Siffofin Shugaban Da Ya Kamata Mu Zaɓa

0
36

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwana al’ummar Najeriya masu daraja! Hakika na yi bincike lokaci mai tsawo a cikin Alkur’ani mai girma da littattafan tafsirai daban-daban, musamman akan ƙissar Bani Isra’ila, Annabi Shamwilu da Daluta; da ƙissar Annabi Musa, da ƙissar Annabi Dawud; da kuma Hadisan Manzon Allah (SAW) da littafan addinin Musulunci waɗanda suka yi magana akan shugabanci da muhimmancinsa da kuma siffofin irin shugaban da ya kamata ya shugabanci al’umma, domin a samu ingantaccen shugabanci nagari wanda zai amfani al’ummah baki ɗaya.

Kuma kowa ya ji daɗi, a samu zaman lafiya, haɗin kai da cigaba mai ɗorewa. Na binciki littafai irin su Ahkam Al-Sultaniyyah na Imam Al-Mawardi da Ahkam Al-Sultaniyyah na Imam Abu Ya’ala da As-Siyasah Ash-Shar’iyyah na Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah, da sauran littafai muhimmai, ire-irensu, waɗanda suka yi magana akan shugabanci da siffofin shugaba nagari.

A cikin binciken da na yi, alhamdulillahi, na fitar da siffofi guda ashirin (20), waɗanda Allah da Manzonsa (SAW) da kuma malamai suka bayyana; siffofin da ya kamata a ce duk shugaban da zai shugabance mu yana da su. Shawarwari ne da jan hankali, waɗanda addinin Musulunci ya bai wa al’umma, waɗanda ya kamata su yi la’akari da su, musamman wurin zaɓen shugaba, in dai har suna son samun walwala da ci gaba a cikin al’ummarsu.

Waɗannan shawarwari haƙiƙa, idan al’umma ta bi su wurin zaɓen shugabanni, to za su yi nasara kuma su ji daɗi. Amma kuma idan al’umma suka ƙi bin waɗannan shawarwari, suka bi son zuciyarsu, to tabbas sai sun yi dana-sani game da sha’anin lamarin shugabancinsu.
Saboda sha’anin shugabanci ba abun wasa ba ne da za mu yi wasa ko sakaci da shi, ko kuma mu taƙaita shi akan la’akari da wata jam’iyyah ta siyasa, ko kuma la’akari da yaren shugaba ko ƙabilarsa, ko yankin da ya fito, ko kuma mu mayar da shi akan tafarki na karɓa-karɓa.

Wanda duk waɗannan hanyoyi ne na shirme da shiririta! A sha’anin shugabanci, cancanta kawai ake bi da dacewa. Wanda ya cancanta kuma ya dace, shi ne ya zama wajibi mu zaɓa. Idan muka kuskura muka zaɓi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, to lallai mu sani, za mu sha wahala a nan duniya, kuma lahira za mu amsa tambayoyi a gaban Allah, akan duk wata irin gudunmawa da muka bayar wurin ɗora shugaban da muka san bai dace ba akan al’ummah!

Ya ku jama’ah! Ku sani, lallai sha’anin shugabanci ya wuce haka, kuma yafi ƙarfin haka. Bai kamata mu taƙaita maganar shugabanci da wani son zuciya ba, kasancewar duk wanda zai shugabance mu, lamarin rayuwar mu gaba ɗaya ya rataya ne akan yanayin irin shugabancin da ya yi mana.

Duk wanda ya zama shugaba a cikin mu, ya zama wajibi ya kare addininmu, da rayukanmu, da dukiyoyinmu, da hankalin mu da nasabar mu ko dangantakar mu, tare da ƙoƙarin samar mana da sauran ababen more rayuwa, domin rayuwar mu ta inganta, mu ji daɗin bautawa Allah cikin hayyacinmu.

To tun da haka ne, kenan ya zama dole, kuma wajibi mu san wanene zai shugabance mu. Ga siffofin shugaban da ya kamata ya shugabance mu kamar haka:

1. Dole ne duk shugaban da za mu zaɓa ya zamanto yana da ilimi, yana da hikima, yana da hangen nesa da ƙwarewa (Knowledge, wisdom, vision and competence).

2. Dole ne shugaba ya zamanto mai ƙarfi a jiki, mai kazar-kazar, mai kwarjini (Power/Strength).

3. Dole shugaba ya zamanto yana da hikima wurin zartar da hukunci, domin ya iya zartar da hukunci ingantacce (Sound Judgement).

