An haifi Kamilu Hussain a shekarar 1980 a ƙauyen Beta Ƙaramar Hukumar Sumaila da ke Jihar Kano a Tarayyar Nijeriya. Cikakken sunansa shi ne Kamilu, amma alkunyarsa ita ce “Almajirin Mawaƙa”.
Sunan mahaifin Almajirin Mawaƙa shi ne Malam Hussaini wanda shi ne Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na Ƙauyen Beta a wancan lokacin; kafin daga baya ya yi Ƙaura zuwa Ƙaramar Hukumar Nguru da ke Jihar Yobe.
Kamilu tun yana ɗan shekara huɗu mahaifinsa ya tura shi Ƙaramar Hukumar ta Nguru; inda ya fara karatun Alƙur’ani mai girma a wurin Malam Sani Dogon Ƙwami.
Bayan ya fara tasowa ne, sai ya shiga neman ilmin littattafai; inda ya tafi wani ƙauye mai suna Ƙauyen Mamuda a can ƙasar Wudil da ke Jihar Kano, inda ya yi karatu a wurin Malam Hamidu, daga bisani ya koma Ƙaramar Hukumar Nguru.
Bayan ya ɗauki kamar shekaru goma sha biyar, sai mahaifansa suka yi ƙaura suka koma Nguru (wato inda yake gardanta).
A ɓangaren sana’a kuwa, bayan ya gama karatunsa na Alƙur’ani da wasu littattafan Addinin Musulunci, sai ya fara sana’ar ɗinki, inda ya ƙware matuƙa; har ma yana da yara a ƙarƙashinsa.
Bayanin Almajirin Mawaƙa Ta Fuskar Waƙa
Ta fuskar waƙa kuwa, Kamilu taka-haye ya yi, domin bai gaje ta daga iyaye ba, sha’awa ce ta sanya shi fara waƙa; inda kuma ya fara a shekarar 2008, amma bai iya tuna waƙar da ya fara ba. Kamilu ya dai tabbatar da cewa akwai waƙar da ta fito da shi duniya aka san shi; wato waƙar da ya yi mai taken “Kai Ka Zagi Bala”.
Bugu da ƙari, Kamilu ya bayyana cewa waƙa ta yi masa komai na rayuwa, domin a dalilinta sunansa ya ɗaukaka, ya je aikin Hajji, ya mallaki kayan more rayuwa na duniya. Yanzu haka shi ne mai kamfanin Beta Studio da ke kan kwanar Total titin Zoo Road; sannan yana zaune a Birnin na Kano tare da iyalansa.
Ya yi waƙoƙi da dama a ɓangarori daban-daban, amma sunansa ya fi haskawa a ɓangaren waƙoƙin siyasa (Adamu, 2014).
Ba mu sami tsayayyiyar rana ko watan da aka haife shi ba; Har yanzu yana raye, kuma yana zaune a ɓangaren Shuwarin da ke unguwar Hausari a Ƙaramar Hukumar Nguru.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Wayon Roƙo a Adabin Baka: Nazarin Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.
Domin karanta cikakken bayani a kan Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa danna nan.
Domin karanta bayani akan Asalin Kiɗan Fiyano danna nan