So Da Shaƙuwa

0
10

Akwai hanyoyi da dama, waɗanda miji zai iya samun so da shaƙuwa mai tsanani a wajen matarsa, kamar su kyauta, kulawa, yabo, kwalliya, zantawa da sauransu.

1. Kyauta: Tana ɗaya daga cikin abubuwan da miji zai iya samun so da shaƙuwa a gurin matarsa. Saboda yawan kyauta tana ƙara danƙon ƙaunar shiga cikin fagen zandagaryar soyayya a cikin zukatan ma’aurata har da samari da ‘yan mata.

2. Kulawa: Tana ɗaya daga cikin abin da miji zai iya samun so da shaƙuwa mai tsanani a gurin matarsa. Saboda shi kan shi aure an gina shi ne akan kulawa da juna da dai sauransu. Har ila yau,idan miji yana kulawa da matarsa a kowane lokaci, zai iya samun so da shaƙuwa mara adadi, misali kamar su yawan zolaya da wasanni, sannan da bibiyar halin da take ciki da zarar ka ga yanayinta ya canza, sai ka binciko mai ke damunta, don yi mata maganin abin da ke damunta.

Yana daga cikin kulawa idan miji zai fita daga gidansa, ya zauna da matarsa su yi hira kafin ya fita wajan aikinsa, sai ya faɗa mata yana sonta yana ƙaunarta. Bugu da ƙari kuma, idan ya fita wajan aikinsa ko sana’arsa sai ya kira ta ya faɗa mata yana matuƙar ƙaunarta da kalamai masu nishaɗi, sannan ya sanar da ita halin da yake ciki a wajan aikinsa.

Haka miji zai aikata duk bayan rabin awa ko awa ɗaya ko lokaci bayan lokaci, sannan za ka iya kiranta a waya ko tura saƙo akan  waya ko takarda, idan gidan na ka a kusa yake, haka ma su mata za su aikata idan suna so su mallake mijinsu.

3. Yabo: Yana ɗaya daga cikin abin da miji zai iya samun so da shaƙuwa a gurin matarsa, saboda duk abin da mace ta aikata ko ta yi,to tana buƙatar yabawa, misali idan matarka ta yi abinci mai daɗi, sa’annan kuma  kai ka ji daɗin abinci, sai ka yabe ta sosai da irin abincin da tayi.

Bugu da ƙari ma idan ta yi kwalliya, wadda ta haɗu sosai, sai ka zuga ta ko ka yabe ta sosai, haka nan miji zai yi a duk irin abin da matarsa ta yi, haka ita za ta aikata idan tana so ta mallake mijinta.

Misali “ya zankaɗeɗiyar santaleliyar zuƙeƙiyar hamshaƙiyar tauraruwar ‘yar santimantiliyar kyakkyawar zabgegiyar gimbiyar jarumar zaƙaƙurar amaryata” Wannan kwaliyar taki ta yi kyau ko abinci ko dai waɗansu abubuwan.

4. Kwalliya: Tana  ɗaya daga cikin abin da ɗa namiji yake so, kuma zai iya janyo so da shaƙuwa a wajan matarsa, saboda ita kwalliya tana ƙarawa mutum kyau da fito da mutum sosai kamar yadda muka yi bayani a babin mutuwar aure.

6. Zantawa: Tattaunawa  tana ɗaya daga cikin abin da ke kawo so da shaƙuwa a tsakanin ma’aurata, saboda idan kana yawan magana da mutum yakan sa ku fahimci juna da samun shaƙuwa da juna, haka nan ma ma’aurata idan suna zantawa da junansu yakan sa su fahimci junansu da ƙara samun so da shaƙuwa, sannan za su fahimci abubuwan da kowannensu ya fi so a rayuwarsa da dai sauransu, Allah yasa mu dace.

Don karanta abubuwan da ke sa wa miji ya zama mafi soyuwa a wajen matarsa danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceDabarun Bunƙasa Noman Masara
Labarin na GabaBabban Kundi