4. Dole shugaba ya zamanto mai haƙuri, mai juriya, sannan mai yafiya (Patience, Tolerance and forgiveness).

5. Dole shugaba ya zamanto adali kuma marar nuna bambanci tsakanin ‘yan ƙasa (Justice and fairness).

6. Dole ne shugaba ya zamanto yana da fasaha, hikima da basira wurin isar da saƙo zuwa ga al’umma (Communication skills).

7. Dole ne shugaba ya zama mai tsoron Allah (Piety/At-Taqwah).

8. Dole shugaba ya zama mai sauƙin kai, ba mai kafiya ko kangara ba, mai kwarjini da kazar-kazar sannan mai cikakken hankali da tunani (Simplicity, emotional and spiritual intelligence).

9. Dole shugaba ya zamanto mai gaskiya ba abun zargi ba (Truth).

10. Dole shugaba ya zama lafiyayye; mai lafiyar ƙwaƙwalwa da ruhi da jiki (Sound and good health/Soundness in mental and physical condition).

11. Dole ne shugaba ya zamanto mai amana da iya riƙon amana kuma mai mutunci (Trust and Integrity).

12. Dole be shugaba ya zama mai tuntuɓa kafin ya zartar da wani abu (Consultation).

13. Dole ne shugaba ya zamanto mai iya zartar da hukunci bayan ya tuntuɓi masu ilimin fannin, ba tare da tsoro ko fargabar kowa ba (Decisiveness/Decision making ability after consultation).

14. Dole ne shugaba ya zamanto mai dogaro tare da tawakkali ga Allah, ya zamo jarumi, marar tsoro, kuma mai cikakken yaƙini (Dependence on Allah, courage, bravery and confidence).

15. Dole ne shugaba ya zamanto mai sadaukarwa wurin kowane lamari (Spirit of sacrifice).

16. Dole shugaba ya zama mai cika alkawari, kuma mai mutunta alƙawurran da ya ɗaukar wa al’umma, ba mai karya alkawari ba (Honouring the pledge).

17. Dole ne shugaba ya zamanto mai kyauta, mai alkhairi, karimi ba marowaci ba (Generosity).
18. Dole ne wanda za’a zaba ya zamanto shugaba ya kasance zai iya, kar mu zaɓi wanda muka san cewa ba zai iya ba, ko dukkanin alamu sun nuna ba zai iya ba (Capacity to govern).

19. Dole ne shugaba ya zama yana ƙoƙarin binciken kansa da kuma dukkanin ma’aikatansa. Dole ya zama mai tsantseni da kula da dukiyar baitul mali. Kar mu zaɓi shugaban da muka san cewa zai yi ƙoƙarin arzurta kansa da dukiyar al’umma. Kuma kar mu yarda mu ɗora almubazzari akan dukiyar ƙasa (Accountability/Ihtisab).

20. Dole ne shugaba ya zamanto mai faɗa da cikawa; wanda zai yi wa al’umma aiki, ba surutun banza da yawan magana ba. Kar mu ɗora wanda muka san mai faɗa ne kawai, amma ba zai cika ba (Action not just words).

Ya ku ‘yan uwa! Waɗannan kaɗan kenan daga siffofin shugaba nagari da ya kamata mu zaɓa a wannan zaɓe mai zuwa da ikon Allah. Tun daga zaɓen shugaban ƙasa har zuwa na Gwamnoni; kar mu yarda mu yi sake, ko kuma mu zaɓi shugaban da muka san bai cancanta ba ko bai dace ba.

Ku sani, ana maganar Najeriya ce fa, ƙasar mu ta gado; ƙasar da muke so kuma muke ƙauna. Ƙasar da ba mu da wani wurin zuwa idan ba ita ba. Kasa mai arziƙi, wadata da yalwa, amma rashin samar da shugabanci nagari ya sa muna ta shan wahala. Kasa mai ɗauke da al’ummomi har mutum sama da miliyan dari biyu.

Kasa irin wannan, wallahi bai kamata mu kasance masu sakaci wurin zaɓar mata shugabanni ba. Ko kuma mu rungume hannu, muna kallo a rinka ɗora mana shugabannin da mun san ba za su iya ba, ko kuma ba su dace ba, ba su cancanta ba! Ya zama wajibi mu zaɓi shugabanni nagari, waɗanda suke son mu muke son su, suke yi muna addu’a muke yi masu addu’a.

