Da yake ana tariyar abin da ya wuce ne game da wannan fage na Adabin Kasuwar Kano, ta yaya za a iya gane aikin adabin da za a ce na Kasuwar Kano ne idan an gan shi, ko kuma waɗanne siffofi ne za a ce su ne na Adabin Kasuwar Kano? Amsar na da sauƙi ganin cewa an riga an yi shimfiɗa game da Adabin Kasuwa na bai ɗaya a cikin babi na uku.
Saboda haka abin da aka yi a nan shi ne a fitar da kamannun da su ne za a iya gani a ce wannan na daga cikin siffofin Adabin Kasuwar Kano. Haka kuma yin hakan ya zo da sauƙi domin daga cikin siffofi na bai ɗaya da aka gani can baya game da adabin kasuwa da manazarta suka ayyana, an fahimci yana ɗauke da manyan siffofi guda huɗu:
- Adabi ne da ke yin tashe a wani zamani daga baya ya kau.
- Adabi ne da yake gudana tsakanin wasu gungun mutane kurum ba kowa da kowa ba.
- Adabi ne na kasuwa ko na yayi.
- Adabi ne da ake alaƙanta shi da wani wuri ko gari ko zamani ko yanayin da ya sami kansa.
Idan muka dubi littatafan adabin da ake yi wa laƙabi da Adabin Kasuwar Kano kamar yadda muka zayyana a baya, za a ga cewa sun shiga cikin sahun adabin kasuwa kamar yadda suke zayyane a sama.
Tun da farko wannan harka ta samo asali ne a wani ayyanannen lokaci, wato daga farkon shekarun 1980, musamman a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1984 ya zuwa farkon ƙarni na 21 inda daga lokacin ya fara salamcewa, domin harkar fim ta sha gabansa.
Saboda haka shi ma kamar sauran ayyukan adabin kasuwa irinsa, ya samu wani lokacin da ya fara da kuma lokacin da ya girma, kuma zai kasance ya koma cikin taskar tarihi a cikin wani lokaci mai zuwa. A halin yanzu dai an samu sama da shekara 25 ana aiwatar da wannan tsari na adabin kasuwa a ƙasar Hausa.
Haka kuma adabi ne na gungun matasa, ba na kowa da kowa ba, yawancin masu yin sa da karanta shi ba su wuce ‘yan shekara 18 zuwa 35 ba. Idan aka dubi samuwar wannan fasalin rubutu daga 1983, marubuta biyu ne daga cikin 13 da ake da su, suka haye shekara 25, wato Balaraba Ramat da Ƙamarradeen Imam, saura duk ‘yan ƙasa da 25 ne.
Sa’annan kuma adabi ne na ‘talakawa’, wato waɗanda suke da ƙaramin ƙarfi, ba dole sai masu kuɗi ko tajirai za su iya sayen sa ba, kamar yadda yake a gangariyar adabi. Da yake kuma adabin talakawa ne, shi kuma adabin talakawa yana zuwa da nasa siffofin na daban; daga ciki zai kasance mai sauƙin karantawa, wato mai jimloli marasa sarƙaƙiya.
Haka kuma nahawunsu zai kasance sassauƙa, ba nannauya ba. Ke nan wannan adabin yakan kasance bai da yawan shafi, ma’ana, bai ɗaukar lokaci za a iya karance shi. Idan aka dubi nazarin da aka yi a sama za a ga cewa wannan fasali ya fito fili. Yawancin littattafan sun kasance masu sauƙin karantawa ga ɗan firamare ko sakandare, haka ma wanda ya yaƙi jahilci.
Idan aka koma kan batun cewa adabin kasuwa ana alaƙanta shi da wani wuri ko zamani ko gari ko yanayi, za mu iya cewa lallai haka abin ya faru da Adabin Kasuwar Kano. Mun dai ga cewa zamanin Sarauniya Elizabeth ya haifar da Adabin Kasuwar Elizabeth a Ingila, na Kitsch ya haifar da Adabin Kasuwar Kitsch a Jamus, kasuwar Onitsha ta haifar da Adabin Kasuwar Onitsha a Nijeriya.
Saboda haka sanya wa Adabin Kasuwar Kano sunan na kasuwar Kano ya danganta ne da ganin cewa Kano tana da fitacciyar kasuwa wadda daga ko ina ana zuwa cin wannan kasuwa. Kamar yadda kasuwar Onitsha ta yi fice a duk faɗin Afrika, ta yadda duk wani littafi da aka wallafa a wannan ɓangare za a iya samun shi a wannan kasuwa ya ba da damar a sa masa wannan suna.
Ko da kuma aka gama cin kasuwar a ƙasar Inyamurai, a tsakanin shekarun 1947 zuwa 1969, kasuwar ta watse a 1975, sai aka yi wa wannan rayuwa da abin da ta haifar laƙabi da Adabin Kasuwar Onitsha (Okoro, 2002). Saboda haka ba sai an faɗa ba, tun da Kano birni ne na kasuwanci, sa wa adabin kasuwa laƙabin Kano, an yi shi ne da sani da kuma amincewar haka abin yake a tarihin adabin duniya.
Kasuwanci dai a birnin Kano ya sami gindin zama sama da shekaru dubu da suka wuce. Birnin Kano ya kasance matattarar kasuwanci da daɗewa tsakanin ƙasashen Hausa, tun zamanin cinikin bayi. Saboda haka ko da waɗannan litattafai suka soma ɓuɓɓugowa daga Kano da Kaduna, Kano suka yada zango.
Kuma daga shekarar 1984 da Talatu Wada ta fiddo littafinta, wanda shi ne ya yi wa wannan fasali mazaunin farko, Kano aka kawo shi domin sayarwa ga sassan duniya a can kuma ya samu karɓuwa sosai. Daga wannan lokaci ne Kanawa da ke bin wannan sana’a suka shiga sayar da litattafan, suna sarar duk wani littafi da ya fito, su dinga biyan marubuta a hankali.
Wasu masu sayar da litattafan suka shiga buga litattafan da kansu, wato su bayyana wa marubuci irin labarin da suke so a rubuta, su kuma sa kuɗi su buga, su rarrabar, su sami riba, (Adamu, 1998 da 2002).
Shafuka
Rashin yawan shafuka kamar yadda bincike ya nuna bai rasa nasaba da dalilai da dama. Na farko, tunanin yawancin marubutan irin waɗannan littattafai bai cika cokali ba, don haka ko sun tashi yin tunani mai zurfi don su tsawaita labarin, sai ka ga zaren ya tsinke, sun ƙuge ga shafuka 40 zuwa 80.
Daga baya ne dabarar tsinka labaran ta shigo ga marubutan, domin su ninka ribar da suke samu. Wannan shi ya haifar da littafi na ɗaya da na biyu, ko uku, ko ma fiye, kamar yadda aka sami irin wannan siffa a ayyukan adabin Onitsha.
Ƙila abin da wani zai tambaya shi ne me ya sa littattafan za su kasance marasa yawan shafi? Kamar yadda bincike ya nuna, yawancin marubutan da suka yi tashe daga 1984 zuwa 1991, an fahimci cewa ba su yi zurfi a ilmin zamani ba. Alal misali Ado Gidan Dabino, bai yi karatun zamanin ba, makarantar dare ya yi, daga baya ne ya wuce zuwa ƙaro ilimi, shi ma bayan ya zama wani abu a cikin fagen rubuta irin waɗannan littattafai.
Su kuwa sauran matan da suka shahara a wannan fage ba su wuce karatun firamare da sakandare ba, irin su Zuwaira Isa da Bilkisu Ahmed Funtua, sun isa misali. Wasu kuma sun yi tishin karatun ne bayan sun yi shekaru da gama firamare, har an yi musu aure, suka koma fagen rubutun.
Irin su Zuwaira Machika, sun zama misali. Saboda haka duk yadda irin waɗannan marubuta ke son su tsawaita littatafan, sai a ga abin ya faskara. Sa’annan kuma uwa-uba, siffar irin waɗannan littatafai ke nan, ba a yi su domin yawan shafuka ba.
Yanayin Bugu
Duk adabin da bai da wani kamfani takamaimai ko wurin ɗab’i da hukuma ta san da shi, ko kuma bai bin tsari da doka na ɗab`i kamar yadda aka tanada, to wannan adabi, na kasuwa ne. Duk wani adabi da ba a san shi a manhajar karatu ta firamare ko sakandire ko wani mataki na karatu daban da waɗannan ba, ko kuma ya bi tsarin shigar da shi cikin manhajar ba, wato ta bin doka, to wannan adabi na kasuwa ne.
Idan haka ne to da wuya irin waɗannan littattafai su kasance ba na kasuwa ba. Wannan ya zama haka ne ganin cewa ana buga su ne a bakin titi ko wurin buga littattafai da ke maƙare a cikin kasuwa. Haka kuma ba sa shiga cikin manhajar karatu kamar yadda hukuma ta tsara domin da ma ba gangariyar ba ne.
Idan har aka ga ana karanta su a sakandare ko jami’a to wani shiri ne tsakanin marubutan da malamai, ba wai hukumomin makarantun sun san da shirin ba. Ba wannan ba ma, hatta waɗanda ke wallafa littattafan ba suna wallafa su ne domin su yi ƙarƙo ne ba, a dai buga da takarda mafi sauƙi, da bango mafi arha, a kuma injuna marasa caji da tsada.
Domin fahimtar wannan siffa sosai, ya dace a gane cewa takarda kala biyu ce ake amfani da ita wajen wallafa ire-iren waɗannan littattafai; akwai news print da kuma bond. Ita newsprint tun asali ita ce ake amfani da ita, domin ta fi arha. A daidai lokacin da aka soma wannan harka, da naira ɗari biyar zuwa dubu ɗaya za a iya sayen takardar da za a buga kwafe dubu zuwa dubu biyu, Saboda haka duk tsadar littafin bai wuce naira 5 zuwa 10 daga haihuwa zuwa ƙuruciya, a kuma samu sami riba in an sayar.
Hatta bangon littafin ba da takardar ƙwarai ake buga shi ba, saboda a rage tsadarsa. Baya ga wannan masu bugawar ba su da kayan aiki na ƙwarai da suka haɗa da injuna da tawada da makamantan su. Ke nan duk wani littafin da ya sami kan sa a cikin irin wannan hali, to za a ga bugun zai kasance ba na ƙwarai ne ba, kamar dai yadda muka ga haka game da littattafan Grub Street a ƙasar Ingila da Kitsch a Jamus.
Saƙo Ko Jigo
Saƙon da litattafan Adabin Kasuwar Kano ke isar wa a fili suke, domin kamar yadda (Adamu, 2006:150) ke cewa, kusan marubuta na farkon-farkon, wato irin su Talatu Wada Ahmed mai (Rabin Raina) da sauran su, soyayya ce suka tanada a cikin littattafan nasu, ba don komi ba sai don su ne ke shere masu karatu.
Shi ya sa Adamu (2006:138) yake nuni da cewa kusan tun daga bangon litattafan za a fahimci jigonsu, saboda daga bangayen, jigon zai bayyana cewa waɗannan litattafai na soyayya ne, domin ba abin da za ka gani daga ‘In Da So Da Ƙauna’, sai ‘Dace Da Masoyi’, sai ‘Kwabon Masoyi’, sai ‘So Tsunstu’, sai ‘Ruwan Soyayyar Zuciya’, sai ‘Kibiyar Soyayya’ da dai sauransu da dama masu ɗauke da irin waɗannan sunayen.
Da tafiya ta yi tafiya sai aka fara samun wasu masu magana kan auren da yanayin auren Hausawa da matsalolin da ke tattare da su. Ya zuwa shekarar 2002 zuwa 2008 sai ya kasance saƙonnin ko jigogin litattafan sun canza fasali gaba ɗaya, domin kuwa sama da kashi casa`in da takwas na litattafan sai suka koma ba su maganar komai sai labaran soyayya, kamar dai yadda suka faro daga farko.
Sannan kuma daga abin da masu karatu suka faɗa game da saƙonni ko jigogin littattafan sai aka fahimci cewa soyayya da rayuwar zaman aure su suka fi tashe, sai kuma zamantakewar yau da kullum (Bashir, 2009:202). Sai dai domin a fidda wannan fasali fili, ya dace mu nazarci saƙonni ko jigogin waɗannan littattafai sosai.
Tuni dai (Adamu, 2006:150) ya taɓa gudanar da makamancin wannan aiki, sai dai littattafan da ya nazarta ba su wuce 453 ba. Wannan nazari ya ɗora bisa wancan, an samu ganin cewa saƙonnin da ke cikin litattafai sama da 712 da aka yi nazari sun kasance mabambanta, duk da haka dai jigon soyayya shi ne kan gaba. Ga yadda jadawalin ya kasance.
JIGO | ADADIN LITATTAFAI |
Soyayya | 250 |
Rayuwar Aure | 62 |
Zamantakewa | 164 |
Rikici | 30 |
Kishi | 27 |
Yaudara | 25 |
Biyayyar Iyaye | 12 |
Ban Dariya | 8 |
Siyasa | 12 |
Haƙuri | 20 |
Waɗanda Ba A Tantance Ba | 102 |
Kamar yadda Adamu (2006) ya nuna daga nasa binciken kimanin kashi 35 ne kaɗai suke da jigon Soyayya, sauran kashi 65 kuwa suna magana ne kan wasu jigogin na daban, amma duk da haka wai manazarta na ta sukar marubutan, da cewa sun ta’allaƙa ne kan jigon soyayya.
Amma daga nawa binciken, ana iya ganin cewa kaso mafi tsoka daga cikin littatafan da aka nazarta kusan 712 na soyayya sama da 250 ne, sai sauran jigogin da marubutan sukan taɓo.
Daga binciken da aka gudanar sauran jigogin da waɗannan marubutan sukan taɓo sun haɗa da Rayuwar aure (misali, Matsalar Mu Ce na Fauziyya D. Sulaiman,) da Kishi, (misali, Baƙin Kishi na Muhammad Lawan Barista) da Yaudara, (misali, Mayaudariya na Abubakar Umar Mani) da Rayuwar Duniya, (misali, Zaman Farko na Ibrahim Birniwa) da Haƙuri, (misali, Mahaƙurci, na Sa’adatu Saminu Kankiya) da Ban Dariya, (misali, Namijin Kunama na Balarabe Abdullahi Yola) da Biyayyar Iyaye, (misali , Tsakanin Ɗa da Mahaifi na Sanusi Hashim,) da Rikici, (misali, Sadauki Diknar na Abdulƙadir Mu’azu Isa,) da Tsaro, (misali, An Yanka Ta Tashi na Bala Anas Babinlata da dai sauransu.
Su ma idan aka yi musu nazarin ƙwaƙƙwafi za a ga cewa wasu daga cikinsu na soyayyar ne kodayake ba kai tsaye ba, amma dai suna da alaƙa da soyayyar, musamman waɗanda suka shafi rayuwar aure da kishi da makamantan su.
Bincike ya nuna cewa an samu waɗannan canje-canjen ne dangane da fasalce-fasalcen waɗannan littattafai da muke magana a kai daga mabambanta dalilai. A cikin shekara bakwai da fara wannan harkar adabi, wato lokacin da shekarar 1991 ke ƙaratowa, abubuwan sun bunƙasa sosai a wannan fage.
Wannan sabon salon rubutu ya cika da batsewa, ya kuma fantsama a ko ina a ƙasar Hausa, musamman wurin mata da matasa. Haka kuma ya kasance rubutun ya tashi daga ƙagawa da aka fara gani a rubucen-rubucen farko, sai ya koma kwashewa ko gamaɗe. Marubuta littattafan sai suka koma kwaso kayan cikin adabin daga fina-finan Indiya da majigin Turawa da Larabawa da kuma litattafan soyayyar Turawa suna mayar da su nasu.
Daga shekarar 1991, lokacin da su Ado Gidan Dabino suka yi ruwa, suka yi tsaki, harkar buga litattafan ta koma tamkar kamfani, ƙungiyoyi daban-daban suka shiga ɓullowa, tare da shugabanni da mambobi da kuma masu tallata litattafan da suke wallafawa. Wannan kamar yadda muka yi bayani a baya ya taimaka sosai wajen tabbatuwar wannan harka, wanda ya sa aka samar da litattafai sama da 1,860 zuwa shekarar 2007 (Furniss, 2007).
Bayan samun gindin zama da Adabin Kasuwar Kano ya yi, har ta kai ga sun kakkafa ƙungiyoyi domin tafiyar da harkokin rubuce-rubucensu, sai kuma sauran jama`ar gari suka bi sahu. Manazarta da `yan jarida da kuma sauran mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu kan yanaye-yanayen wannan adabi. Wasu suke yabawa, yayin da wasu kuma sun nuna irin yadda rubuce-rubucen suka dagule, musamman idan aka haɗa su da gangariyar aikin adabi da suka gabata.
Da dama mutane sun nuna rashin jin daɗinsu na yadda batsa da mugayen kalamai suka fara gurɓata al`adun Hausawa daga cikin rubuce-rubucen Adabin Kasuwar Kano. Su kuma marubutan a koyaushe ƙoƙarin kare kansu suke yi daga zarge-zargen da ake masu. Sukan nuna cewa jigon soyayya da suka ɗauka don gina ayyukansu, suna yi ne saboda ya dace da zamani ne.
Wannaan ya sanya a lokacin idan mutum ya duba kasuwannin litattafai na Hausa ba abin da zai tsinkaya sai dalar litattafai daban-daban na soyayya, irinsu; In Da Rai… ko Rabin Raina ko Budurwar Zuciya ko Furen Soyayya ko Idan So Cuta Ne. Akwai kuma irin su Garin Masoyi da Marurun Soyayya da So Marurun Zuciya da Duniya Bautar Mata da sauransu dai da dama.
Masu Sayarwa
Kamar kowane irin tsarin adabin kasuwa, Adabin Kasuwar Kano ya zo da nasa fasalin sayar da littattafan. Sai dai shi ma kamar sauran ana sayar da littatafan ne a manyan kasuwannin ƙasar Hausa da suka haɗa da Kano da Kaduna da Jos da Sakkwato da Zaria da Gusau da Gombe da Bauchi da Minna da Katsina da sauransu da dama.
Waɗanda suka taimaka a wannan fage kamar yadda Adamu (2002) ya bayyana su ne dillalai ko masu bugawa da sayarwa a kasuwannin Kano da sauran sassan ƙasar Hausa, musamman da yake a wancan lokaci ba wani shago da ake da shi da ke tallata littatafan Hausa kurum. A birnin Kano, inda nan ne harkar ta zaunu sosai akwai irin su Alhaji Baba, mai Jakara City Bookshop da Alhaji Musa Ɗanbala, mai Sauƙi Bookshop da Alhaji Garba Mohammed, mai Garba Mohammed Bookshop.
Da farko dai waɗannan shaguna suna dillancin littatafan ne da masu rubutawa ke kawo musu su sayar, amma daga baya sai suka koma masu wallafawa da bugawa su da kansu. Za su sayi littafi hannun mai shi ko kuma su sayi wanda ba a buga ba, su su buga suna sayarwa. Daga nan Kano harkar ta koma sauran biranen, su ma da manyan dillalansu da suka haɗa da irin su Alhaji Abdullah a kasuwar Sakkwato da kuma shagunan littattafai irin su Anti Bilki Bookshop a Funtua da makamantansu da dama.
Haka wannan harkar ta ci gaba da wanzuwa har ta kai an samar da shaguna da suke ba sayarwa kurum suke yi ba suna bayar da hayar waɗannan littatafai ga waɗanda ba su da ƙarfin sayen littattafan ko kuma ba su son su tara su jibgi a gida.
Masu Karatu
Masu karatun waɗannan litattafan kamar yadda muka gani a can baya mafi yawa matasa ne. Sai dai domin mu fahimci inda aka fito dangane da wannan ɓangare na bincike, na ga ya dace a bi diddigin game tunanin masu karanta waɗannan littatafai. Hanyar da aka bi domin yin haka, ita ce ta rarraba takardun neman bayanai domin a ji daga bakin masu karatu game da abubuwa da dama da suka shafi wannan harka.
Daga cikin takardun neman bayanai sama da 400 da aka rarraba a sassan garuruwan ƙasar Hausa, kamar Katsina da Kano da Kaduna da Sakkwato da Zariya da Gombe da Dutse da kuma Bauchi, an samu guda 350 da suka dawo hannu. An yi amfani da waɗannan takardun bayanai domin gane matsayin makaranta waɗannan littattafai. Ga dai fasalin rabe-raben takardun neman bayanin da aka samu.
Jadawali Na Farko: Bayanai Dangane Da Shekaru
Shekara | Waɗanda suka maido | Adadi |
1-20 | 40 | Kashi 2 |
21-40 | 287 | Kashi 97 |
41-60 | 23 | Kashi 1 |
Jimilla | 350 | