ci gaba da cewa idan kuwa za mu yi wa wannan ma`ana gyara domin mu dubi salo a cikin waƙa, sai a ce, ‘salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo.

    Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya, ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai sauraro ko karatun waƙar’. Idan muka kalli wannan ma`ana da Yahya (2001:2) ya ba salo a cikin waƙa, za mu ga cewa duk sun yi kaka-gida a cikin ƙagaggun zube ko makamantansu, ciki kuwa har da wannan makeken fage na Adabin Kasuwar Kano.

    Shi ma a nasa ra`ayin Mukhtar (2004:99) yana cewa ‘salo wata baiwa ce ta mawallafi wadda kuma ta taƙaita a kansa, domin wurinsa kawai za ka samu irin wannan baiwar da ya yi amfani da ita a wallafarsa’. Saboda haka, muna iya cewa marubuta sun bambanta dangane da zaɓin da suke yi wajen isar da saƙonsu da baki ko a rubuce.

    A fage irin na Adabin Kasuwar Kano marubutan sun kasu kashi-kashi dangane da salo na rubuce-rubucensu, wasu su yi amfani da hanya mafi sauƙi wajen isar da saƙonsu, yayin da wasu kan zaɓi hanya mai sarƙaƙƙiya don isar da nasu saƙon.

    Bayan salon a gaba ɗaya akwai kuma mataimakan salo waɗanda ke ƙara fiddo salon fili, musamman a rubuce, waɗannan kuwa sun haɗa da zaɓen kalmomi da ƙirƙirar jimla da yanayi ko nau’o’in jimla da tsarin tunanin marubuci da sauransu. Haka kuma shi kansa salon ya kasu kashi-kashi; akwai miƙaƙƙen salo da salo mai armashi da raggon salo da sauransu (Ɗangambo, 2007:38).

    Miƙaƙƙen salo shi ne salo mai sauƙin fahimta da sauƙin isar da saƙo, a cikinsa mai karatu bai cika fuskantar matsala ba wajen fahimtar manufar marubucin. A irin wannan salon ba kasafai ake yin amfani da karin magana ko amfani da tsofaffi da sababbin kalmomi ba.

    Salo mai armashi kuwa, salo ne mai burge mai karatu ko saurare,  a cikinsa ana amfani da maganganun hikima, ko karin magana da sauran dubarun jawo hankali, domin ƙara armashin batutuwa.

    Shi kuwa raggon salo, salo ne mai wuyar ganewa, wato akwai sarƙaƙiya sosai a cikinsa. A cikin irin wannan salo, marubuci kan yi amfani da abubuwa barkatai, kamar amfani da karin harshe iri-iri, sanyo tsofaffi ko sabbin kalmomi, kara-zube. Akan samu kwan-gaba-kwan-baya sannan uwa-uba ba kasafai ake gane gundarin saƙon da ake son isarwa ba (Sarɓi, 2009:130).

    Idan muka koma ta fuskar jigo kuwa, kamar yadda kalmar ta bayyana tana nufin maƙasudin abin da  ake bayani, wato abin da wani abu ya sa wa gaba. Amma a adabi, jigo na nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara a kanta. Saboda haka, jigo shi ne saƙon da marubuci ke son sadarwa ga jama`a.

    Akwai ire-iren jigo gida biyu; gundarin jigo da kuma ta`allaƙaƙƙen jigo. Gundarin jigo shi ne babban jigo, wato babbar manufar da marubuci ke son isarwa. Akan samu babbar manufa guda ɗaya da marubuci ke yin magana kanta. Shi kuwa ta`allaƙaƙƙen jigo na nufin ƙaramin jigo, wanda ba ya tafiya sai da babban jigo. Ke nan a iya cewa kamar ƙaramar manufar marubuci ke nan (Sarɓi, 2009:69.)

     Idan muka kalli litattafan da muka zaɓa domin nazari za a iske cewa duk suna ɗauke da waɗannan abubuwa kamar sauran litattafai na ƙagaggen labari. Saboda haka, za a kalli yadda kowane daga cikinsu yake dangane da salo da jigo.

    Littafin Rabin Raina

    Littafin Rabin Raina kamar yadda muka yi bayani a baya, kusan a iya cewa shi ne ake gani a matsayin na  farko a sahun Adabin Kasuwar Kano, an samar da shi ne a shekarar 1984, an kuma gina labarin ne a kan soyayyar Usman da Maryam.

    A cikin labarin soyayyar wanda mawallafiyar ta tabbatar da cewa ta samar da shi ne a makaranta daga gyauron labaran da take ba ƙawayenta, an nuna ginuwar soyayyar Usman ɗin da Maryam inda aka nuna cewa da abokan faɗan juna ne a cikin unguwa, kasancewar unguwarsu guda, amma daga baya sai suka fahimci so da ƙauna ya shiga tsakaninusu.

    An dai nuna cewar sun fara soyayya ne bayan tafiyar Usman makaranta, sai Maryam ta ji tana matuƙar kewar Usman ɗin, yayin da shi kuma a makaranta yake jin wani abu mai santsi game da Maryam. Bayan dawowarsa daga makaranta ya yi ta saƙe-saƙe na ko ya je wajen Maryam, amma yana fargaba, yayin da ita kuma ta ga cewa tsokanar faɗa da Usman ke mata ya daina, hasali ma kamar ba ya ganinta.

    Usman dai ya yi ta maza, inda ya je gidan su Maryam ya aika aka kira ta, da ta fito ta ga Usman ta yi mamaki, amma ta ce a zuciyarta ko kashe ta za ya yi sai dai ya kashe ta, ai dai ta gan shi, shi kuma ya rasa abin da zai ce mata, sai ya ɓuge da cewar ta yafe masa abubuwan da ya yi mata a baya, ita kuma ta ce ta yafe, daga nan wannan soyayya ta samo asali.

    Ko bayan komawar Usman makaranta, soyayya mai ƙarfi ta ci gaba da wanzuwa tsakaninsu. Haka bayan ya gama sakandire, a wannan lokacin ne kuma ita Maryam ta samu damar tafiya sakandire ta kwana, kuma daga nan ne suka ci gaba da soyayyarsu ta hanyar wasiƙa har zuwa lokacin da Usman ya tafi karatu Ingila.

    Ko da yana Ingilar soyayyarsu da Maryam ta ci gaba da gudana tare da alƙawarin aure a tsakaninsu. An nuna cewa ya yi ta samun farmakin mata abokanan karatunsa musamman wata da aka kira Becky ita ce ta liƙe ma shi, amma ya zame da cewar yana da mata a gida, amma duk da haka ta dage kan sai an yi da ita. A gida kuwa samari suka yi wa Maryam caa, da sunan suna son ta, amma ta ce ta ƙi sauraron kowa ita sai Usman ɗinta.

    Bayan dawowar Usaman daga Ingila ya je aikin hajji, da ya dawo kuma ya samu aiki mai tsoka har da gida da mota. Ita kuma Maryam bayan ta gama karatunta, ita ma ta samu aikin koyarwa. Daga baya dai an yi auren Usman da Maryam bayan doguwar rashin lafiya da ita Maryam ɗin ta yi, sakamakon wai hawayen da ta zubar ba lokacin da Usman ya dawo daga Ingila.

    Bayan biki, masoyan biyu sun samu ƙaruwar ɗa namiji mai suna Ƙassim, a haka suka ci gaba da rangaɗa soyayyarsu har zuwa lokacin da mahaifin Maryam ya rasu, bayan zaman makoki suka ci gaba da rayuwarsu ta masoya a gidan aure.

    Jigo a Littafin Rabin Raina

    Jigon littafin Rabin Raina ba komai ba ne face tsagwaron soyayya. Domin tun daga farkon littafin har ƙarshensa an nuna soyayyar da ta auku tsakanin Usman da Maryam wadda har ta kai su ga yin aure.

    Jigon kuma ya fito fili tun daga lokacin da Maryam ta ce wa Usman kada ya ƙara zuwa gidansu domin an yi mata faɗa, shi kuma gogan naka da ya koma gida sai rashin lafiya ta kama shi saboda ta ce kada ya ƙara zuwa wurinta, ciwo dai ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa har sai ranar da Maryam ta zo ganin Usman da jiki, ga abin da ya faru;

    ‘Ya sa hannu ya share idon sa. Bayan ya tabbata Maryam ce,

    Sai kawai ya kama ta ya ƙaƙume, ya sumbace ta yana ta

    magana  a cikin kunnenta.’

    Wannan ya nuna mana cewa saboda tsananin son da yake yi wa Maryam, rashin lafiya ta kama shi, amma da yake yanzu ya gan ta, ciwo ya warke sarai! Haka kuma marubuciyar ta ƙara tabbatar mana da cewa soyayya dai ita ce jigon littafin nan domin can a shafi na 10 ga abin da ta ce:

    ‘Haka wannan alƙalamin soyayya ya kasance Tare da waɗannan masoya’.

    Salo a Littafin Rabin Raina

    Salon littafin Rabin Raina mai sauƙi ne, domin duk wanda ya karanta littafin yana iya fahimtar shi, ga kalmomi da jimloli masu sauƙin ganewa, sannan marubuciyar duk da cewar ta yi amfani da baƙin kalmomi irin su; Likita, recorder, camera, Ingila, da sauransu, amma ba a cika samun karin magana a cikin littafin ba.

    Zaren tunanin labarin dai bai tsinke ba tun daga farko har ƙarshe. Sannan kuma duk da cewar labarin a zube ya zo, marubuciyar ta jefo waƙa da kuma salon wasan kwaikwayo a ciki.

    Littafin So Jinin Jiki

    An samar da wannan littafi na So Jinin Jiki a 1995 wanda Alkhamees Bature Makwarari ya rubuta. Shi ma kamar sauran litattafan wannan zango, yana magana ne kan soyayya, sai dai shi ta wata siga daban.

    Littafin yana ba da labarin soyayyar wani matashi ɗan ƙwalisa mai suna Muzaffar da budurwarsa, Weedat wadda ta yi ta gasa masa aya a tafin hannunsa saboda ta lura da yadda yake mutuwar sonta. Kasancewar Weedat ta ga tana da matsanancin kyau, kuma samari ‘yan birni na ruguguwar zuwa wajenta, ya sanya take jan zarenta yadda take so.

    Muzaffar ya dage kai-da-fata bisa ga son da yake yi wa Weedat, ita kuma duk da cewar duk cikin samarin da ke nemanta ta fi son Muzaffar ɗin, amma wannan bai hana ta yi masa wulaƙanci yadda ta ga dama ba. Daga cikin wulaƙancin da Weedat ta yi wa Muzaffar ba wanda ya fi fice sai lokacin da ya samu haɗari sanadiyyar ita Weedat ɗin, ga abin da ta ke cewa;

    ‘Wai kai ba ka san idan zamani ya riski manshanu ko an toya shi ba ya ƙamshi ba? Ga lafiyayyun samari ‘yan birnin asali zan tsaya na saurari kwalmaɗaɗɗen saurayi gurgun mage? Daga ji an san cewa wani irin wulaƙanci ne aka yi wa saurayin duk ko da soyayyar da ke tsakaninsu.

    Kasancewar Muzaffar saurayi mai farin jini ya sa ‘yan mata ke ta kawo masa caffa, amma shi ya ƙuƙe sai Weedat, a irin wannan hali wata budurwa mai suna Santisima da ta daɗe tana son Muzaffar, shi kuma ya ƙi ta, ta shammace shi suka tafi wani wuri ta neme shi da su riƙa yin safarar miyagun ƙwayoyi shi kuma ya ƙi, wannan ƙiyawa da ya yi ta jawo masa barazanar kisa daga wurin Santisima, da ƙyar da jiɓin goshi ya samu ya gudo.

    Muzaffar ya sake samun haɗari inda wata budurwa ta banke shi, wanda har ya ja masa kwanciya asibiti, bayan ya warke kamar wasa sai soyyaya ta ƙullu tsakaninsu da wannan budurwa mai suna Munazzafa. Ga mamakin Muzaffar sai ga Weedat ta dawo tana neman soyayyarsa, bayan ta gama wulaƙanta shi, amma ya ƙiya, ya kuma sha alwashin ɗaukar fansar abin da Weedat ɗin ta yi masa.

    Daga ƙarshen littafin dai Muzaffar ya auri Munazzafa, sannan kuma ya ɗauki fansar abin da Weedat ta sanya aka yi masa, ita kuma Weedat ɗin ta yi nadamar wulaƙancin da ta yi wa Muzaffar.

    Jigo a Littafin So Jinin Jiki

    Jigon wannan littafi kamar saura na wannan zangon bai wuce soyayya ba tsakanin saurayi da budurwa ba kamar yadda Muzaffar ya tabbatar ga Munazaffa.

    ‘ Ko kusa ko alama idan kin lura ai soyayyarmu da ke haɗuwar jini ce, da kuma tsabar fahimtar juna. Kin ga duk wata maganar sihiri ba ta taso ba…, Duk masoyan da Jinin Jikinsu ya gauraya soyayyarsu ta fi ƙarko da nagarta. Kuma za su iya bayyana tsananin begensu da  ƙaunar da suke yi wa juna ba tare da jin kunya ba.’

    Wannan ya nuna mana cewa jigon wannan littafin soyayya ce, kai ko ginin littafin ma, duk wanda ya karanta shi ba abin da zai ji da gani sai labarin soyayya.

    Salo a Littafin So Jinin Jiki

    Salon littafin So Jinin Jiki mai sauƙin gane wa ne, marubucin ya yi amfani da kalmomi masu sauƙi, sannan zaren tunanin littafin a jere yake, babu kwan-gaba-kwan-baya. Kasancewar marubucin ƙwararre wajen sarrafa harshe, wannan ya sanya karin magana da ba’a da habaici ya cika littafin, ga kuma amfani da salon zayyana ta yadda ko ɗaki aka ce na wane ko wance ce sai an bayyana yadda yake.

    Haka kuma ko budurwa ce za a zana surarta a tsaye, ta yadda mai karatu zai dinga ganin kamar ya ɗauki hoton wannan budurwa yana kallo, da dai sauran ire-iren waɗannan abubuwa da Al-khamis Bature Makwarari ya ƙware kansu.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Danna nan ka karanta Tsokaci Kan Adabin Kasuwar Kano A Jaridu Da Mujallu

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Tsokaci Kan Adabin Kasuwar Kano A Jaridu Da Mujallu

    Tsokaci Kan Adabin Kasuwar Kano A Jaridu Da Mujallu

    Daga bayanan da muka gani a sama, mun gane kowane daga cikin rukunin al’ummar Hausawa da yadda suke kallon wannan abu na adabi da ya auku a cikin wannan zangon rayuwa. To sai dai domin a ga yadda fasalin yake da yadda tabbatuwar wanzuwar adabi ta kasance a tsakanin jama’a, muna iya cewa shiga cikin rayuwar mutane da ya yi a cikin zamanin samuwar sa da tashensa da lokacin da ya soma gushewa za su iya yi mana jagora.

    A nan za  mu dubi abubuwan da suka faru ta hanyar Muhawarorin da aka yi kan wannan matsala a tsakanin al’ummar baki ɗaya. Sai dai su ma irin waɗannan Muhawarori kamar yadda suka wanzu a zamanin Elizabeth a Ingila da birnin Munich na Jamus a lokacin Kitsch da kuma waɗanda suka wanzu a zamanin Adabin Kasuwar Onisha a Nijeriya sun ɗauki salo iri daban-daban yayin gudanar da su. Mun kasa Muhawarorin zuwa gida-gida domin sauƙin fahimta:

    • Akwai waɗanda aka dinga yi a cikin jaridun Hausa da suka haɗa da Nasiha da Gaskiya Ta Fi Kwabo da Almizan.
    • Akwai waɗanda aka yi a cikin mujallun Hausa da suka haɗa da Rana da Gwagwarmaya.
    • Akwai kuma waɗanda suka kasance a jaridun Ingilishi, musamman jaridun New Nigerian da Weekly Trust da Triumph.
    • Akwai Muhawarorin da aka yi ko dai a masallatai ko kuma a sauran wuraren bukukuwan addini.

    Jaridar Nasiha

    Ra’ayi na farko game da wannan matsala ta Adabin Kasuwar Kano ya fito ne daga wata Hauwa Sheriff inda ta yi sharhinta a cikin jaridar Nasiha ta ran 6/09/1991 a wata hira mai suna ‘Ba a Nan Take ba’. A cikin wannan hirar da suka yi da Ibrahim Sheme ta nuna cewa mutane sun gaji da labaran soyayya, kuma ta ce tana so ta rubuta wani labari wanda bai shafi soyayya ba domin ta yi wa sauran marubuta nuni.

    Wannan rubutu na Hawwa shi ya sanya wani malamin jami’a, Ibrahim Malumfashi ya yi nasa sharhin mai taken ‘Akalar Rubutun Hausa Na Buƙatar Sauyi’ a ran 15/11/1991. Nazari da sharhi ne da ya bibiyi tarihin adabi, ya kuma tattauna yadda adabin Hausa ya kamata ya kasance.

    Daga wannan lokaci ne muhawarar ta soma sosai da sosai, musamman ganin cewa Ado Gidan Dabino ya shigo da sharhinsa ‘Zamani Zo Mu Tafi’,  a cikin jaridar Nasiha ta ran  24 da 31, Yuli 1992, ya shigo don mayar da martani. Ya nuna cewa sharhin da Ibrahim Malumfashi ya yi masu, bai yi shi bisa tsari ba, domin rubutunsu na zamani ne, saboda haka tun da zamani ne ya kawo, shi ya sanya suke yin haka.

    Daga nan sai Ibrahim Malumfashi ya dawo cikin jaridar Nasiha dai ta ran  24-31/7/1992 domin ya warware wa Gidan Dabino zare da abawar abin da yake nufi da wancan bayani inda ya bambanta Tsakanin Gwanjo da Orijina. A ciki ya rarrabe tsakanin adabi mai kyau da kuma wanda ya kira jabu (Tsakanin Gwanjo Da Orijina)

    Kwatsam sai ga Yusuf Adamu ya shigo don kare littafinsa, shi ma a cikin Jaridar Nasiha, 21/08/1992 (Idan So Cuta Ne) wanda yana daga cikin litattafan da bulalar Ibrahim Malumfashi ta ba kashi, inda yake kare littafin daga caccakar da Malumfashi ya yi masa na cewa ya kwaso kayan aikin Turawa ne, inda yake cewa (Ina Da Ja, Ibrahim Malumfashi!).