Ba shugabannin da za su rinƙa zagin mu ba muna zaginsu, suna la’antarmu muna la’antarsu. Don haka, muna kira ga al’umma baki ɗaya cewa, in dai har da gaske ne muna son Allah ya taimake mu, ƙasar mu ta gyaru, to sai kowa ya tashi tsaye wurin yin abun da ya kamata wurin zaɓen shugaba nagari, tare da yin addu’ar Allah ya kawo mana sauƙi, ya fitar da mu daga tsananin da muke ciki.

Mu gyara halayenmu da ɗabi’unmu, kuma mu yi ta addu’a da roƙon Allah ya arzurta mu da shugaban ƙasa nagari a wannan zaɓe mai zuwa; shugaba mai tausayi, mai fahimta, mai son al’umma, mai ƙwarin jiki da lafiyar jiki da ta hankali, mai son haɗin kan ƙasa, mai kishin Najeriya da ‘yan Najeriya da arewa da kowane yanki baki ɗaya; mai sauƙin kai da karɓar shawara, sannan kuma ƙwararre wurin iya mulkin ƙasa, wanda ba ɗan koyo ba kuma ba sabon shiga ba.

Mu yi fatan irin wannan shugaba Allah ya ba shi nasarar cin zaɓe a wannan zaɓe mai zuwa, kuma Allah ya ba shi nasara wurin aikata alheri a cikin shugabancinsa. Sannan game da abinda yake faruwa a ƙasarmu, game da canjin kuɗi a halin yanzu, ina kira da mu yi haƙuri. Mu sani, babu wani gyara da za a yi a duniya, kuma a ko’ina ne, ba tare da an sha wahala ba! Mu bincika da kyau mu gani, duk wata ƙasa a duniya, mu koma mu bibiyi tarihin manyan ƙasashen duniya, kafin su kai matsayin da suke akai a yau, sai da suka sha wahala sosai!!

Kai a wasu ƙasashen ma, wasu jinin su suka ba da, balle wai don muna shan wahala saboda canjin kuɗi. Malamai magana fa ake yi ta gyaran Najeriya da izinin Allah da iyawarsa! Mu yi haƙuri har a yi zaɓe lafiya a gama lafiya. Kar mu yarda a zuga mu, ko a harzuƙa mu, ko a yi amfani da mu, mu tayar da hankali, ko mu yi hargitsi, ko mu yi wata zanga-zanga ko hayaniya.

Mu sani, komai mai wuce wa ne da yardar Allah, kuma da izinin Allah, wata rana sai labari. Amma dai mu yi ƙoƙari mu zaɓi shugaba nagari a ranar zaɓe, wanda da ikon Allah, Allah zai yi amfani da shi wurin taimakon Najeriya da taimakon dukkanin ‘yan ƙasa baki ɗaya.
Kar mu yarda mu biye wa ‘yan wasu yanki masu ƙone-ƙone da kashe-kashe da tayar da hankula da zanga-zanga, domin mu irin wannan aiki sam ba tarbiyyar mu ba ce.

Sannan kar mu yarda mu biye wa wasu Gwamnoni masu ƙoƙarin harzuƙa mu da zuga mu akan mu yi tawaye, da sunan wai saboda talakawa suke yi, alhali duk wani mutum mai hankali ya san ba domin talakawa suke yi ba, domin kawunansu kawai suke yi. Kar mu taɓa yarda da duk wani abu da zai tayar da hankalin ƙasarmu mai albarka!

Sannan mu sani, duk mai hankalin da ya kai shekarun zaɓe, tabbas ya san dacewa da cancantar wanda ya kamata ya zaɓa, kar ka yarda da wai wani yasa ka zaɓi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, domin mun san irin wahalhalun da muka sha, da irin bala’in da Allah ya jarabe mu da shi. Kuma masu hikima sun ce idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira!

Kuma idan wani yasa ka zaɓi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, to ka sani, a ranar da za ka amsa tambayoyi a gaban Allah, wannan mutum ko waye shi ba ya wurin bare har ya cece ka daga azabar Allah! Wassalamu Alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.

Domin karanta Haƙƙoƙin Mabuya Akan Shugabanni danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu
labarin da ya wuceWaƙar Ilimi
Labarin na GabaKira Ga Masu Son Yin Ƙiba