    A dai wannan ranar, wato juma’a 21/08/1992, shi ma wani Shehu Gambo ya shigo fage don ya nuna goyon bayansa ga irin bugun da bulalar Malumfashi ta yi wa waɗannan littattafai. Shehu ya nuna cewa ai Ado Gidan Dabino na rubuta litattafansa ne don kasuwanci kawai, ba don ilmantarwa ba, ya kira nasa taken da ‘Jigon Soyayya: Holoƙo Hadarin Kaka’.

    Kamar haɗin baki, sai ga Nasiru Mudi Giginyu a dai wannan ranar ta juma’a 21/08/92 a cikin jaridar Nasiha, ya jefo nasa ra’ayi don nuna goyon bayansa ga rubutun Malumfashi inda ya mai da wa Ado Gidan Dabino martani. A ciki yake zargin Ado ɗin da jefa wasu ‘yan mata cikin haɗari saboda irin rubutunsa na soyayya domin kuwa ya nuna wata yarinya ta kashe kanta a Kaduna ta faɗawa rijiya, kamar yadda jaridar New Nigeria ta ranar 24/11/91 ta ruwaito, saboda karanta littafin Ado ɗin. Ya yi wa sharhin nasa taken ‘Ƙaramin Sani Ƙuƙumi Ne: Martani Ga Ado Ahmed Gidan Dabino,’.

    Duk waɗannan abubuwa na faruwa ne ganin cewa a wannan lokacin Ibrahim Sheme, wanda yake shi ne Editan shafin adabin wannan jarida, wadda ake ta gumurzu a cikinta, ya shigo fage domin wai ya raba faɗa tsakanin masu wannan badaƙala, amma kuma sai ga shi ya ƙara rura wutar ne maimakon raba gardama, ya yi wa nasa taken ‘Raba Matasan Marubutan Hausa Faɗa,’ wanda aka buga a cikin Nasiha, ta dai wannan ranar 21/08/1992).

    Bayan an sake buɗe kamfanin Nasiha a karo na biyu, mahawarar ta sake kunno kai a inda aka san ta, a wannan lokaci Ibrahim Malumfashi ne editan shafin adabin jaridar Nasiha. Abu na farko da ya sake ta da ƙayar baya shi ne batun da Ibrahim Malumfashi ya yi a cikin jaridar ta Nasiha ta ranar 3 zuwa 29 ga watan 7 a shekarar 1994.

    A ciki ne ya raɗa wa wannan batu ADABIN KASUWAR KANO a karo na farko, domin  ya yi bayanin ko mene ne Adabin Kasuwar Kano tare da faɗar fasalinsa da kuma rarrabewa tsakanin adabin, kuma a nan ne ya goyi bayan Ɗanjuma Katsina kan matsalolin Adabin Kasuwar Kanon. Ya dai yi wa rubutunsa suna ‘Adabin Kasuwar Kano’.

    Wannan ne ya sa Nasiru Mudi Giginyu ya yi nasa sharhin da ya kira ‘Ina Ruwan Biri da Gada?’ a cikin Nasiha, ta 4 ga Satumba, 1994). Inda martani ne ga Ado Gidan Dabino, inda yake nuna cewa marubutan suna yi ne kawai don kuɗi ba ɗaukaka adabi ba, sannan kuma ya yi kira ga marubuta irinsu Ado da su juya akalar rubutunsu ko da na soyayya ne ta yadda zai rinƙa gyara ga yanayin rayuwa da halin da ake ciki.

    Kamar da ƙasa, sai ga Muhammad Abdullahi  ya shigo a dai wannan rana ta juma’a 4/09/94, da sharhin ‘Shin Marubuta Soyayya Sun Kuwa San Soyayyar?’ A ciki dai ya yi bayanin ko mecece soyayya da yadda tasirinta yake ga matasa.

    Muhammad Kabir Assada, a nasa sharhin mai taken, “Ramin Ƙarya ƙurarre Ne”,  a Nasiha, ta 16 zuwa 22 Satumba, 1994 ya yi nuni da cewa abin da Ibrahim Malumfashi ya faɗa haka ne domin yawancin marubutan na ɗauko labaran ne daga finafinan Indiya, inda ya nuna cewa wani littafi mai suna  Alƙawarin So na Aminu Adamu, fim ɗin Indiya mai suna Romance ne aka kwaikwaya, don haka a canza salon rubutun.

    Shi kuma Gidan Dabino sai ya mayar da martani ga Ibrahim Malumfashi da nasa sharhin mai taken “Wanda Ya Raina Tsayuwar Wata Ya Hau Ya Gyara”, a cikin Nasiha ta ran 16 ga Satumba da kuma ta ran 6 ga Oktoba 1994. Ado ya nuna cewa yawancin zargin da Ibrahim Malumfashi ya yi ba su da tushe, domin ana karanta littattafan a makarantu.

    Shi kuwa Muhammad Qaseem ya shigo da nasa sharhin ‘An Ƙi Cin Biri, An Ci Dila’ ne ranar juma’a 7/10/1994 yana mai nuna rashin amincewarsa kan abin da Malumfashi ya faɗa a baya game da littatafan, har yake nuna cewa ai littafin Ibrahim Malumfashi na Wankan Wuta idan haka ne shi ma an kwaso shi ne daga fim ɗin Indiya Kudgaaz kuma na soyayya ne. Wato dai shi ma Malumfashin ya zama marubucin litattafan soyayya.

    Bayan ‘yan watanni ne sai ga Suwaiba A. Aliyu ta shigo fagen ita ma a ranar 2 ga watan 12,1994 da nata sharhin ‘Sharhi Ba Zargi Ba Ne’, ita ma tana ba masu sukar littattafan shawarar da su san abin da za su ce game da wannan sabon salon rubutu, tana kare marubata soyayya tare da cewar yin rubutu kan soyayya ba ya da illa, kuma ba an samo asalinsa ne daga Turawa ba, ya samo asali ne daga Larabawa. inda ta nuna Larabawa suna yin rubutu kan soyayya sosai.

    Mako biyu tsakani, wato ranar juma’a  16 ga watan 12, 1994 sai ga Sani Yusuf Ayagi yana ƙoƙarin kare marubutan soyayyar da ‘Yabon Gwani Ya Zama Dole’, shi ma yana mai da martani ga Ibrahim Malumfashi da Nasiru Mudi Giginyu tare da yabo ga marubutan irin su Ado, har yake cewa shi bai yarda da cewar litattafai irin waɗanda su Ado ke rubutawa su ne ƙashin bayan gurɓata tarbiyya ba.

    Shi ko Bashir Yahuza ya zo a ranar 2 ga watan 6, 1995, yana tabbatar da abin da Malumfashi ya faɗa da sharhin ‘Marubutan Zamani Da Adabin Zamani’; yana cewa ayyukan marubutan ba su samun tacewa daga ƙwararru kuma mafi yawan masu yin su ba su kai aikin ɗab`in a wuraren ɗab`in da hukuma ta aminta da su.

    An dai yi shiru na wani lokaci, kusan bayan tsawon shekara biyu ba a ƙara cewa komi ba, musamman ganin cewa an rufe gidan jaridar da Sheme ke wa aiki ya koma wani wurin da aiki zuwa kamfanin Hotline da buga mujallar Rana.

    Mujallar Rana

    Kamar yadda muka yi bayani bayan mahawarar da aka tabka a cikin jaridar Nasiha, sai akalar mahawarar ta koma mujallar Rana, wannan kuwa bai rasa nasaba da cewar jagorar gudanar da wannan mahawara, wato Ibrahim Sheme ya taso daga Nasiha ya koma mujallar Rana ɗin. Wannan ya bada dama aka buɗe wannan sabuwar muhawarar a mujallar Rana.

    Shemen ne kuma a nan ya yi wata hira da Bashir Sanda Gusau a mujallar Rana ta 8/02/93, mai taken ‘Abin da Ya Sa Muke Rubuta Labaran Soyayya’ inda ya faɗi dalilan da ya sa suke rubuta labaran soyayya. Wannan ya sa Ibrahim Sheme ya yi bincike mai taken ‘Aibin Biro Ko Amfaninsa’ domin jin ra’ayin jama’a game da litattafan na soyayya, inda wasu suka nuna rashin jin daɗinsu na yadda marubuta suka tsaya kan jigon soyayya kaɗai.

    Wasu daga cikin mutanen da aka zanta da su akwai Hauwa Ibrahim Sharrif, wadda ita ce ta fara buɗe wancan maharawa ta farko a jaridar Nasiha ta yi nuni da cewa da marubutan sun canza alƙiblar rubutunsu da an karɓe su hannu biyu.

    A dai wannan fitowar ta mujallar Rana 8/02/1993, an yi hira da wata Zabba’u Garba Musawa, mai taken ‘A Yi Rubutun Da Zai Inganta Rayuwa’ inda ta nemi marubuta da su rinƙa yin rubutun da zai gyara rayuwa da sauran ɓangarori, ba su tsaya kan soyayya ba kawai  a hirar da suka yi da Sheme.

    Mujallar Gwagwarmaya

    A cikin wannan mujallar ma wadda wani Ɗanjuma Katsina ke wa Edita an ci gaba da fafatawa kan litattafan soyayya ko kuma Adabin Kasuwar Kano. Wannan ya faru ne ganin irin taƙaddamar da ke wanzuwa a cikin mujallar Rana da Sheme ke wa Edita, kuma da alama abin da marubutan ke bayyanawa ne ya jawo mujallar Gwagwarmaya ta yi nata binciken.

    Da farko dai doguwar wasiƙa ce Ɗanjuma Katsina ya rubuta ga marubuta: ‘Zuwa Ga Marubutan Soyayya; ta 11, a shekarar 1993, inda ba kawai ya yi masu nasiha ba ne, har nunawa ya yi cewa abin da marubutan suke rubutawa saɓon Allah ne, domin wani daga cikin jigon su shi ne auren dole da sauran su. Sannan ya nuna cewa ana nuna cakuɗar maza da mata cikin wasu litattafn wanda Musulunci ya hana.

    Ba tare da ɓata lokaci ba wata wai ita Hadiza Mohammed ta maido wa Ɗanjuma da martani tare da inkarin maganar da ya yi ta kafircewar marubuta soyayya, a sharhinta ‘Kafircewar Marubutan Soyayya: Martani Ga Editan Gwaggwarmaya,’na 31/05/1993). kuma ta nuna wa Editan cewar bai yi wa marubutan adalci ba.

    Sai wata hira da Ɗanjuma Katsina ya yi da Ado Ahmed Gidan Dabino, ‘Ba Laifinmu Ba Ne!’  a fitowa ta 13 a shekarar 1993. inda shi Ado ɗin yake nuna cewa ba laifinsu ba ne, domin ko kafin su fara rubutun litattafansu ana aiwatar da wasu abubuwan assha a birnin Kanon.

    Shi dai Ɗanjuma Katsinan ya dawo da nasa raddi kan Hadiza Mohammed,‘Kafircewar Marubutan Soyayya: Raddin Editan Gwagwarmaya’, a fitowa ta 14 a shekarar 1993, yana mai nuna cewa ƙila ma ba wata Hadiza, wani ne ya yi amfani da sunan kawai domin a laɓe da guzuma a harbi karsana.

     Jaridar New Nigerian

    Da kuma aka sake rufe kamfanin jaridar Nasiha a karo na biyu a shekarar 1995 sai lamarin mahawara ya sake kwantawa. A daidai kuma wannan lokaci mujallun Rana da Gwagwarmaya sun watsar da batun, musamman ganin mujallar Gwagwarmaya ta yi laushi, shi kuma Ibrahim Sheme da ke a mujallar Rana, ya bar ta ya koma jaridar New Nigeria, sai mahawarar ta canza salo.

    Shehu Gambo ne ya soma da yin nasa sharhin, ‘A Harmful Love’,  a ranar 21-02-1997, yana yin kira ga iyayen ƙasa da su tashi tsaye domin yin yaƙi da wannan salon rubutun soyayya da ke lalata matasa.

    A dai wannan fitowar ta wannan Jarida 21-02-97, wani Ibrahim Musa ya shigo da tasa shawarar cewa a samu hukumar da za ta riƙa tace waɗannan litattafai, a cikin sharhinsa na ‘Censoring The Romantics’. Duk da cewa ya nuna bai damu da karanta waɗannan litattafan ba, amma ya nemi da a rinƙa tsarkake su domin ya siffanta su da ciwon daji.

    Ana cikin haka sai ga rubutun wani Bature mai bincike Brian Larkin, shi ma ya shigo da bayanin sabon yanayi na yin finafinan Hausa da rubuce-rubuce na zamani wanda aka buga a jaridar New Nigeria ranar 21-26/02/97 mai taken ‘Modern Lovers: Indian Films, Hausa Drama And Love Novels Among Hausa Youth.’  Wannan rubutu ba wai domin mahawarar ya shigo ba, domin kuwa maƙala ce da Brian ya fara gabatarwa a Amurka, sannan daga baya Sheme ya buga ta a wannan jaridar, domin nuna wa duniya halin da wannan salon rubuta ya shiga.

    Shi kuwa Maigari Ahmed Bichi ya yi nazarinsa ne kan wanda ya fara assasa wannan abu da ake ce da Adabin Kasuwar Kano, a nasa sharhin, ‘Kano Market Literature:The Man Behind It” ranar 20-06-97. A nan yana mai ƙara nuna ra`ayinsa na goyon bayan Ado Gidan Dabino tare da nuna cewa shi fitacce ne.

    Haka kuma A`ishatu Haruna ta shigo ita ma a wannan ranar ta juma’a 20-06-97 da kalmomin yabo ga Ado Gidan Dabino, ta ce ‘The Hausa Writer Who Never Went To School,’ tare da nuna cewar shi ƙwararren marubuci ne, wanda bai taɓa halartar wata makaranta ba.

    A dai wannan rana ta 20-06-97, Yusuf Adamu ya shigo da nasa ra’ayin ne, ‘Hausa Writer And Writing Today’,  ta yin fashin baƙi dangane da matsayin rubutun soyayya, inda ya yi tambihin samuwar ƙagaggun labaran Hausa. Shi ma dai maƙala ce da ya gabatar aka buga domin jan hankali kan wannan maharawa.

    A cikin wannan bugun dai aka kawo ra’ayin Ibrahim Malumfashi  kan ‘The Hausa Writer And The Reading Culture’, a nan ya fito ne yana bayanin samuwar karatu da rubutu a ƙasar Hausa, har zuwa yadda rubutun Adabin Kasuwar Kano ya samu dawwama, kuma nan ne Malumfashi ya ƙara jaddada matsayin shi kan Adabin Kasuwa Kano, bayan wanda ya fara nunawa a jaridar Nasiha can baya.

    Daga nan kuma Ibrahim Sheme ya sake tsokano manazarta a ranar 25-06-97 da nasa sharhi, ‘Much Ado About Soyayya Writers’ yana yin bayanin irin Muhawarorin da ake ta fafatawa, musamman a kan Ado Gidan Dabino.

    Shi kuwa Ɗanjuma Katsina nuni ya sake yi a cikin sharhinsa na ranar 05-09-97, ‘Hausa Writers: The Good The Bad And The Ugly; inda  yake cewa a cikin marubuta litattafan nan akwai masu kyau akwai marasa kyau, sannan akwai kuma waɗanda muninsu ya ƙazanta, domin kuwa yana nuna cewa wasu marubutan ba su lura da ƙa’idojin rubuta, kuma jigon nasu ma ya bambanta.

    Daga baya kuma Ɗanjuma Katsina ya dawo a ranar 19-12-97, yana yabon wata hira da Ibrahim Sheme ya fassaro wadda aka yi da Abubakar Imam, ‘Lessons From The Abubakar Imam Interview’, tare da fiddo wasu darussa da yake ganin ana iya kwaikwayo daga hirar.

    Jaridar New Nigerian Weekly

    Da kuma hukumar gidan jaridar New Nigerian ta samar da jaridar New Nigerian Weekly da take fitowa kowace ranar asabar, ta naɗa Ibrahim Sheme Mataimakin Edita, sai shafukan adabi da ke fitowa ranar juma’a suka koma cikin wannan jarida. Saboda haka sai muhawarar Adabin Kasuwar Kanon ta koma cikin wannan sabuwar jarida.

    A wannan karon Ɗanjuma Katsina ne cikin jaridar NNW ta ranar 28/02/1998 mai taken ‘Hausa Literature: Why Novian Whitsitt Couldn`t Get It Right’, inda ya yi kaca-kaca da wani bincike wanda wani Bature ya gudanar domin samun takardar shaidar kammala digiri na biyu a Amurka kan wata marubuciya Balaraba Ramat da sauran mata marubuta na Hausa.

    Shi Novian Whitsitt ya yi magana kan ƙagaggun labaran Hausa da addinin Musulunci. Ɗanjuma ya nuna rashin jin daɗinsa na yadda wannan bature ya gudanar da bincikensa, ya kuma nuna cewa da wannan manazarci ya tuntuɓi manyan malaman Musulunci sun ba shi ƙarin haske kan ‘yancin mata a Musulunci da aikin ya yi kyau. A taƙaice dai Ɗanjuma ya yi wa aikin wannan Bature jina-jina.

    Mako biyu bayan wannan hukunci na Ɗanjuma wato ranar 14/03/1998 sai ga Baturen ya fito fili yana kare kansa da nasa sharhin ‘Hausa Literature: Why Ɗanjuma Failed To Get It Rigtht’, inda ya nuna cewa ai Ɗanjuma ma bai fahimci abin da yake nufi ba a bincikensa da ya gudanar shi ya sa ya yi masa mummunan fassara.

    A wannan fitowar dai ta ranar 14-03-98, wani mai take wa Baturen  baya ne  ya yi nasa bayanin mai taken ‘..And Why Whitsitt Should Have It As Such’ don ya ƙara nuna wa Ɗanjuma abin da ya sanya ubangidan nasa ya yi aikinsa haka, kuma ya ma nuna cewa lallai wannan takalar faɗan ta Ɗanjuma na da gangan ne, har yake nuna cewa ai Whitsitt ɗin bai ma gama bincikensa ba, ko kuma yanzu ya fara.

    Daga wannan lokaci ne Ibrahim Malumfashi ya sake shigowa fage da sharhinsa ‘Kano Market Literature: A Love Story’, kodayake ba da sharhin muhawara ba a ranar 14-03-98, inda yake bayanin sabon salon rubutun adabin da ya bayyana a baya, tare da bayanin cewa ai marubutan ma ba su da wani zurfin ilimi. Maƙala ce da ya taɓa gabatar wa a  jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, daga baya aka buga ta a jaridar.

    Shi kuwa Yusuf Adamu ya zo da nasa bayanin ne dangantakar da ke tsakanin birnin Kano da kafafen watsa labarai da kuma adabin al’umma, mai taken ‘Kano: The City, The Media And The Literature; a ranar 14-03-98 yana bayanin rashin jin daɗin dangantakar marubuta da `yan jarida a birnin Kano, ya nuna cewa lallai marubuta a jihar Kano ba su jin daɗin yadda ‘yan jarida ke ba da dama ana caccakarsu, amma su ba a ba su irin wannan damar.

    Hamisu Abdullahi Gumel ya yi nasa Sharhin Mai Taken ‘Of Hausa Novel And Moral Decadence’, a ranar 16-05-98, yana nuna cewa ai waɗannan litattafan soyayya na Hausa suna gurɓata al`adun Hausawa, ya yi kira ga hukuma da ko dai ta hana yin su, ko kuma ta tsaftace wannan harka, wato ta sanya a riƙa tace waɗannan litattafan.

    Haka dai Yusuf Adamu ya dawo ranar 6/06/98 domin kare gwarzon nasa litattafan soyayya, ‘Long Live The Hausa Novel’, kan sukar da Gumel ya yi masa, yana nuni da cewa lallai marubutan nan sun taka rawar gani, bai kamata a yi ta sukar su ba kai ba gindi ba.

    Yusuf Adamu ɗin dai ya dawo ranar 18-07-98 domin mai da raddi ga A`isha Umar Yusuf (wadda ta yi magana cikin jaridar Weekly Trust ta ran 19/07/98), mai taken ‘Hausa Novel: Beyond The Great Debate’ kan sukar da ta yi wa gwanin nasa, tare da nuna cewa lallai A’isha ba ta san wainar da ake toyawa a fagen ƙagaggun labaran Hausa ba, musamman da ta ce babu wanda ya san lokacin da aka fara wannan muhawarar.

    Ya nuna mata cewa ai Ibrahim Sheme shi ya buɗe wannan gumurzu a shekarar 1991, sannan ya ci  gaba da lissafo waɗanda suka kasance ƙashin bayan wannan muhawarar, kamar su Ibrahim Malumfashi da Ɗanjuma Katsina da ya shigo fagen a 1993, da shi kansa Yusuf Adamu da sauransu.

    A ranar 16-08-98 Ibrahim Sheme ya yi hira da Bilkisu Ahmed Funtuwa, wadda ita ce marubuciya mace da aka fara yin hira da ita kan wannan batu a jarida, inda ta yi bayanin ‘I Write To Enlighten Northern Women’, ta ƙara da cewa ita fa tana yin rubutu ne don ta fadakar, da kuma dalilan da suka sanya ta fara rubutu.

    Ɗanjuma Katsina ya dawo da zafafan kalamansa ranar 05-09-98 domin mai da wa Yusuf Adamu raddi, inda har yake cewa ‘Death To The Soyayya Novel’, inda yake cewa iyaye sun gwammace su sayi litattafan addini fiye da irin waɗanda ake rubutawa. Ya ce su a Al-mizan sun yi bincken da ya nuna cewa mutane sun fi son su sayi litattafan addini da su sayi litattafan soyayya da ake ta samarwa.

    Bayan kamar wata ɗaya, wato ranar 17-10-98 sai ga Ɗanjuma ya sake shigowa sahu, da ‘The Best Hausa Books’. Ɗanjuma Katsina ya fito da wasu litattafai na Hausa ne da yake ganin sun fi saura ƙima, wato kamar ya yi amai ya lashe ke nan!

    Bayan wani lokaci, wato ranar 19-12-98 sai ga Mansur Ahmed ya zo domin nuna goyon bayansa ga Ɗanjuma Katsina da nasa sharhi ‘Re-The Best Hausa Books’. Daga wannan lokaci ne Abdallah Uba Adamu ya biyo layi da nasa sharhin a ranar 1-05-99, ‘Hausa Literature In The 1990’s’, inda ya nuna goyon bayansa ga littattafan soyayya.

    A nan dai ya yi sharhi mai tsawo kan waɗannan litattafai da kuma muhimmancinsu a cikin al’umma. Wannan shi ne ya buɗe fage na biyu na taƙaddama kan waɗannan littattafai tsakaninsa da Ibrahim Malumfashi domin a ranar 15/05/99 sai ga Ibrahim Malumfashi da  nasa martani ga Abdallah, ‘Beyond The Market Criticism’ inda yake cewar Abdallah na nunin al’ummar Hausawa daga shekarun 1991-1998 suna cikin soyayya ne kurum. Sannan kuma yana ta nuna cewar waɗannan litattafan da wuya su yi tsawon rai.

    Abdul`aziz Malumfashi ma ya yi nasa sharhin ‘Babinlata: A Writer With A Difference,’  a ranar 22/05/99 da kalamai na yabo da koɗawa ga Bala Anas Babinlata, da nuna cewa aikin Babinlata ɗin ya sha bamban da sauran marubuta.

    Ibrahim Sheme wanda shi ne mai raba faɗa a da, sai ga shi ya shigo ranar 05-06-99 don mai da wa Ibrahim Malumfashi da martani mai taken ‘Of Market Forces And Hausa Novels’ inda ya nuna ƙin yarda da abin da ya faɗa, tare da nuna cewa ko da wannan salon adabin yake baƙo a al’ummar Hausa, amma dai akwai barbaɗinsa, sannan kuma ya nuna cewar ko ba komi waɗannan marubutan sun adana wasu daga cikin al’adun Hausawa.

    Abdallah Uba Adamu shi ma ya dawo ranar 12-06-99 don yin martani ga Ibrahim Malumfashi, ‘Idols Of The Market Place’, inda yake nuna ai waɗannan marubuta sun taka rawar gani, domin ko ba komi wasu daga cikinsu irin su Zinaru na Bala Anas, sun taɓo matsalolin yau da kullum fiye da yadda Shehu Umar ma ya nuna.

    Ibrahim Malumfashi ya dawo domin kare zarge-zarge da dama da aka yi masa a ranar (10-07-99) da nasa martani mai taken, ‘Dancing Naked in the Market Place’, kuma ya ma nuna cewa ai yawancin marubutan ma tamkar suna yin rawa zindir ne a kasuwa, domin kuwa suna kwaso kayan aikin wasu ne don su gina nasu.

    Ranar 25-09-99 sai ga Mohammed Ɗantala Aliyu ya shigo domin nuna takaicinsa da nasa  sharhi, ‘Why Some Academicians Hate The Soyayya Novel’ ya nuna yadda wasu malaman Jami`a irin su Abdallah suke goyon bayan wannan adabi na Kasuwar Kano, tare da nuna rashin jin daɗinsa da Malumfashi ya bar tofa albarkacin bakinsa, ya kuma nuna cewar to idan malaman jami’a kamar su Malumfashi ba su yaƙi wannan adabin ba ya za a gyara.

    Habeeb Idris Pindiga ya shigo yana mai da martani ga Ɗantala a ranar 23-10-99, yana cewa ‘Soyayya Novels Are The Real Hausa Literature’, yana nuna cewa ai waɗannan ayyukan na Adabin Kasuwar Kano su ne mafi dacewar aikin adabi a ƙasar Hausa, ya kuma tambaye shi waɗanne litattafan adabin ne masu inganci, shin fassarar da Garba Funtuwa ya yi, ko kuwa labarin ta’addanci na Bature Gagare da sauransu.

    Ga alama wannan karon taron dangi aka yi wa Ɗantala, domin kuwa kwatsam sai ga Abdallah shi ma ya dawo ranar 01/11/99 domin mai da martani ga Ɗantala, ‘Emotions In motion: Sleaze, Salacity, Moral Codes And Hausa Literature’, yana mai nuna cewa in har ana son gyara rubutun soyayya, sai al`umma sun fara gyara kansu.

    Ibrahim Sheme ya kuma bayyana nasa ra’ayi ranar 21-07-2001 kan wani biki da Ibrahim Malumfashi ya yi kan shekaru ishirin bayan rasuwar Abubakar Imam, ‘Imam: Beyond Nostalgia’ inda ya kawo wasu marubutan kamar su Bature Gagare da Sulaiman Ibrahim Katsina da sauransu da ya ce sun kamo Imam. Sannan ya nuna cewa shekaru ishirin bayan rasuwar Abubakar Imam babu wani ƙoƙari da aka yi domin tallafa wa ƙananan marubuta.

    Sumaila Umaisha, wanda ya gaji Sheme a matsayin editan shafin adabi a jaridar ya yi hira da Ado Gidan Dabino, ‘The Making Of The King Of Soyayya’, inda har yake nuna cewa shi sukar da ake masa ba ta canza shi, sai dai ta ƙara masa ƙwarin gwiwa, sannan kuma ya taɓo harkar fim da ta fara canza akalar marubuta.

    Jaridar Weekly Trust

    Duk da cewa mun ga yadda aka gwabza a cikin jaridar New Nigerian, to ba nan kaɗai abin ya tsaya ba, mun ga yadda akalar muhawarar ta koma cikin jaridar Weekly Trust, ita ma ɗin dai da taimakon Ibrahim Sheme wanda ya koma can yana aiki, kuma yana kula da shafin adabi.

    A wannan karon Hajiya A`isha Umar Yusuf ce ta shigo fagen, da ‘The Great Soyayya Debate’, wanda kamar yadda muka gani a bayanin da muka yi kan jaridar New Nigerian Weekly, wasu sun maida mata martani kan abin da ta faɗa. Ita dai Hajiyar ta yi nata sharhin ne ranar 19/06/1998, kuma duk da cewa litattafai 10 kawai ta karanta, ta fito tana mai nuna rashin goyon bayanta ga litattafan saboda yadda suke kwaso aikinsu daga ayyukan Turawa.

    Ta kuma yi kiran da a samar da hukumar da za ta rinƙa tace waɗannan litattafan tun da wuri, kafin a zo a yi da na sani. Rubutun kamar yadda muka gani a sama shi ne ya jawo  raddi daga Yusuf Adamu cikin jaridar NNW, ‘Hausa Novels: Beyond The Great Debate’ ta ran 18/07/1998.

    Shi ma Ibrahim Malumfashi ya mai da martani ga Abdallah, ‘Beyond The Market Criticism,’ duk da cewa ya aika wa jaridar New Nigerian Weekly ‘Beyond The Market Criticism,’ ranar 15/05/99).

    Aliyu Tilde shi ma ya shigo domin bayyana fahimtarsa kan Adabin Kasuwar Kano yana mai nuna cewa ba su da wani ingancin aiki, kuma ba ingancin bugu a cikin ‘Prudence And The Contemporary Hausa Novel’ da aka buga a ranar (06-08-99).

    Shi kuma Adamu Mohammed Nababa ya shigo domin neman daidaito tsakanin marubutan da nuna cewa duk da cewa ba a samu wani marubuci kamar Abubakar Imam ba, to ana fa iya samu, a nasa sharhin ‘A Dialogue With A Deaf,’ da aka buga ranar  7-04-2000).

    Daga nan kuma Ibrahim Malumfashi ya dawo domin warware zare da abawa, musamman kan raddin da Ibrahim Sheme ya yi masa kan Imam. Ya fara da cewa yana girmama Sheme a fagen adabi na Ingilishi, amma ya ce yana mamakin yadda yake yin ruwa ya yi tsaki a na Hausa.

    Kuma daga ƙarshe yake fatan cewa waɗannan marubutan za su dawo wa adabin gaskiya da zaran Adabin Kasuwar Kano ya kau. Ya dai ba taken aikin nasa da take ‘Between The Classics And Sheme`s Diatribe,’ da aka buga a jaridar NNW ta ran 25-08-2001, da kuma Weekly Trust, 21-09-2001).

    Shi ma Ibrahim Sheme bai yi ƙasa a gwiwa ba, domin ya dawo domin nuna tasa fasahar, musamman kan dai Adabin Kasuwar Kanon, ya yi bayanin yadda adabi na duniya ya samu tun daga adabin Turanci da marubutan, har zuwa na Hausa a cikin abin da ya kira da ‘An agenda for Hausa writing,’ da aka buga a cikin NNW ta ran 06-10-2001 da kuma Weekly Trust ta ran, 26/10 da 1-11-2001).

    Jaridar Triumph

    Daga abin da muka gani a can baya za a ɗauka cewa dukkan hayaniyar da ta faru game da Adabin Kasuwar Kano ta soma ne daga jaridar Nasiha sai a ga cewa ba haka ba ne, domin kuwa an fara ne a cikin jaridar Triumph ta Kano. Sai dai shi wancan sharhin na Maigari Ahmed Bichi na ran 12 da 17 /03/1992 bai takalo ka-ce-na-ce ba shi ya sa, amma ana iya cewa ya soma taɓo batutuwan da suka zo daga baya suka yi tashe. Yadda ya shigo da yabo ga Ado Ahmed Gidan Dabino cikin sharhinsa mai taken The Author`s Imagination, cikin jaridar  ya ƙara nuna mana daga ina wannan hayaniya ta samo asali.

    Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo

    Haka kuma dai wannan muhawarar ta samu shiga cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, inda nan ma aka fafata a ranar 29/07/1993. Kuma da alama ko da ake yi a cikin Nasiha, jaridar Gaskiya ma ta kwashi nata rabon.

    Wani Muhammad Lauwali Ahmed shi ya somo sukar rubutun ranar alhamis 29/07/93, yana nuna cewa gara ma marubutan su koma rubutu kan Musulunci da sauran al’ammurran duniya a cikin ‘Marubutan Soyayya Ko Maɓarnata Al`umma?

    Sakamakon Muhawarori

    Waɗannan Muhawarori da masana da manazarta da makaranta da kuma ‘yan jarida suka yi ta tabkwa sun taimaka ƙwarai da gaske wajen fito da waɗannan littattafai ta fuskar yabo da kuma suka.

    Da dama wasu mutanen ba su san wainar da ake toyawa ba game da waɗannan litattafai, amma saboda muhawarar da ake tabkawa ko dai a cikin Jaridu da Mujallu, ko kuma a wurin taron ƙara wa juna sani da a wajen muhawara ya sanya suka san da hayaniyar da ake yi da kuma illa ko kuma taimakon da suke ba da wa ga al’ummar Hausawa.

    Misali a nan shi ne shahararren mai yin sharhin nan cikin Jaridu wato Dr. Aliyu Tilde (06-08-99) da shi ma sakamakon abinda yake gani ana tabka muhawara kan sa shi ma ya jefo nasa tunanin.

    Muna dai iya cewa waɗannan Muhawarori sun taimaka ƙwarai da gaske wajen fito da waɗannan littattafan ga sauran jama’a da ba su san wainar da ake toyawa ba .

    Naɗewa

    A wannan babin an dubi irin zangunan da Adabin Kasuwar Kano ya kutso a ƙasar Hausa, da kuma irin rawar da ya taka wajen ginuwar wani ɓangare na ƙagaggun labaran Hausa, kama daga rayuwar farko da ta wanzu tsakanin shekarun 1984-1989 wanda wannan ne kusan zangon farko da ya samar da littattafan Adabin Kasuwar Kano, da kuma waɗanda suka taka rawa wajen samar da bunƙasa shi.

    Sai kuma zango na biyo wanda ya fara daga 1990 zuwa 1995 wato lokacin da wannan adabi ya bunƙasa tare da shigowar wasu marubuta da suka ƙara inganta wannan zango. Daga wannan zango, sai wanda ya fara bayansa da ya samu daga shekarar 1996 zuwa 2001 wanda shi kuma ya zo da salon samar da ƙungiyoyin marubuta da na makaranta sannan a wannan zango ne dai saye da sayar da waɗannan littattafi ya ƙara samun tagomashi sosai da sosai.

    Zango na ƙarshe a wannan aikin ya fara ne daga 2002 zuwa 2008 wanda ya zo da nashi fasalin na samar da wasu marubutan da suke ganin sun canza wa zangon fasali musamman ganin cewa marubutan da suka shahara a baya wasu sun watsar da rubutun, wasu kuma sun kama wata sana’ar.

    An kuma kalli siffofin Adabin Kasuwar Kano da kuma saƙon da littattafan suke ɗauke da shi sannan kuma an nazarci Muhawarorin da aka yi ta tabkawa cikin Jaridu da Mujallu da ake ganin sun taka muhimmiyar rawa.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Domin karanta Siffofin Adabin Kasuwar Kano danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Siffofin Adabin Kasuwar Kano

    Siffofin Adabin Kasuwar Kano

    Da yake ana tariyar abin da ya wuce ne game da wannan fage na Adabin Kasuwar Kano, ta yaya za a iya gane aikin adabin da za a ce na Kasuwar Kano ne idan an gan shi, ko kuma waɗanne siffofi ne za a ce su ne na Adabin Kasuwar Kano? Amsar na da sauƙi ganin cewa an riga an yi shimfiɗa game da Adabin Kasuwa na bai ɗaya a cikin babi na uku.

    Saboda haka abin da aka yi a nan shi ne a fitar da kamannun da su ne za a iya gani a ce wannan na daga cikin siffofin Adabin Kasuwar Kano. Haka kuma yin hakan ya zo da sauƙi domin daga cikin siffofi na bai ɗaya da aka gani can baya game da adabin kasuwa da manazarta suka ayyana, an fahimci yana ɗauke da manyan siffofi guda huɗu:

    • Adabi ne da ke yin tashe a wani zamani daga baya ya kau.
    • Adabi ne da yake gudana tsakanin wasu gungun mutane kurum ba kowa da kowa ba.
    • Adabi ne na kasuwa ko na yayi.
    • Adabi ne da ake alaƙanta shi da wani wuri ko gari ko zamani ko yanayin da ya sami kansa.

    Idan muka dubi littatafan adabin da ake yi wa laƙabi da Adabin Kasuwar Kano kamar yadda muka zayyana a baya, za a ga cewa sun shiga cikin sahun adabin kasuwa kamar yadda suke zayyane a sama.

    Tun da farko wannan harka ta samo asali ne a wani ayyanannen lokaci, wato daga farkon shekarun 1980, musamman a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1984 ya zuwa farkon ƙarni na 21 inda daga lokacin ya fara salamcewa, domin harkar fim ta sha gabansa.

    Saboda haka shi ma kamar sauran ayyukan adabin kasuwa irinsa, ya samu wani lokacin da ya fara da kuma lokacin da ya girma, kuma zai kasance ya koma cikin taskar tarihi a cikin wani lokaci mai zuwa. A halin yanzu dai an samu sama da shekara 25 ana aiwatar da wannan tsari na adabin kasuwa a ƙasar Hausa.

    Haka kuma adabi ne na gungun matasa, ba na kowa da kowa ba, yawancin masu yin sa da karanta shi ba su wuce ‘yan shekara 18 zuwa 35 ba. Idan aka dubi samuwar wannan fasalin rubutu daga 1983, marubuta biyu ne daga cikin 13 da ake da su, suka haye shekara 25, wato Balaraba Ramat da Ƙamarradeen Imam, saura duk ‘yan ƙasa da 25 ne.

    Sa’annan kuma adabi ne na ‘talakawa’, wato waɗanda suke da ƙaramin ƙarfi, ba dole sai masu kuɗi ko tajirai za su iya sayen sa ba, kamar yadda yake a gangariyar adabi. Da yake kuma adabin talakawa ne, shi kuma adabin talakawa yana zuwa da nasa siffofin na daban; daga ciki  zai kasance mai sauƙin karantawa, wato mai jimloli marasa sarƙaƙiya.

    Haka kuma nahawunsu zai kasance sassauƙa, ba nannauya ba.  Ke nan wannan adabin yakan kasance bai da yawan shafi, ma’ana, bai ɗaukar lokaci za a iya karance shi. Idan aka dubi nazarin da aka yi a sama za a ga cewa wannan fasali ya fito fili. Yawancin littattafan sun kasance masu sauƙin karantawa ga ɗan firamare ko sakandare, haka ma wanda ya yaƙi jahilci.

    Idan aka koma kan batun cewa adabin kasuwa ana alaƙanta shi da wani wuri ko zamani ko gari ko yanayi, za mu iya cewa lallai haka abin ya faru da Adabin Kasuwar Kano. Mun dai ga cewa zamanin Sarauniya Elizabeth ya haifar da Adabin Kasuwar Elizabeth a Ingila, na Kitsch ya haifar da Adabin Kasuwar Kitsch a Jamus, kasuwar Onitsha ta haifar da Adabin Kasuwar Onitsha a Nijeriya.

    Saboda haka sanya wa Adabin Kasuwar Kano sunan na kasuwar Kano ya danganta ne da ganin cewa Kano tana da fitacciyar kasuwa wadda daga ko ina ana zuwa cin wannan kasuwa. Kamar yadda kasuwar Onitsha ta yi fice a duk faɗin Afrika, ta yadda duk wani littafi da aka wallafa a wannan ɓangare za a iya samun shi a wannan kasuwa ya ba da damar a sa masa wannan suna.

    Ko da kuma aka gama cin kasuwar a ƙasar Inyamurai, a tsakanin shekarun 1947 zuwa 1969, kasuwar ta watse a 1975, sai aka yi wa wannan rayuwa da abin da ta haifar laƙabi da Adabin Kasuwar Onitsha (Okoro, 2002). Saboda haka ba sai an faɗa ba, tun da Kano birni ne na kasuwanci, sa wa adabin kasuwa laƙabin Kano, an yi shi ne da sani da kuma amincewar haka abin yake a tarihin adabin duniya.

    Kasuwanci dai a birnin Kano ya sami gindin zama sama da shekaru dubu da suka wuce. Birnin Kano ya kasance matattarar kasuwanci da daɗewa tsakanin ƙasashen Hausa, tun zamanin cinikin bayi. Saboda haka ko da waɗannan litattafai suka soma ɓuɓɓugowa daga Kano da Kaduna, Kano suka yada zango.

    Kuma daga shekarar 1984 da Talatu Wada ta fiddo littafinta, wanda shi ne ya yi wa wannan fasali mazaunin farko, Kano aka kawo shi domin sayarwa ga sassan duniya a can kuma ya samu karɓuwa sosai.  Daga wannan lokaci ne Kanawa da ke bin wannan sana’a suka shiga sayar da litattafan, suna sarar duk wani littafi da ya fito, su dinga biyan marubuta a hankali.

    Wasu masu sayar da litattafan suka shiga buga litattafan da kansu, wato su bayyana wa marubuci irin labarin da suke so a rubuta, su kuma sa kuɗi su buga, su rarrabar, su sami riba, (Adamu, 1998 da 2002).

    Shafuka

    Rashin yawan shafuka kamar yadda bincike ya nuna bai rasa nasaba da dalilai da dama. Na farko, tunanin yawancin marubutan irin waɗannan littattafai bai cika cokali ba, don haka ko sun tashi yin tunani mai zurfi don su tsawaita labarin, sai ka ga zaren ya tsinke, sun ƙuge ga shafuka 40 zuwa 80.

    Daga baya ne dabarar tsinka labaran ta shigo ga marubutan, domin su ninka ribar da suke samu. Wannan shi ya haifar da littafi na ɗaya da na biyu, ko uku, ko ma fiye, kamar yadda aka sami irin wannan siffa a ayyukan adabin Onitsha.

    Ƙila abin da wani zai tambaya shi ne me ya sa littattafan za su kasance marasa yawan shafi? Kamar yadda bincike ya nuna, yawancin marubutan da suka yi tashe daga 1984 zuwa 1991, an fahimci cewa ba su yi zurfi a ilmin zamani ba. Alal misali Ado Gidan Dabino, bai yi karatun zamanin ba, makarantar dare ya yi, daga baya ne ya wuce zuwa ƙaro ilimi, shi ma bayan ya zama wani abu a cikin fagen rubuta irin waɗannan littattafai.

    Su kuwa sauran matan da suka shahara a wannan fage ba su wuce karatun firamare da sakandare ba, irin su Zuwaira Isa da Bilkisu Ahmed Funtua, sun isa misali. Wasu kuma sun yi tishin karatun ne bayan sun yi shekaru da gama firamare, har an yi musu aure, suka koma fagen rubutun.

    Irin su Zuwaira Machika, sun zama misali. Saboda haka duk yadda irin waɗannan marubuta ke son su tsawaita littatafan, sai a ga abin ya faskara. Sa’annan kuma uwa-uba, siffar irin waɗannan littatafai ke nan, ba a yi su domin yawan shafuka ba.

    Yanayin Bugu

    Duk adabin da bai da wani kamfani takamaimai ko wurin ɗab’i da hukuma ta san da shi, ko kuma bai bin tsari da doka na ɗab`i kamar yadda aka tanada, to wannan adabi, na kasuwa ne. Duk wani adabi da ba a san shi a manhajar karatu ta firamare ko sakandire ko wani mataki na karatu daban da waɗannan ba, ko kuma ya bi tsarin shigar da shi cikin manhajar ba, wato ta bin doka, to wannan adabi na kasuwa ne.

    Idan haka ne to da wuya irin waɗannan littattafai su kasance ba na kasuwa ba. Wannan ya zama haka ne ganin cewa ana buga su ne a bakin titi ko wurin buga littattafai da ke maƙare a cikin kasuwa. Haka kuma ba sa shiga cikin manhajar karatu kamar yadda hukuma ta tsara domin da ma ba gangariyar ba ne.

    Idan har aka ga ana karanta su a sakandare ko jami’a to wani shiri ne tsakanin marubutan da malamai, ba wai hukumomin makarantun sun san da shirin ba.  Ba wannan ba ma, hatta waɗanda ke wallafa littattafan ba suna wallafa su ne domin su yi ƙarƙo ne ba, a dai buga da takarda mafi sauƙi, da bango mafi arha, a kuma injuna marasa caji da tsada.

    Domin fahimtar wannan siffa sosai, ya dace a gane cewa takarda kala biyu ce ake amfani da ita wajen wallafa ire-iren waɗannan littattafai; akwai news print da kuma bond. Ita newsprint  tun asali ita ce ake amfani da ita, domin ta fi arha. A daidai lokacin da aka soma wannan harka, da naira ɗari biyar zuwa dubu ɗaya za a iya sayen takardar da za a buga kwafe dubu zuwa dubu biyu, Saboda haka duk tsadar littafin bai wuce naira 5 zuwa 10 daga haihuwa zuwa ƙuruciya, a kuma samu sami riba in an sayar.

    Hatta bangon littafin ba da takardar ƙwarai ake buga shi ba, saboda a rage tsadarsa. Baya ga wannan masu bugawar ba su da kayan aiki na ƙwarai da suka haɗa da injuna da tawada da makamantan su. Ke nan duk wani littafin da ya sami kan sa a cikin irin wannan hali, to za a ga bugun zai kasance ba na ƙwarai ne ba, kamar dai yadda muka ga haka game da littattafan Grub Street  a ƙasar Ingila da Kitsch a Jamus.

    Saƙo Ko Jigo

    Saƙon da litattafan Adabin Kasuwar Kano ke isar wa a fili suke, domin kamar yadda (Adamu, 2006:150) ke cewa, kusan marubuta na farkon-farkon, wato irin su Talatu Wada Ahmed mai (Rabin Raina) da sauran su, soyayya ce suka tanada a cikin littattafan nasu, ba don komi ba sai don su ne ke shere masu karatu.

    Shi ya sa Adamu (2006:138) yake nuni da cewa kusan tun daga bangon litattafan za a fahimci jigonsu, saboda daga bangayen, jigon zai bayyana cewa waɗannan litattafai na soyayya ne, domin ba abin da za ka gani daga ‘In Da So Da Ƙauna’, sai ‘Dace Da Masoyi’, sai ‘Kwabon Masoyi’, sai ‘So Tsunstu’, sai ‘Ruwan Soyayyar Zuciya’, sai ‘Kibiyar Soyayya’ da dai sauransu da dama masu ɗauke da irin waɗannan sunayen.

    Da tafiya ta yi tafiya sai aka fara samun wasu masu magana kan auren  da yanayin auren Hausawa da matsalolin da ke tattare da su. Ya zuwa shekarar 2002 zuwa 2008 sai ya kasance saƙonnin ko jigogin  litattafan sun canza fasali gaba ɗaya, domin kuwa sama da kashi casa`in da takwas na litattafan sai suka koma ba su maganar komai sai labaran soyayya, kamar dai yadda suka faro daga farko.

    Sannan kuma daga abin da masu karatu suka faɗa game da saƙonni ko jigogin littattafan sai aka fahimci cewa soyayya da rayuwar zaman aure su suka fi tashe, sai kuma zamantakewar yau da kullum (Bashir, 2009:202). Sai dai domin a fidda wannan fasali fili, ya dace mu nazarci saƙonni ko jigogin waɗannan littattafai sosai.

    Tuni dai (Adamu, 2006:150) ya taɓa gudanar da makamancin wannan aiki, sai dai littattafan da ya nazarta ba su wuce 453 ba. Wannan nazari ya ɗora bisa wancan, an samu ganin  cewa saƙonnin da ke cikin litattafai sama da 712 da aka yi nazari sun kasance mabambanta, duk da haka dai jigon soyayya shi ne kan gaba. Ga yadda jadawalin ya kasance.

    JIGO ADADIN LITATTAFAI
    Soyayya 250
    Rayuwar Aure 62
    Zamantakewa 164
    Rikici 30
    Kishi 27
    Yaudara 25
    Biyayyar Iyaye 12
    Ban Dariya 8
    Siyasa 12
    Haƙuri 20
    Waɗanda Ba A Tantance Ba 102

    Kamar yadda Adamu (2006) ya nuna daga nasa binciken kimanin kashi 35 ne kaɗai suke da jigon Soyayya, sauran kashi 65 kuwa suna magana ne kan wasu jigogin na daban, amma duk da haka wai manazarta na ta sukar marubutan, da cewa sun ta’allaƙa ne kan jigon soyayya.

    Amma daga nawa binciken, ana iya ganin cewa kaso mafi tsoka daga cikin littatafan da aka nazarta kusan 712 na soyayya sama da 250 ne, sai sauran jigogin da marubutan sukan taɓo.

    Daga binciken da aka gudanar sauran jigogin da waɗannan marubutan sukan taɓo sun haɗa da Rayuwar aure (misali, Matsalar Mu Ce na Fauziyya D. Sulaiman,) da Kishi, (misali, Baƙin Kishi na Muhammad Lawan Barista) da Yaudara, (misali, Mayaudariya na Abubakar Umar Mani) da Rayuwar Duniya, (misali, Zaman Farko na Ibrahim Birniwa) da Haƙuri, (misali, Mahaƙurci, na Sa’adatu Saminu Kankiya) da Ban Dariya, (misali, Namijin Kunama na Balarabe Abdullahi Yola) da Biyayyar Iyaye, (misali , Tsakanin Ɗa da Mahaifi na Sanusi Hashim,) da Rikici, (misali, Sadauki Diknar na Abdulƙadir Mu’azu Isa,) da Tsaro, (misali, An Yanka Ta Tashi na Bala Anas Babinlata da dai sauransu.

    Su ma idan aka yi musu nazarin ƙwaƙƙwafi za a ga cewa wasu daga cikinsu na soyayyar ne kodayake ba kai tsaye ba, amma dai suna da alaƙa da soyayyar, musamman waɗanda suka shafi rayuwar aure da kishi da makamantan su.

    Bincike ya nuna cewa an samu waɗannan canje-canjen ne dangane da fasalce-fasalcen waɗannan littattafai da muke magana a kai daga mabambanta dalilai. A cikin shekara bakwai da fara wannan harkar adabi, wato lokacin da shekarar 1991 ke ƙaratowa, abubuwan sun bunƙasa sosai a wannan fage.

    Wannan sabon salon rubutu ya cika da batsewa, ya kuma fantsama a ko ina a ƙasar Hausa, musamman wurin mata da matasa. Haka kuma ya kasance rubutun ya tashi daga ƙagawa da aka fara gani a rubucen-rubucen farko, sai ya koma kwashewa ko gamaɗe. Marubuta littattafan sai suka koma kwaso kayan cikin adabin daga fina-finan Indiya da majigin Turawa da Larabawa da kuma litattafan soyayyar Turawa suna mayar da su nasu.

    Daga shekarar 1991, lokacin da su Ado Gidan Dabino suka yi ruwa, suka yi tsaki, harkar buga litattafan ta koma tamkar kamfani, ƙungiyoyi daban-daban suka shiga ɓullowa, tare da shugabanni da mambobi da kuma masu tallata litattafan da suke wallafawa. Wannan kamar yadda muka yi bayani a baya ya taimaka sosai wajen tabbatuwar wannan harka, wanda ya sa aka samar da litattafai sama da 1,860 zuwa shekarar 2007 (Furniss, 2007).

    Bayan samun gindin zama da Adabin Kasuwar Kano ya yi, har ta kai ga sun kakkafa ƙungiyoyi domin tafiyar da harkokin rubuce-rubucensu, sai kuma sauran jama`ar gari suka bi sahu. Manazarta da `yan jarida da kuma sauran mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu kan yanaye-yanayen wannan adabi. Wasu suke yabawa, yayin da wasu kuma sun nuna irin yadda rubuce-rubucen suka dagule, musamman idan aka haɗa su da gangariyar aikin adabi da suka gabata.

    Da dama mutane sun nuna rashin jin daɗinsu na yadda batsa da mugayen kalamai suka fara gurɓata al`adun Hausawa daga cikin rubuce-rubucen Adabin Kasuwar Kano. Su kuma marubutan a koyaushe ƙoƙarin kare kansu suke yi daga zarge-zargen da ake masu. Sukan nuna cewa jigon soyayya da suka ɗauka don gina ayyukansu, suna yi ne saboda ya dace da zamani ne.

    Wannaan ya sanya a lokacin idan mutum ya duba kasuwannin litattafai na Hausa ba abin da zai tsinkaya sai dalar litattafai daban-daban na soyayya, irinsu; In Da Rai ko Rabin Raina ko Budurwar Zuciya ko Furen Soyayya ko Idan So Cuta Ne. Akwai kuma irin su Garin Masoyi da Marurun Soyayya da So Marurun Zuciya da Duniya Bautar Mata da sauransu dai da dama.

    Masu Sayarwa

    Kamar kowane irin tsarin adabin kasuwa, Adabin Kasuwar Kano ya zo da nasa fasalin sayar da littattafan. Sai dai shi ma kamar sauran ana sayar da littatafan ne a manyan kasuwannin ƙasar Hausa da suka haɗa da Kano da Kaduna da Jos da Sakkwato da Zaria da Gusau da Gombe da Bauchi da Minna da Katsina da  sauransu da dama.

    Waɗanda suka taimaka a wannan fage kamar yadda Adamu (2002) ya bayyana su ne dillalai ko masu bugawa da sayarwa a kasuwannin Kano da sauran sassan ƙasar Hausa, musamman da yake a wancan lokaci ba wani shago da ake da shi da ke tallata littatafan Hausa kurum. A birnin Kano, inda nan ne harkar ta zaunu sosai akwai irin su Alhaji Baba, mai Jakara City Bookshop  da Alhaji Musa Ɗanbala,  mai Sauƙi Bookshop  da Alhaji Garba Mohammed, mai Garba Mohammed Bookshop.

    Da farko dai waɗannan shaguna suna dillancin littatafan ne da masu rubutawa ke kawo musu su sayar, amma daga baya sai suka koma masu wallafawa da bugawa su da kansu. Za su sayi littafi hannun mai shi ko kuma su sayi wanda ba a buga ba, su su buga suna sayarwa. Daga nan Kano harkar ta koma sauran biranen, su ma da manyan dillalansu da suka haɗa da irin su Alhaji Abdullah a kasuwar Sakkwato da kuma shagunan littattafai irin su Anti Bilki Bookshop a Funtua da makamantansu da dama.

    Haka wannan harkar ta ci gaba da wanzuwa har ta kai an samar da shaguna da suke ba sayarwa kurum suke yi ba suna bayar da hayar waɗannan littatafai ga waɗanda ba su da ƙarfin sayen littattafan ko kuma ba su son su tara su jibgi a gida.

    Masu Karatu

    Masu karatun waɗannan litattafan kamar yadda muka gani a can baya mafi yawa matasa ne. Sai dai domin mu fahimci inda aka fito dangane da wannan ɓangare na bincike, na ga ya dace a bi diddigin game tunanin masu karanta waɗannan littatafai. Hanyar da aka bi domin yin haka, ita ce ta rarraba takardun neman bayanai domin a ji daga bakin masu karatu game da abubuwa da dama da suka shafi wannan harka.

    Daga cikin takardun neman bayanai sama da 400 da aka rarraba a sassan garuruwan ƙasar Hausa, kamar Katsina da Kano da Kaduna da Sakkwato da Zariya da Gombe da Dutse da kuma Bauchi, an samu guda 350 da suka dawo hannu. An yi amfani da waɗannan takardun bayanai domin gane matsayin makaranta waɗannan littattafai. Ga dai fasalin rabe-raben takardun neman bayanin da aka samu.

    Jadawali Na Farko: Bayanai Dangane Da Shekaru

    Shekara Waɗanda suka maido Adadi
    1-20 40 Kashi 2
    21-40 287 Kashi 97
    41-60 23 Kashi 1
    Jimilla 350 Kashi 100

    Kamar yadda muka gani a sama, mafi yawan masu karanta waɗannan litattafan da suka amsa tambayoyin neman bayani shekarunsu sun kama daga shekara 21 zuwa shekara 40. Sai kashi ɗaya waɗanda shekarunsu suka kama daga shekara 41 zuwa shekara 60. sai sauran da shekarunsu ya kama daga 1 zuwa ashirin.

    Jadawali Na Biyu: Bayanai Dangane Da Addini

    Addini Waɗanda suka maido Adadi
    Musulunci 350 Kashi 100
    Kiristanci 0 0
    Jimilla 350 Kashi 100

    Haka kuma an dubi addinan waɗanda suka maido bayanan daga waɗanda suke karanta waɗannan litattafan. Su kuma kashi 100 cikin ɗari dukkan su musulmi ne. Wannan shi ma bai zama abin mamaki ba, musamman ganin cewa yawancin garuruwan da aka rarraba takardun na musulmi ne.

    Jadawali Na Uku: Bayanai Dangane Da Ƙabila

    Ƙabila Waɗanda suka maido Adadi
    Hausa/ fulani 350 Kashi 100
    Sauran Ƙabilu Kashi 0
    Jimilla 350 Kashi 100

    Daga takardun da muka samu karɓa na neman bayanai mun fahimci cewa mafi yawan waɗanda suka yi mana bayanan Hausawa da Fulani ne, domin kamar yadda ya zo a teburi na uku, kashi ɗari na daga masu karanta litattafan Hausawa da Fulanin ne. Wannan ko bai rasa nasaba da cewa Hausawa da Fulani ke zaune inda aka rarraba waɗannan takardun neman bayanai.

    Sannnan kamar yadda ya zo a teburi na huɗu a ƙasa, mai nuna matakin ilimin waɗanda suka amsa tambayoyin namu, mun ga cewa matakin ilminsu bai yi zurfi ba, domin sun kama daga matakin sakandare, mai kashi 27 cikin 100 ne, zuwa matakin karatun difloma ko NCE, ko kuma wata babbar shedar karatu, masu kashi 70 cikin 100. Sai dai akwai waɗanda suka yi digiri masu rabin kashi da kuma waɗanda suka yaƙi jahilci masu kashi ɗaya. Sai kuma masu ilmin addini kurum, masu kashi ɗaya su ma.

    Jadawali Na Huɗu: Bayanai Dangane Da Matakin Ilimi

    Matakin ilimi Waɗanda suka maido Adadi
    Ilimin addini 14 Rabin kashi
    Ilimin sakandire 120 Kashi 27.1
    N.c.e/difloma 148 Kashi 70
    Digiri 10 Rabin kashi
    Yaƙi da jahilci 58 Kashi 1
    Jimilla 350 Kashi 100

    Dangane da garuruwan da waɗanda suka amsa tambayoyin suka fito, wannan binciken ya nuna cewa Katsina (da kashi 40) da Kano (da kashi 34), nan ne aka samu yawancin amsar tambayoyin bayanan da aka nema. Katsina dai ba abin mamaki ba ne, domin mai binciken a nan yake da zama, ke nan ana iya samun takardun neman bayanin da suka dawo masu yawa a nan. Kano dama can ake sayar da litattafan, saboda haka ba abin mamaki ba ne don an samu amsar tambayoyi da dama daga can. Haka akwai sauran sassan garuruwan da aka dawo da amsoshi kamar yadda yake a teburi na ƙasa.

    Jadawali Na Biyar: Bayanai Dangane Da Gari

    Gari Waɗanda suka maido Adadi
    Katsina 142 Kashi 40
    Kano 92 Kashi 34
    Gumel 2 Rabin kashi
    Sokoto 40 Kashi 10
    Bauci 2 Rabin kashi
    Gombe 2 Rabin kashi
    Zariya 25 Kashi 5
    Kaduna 45 Kashi 10
    Jimilla 350 100

     

    Jadawali Na Shida: Bayanai Dangane Da Jinsi

    Jinsi Waɗanda suka maido Adadi
    Namiji 112 Kashi 30
    Mace 178 Kashi 65
    Ba jinsi 60 Kashi 5
    Jimilla 350 Kashi 100

    Dangane da jinsin waɗanda suka mayar da takardu kuwa, daga binciken da aka gudanar a teburi na 6, ya nuna cewa kashi 65 daga cikin waɗanda suka mayar da bayanai mata ne, sai mai bi musu, maza, masu kashi 30. Akwai kuma waɗanda ba su bayyana jinsinsu ba.

    Jadawali Na Bakwai: Bayanai Dangane Da Sunan Adabin Kasuwar Kano

    Shekara Waɗanda suka maido Adadi
    1-20 20 Kashi 1
    21-40 320 Kashi 98
    41-60 10 Kashi 1
    Jimilla 350 Kashi 100%

    Daga binciken da aka yi sama da kashi 98 sun san da ana kiran waɗananan littattafan da littattafan soyayya ko kuma Adabin Kasuwar Kano, ƙalilan ne daga ciki ba su sani ba, su ma kuma ɗin daga abin da aka kalato, rashin sanin nasu ba ya rasa nasaba da cewar ko dai ba su mai da hankali ba ne ko kuma suna yin karatun ne ba tare da sanin ana kiran su da wani suna ba, face Hadisan Kano da suka ce suna jin ana kiran su da shi.

    Yawancin waɗanda suka san da sunan littattafan Littattafan Soyayya ko Adabin Kasuwar Kano, matasa ne masu shekara 21 zuwa 40 kamar yadda yake a teburin na bakwai. Mafi rinjaye daga masu karatun da suka san da waɗannan sunaye da ake kiran waɗannan littattafai da su  suna karanta littatafan domin. kusan kashi 70 na waɗanda aka nemi bayanansu, suna karanta litattafan musamman matasa, kamar yadda muka gani a teburi na uku.

    Sai dai wasu daga cikin waɗannan kashi ɗin suna ganin cewa sunan da ake kiran waɗannan littattafai da shi bai dace da shi ba. Kusan kamar kashi uku na daga wannan kason suna ganin bai dace a rinƙa kiransu da Adabin Kasuwar Kano ba, sai dai a kira su da litattafan soyayya ko kuma a canza masu wani suna daban.

    Jadawali Na Takwas: Bayanai Kan Inda Ake Sayen Litattafan

    Inda ake sayen litattafan Waɗanda suka maido Adadi
       Kasuwa 345 Kashi 99.9
    Kantunan saida litattafai 5 ½
    Jimilla 350 Kashi 100

    Sannan dangane da kuɗaɗen da ake sayen littattafan ma bayanai sun zo daidai, domin akasarin amsoshin da aka maido sun nuna kuɗin littattafan sun kama daga Naira 40 zuwa Naira 200.

    Dangane da maganar ba da hayar waɗannan littattafan, su ma ɗin kusan kaso 80 cikin 100 na waɗanda suka amsa tambayoyin sun tabbatar da cewa sun san ana ba da hayar waɗannan littattafai. Kashi kamar ishirin ne ba su sani ba, su ma ɗin wataƙila don sayen littattafan kawai suke yi, ba su mai da hankali ga lura da cewar ana ba da hayar ba.

    Jadawali Na Tara: Bayanai Dangane Da Ko Ana Ƙaruwa Da Karatun Litattafan.

    Sama da kashi 85 cikin 100 da suka amsa tambayoyin sun nuna ba su ƙaruwa da komai daga karanta waɗannan littattafan, suka ci gaba da cewar suna karanta litattfan ne kawai ko dai don rashin abin yi ne ko kuma don nishaɗi. Kaso kamar 15 cikin 100 su ne suka ce suna ƙaruwa da saƙonnin littattafan, kuma daga cikinsu mafi yawanci mata ne suka ce suna ƙaruwar da ko dai zaman aure ko kuma soyayya ko mallake miji da dai sauransu.

    Sannan kuma ko a maganar darussan da ke cikin litattafan maganar ba ta canza zane ba, saboda abin da aka zaƙulo, masu karatun sun nuna cewa sun fi sha’awar daga na soyayya, sai zamantakewar aure ko rayuwar jama’a da dai sauransu. Ga dai yadda fasalin yake a teburi na ƙasa.

    Ana ƙaruwa da karatun litattafan

     

    Waɗanda suka maido Adadi
             Eh 15 15
            A a 335 85
          Jimilla 350 Kashi 100

    Dangane da masu sana’ar ta ko dai rubuta litattafan ko kuma buga su, su ma babu abin da suke cewa da ya wuce sun shiga harkar ne don bunƙasa adabi, sai kuma don neman kuɗi. Wasu sun nuna cewar lallai harkar akwai riba, amma wasu sun nuna cewa babu wata riba sai dai a yi don bunƙasar adabin kawai. Haka kuma  kan maganar matsalolin da suke fuskanta wajen rubutun, maganar kuɗi ita ce gaba, sai kuma kayan aiki na ɗab’i da sauransu.

    Bayanai Dangane Da Sauran Tambayoyin Bincike

    Dangane da tambayar da aka yi na a kawo sunayen wasu daga cikin litattafan da aka karanta, mafi yawanci sun yi ƙoƙarin kawo waɗanda suka karanta ɗin na ainihi, wasu kuma suna haɗawa har da litattafai irin su Ruwan Bagaja da Shehu Umar da sauransu, wanda ya ƙara tabbatar da cewa ba duka suke iya bambancewa tsakanin abin da ake kira Adabin Kasuwa da gangariyar adabin ba.

    Sannan kuma bayanai sun nuna cewa kusan kashi 99.9 na daga cikin takardun da aka maido amsar kan inda ake sayen litattafan sun nuna cewa nan a kasuwa ne, domin kuwa abin da ake faɗa daga amsoshin yawanci suna nuna cewa daga kasuwa ko dai ta Kurmi a Kano, ko kuma ta Abubakar Rimi a Kanon, ko bakin Bata a Kanon, ko kuma Kasuwar Bacci a Kaduna ko kuma kasuwar `Yarkutungu a Katsina ko babbar kasuwar Sakkwato, a Sakkwato ko kuma shagunan sai da littattafai da finafinan Hausa a waɗannan garuruwan da aka gudanar da binciken.

    Kashi ƙalilan ne kawai suka ce sukan sayi wasu daga cikin littattafan a shagunan sai da litattafai na zamani. Amma fa a kula, ko su ɗin littattafan da sukan ce sun saya, suna daga cikin tsofaffin litattafn Hausa ne kamar su Ruwan Bagaja da Shehu Umar da Iliya Ɗanmaiƙarfi da sauran litattafan da suka fito a wancan zangon.

    Saboda haka daga abin da muka gani daga waɗanda suka amsa tambayoyin namu, kusan dukkan litattafan nan da ake wa laƙabi da litattafan Adabin Kasuwar Kano, ana sayen su ne a kasuwanni ko shagunan sai da finafinan Hausa da littattafan, kamar dai yadda ya zo a teburi na takwas.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Danna nan ka karanta Nazarin Rayuwar Adabin Kasuwar Kano

    Edita@rumasau-kallamu

  • Nazarin Rayuwar Adabin Kasuwar Kano

    Nazarin Rayuwar Adabin Kasuwar Kano

    Balaga: 1990 zuwa 1995

    Nazarin rayuwar Adabin Kasuwar Kano a zamanin da muka kira na balaga ya fito mana da siffofi mabambanta. Da farko dai lokaci ne da littattafan da suka samu wanzuwa daga shekarar 1984 suka samu karɓuwa tsakanin makaranta da masu buga littatafan da kuma masu sayar da su.

    A daidai wannan zamani ne na shekarar 1990 zuwa 1995 za a ce Adabin Kasuwar Kano ya shiga tashen balaga, marubutan da suka yi suna da karɓuwa a tsawon shekaru, suka bayyana. Cikin irin waɗannan marubuta akwai Ɗan Azumi Baba Cheɗiyar ‘Yan Gurasa, wanda ya wallafa littatafai guda 9 a cikin wannan tsakani da kuma Aminu Abdu Na’inna da ya fitar da littatafai guda 6.

    Akwai kuma irin su Ado Ahmad Gidan Dabino da Bala Anas Babinlata da Badamasi S. Burji da suka wallafa littattafai 4 kowanensu, haka kuma akwai marubuta irin su Balaraba Ramat da Yusuf Lawan Gwazaye da Alkhamees Bature da suka fitar da littattafai bibiyu kowane. Saura kuwa, irin su Ibrahim Mandawari da Ibrahim Sheme da Bashir Sanda, kowane ya fitar da littafi guda.

    A ɓangaren mata kuwa, a wannan lokaci ne aka sami fitowar manyan marubuta mata da suka yi tashe a cikin wannan harka da daɗewa, marubuta irin su Bilkisu A. Funtua da Hadiza S. Aliyu da Hawwa Aminu da Atika S. Sidi da suka antayo daga shekarar 1994.

    Abin la’akari dangane da wannan zamani na balaga shi ne, yawancin littattafan da aka samar daga cikin sama da 110 da aka wallafa a wannan tsakani sun fito ne daga taskar ƙungiyar Raina Kama da muka yi bayani a baya, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Ado Gidan Dabino.

    A daidai wannan lokaci za a fahimci cewa wanda ya fi tashe a cikin wannan ƙungiya shi ne Ɗan Azumi Baba, wanda ya fito da wani salo na labaran aljannu da dodanni da muridai, sai ko Ado Gidan Dabino da ya ɗauki fagen soyayy wanda kuma ya fi kowane daga cikin marubutan shahara saboda alaƙarsa da ‘yan jarida da suka yayata shi da kuma irin rawar da ya taka wajen tallata kansa da kuma ƙwazonsa wajen gina labari.

    Daga jadawalin marubutan da muka samu kai hannu kansu, mun fahimci nan ma maza suka fi shahara a fagen rubutun domin kuwa mata 12 ne suka tusgo, alhali maza 60 suka wallafa littattafai a wannan zango na Adabin Kasuwar Kanon (Dubi rataye na 8.0)

    Tsufa Da Hayayyafa: 1996 zuwa 2001

    Daga lokacin da kasuwar littatafan Adabin Kasuwar Kano ta yi tashin gwauron zabbi daga shekarar 1995  zuwa 1996 amon wannan sabon tsarin rubutu ba inda bai kai ba, wannan ne ya sa harkar ta koma irin ta wani babban kamfani. Ƙungiyoyin marubuta da suka ɓullo daga shekarar  1990  kamar su Kungiyar Matasa Marubuta da Kukan Kurciya da Raina Kama  da Jigon Hausa duk a cikin birnin Kano da Ruwan Dare a  Kaduna da kuma Kungiyar Matasa Marubuta ta Jihar Sakkwato a Sokoto (Adamu, 2006) su ma suka ƙara wa wannan harka martaba da ɗaukaka a idon mutane.

    Haka kuma ƙungiyoyin makaranta irin su Dakata Readers Association da Kabuga Readers Association da Tudun Wada Readers Association da Hotoro-South Readers Association duk a cikin Kano sun agaza wajen tabbatuwar wannan harka.

    Daga cikin kuma masu sayar da littattafan da suka agaza sosai a daidai wannan lokaci akwai irin su Alhaji Baba  na Jakara City Bookshop da Alhaji Musa Ɗanbala na Sauƙi Bookshop kuma Alhaji Garba Mohammed na Garba Mohammed Bookshop da ke Sabon Gari Kano.

    Wannan aure na marubuta da makaranta da masu sayar da littattafai da kuma ƙungiyoyi daban-daban, shi ne za a iya cewa ƙashin bayan wannan fasali na Adabin Kasuwar Kano, wanda ya sanya harkar ta hayayyafa, ta kuma bunƙasa fiye da yadda ake tsammani.

    Wannan ne ya sa aka sami yawancin tarin littattafan adabin Kasuwar Kanon masu yawan gaske da suka kai sama da 400, a tsakanin 1996 zuwa 2001. Daga wannan zango ne mata suka fara kunno kai sosai da sosai domin kuwa an sami marubuta mata sama da 50.

    ’Ya’ya Da Jikoki: 2002 zuwa 2008

    Littattafan da aka yi wa laƙabi da ‘ya’ya da jikoki su ne ƙagaggun labaran da aka samu daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2008. Nazarin da aka yi wa waɗannan littatafai an fahimci cewa duk da sauye-sauyen da aka samu na litattafan Adabin Kasuwar Kano a wannan zango, ba a bar fasalin da aka saba ba, wato na yin rubutun bisa tsarin ni na rubuta, ni na gyara, ni na kai inda za a buga mini, ni kuma ke sayarwa da kaina.

    An dai samu wasu sababbin marubuta ne da irin nasu fasali, sun ɓullo domin taka rawa irin tasu. Sai dai kamar yadda muka fahimta, wannan ba ya rasa nasaba da ganin cewa tsofaffin marubutan da suka yi tashe a baya, wasu sun watsar da rubutun, ko dai saboda sun yi aure ko kuma yayinsu ya wuce, wasu kuma sun koma wata sana’ar, musamman shirya finafinai, ga shi kuma buƙatar litattafan ba ta kau baki ɗaya ba, wannan ya jaza fitowar sababbin marubuta domin nuna irin tasu fasahar. An dai ga cewa an samar da littattafai na wannan zangon kimanin 248.

    A wannan zangon kamar yadda muka nazarta, marubuta mata sun sami filin baje kolinsu. Daga cikin littattafan da muka samu kai hannu kansu marubuta mata sama da 76 ne suka yi tashe. Wannan shi ne karon da mata suka yi ambaliya sosai. Haka kuma daga hirar da na yi da makaranta littattafai a wannan zango sun nuna sha’awarsu kan rubuce-rubucen matan, ƙila wannan shi ya ƙara sa yawan marubuta matan.

    A cikin waɗannan jerin littattafan na wannan zango, wadda ta fi yawan littattafai ita ce marubuciya Sa’adatu Saminu Kankiya tana da 14 da suka yi fice sosai, wannan kuma alama ce da ke nuna littattafanta sun fi samun karɓuwa ga makaranta. Mai yiwuwa saboda suna ɗauke da labaran da suka shafi soyayya da aure waɗanda bisa ga nazarin da aka gudanar su ne suka fi tashe a wannan zango.

    Akwai kuma wasu marubutan mata da suka fi shahara a wannan zango da suka haɗa da Saliha Abubakar Zariya da Hadiza Salisu Sharif da Amina Abdullahi Sharaɗa da Zainab Birged da su Sa’adiya Kankiya da Rahmatu Hassan Sanda.

    Duk da cewa yawancin waɗannan sababbin marubuta ne, duk da haka akwai fitattu da suka yi tashe, wasu tun daga haihuwa da ƙuruciya, ba su kuma daina ba har zuwan ‘ya’yan da jikoki. Cikin irin wannan fasali akwai irin su Rahma A. Majid da kuma su Hafsat A. Sodangi da Zuwaira Isa da Bilkisu Ahmed Funtua, da dai sauransu da dama.

    Daga cikin maza kuwa, littattafan Nazir Adam Salihi su ne suka fi karɓuwa da tashe kuma ya rubuta littattafai guda 13. Shi kuma yanayin gabatar da jigon littattafansa ya sha bamban da na sauran marubutan wannan zamani, domin wani lokaci za ka ga labaran nasa na soyayya ne, amma cikin ban takaici, wata sa’a ma da ban tsoro. Sai dai irin yadda yake wasa da harshe a cikin littattafan nasa ya sa yawancin masu karatu ke biye da shi a kullum.

    Maje El-Hejeej Hotoro shi ma wani marubucin ne da litattafansa da kuma tauraruwarsa, musamman a wannan zango suka yi tashe. Shi ma ɗin yakan yi amfani da jigon soyayya ko kuma jigon ban tsoron da jan hankali.

    A daidai kuma cikin wannan zango ne aka soma ganin ɓullar sabon tsarin rubutun Adabin Kasuwar Kanon. Da farko dai an sami marubutan da suka canza akalar rubutun nasu domin ya dace da zamani musamman ganin cewa an sha suka da taƙaddama kan yawaitar rubuce-rubuce kan soyayya da aure. Ire-iren waɗannan marubuta sun haɗa da Bala Anas Babinlata da Ibrahim Sheme da Sakina A. Aminu da Rahma A. Majid da Saliha Abubakar Abdullahi da sauransu da dama.

    Daga nazarin da aka yi, an fahimci cewa yawancin waɗannan marubuta ko dai ilminsu na zamani ne da suka yi nisa a ciki ya sa littattafan nasu suka yi armashi; wato kamar Ibrahim Sheme da Rahma Majid da suka nazarci adabin duniya daban-daban, da yake sun yi digiri, Ibrahim Sheme har digiri na biyu ya yi, ko kuma sun dai tsara littattafan ne domin su ɗan sha bamban da waɗanda aka saba ji da gani a wannan zango bisa sani, domin sun ga yadda aka daɗe ana ta kai-kawo game da neman sauyi, wato kamar su Babinlata da Rahma da Saliha da Abdullahi da Mukhtar Yaron Malam.

    Duka dai alamu ne da ke nuni da cewa sabon yanka rake na Adabin Kasuwar Kano ya shigo kasuwa. Baya ga wannan kuma ga gasar ƙaga littattafai da ta kunno kai, musamman ta Bashir ƙaraye da aka fara a shekarar 2007, wadda ta ba da dama aka sake ɗaga martabar rubutun da kuma marubutan wannan zango. A nan ana maganar irin su Ibrahim Sheme da Lawan Barista da Maje El-Hajeej da suka cinye gasar rubutun a cikin wannan zango. 

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Karanta Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

    Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

    A wannan babin an yi ƙoƙarin bin yadda aka samar da adabin kasuwa a ƙasar Hausa. Abin nufi, bayan ganin yadda fasalin adabin kasuwa ya kasance a sassan duniya daban-daban, da kuma ganin irin yadda ya samu ga maƙwabtanmu, Inyamurai, sai kuma mu gangaro domin ganin yadda ya samu a ƙasar Hausa.

    Don haka, a wannan babin an dubi irin zangunan da Adabin Kasuwar Kano ya shiga a ƙasar Hausa, da kuma irin rawar da ya taka wajen ginuwar wani ɓangare na ƙagaggun labaran Hausa.

    Samuwar Adabin Kasuwar Kano

    Daga abubuwan da aka gani a babin da ya gabata ke nan ba abin mamaki ba ne idan aka ci karo da Adabin Kasuwa a Amurka ko Turai ko Rasha ko cikin ƙasashen Asiya ko Larabawa, kai ko ma ina ne a cikin duniya.

    Hakan na faruwa ne ganin cewa ai ba ƙasashen Turawa ko waɗanda suka ci gaba ne ke da damar su samar da adabin kasuwa su kaɗai ba, haka kuma ba dole sai harshen Ingilishi ko wani harshen da ya sami ci gaba kaɗai ne zai iya samar da shi ba; kowace ƙasa, kuma kowane irin harshe zai iya samun adabin kasuwa a cikin wani zangon rayuwar adabin. Domin inganta bincike, ya dace mu bi salsala, mu ga yadda aka samar da abin da yawanci ake kira Adabin Kasuwar Kano tsakanin Hausawa.

    Rayuwar Farko : 1984-1989

    Abin da aka daɗe ana kira Adabin Kasuwar Kano ya samo asali ne a farkon shekarun 1980, kuma wannan shekaru a ƙasar Hausa ko Arewacin Nijeriya baki ɗaya, shekaru ne masu tarihi a ɓangaren samuwar ilmin boko da rubutu.

    A daidai wannan zangon rayuwa ne ɗaliban UPE, shirin gwamnatin tarayya da aka soma daga 1976 domin ba kowane yaro damar samun ilimin furamare kyauta, suka fara shiga kasuwar rubutu da karatu da rububin abubuwan karantawa, domin ɗaliban farko na wannan shiri sun baro firamare a shekarar 1982, daga wannan lokaci har zuwa 1984, an yaye ɗalibai har kashi huɗu. Saboda haka an samar da sababbin makaranta da suke buƙatar abin karantawa.

    Haka wannan zango ya zo daidai da lokacin da babban kamfanin wallafa da ɗab’i a ƙasar Hausa wato NNPC ya soma shiga tasku, ya soma sukurkucewa da neman durƙushewa. A daidai wannan lokaci kamfanin NNPC ya daina buga littattafan hira da nishaɗi, bayan kuma ga dubban matasa da aka yaye daga shirin na UPE sun antayo cike da  shauƙin irin waɗannan littattafai da babu su.

    Wannan shiri na UPE, duk da cewa bai zaunu da gindinsa ba, amma ya samar da sababbin makaranta a farkon shekarun 1980. Kuma a daidai wannan lokaci sai ga shi tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙara inganta, saboda gano man fetur da aka yi, ya ƙara wa ƙasar hanyar samun kuɗaɗen shiga masu yawa.

    Bincike kuma ya nuna cewa duk lokacin da irin wannan harka ta kasance haka, wato ga masu ilmi gwargwado, sa’annan ga ‘yan kuɗi a hannun jama’a, kamar yadda muka gani a fasalin Adabin Kasuwar Kitsch na Jamus, sai ka ga hanyoyin samar da adabi, mai kyau ko maras kyau, suna wadatuwa.

    Da yake tun can azal akwai kayayyakin rubutu da ɗab’i gwargwado a ƙasar Hausa, sai ya ba matasa damar da suka tsunduma cikin wannan harka ta wallafa littattafai ba ji ba gani, kamar yadda Furniss (2001) ya yi nuni. Sai dai ko kafin shekarar 1984 da littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed ya fito kasuwa akwai ɓirɓishin rubuce-rubuce na soyayya a ƙasar Hausa.

    Idan ba a manta ba a shekarar 1978 kamfanin NNPC ya shirya gasa da ta samar da littattafai a shekarar 1980, kamar su Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina da So Aljannar Duniya na Hafsat Abdulwaheed da kuma Amadi na Malam Amah na Magaji Ɗambatta, (Haruna, 2009).

    Sai dai abin lura shi ne waɗannan littatafai daga gasa suka fito, wato sai da aka yi shiri da tsari, haka kuma na hukuma ko kamfani ne, don haka sun biyo tsari da ingancin da ya bambanta su da adabin kasuwa. Ke nan za a iya cewa waɗannan littatafai na gasar 1978 sun dai nuna hanya ne na irin adabin da zai iya biyo bayansu, ba su ne farkon adabin na kasuwa a ƙasar Hausa ba.

    A ɗaya ɓangaren kuma an danganta littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed da tushe ko tubalin samuwar adabin kasuwa a ƙasar Hausa saboda yanayin da ya samu da kuma yadda ya shiga kasuwa. Shi ma ba wai zama aka yi domin assasa wannan fage na adabin kasuwa ba tattare da shi ba.

    Kamar yadda a karo na farko wadda aka danganta aikinta da Adabin Kasuwar Kano, Talatu ta bayyana wa Mujallar Garkuwa (2000) yadda ta samar da littafin, ta ce ita ba ta san da wani abu wai shi adabin kasuwa ba lokacin da take rubuta littafinta. Ta ƙara da cewa ta dai rubuta shi ne a lokacin tana makarantar WTC Katsina, tana aji uku, wato wajajen shekarar 1980.

    Ta kuma rubuta shi ne daga gyauron labaran da take ba ‘yan uwanta ɗalibai lokacin suna makaranta can da dare kafin su yi barci. Bayan ta gama sakandire ne ta fitar da shi ta hanyar aika shi gidan rediyon tarayya Kaduna domin a karanta a shirin Shafa Labari Shuni, amma aka daɗe ba a karanta shi ba, daga baya ta miƙa wa wani kamfanin bakin hanya da ake kira Ogwu a Kaduna domin ya buga mata shi.

    Kamfanin Ogwu ya buga, ya kuma shiga sayar da littafin da ya ga mutane sun dami suna son su karanta. A lokacin da Kamfanin Ogwu ya shiga sayar da littafin, ita Talatu tana Kwalejin Ilmi ta Kafanchan wajen ƙaro ilmi, a can ne wata ƙawarta ta zo da littafin, tana yi mata bayanin yadda littafin ya yi kasuwa, ita ba ta ma sani ba. Wannan daɗin abin da ya faru ya sa ta koma gida ta ji abin da ya auku.

    Mahaifiyar Talatu ta ba ta kuɗin da aka samu, ta yi murna ƙwarai da ganin arzikin da wannan littafi ya jawo mata. Daga wannan lokaci ne ta shiga sake buga littafin, ana watsawa a cikin ƙasar Hausa, ta yadda abin ya dinga ba ta mamaki na ganin cewa mutane, musamman masu sayar da littatafai daga ko ina a faɗin ƙasar Hausa ke kira ko yo saƙon don Allah ta aika masu da kwafe 500 ko dubu ko dubu biyu ko ma fiye.

    Fitar wannan littafi da yanayin da ya samu kan sa lokacin bugu da sayarwa da kuma hanyoyin da aka bi aka samar da shi ya nuna wa sauran marubuta cewa ashe akwai wata hanyar rubutu da wallafa littattafai ba dole sai ta bin kamfanonin bugu da wallafa na gwamnati ba.

    Saboda haka daga samuwar wannan littafi na Rabin Raina a shekarar 1984 za mu iya cewa akalar adabin hira ko ƙagaggen labari ta soma sauyawa, kuma a iya cewa daga wannan lokacin ne Adabin Kasuwar Kano ya fara ginuwa. Sai dai abin da ke da muhimmanci a nan shi ne ba wai zama aka yi ba domin a tsara da gina wannan fasali na Adabin Kasuwar ta Kano ba, abu ne da ya kasance caccakuɗe, kuma tattare da abubuwa mabambanta da suka haɗa da :

    • Tun da farko dai akwai matsalar abubuwan karantawa a makarantu da kuma tsakanin sababbin makaranta kamar yadda muka yi bayani.
    • Ga halin da kamfanin NNPC ya shiga daga farkon shekarun 1980 da rashin buga littatafan hira.
    • Ga kuma ɗaruruwan ‘yan makaranta da waɗanda suka kammala makarantun, sun kuma rubuta littattafai masu yawa, ba wurin buga su, balle a san da su.
    • Shirin gidan Rediyon Tarayya Kaduna na Shafa Labari Shuni da wasu da dama a gidajen rediyon jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu wurare da dama ya taimaka wajen fito da waɗansu daga cikin marubutan da ke ɓoye.
    • Bugun littafin Talatu na bakin kasuwa da yadda ya sami karɓuwa ya sanya wasu, ƙila suka ce su ma bari su gwada bugawa da sayarwa.

    Saboda haka littattafan da ake ta yayatawa a halin yanzu a matsayin waɗanda suka biyo bayan littafin Talatu daga 1984, ba wai shawara suka yi da juna ba, kuma ba su san wani na yin irin wannan aiki ba, kamar yadda bincike ya nuna a halin yanzu. Ke nan jawabin da Malumfashi, (1994) ko wanda Adamu, (1996) da Adamu (2000) suka yi na lissafa littatafan da suka biyo na Talatu kamar haka ba daidai ba ne, sai dai daga littafin Talatu na Rabin Raina sai:

    • Ibrahim Hamza Abdullahi da Soyayya Gamon Jini a 1986.
    • Idris S. Imam da In Da Rai a 1987.
    • Balaraba Ramat da Budurwar Zuciya a 1987.
    • A.M Zaharadden da Kogin Soyayya a 1988.
    • Idan so cuta ne, na Yusuf M. Adamu a 1989.

    An yi wannan hasashe bisa hujjar da ta nuna cewa babu wani bincike da ya tabbatar da jeruwa da daidaituwar wannan tsari ko kuma wani bayani da ya ce an tattauna tsakanin waɗannan mutane na biyo sahun Talatu Wada.

    Bari mu yi nazarin batun da kyau, tun da farko dai garuruwan marubutan daban-daban suke, Talatu na Kaduna, Ibrahim Hamza na Kano, Idris S. Imam kuwa tun 1984 aka buga littafin nasa ba wai a 1987, Balaraba kuwa ko kafin ta shigar da littafinta na Budurwar Zuciya a layin adabin kasuwa ta fuskar shiga ƙungiyar Raina Kama, an riga an buga littafin a Zaria,(Gaskiya Corporation a 1984).

    Haka shi ma Zaharradeen a Kano yake, shi kuwa Yusuf Adamu yana ɗalibta a Sakkwato ne ya shigo da nasa littafin. Haka kuma daga binciken da aka gudanar an fahimci cewa ko kafin Ibrahim Hamza Abdullahi da littafinsa na Soyayya Gamon Jini a 1986, an samar da Hannunka Mai Sanda I na Ƙamarradeeen Imam a 1985, me ya sa ba a shigar da shi cikin layin na farko ba? Haka kuma a tsakanin 1984 da aka samar da littafin Talatu, ba wai littattafai huɗu ne kurum suka yi tashe ba, guda 13 ne.

    Ke nan ba wata ƙungiya ba ce ko kuma wani taro aka yi ba aka ce a samar da wannan abu da aka kira Adabin Kasuwar Kano daga baya. Shi kuma Malumfashi (1994) da ya kira shi da wannan suna, ya yi haka ne daga abin da ya gani masu kama da juna tsakanin littattafan da irin waɗanda aka samar a Onisha kamar yadda ya bayyana daga baya, (Malumfashi, 2004).

    Kamar yadda muka gani can baya, rayuwar adabi takan shiga cikin wani sauyi ne na wani lokaci, daga baya kuma ta kasance cikin wani tsari na daban, irin wannan shi ne ya faru da abin da aka kira Adabin Kasuwar Kano yanzu. Sai dai wani abu da za a yi la’akari da shi, shi ne, yawancin matasan da suka yi tashe a wancan lokaci a wannan fage ba su yi amfani da kamfanonin ɗab`i da ake da su don bayyanar da ayyukansu na adabi ga jama’a ba, ba don komi ba kuwa sai don ba wani kamfani da ya damu ya buga ire-iren waɗannan littattafai.

    Ba kuma wai don ba su da kasuwa ko kuma ba su sami karɓuwa ba a tsakanin al`umma ba, a a, a tsakanin shekarun 1978-1982 ba abin da ya fi tashe da karɓuwa irin labaran da wasu suke rubutawa, suna aika wa gidajen rediyoyi daban-daban ana karantawa. Ba wani abu ya jawo hakan ba sai ganin litattafan da aka samar daga gasar da aka shirya a 1978 da suka samar da litattafan soyayya na farko da za a iya kira `yan zamani, sun yi tasiri ga rayuwar irin waɗannan matasa.

    Sai dai da alama amfani da aka yi da kafar rediyo, wadda ta sanya ƙagaggun labarai irin waɗannan suka sami martaba, ba wai kawai tsakanin waɗanda suka yi boko ba kurum, har ga waɗanda aikinsu shi ne sauraron rediyo, ba su iya karatun ba.

    Bisa wannan tafarkin aka shiga samar da sababbin marubuta, wasu ta hanyar kwaikwayon abin da aka rubuta, suka aika gidajen rediyoyin, wasu kuma ta sake wa tatsunniyoyi da labaran Hausa fasali, wasu ko ta kwaikwayo ko ɗaukar fasalin wasu labaran Ingilishi ko fassara kai-tsaye ko kuma naɗe fina-finan Indiya da na Turawa zuwa takarda.

    Cikin ɗan lokaci ƙanƙani sai ga kabod-kabod na gidajen rediyoyin nan sun cika maƙil, wasu ma suka shiga ƙonawa, wanda ya sa masu rubutun suka shiga guna-guni idan ba a karanta nasu labaran ba. Sai dai kuma waɗanda Allah ya tarfa wa garinsu nono daga cikin waɗanda aka karanta nasu a gidajen rediyoyin, sai ga shi sun fara samun suna da ɗaukaka.

    Wannan ya jawo wasiƙu suka shiga gilmawa zuwa gare su, ana yaba masu, ta haka kuma aka ga cewa ga wata kafa ta samu ta kashe waccan ƙishirwa ta rashin labaran Hausa da ta addabi matasa, ta yadda a tsakanin shekarar 1984 zuwa 1998 marubuta da sababbin littatafai suka baje kasuwarsu a ƙasar Hausa.

    Idan aka yi nazari sosai za a ga ko da Talatu ta bayyana a 1984 a Kaduna, ba a Kadunar ta tsaya ba, domin littattafan sun baje duk faɗin ƙasar Hausa, musamman a Kano da suka dasa rayuwarsu. A Kanon akwai irin littafin Talatu Wada da ya riga ya shiga kasuwa shi ma kafin ma bayyanar na Talatu, wato Wasiyar Baba Kere na Ibrahim Sale Gumel, a kuma wannan shekara ta 1984, an sami ɗan uwan na Talatu, wato In Da Rai Da Rabo na Idris S. Imam.

    Saboda haka ko da Ƙamarradeen ya shigo da nasa littafin a 1985, ba dole ba ne ya san da abin da Talatu ta yi ko kuma sauran da suka riga nata shiga kasuwa; musamman ganin cewa ɗa ne ga marigayi Abubakar Imam, kuma yana aiki da kamfanin Huda-Huda da ke Zaria, waɗanda su ne mawallafansa.

    Yadda Kano ta shigo cikin harkar da litatattafan da ‘yan Kanon suka samar bai rasa nasaba da suna da tashe da littafin Talatu da na Idris da Ibrahim suka yi a kasuwar Kanon. Littattafai goma sha uku ne suka wanzu a wannan lokaci a tsakanin 1986 zuwa 1989. Ga alama kuma su ne suka sanya Kano ta sami karɓuwa da tagomashi a wannan harka ta yadda daga baya Gusau ta shigo sahu, Kanon ta sake bayyana daga can kuma sai Sakkwato tare da Yusuf Adamu.

    Ga jerin waɗannan littattafai da suka kasance na farko ko suka kasance jijiyar da ta gina wannan sabon yanayin rubutu na Adabin Kasuwar Kano. Daga marubuta waɗannan littattafai an fahimci marubuta mata guda biyu suka wanzu, sauran kuma duk maza ne.

    LAMBA LITTAFI MAWALLAFI SHEKARA
    1 Wasiyyar Baba Kere Ibrahim Saleh Gumel 1983
    2 In Da Rai da Rabo Idris S. Imam 1984
    3 Rabin Raina Talatu Wada Ahmed 1984
    4 Hannunka Mai Sanda 1 Ƙamaruddeen Imam 1985
    5 Soyayya Gamon jini Ibrahim Hamza Bici 1986
    6 Daji Bakwai Abba Ado Ɗandago 1987
    7 In Da Rai… Idris S. Imam 1987
    8 Kogin Soyayya Ahmed Mahmoud Zaharaddeen 1988
    9 Turmi Sha Daka Kabiru Ibrahim Yakasai 1988
    10 Budurwar Zuciya Balaraba Ramat Yakubu 1989
    11 Soyayya Danƙon Zumunci Bashir Sanda Gusau 1989
    12 Tsalle Ɗaya… Idris S. Imam 1989
    13 Idan So Cuta Ne Yusuf M. Adamu 1989

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Danna nan don karanta Jigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe

    Edita@rumasau-kallamu

  • Jigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe

    Jigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe

    Saƙonni ko kuma jigogin da waɗannan ayyuka na adabi suke isar wa sun bambanta ne daga wannan gari zuwa wancan ko kuma daga wannan ƙasa zuwa waccan, amma dai abu muhimmi shi ne kowane da abin da yake son ya isar ga al’ummar.

    Alal misali daga nazarin da aka yi wa Adabin Elizabeth da ya wanzu a zamanin sarauniya Elizabeth ta Ingila a tsakanin ƙarni na 16 da na 17, ya shahara ne ta fuskar wasan kwaikwayo da kuma waƙoƙi, sannan kuma kusan yawancin marubutan suna yin rubutunsu ne domin kare martabar masu mulki da kuma tajirai.

    Wannan ne ma ya sanya tun daga farkon mulkinta, Sarauniya Elizabeth ta kasance tamkar uwar ƙungiyar, kuma mai ba da taimako ga marubutan, ta yadda kamar yadda muka nuna a wasu lokuta har aiwatar da wasan kwaikwayon ake yi a gabanta.

    A adabin Larabawa ma musamman kuwa waƙoƙin lokacin jahiliyya, jigonsu  bai wuce faɗakarwa ta zamantakewa ba, ko kuma rayuwa irin ta yau da kullum ba, sai kuma jigon waƙoƙin yawace-yawace da kuma waƙoƙi na ƙabilanci da kusan kowace ƙabila ke da shi. Amma bayan bayyanar Musulunci da wayewar kai sai abin ya canza, domin kuwa  litattafan adabin Larabci a lokacin sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy,

    Shi kuwa adabin Onitsha na Nijeriya jigoginsu sai suka sha bamban da na sauran sassan duniya, domin kuwa a lokacin da aka fara samar da shi a 1947, sai ya kasance ya ta’allaƙa ne wajen ba da labaran soyayya da suka shafi aure da kuma kasuwanci, a sassan wannan yanki na Nijeriya.

    Ke nan a iya cewa yawancin labaran na Adabin Onisha ba su maganar komai sai labaran soyayya da tatsuniyoyi. Daga baya kuma sun tattauna abubuwa da suka shafi yadda ake rubuta wasiƙa da yadda ake koyon Ingilishi da kuma tallata haja da makamantansu.

    Daga binciken da aka gudanar an dai fahimci cewa yawancin jigogi na yawancin Adubban Kasuwa a kowace ƙasa, suna kasancewa abin da al’ummar wannan wuri ne suka fi so da ko sha’awar gani ko karantawa a daidai lokacin da ake aiwatar shi, ko dai na soyayyar ne ko kuma na kasuwanci, ko rayuwar iyalin ko kuma na masu mulkin, kusan a ce wannan shi ya fi rinjayar masu karanta ko sauraron wannan adabi na wannan yanki.

    Marubuta

    Marubuta waɗannan litattafan dai kamar yadda muka nazarci wasu daga cikinsu, shahararru ne a fagen da suke, wasu kuma fitattun malamai ne a makarantun zamanin. Misali, marubuta adabin Elizabeth, wasunsu sun yi fice matuƙa, marubuta kamar  Roger Ascham, wanda yake fitacce kuma shahararren malami ne, domin har sarauniyar Ingilar ma sai da ya koyar da ita a makaranta, an haife shi a shekarar 1515.

    Sannan ga masana irin su Edmund Spenser da William Shakespeare da Christopher Marlowe da Ben Johnson da Edmund Spencer da John Fletcher da Thomas Kyd da Thomas Middleton da Thomas Nashe da John Webster da John Donne da Philip Sidney, dukkansu fitattun marubuta ne waɗanda suka yi tashe a wannan zamani na Elizabeth da kuma bayan wannan zamani.

    Idan muka dubi marubutan Adabin Kitsch na Jamus, shi ma ya samu fitattun masu zane da rubutu a lokacin, fitattun daga cikinsu kuwa su ne; Gabriel Thuller da Matk A. Cheetham da kuma George Wilhelm Friedrich Hegel.

    A adabin kasuwa na Larabawa da muka gani, shi ma ya zo da nasa fitattun marubutan da suka shahara kuma suka samar da litattafai a lokacin, fitattu daga cikinsu akwai Muhammad Husayn Haykal da Muhammad Tahir Haqqi da Naguib Mahfuz da kuma Al-Hamadhani da fitaccen aikinsa na Maqamatil-Hariri da dai sauransu.

    Haka ma a kasuwar Onisha wanda za a fara cewa ya fara samar da waɗannan litattafan na kasuwar Onitsha ba wai kawai ya yi fice ba ne, mutum ne wanda ya shahara ta fuskar ilimin boko daga baya, wato Cyprian Ekwensi wanda daga baya ya tashi daga wallafa ƙananan litattafai zuwa manya.

    Makaranta

    Makaranta Ayyukan adabin kasuwa su ma sun bambanta, wasu talakawa ne kaɗai ke sauraro ko kallo, yayin da wasu  kuwa kamar na Elizabeth ya kasance masu sarautar Ingila ɗin suna daga cikin masu yi da sauraron wannan adabi. Sai da ta kai ma wasu ayyukan idan aka yi su, sai a ware wanda za a kai wa sarauniyar, da kuma wanda za a gabatar a bainar jama’a.

    Saboda haka sai ya kasance daga cikin masu sha’awar wannan aikin; wato ko dai wasan kwaikwkon ko kuma waƙoƙi sun fito daga masarautar Ingilar. Wannan ne ma ya sa marubuta da dama na wannan lokacin sun ji daɗin yadda ‘yan majalisar Sarauniya ke tarairayar su.

    Shi kuwa adabin Kitsch ba wai na talakawa ba ne kaɗai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kuɗin sayen irin waɗannan ayyuka, amma ƙarfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafaɗa-kafaɗa da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na ƙwarai.

    Shi dai adabin kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kuɗi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da waɗanda suka yi fice ba, duk da haka su ma waɗanda suka yi ficen, ganin ƙarƙo ko kuma yanayin wannan na Kitsch ɗin ya sanya suka fara sayen shi.

    Shi kuwa Adabin Kasuwa na Onitsha ya fi shahara ne a wurin matasa `yan makaranta maza da mata, da kuma  masu ƙaramin ƙarfi don su samu abin karantawa wanda baya da tsada, ta yadda kowa za iya sa kuɗi ya saya ba tare da wani tarnaƙi ba.

    Tsarin Littattafai

    Ko a tsarin waɗannan litattafan, mafi yawancinsu ba su da shafuka da yawa, ana yin su ne ta yadda kowa zai iya karance ce su ba tare da ɗaukar wani dogon lokaci ba. Sannan kamar yadda muka ce kuma harshen da ake rubuta su shi ma mai sauƙi ne, wanda bai yi karatu ba da wanda ya fara bai tasa ba da kuma wanda ya yi karatu mai zurfi da sauransu duk za su iya karantasu, domin ba a  nannaga harshe ko nuna ƙwarewar harshen da zai zama matsala wajen karantawa.

    Saye da Sayarwa

    Duk aikin Adabin da ya kasance ana samun shi a wasu wurare da ba na saida litattafan ko aikin adabi ba ne to wannan adabi zai kasance na kasuwa ne ko yayi ko kuma mai tashe ne. Duk adabin da ake bi kasuwa-kasuwa, da shaguna, da wajen `yan tireda, da masu tura kaya a baro, ko wurin `yan kura, kai ko kawai a hanya, ana nemansa don a saya, adabin kasuwa ne, (Malumfashi, 2002).

    Wannan ya zama gaskiya idan aka yi la’akari da irin wuraren da ake sayar da littattafan zamanin Sarauniyar Ingila Elizabeth Ta ɗaya, yawancin littattafan ana sayar da samunsu a bakin shagunan da marubutan suka buɗe don tallata hajarsu, ko dai a cikin birnin London ko kuma ƙauyukan da ke maƙwabtaka da shi. An fi ganin su a bakin titi, ‘yan ƙalilan ne suka samu shiga shagunan sayar da littatafai na zamani.

    Wasu kuma kamar yadda muka bankaɗo, ana saye da rarraba su ne ta hannu, tsakanin wannan marubuci ko marubuciya zuwa wancan marubuci ko marubuciya. Sai dai za a iya cewa wasu kuma ba ma sayar da su ake yi ba ana aiwatar ko gabatar da su ne a gaban jama’a a lokuttan bukukuwa ko tarurrukan marubuta.

    Kusan irin wannan fasali ne aka gani a adabin Kistch na Jamus, yawancin zane-zanen da ayyukan adabin da suka yi tashe a wannan karon an samar da su ne a kasuwar birnin Munich, inda yawancin masu adabin suka rayu. Saboda haka za a iya cewa adabin da zane-zanen duk ‘yan kasuwa ne, don haka a bisa titi ake samu da sayar da su a tsakanin al’ummar wancan zamani.

    Idan kuma aka lura da tsarin saye da sayarwar littatafan Adabin Kasuwar Onitsha za a fahimci shi ma ya bi irin wannan fasali na baya. Tun da farko dai an yanke wa adabin cibi ne a kasuwar Onitsha, nan yawancin marubutan suka wanzu, sai kuwa wasu sassa na garuruwan Aba da maƙwabta.

    Saboda haka yawancin littattafan ana saye da sayar da su ne a waɗannan kasuwanni. Ba kuma wani wuri na musamman aka tanadar musu ba, inda ‘yan kasuwar ke saye da sayarwar nan ne littattafan suka samu matsuguni.

    Naɗewa

    A wannan babin an kalli samuwar Adabin kasuwa da kuma bambancin da ke tsakanin Adabi da Adabin kasuwa ɗin ko na yayi ko kuma na talakawa. Bayan ganin irin wannan adabi a sassan duniya kamar na sarauniya Elizabeth a Ingila da na Kitsch a Jamus da na Adbul-Mu’athir a ƙasashen Larabawa sannan sai nan gida a garin Inyamurai wato Onitsha, an kuma kalli matakan gane wannan adabi  da sauransu.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Danna nan don karanta Adabin Kasuwa Na Onitsha A Nijeriya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Adabin Kasuwar Kitsch A Jamus

    Adabin Kasuwar Kitsch A Jamus

    Duk da an ce samuwa da ginuwa na adabin jama’a ko yayi ya tusgo ne daga ƙasar Ingila, amma ba a ƙasar Ingila irin wannan rayuwar adabin kasuwa ko yayi ya samu gindin zama ba kawai, a can Jamus a cikin ƙarni na 18 da na 19, an sami irin wannan adabi da ake wa laƙabi da Kitsch.

    A cikin harshen Jamusanci ko Yiddish, kalmar Kitsch na nufin duk wani aikin adabi ko zane da bai da tagomashi ga masu mulki ko tajirai ko ya kasance lami ko kwashe-kwashen ayyukan wasu da aka yi a baya, (Wikipidia.org).

    Adabin Kitsch ya soma watayawa sosai da sosai a ƙasar Jamus a ƙarni na 19, musamman a kasuwannin birnin Munich a tsakanin 1860 zuwa 1870, inda ake kiran duk wani aikin adabi da ke da arha ko na yayi ko mai karɓuwa a tsakanin al’ummar da aka yi domin su ko yake ja a cikin kasuwar sayar da ayyukan adabi da sunan na Kitsch.

    Shi wannan adabin na Kitsch ba wai na talakawa ba ne kaɗai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kuɗin sayen irin waɗannan ayyuka, amma ƙarfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafaɗa-kafaɗa da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na ƙwarai.

    Duk da cewa Kitsch ya samu karɓuwa a tsakanin jama’a, duk da haka bai wuce adabin kasuwa ko yayi ba ga sauran jama’a, musamman masu sarauta da tajirai, domin kuwa ba a yi aikin da kyau ba ko kuma takardun da aka zayyana hoton ko buga aikin adabin sun kasance na banza, ba su da aminci.

    Ke nan adabin Kitsch bai wuce adabin Jamus da bai da mazaunin ƙwarai ba a tsakanin masu mulki da tajirai ko kuma yana magana kan abubuwan da ba su ne aka sa gaba ba a tsakanin al’ummar, ko kuma dai gwanjon adabi ne ko adabi ne da ke kwaikwayon wani adabi, ba tunani ko ƙirƙirar wanda ya samar da shi ba ne ko da kuwa ya samu karɓuwa tsakanin wasu gungun mutane, (Cuddon, 1999).

    Saboda haka kamar yadda muka gani a baya, Kitsch wani nau`in adabi ne da ya wanzu a ƙasar Jamus wanda yake nufin duk wani aiki na zane ko aikin adabi wanda masu mulki ko masu kuɗi ba su yi na`am da shi ba. An samar da wannan adabi ne mai suna Kitsch domin a mai da martani ko ya yi jayayya da ayyukan adabi da aka samar a ƙarni na 18 da na 19 wanda yake ana masa kallo na masu mulkin ƙasaita da fitattun masu kuɗi ne.

    Shi dai wannan salon adabin yana da matuƙar alaƙa da adabin da ke tashe ko kuma na yayi, ba wani abu ya sa aka kira shi da haka ba kuwa sai ganin cewa aikin da aka yi na zanen ko aikin adabin ba a yi shi yadda za a iya cewa ya ginu ko tsaru ba.

    Ke nan adabin Kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kuɗi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da waɗanda suka yi fice ba, duk da haka su ma waɗanda suka yi ficen, ganin ƙarko ko kuma yanayin da wannan adabi ya fita da yadda mutane ke rububinsa ya sanya suka fara saye da karanta shi.

    Za mu iya cewa adabin Kitsch ya kasance na talaka ne kawai domin ganin fasalin yadda aka samar da shi ba mai aminci ba ne, ma’ana kayan da aka yi aiki da su wurin samar da waɗannan zane ko ayyukan adabin ba su da inganci, kuma an samar da su ne ganin cewa waɗanda suke sayen shi ba su iya sayen manyan ayyukan adabi, wato wannan yana da sauƙin kuɗi ga masu sayen shi, kusan kowa zai iya sa kuɗi ya saye shi.

    Wannan ya sa ake danganta adabin Kitsch (Wikipedia.org) da duk wani aikin adabi ko zane da aka samar maras kyau, wanda zai iya biya wa mai saye da buƙatarsa, ma’ana zai kashe masa ƙishirwa daga abin da yake so ya gani ko ya karanta, musamman cikin wata sabuwar kama ko siffa, a ayyukan adabin wanda aka kwaikwaya daga wanda ya gabace shi ko suke rayuwa tare.

    Wannan ne ya sa irin wannan tsari ko fasali ya sha suka daga masana, fitattun daga cikin su kuwa su ne; Gabriel Thuller wanda ya goyi bayan wannan adabi na Kitsch bai dace da zamanin ba, domin ba gwanaye ke yin sa ba. Haka kuma wani fitaccen masani a fannin zane Georg Wilhelm Friedrich Hegel ya jaddada cewa zane-zanen wannan zamani yana da alaƙa da wani yanayi na lokacin da aka samar da shi, ba abin damuwa ba ne, in dai ya samu karɓuwa daga masu karatu.

    Adabin Kasuwa Na Larabawa

    Shi ma adabin Larabci kamar sauran ya sha kwaramniya har zuwa lokacin da aka samar da na zamani wanda yake da alaƙa da na Yammacin Dauri (Neo-Classical) wanda ya nemi ya canza fasalin adabin Larabci gaba ɗaya, wato wanda za a ce ya samo kayan aikinsa daga wanda ya gabata, kamar su Maqamatul Hariri da Alfu Laylah.

    Saboda haka su waɗannan na zamanin sai ya kasance sun koma ko dai suna samo kayan gininsu daga waɗannan ko kuma suna juyar aikin marubuta adabin Yammacin Dauri ne kai tsaye, suna mai da su na Larabci.

    Marubuta da dama a ƙasashen Siriya da Lebanon da Egypt sun samar da ayyukansu na adabi daga Maqama, fitattun daga cikinsu akwai Al-Muwayhili da littafinsa na The Hadith of Issa ibn Hisham a zamanin mulkin Ismail a Egypt, wanda wannan littafin shi ne za a iya cewa ya haifar da wani sabon zango a adabin Larabci.

    Wannan yanayi shi ya ba marubucin nan ɗan ƙasar Lebanon,Goergy Zeidan, wanda kirista ne da ya yi hijira zuwa ƙasar Misira, bayan zanga-zangar da aka yi a Damaskus a 1860 damar fitar da basirarsa a fili sosai.

    An dai fara buga labarin Ziedan a farkon ƙarni na 18 a cikin jaridar ƙasar Misira, wato Al-Hilal. Ba wani abu ya sa aka kira ayyukan waɗannan mutane na yayi ko na kasuwa ba sai ganin cewa su ne ayyukan da mutane suka fi sha`awa, saboda irin yadda aka samar da su da harshen da kalmomin da aka yi amfani da su da kuma yadda aka tsara su, sai kuma ficen da marubutan suka yi. Sauran waɗanda suka kasance a cikin wannan tsarin sun haɗa da Khalil Gibran da Mikha`il Na`ima.

    Amma dai masana da dama na adabin Larabci sun bayyana cewa an fi ganin Littafin Zaynab na Muhammad Husayn Haykal da Adraa Denshawi na Muhammad Tahir Haqqi da kasancewa ayyukan adabi na farko a wannan ƙarni masu kama da ayyukan adabin jama’a ko kasuwa, fiye da waɗancan da muka ambata a baya. (dubi ƙarin bayani a Arabic Literature daga Wikipidia: The free encyclopedia).

    Daga nazarin da aka gudanar an fahimci litattafan adabin yayi ko na jama’a na Larabci sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy inda ya siffanta rayuwar iyali.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila

    Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila

    Da yake mun ga yadda wannan adabi ya kasance da kuma tasirin da ya yi tsakanin al’umma a Ingila, zai dace a nan mu faɗaɗa kan wannan batu domin mu ga yadda fasalin adabin kasuwar ya kansance ta hanyar bayar da misalai.

    Da yake tun da farko mun yi nuni da cewa harkar ta adabin kasuwa ta samo tushe ne daga Ingila, ya dace mu fahimci yadda al’amarin ya kasance, kafin mu shiga wasu sassan na duniya mu ga su kuma irin nasu fasalin.

    Daga nazarin da aka yi an fahimci akwai bambance-bambancen da aka samu a tsawon zamanin aikin adabin Ingilishi, tunanin farko dai ya fara ne daga `yan Sukotlan ba daga Ingila ba, shi wannan adabin ne ya ci gaba da watayawa a tsakanin ƙarni na goma sha biyar zuwa farko, da tsakiyar ƙarni na goma sha shida.

    Wannan ne ya samar da  gagarumin aikin Tottel a shekarar 1557. Shi dai wannan littafin ya shahara ne saboda dalilai da dama; Na farko dai abin da ya fi jan hankalin sababbin makaranta a wannan lokacin shi ne mafi yawan abin da littafin ya ƙunsa abu ne wanda ba a san da shi ba da, haka kuma akwai hasashe ba yaƙini ba a cikin labarin, wanda kuma wannan shi ya fi burge masu karatun ayyukan adabin wannan lokacin, ba kamar ayyukan wasu da suka wallafa ba waɗanda ko dai sun mutu ko kuma sun daɗe ƙwarai da yin rubutun, (Saintsbury,1920).

    Wannan zamani na Sarauniya Elizabeth kamar yadda muka yi bayani akwai aikin manyan masana a ƙasar Ingila, kamar fitaccen marubucin nan na wasan kwaikwayo, Christopher Marlowe da marubuta waƙoƙi irin su Edmund Spenser da kuma shahararrun masana kimiyya irin Francis Bacon.

    Marubuta da dama na wannan lokacin sun ji daɗin yadda ‘yan majalisar Sarauniya ke amsar su in sun kai ziyara, duk da cewa suna daga cikin talakawa (Saintsbury, 1920). Wannan kuwa ya faru ne domin tun farkon mulkin Sarauniya Elizabeth, ita ta kasance tamkar Uwar ƙungiyar, kuma mai ba da taimako ga marubuta labaran wasan kwaikwayo, kai har aiwatar da wasan kwaikwayon ake yi a gabanta.

    A shekarun 1560 aka fitar da wasan Kwaikwayo na Blank Verse Tragedies wanda za a iya cewa shi ne ya buɗe ƙofa wurin samuwar kimiyyar wasan kwaikwayon da ake nazari har zuwa yau. A shekarar 1568 ne aka aiwatar da wasan kwaikwayon a gaban sarauniya a bisa dandamali.

    Irin yadda aka samar da litattafai da ayyukan adabin Elizabeth ya taimaka ƙwarai wurin ceton adabin Ingilishi daga shiga cikin haɗari na kwasar ayyukan da ‘yan kasuwa suke yi, waɗanda kuma ake samarwa da tsada. Misali, a lokacin da Tottel ya fiddo littafin shi na Miscellany ba dukkan mawallafa na lokacin suka san da wannan hanyar ta fiddo da littafin kai tsaye ba, wato ba tare da an miƙa shi ga masu wallafar zamani ba (Saintsbury,1920).

    Ta ɓangaren rubutun zube ma, lokacin mulkin sarauniya Elizabeth ya samu tagomashi sosai, saboda a lokacin ne aka samu ayyukan adabi waɗanda suka yi tashe ko kuma suka zama na yayi, domin a lokacin malaman da ke koyarwa a Jami`ar Kambirij (Cambridge) sun taimaka ƙwarai da gaske wurin samar da ayyukan masana irin su Ascham da Wilson, da sauransu ta fuskar zube.

    Duk da cewar akwai ayyukan magabata irin su Thomas Hoby, amma dai za a iya cewa Roger Ascham shi ne ya fara buɗe fagen da littafinsa Toxophilus da ya rubuta aka kuma wallafa shi a shekarar 1545, amma dai littafinsa da ya fi tashe, wato Schoolmaster bai fito ba sai bayan da ya mutu, (Saintsbury,1920). Shi dai Ascham fitacce, kuma shahararren malami ne domin har sarauniyar Ingilar ma sai da ya koyar da ita a makaranta.

    Kamar yadda muka gani a sama, Adabin Elizabeth na Ingila ya ratsa zangunan mabambanta. Misali, mun dai ga akwai ayyukan adabi da aka yi kafin lokacin Elizabeth ɗin kamar na su Thomas More wanda ya yi rubuce-rubuce, musamman na waƙoƙi da kuma Wyatt da sauransu.

    Ko a lokacin mulkin Sarauniya Elizabeth ɗin ma, ayyukan adabi da suka fi tashe su ne waƙoƙi da wasan kwaikwayo da kuma ƙagaggun labaran, amma dai masu sarrafa waƙoƙin da wasan kwaikwayo sun fi yawa da tashe, wato kamar masana irin su Edmund Spenser da sauransu (Saintsbury,1920).

    A ɓangaren wasan kwaikwayo da ƙagaggun labarai kuwa dole ne masana irin su Shakespeare su shige gaba, sannan ga Marlowe wanda zaƙaƙuri ne, wanda ayyukansa suka yi tashe, ga kuma Ben Jonson wanda ya kwaikwayi ayyukan magabatansa, ya samar da nasa. Ta ɓangaren ƙagaggun labarai kuwa akwai marubuta irin su Philip Sidney da Richard Hakluyt da Francis Bacon da sauransu da dama.

    Daga wannan taƙaitaccen bayani mun fahimci a ƙasar Ingila ne aka samar da wannan fasali na adabin jama’a ko na kasuwa, mun dai fahimci  irin wannan adabi na yayi ko kasuwa ya wanzu tsakanin ƙarni na 16 da na 17 lokacin da adabin sarauniya Elizabeth ya yi tashe tsakanin shekarar 1558 zuwa 1603.

    Shi dai adabin Elizabeth ba yana nufin ita Sarauniyar ce ta wallafa ko buga shi ba (kodayake ita ma ta jefo waƙoƙinta da aka karanta, musamman On Monsiuer’s Departure), sai dai ana iya cewa a lokacin mulkinta ne aka samar da yawancin ayyukan adabin da ake wa laƙabi da na yayi ko kasuwa, duk kuwa da cewa ayyuka ne na ƙwarai.

    Abin da ya sa wannan gangariyar adabi ya kasance adabin kasuwa shi ne ya samu karɓuwa a hannun yawancin jama’ar Ingila a cikin ƙanƙanen lokaci (Wikipidia.org). Duk da cewa akwai ƙagaggun labarai cikinsa, abin da ya fi yin tashe shi ne wasan kwaikwayo da waƙoƙi. Adabin Elizabeth ya somo ne daga zamanin su Tottel da suka wanzu da waƙoƙinsu zuwa masu tsara labarai na zamanin Caroline, (Saintsbury,1920).

    Ba wani abu ya sanya wannan zamani ya kasance na ayyukan adabin al’umma ba sai ganin manyan mashahuran marubutan da suka yi tashe a wancan zamani sun wanzu ne a lokacin, kuma har yau suna tashe a fagen nazari da sharhi. Akwai marubuta ayyukan adabi da suka haɗa da William Shakespeare da Christopher Marlowe da Ben Johnson da Edmund Spencer da John Fletcher da Thomas Kyd da Thomas Middleton da Thomas Nashe da John Webster da John Donne da Philip Sidney da sauransu, duk a wannan zamani suka wanzu.

    An kira waɗannan mutane da ayyukan adabinsu a matsayin na yayi a wancan lokaci, saboda sun kasance mutane ne ko kuma ayyukansu da jama’a ke rububi. Sa’annan kuma yawancin ayyukan nasu kwafe-kwafe ne ko dai daga wasu can da aka yi a baya da suka shahara ko kuma tsakanin marubutan wannan zamani.

    Misali, Thomas Kyd da aikinsa na The Spanish Tragedy, shi ya ba Shakespeare hasken rubuta Hamlet, ba kuma nan kaɗai Shakespeare ya tsaya ba, ya shiga cikin taskar tarihin zamanin da, da kuma zamanin da ya rayu ya kwafo abubuwan da suka taimaka ya gina nasa adabin.

    Bincike ya nuna cewa waƙokin Sonnet da Thomas Wyatt ya ƙaddamar su ne kuma Shakespeare da wasu na zamaninsa suka ci gaba da tallatawa, kuma sun ja ra’ayin Thomas Campion wanda ya rubuce su a takarda, aka shiga rububinsu a gidajen al’ummar wancan zamani, (Wikipidia.org).

    Ke nan ba kamar yadda ake tunani ba, yawancin ayyukan adabin zamanin Sarauniya Elizabeth ta 1, ba wai rashin kyau ko ma’ana ko kuma rashin goyon bayan hukuma ba ne matsalar da ta sa aka kira su na yayi, ba kuma domin ana rubutun domin talakawa ba ne kaɗai ba, sai dai domin yanayin samuwarsu, wato yadda jama’a ke ta wawason su da kuma shiga cikin harkar saye da karantawa da rubutawa, ciki har da masu gari, Sarauniya.

    Babban abin da ya fi fitowa fili game da wannan zamani shi ne yadda gamaɗe da kwashe-kwashen ayyukan wasu ke taimakawa wajen gina sabon adabin da ya burge al’ummar wancan zamani. Saboda haka daga abin da aka tattaro dangane da adabin Sarauniya Elizabeth na Ingila mu iya cewa mafi yawan ayyukan adabi na ƙwarai, an samar da su ne a wannan lokaci, cikin waɗannan shekarun ne aka samar da rubuce-rubucen adabi, musamman abin da ya shafi zane da waƙoƙi, wasan kwaikwayo da sauransu.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya

    Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya

    Daga nazarin da aka gudanar an fahimci cewa adabin kasuwa ko na yayi yana tafiya ne kafaɗa da kafaɗa da gangariyar adabin al’umma. Shi gangariyar adabin yana kasancewa ne tsakanin masu ilmi ko hannu da shuni ko kuma iyayen ƙasa. Duk wani abu da ba na wannan gungun mutane ba ne, yawanci shi ake wa laƙabi da adabin kasuwa ko yayi.

    Alal misali kusan duk yawancin ayyukan adabi da suke da wannan siffa a Turai ko Amurka ko sauran sassan duniya an samar da su ne tsakanin ƙarni na 16 da 17 da na 18, daidai lokacin da fasahar ɗab’i ko buga littattafai ta yi tashe a duniya.

    Kamar yadda bayanai suka yi nuni, yawancin jama’a da masana idan ana maganar adabin ƙarni na 16 da 17 da na 18, ana maganar gangariyar adabi ne ko na masu ilmi ko mulki ko dukiya, amma ba su kaɗai ne suka kwashi nasu kason ba daga rayuwar adabi, akwai adabin talakawa ko na kasuwa, wato na kowa da kowa, adabin da aljihun talaka zai iya biya, ya saya don karantawa.

    Wannan dama ta samu ne domin an samar da injinun buga littattafai na bakin hanya da suka ba talaka damar ya sami gurbin da zai buga nasa adabin. Ire-iren waɗannan ayyukan adabin su ne ake ba sunaye daban-daban da suka haɗa da Grub Street Literature ko Chapbooks. Waɗannan laƙabobi sun wanzu ne saboda la’akari da irin yadda aka samar da adabin ko wuraren da ake samar da littattafan ko kuma yanayin bugawa da sayar da su.

    Su dai Grub Street Literature su ne ayyukan adabin da aka samar daga wuraren buga littattafai da ke kan Titin Grub a Landon. Da yake a tsakanin ƙarni na 16 da 17 da na 18 an samar da marubuta na ƙwarai, sai dai rubutun nasu ya fi mayar da hankali ne ga masu-faɗa-a-ji, bai ta’allaƙa ga sauran jama’a ba, ga shi kuma sun fi sauran jama’ar yawa, wannan ya sa aka shiga neman wasu da za su agaza da nasu rubutun.

    Sai dai yawancin irin waɗannan marubuta ba su da sanayya ta zamani game da fasahar rubutu da ƙaga labarai, shi ya sa idan sun yi rubutu ake biyan su kuɗaɗe kaɗan, wannan ya sa suke rayuwa a cikin talauci da ƙunci.

    Shi kansa inda suke zama a bakin titin domin yin aikin nasu na adabi, wuri ne na ƙazanta da yawan lalata da tashin hankali; nan ake samun ɓarayi da mabarata da dai ire-irensu; nan ne marubutan da injinan buga ayyukansu suka ɗaura aure.

    Su kuwa Chapbooks littattafai ne da ake wa laƙabin littattafai masu arha, su ne ayyukan adabin da suka kasance na yayi ko na jama’a a karo na farko a wancan zamani na ƙarni na 17 da 18.

    Ba ruwansu da kamfanonin hukuma ko na gwamnati, ba kuma ruwansu da manyan kamfanonin ɗab’i da ke neman ƙazamar riba. Ana kuma shirya da buga irin waɗannan littattafai domin isar da saƙo ga talakawa ko masu sha’awar adabi, amma ba su da kuɗin sayen gangariyar adabin da ke wanzuwa a lokacin.

    Wannan damar ce marubutan da masu karatu ke amfani da ita domin su isar da saƙo ga sauran jama’a ba tare da kamfanin ɗab’i ya sa baki ba, yawancin abubuwan da ake samarwa sun haɗa da waƙe-waƙe da labarai da ayyukan addini da saƙonnin siyasa da makamantansu.

    Tarihi ya nuna cewa ko da hada-hadar ɗab’i da rubuce-rubuce ta kankama daga ƙarni na 15 da na 16 akwai ire-iren waɗannan ayyuka masu arha, yawancinsu sun fita kasuwa ne daga ƙarni na 17 da na 18 a Ingila, an nuna sun kai ƙoƙoluwa ne a shekarar 1775 ta yadda ake samar da littattafai sama da 200,000 a kowace shekara.

    Waɗannan littattafai sun taimaka wajen raya ayyukan adabin Ingila a wancan lokaci, sun sanya son karatu ga waɗanda ba su yi nisa a karatun ba, ko suka yi karatun suka watsar daga baya.

    Yawancin waɗannan littattafai ba su da yawan shafi, ba a yi musu bugun ƙwarai, sa’annan ana sayar da su da arha, daga wannan titi zuwa wancan, a maimamkon wuraren da aka tanada domin sayar da gangariyar adabi. Domin ganin yadda wannan fasali ya kasance, bari mu dubi yadda na zamanin Elizabeth ya kasance a Ingila.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Fasalce-Fasalcen Adabin Kasuwa danna nan 

    Edita@rumasau-kallamu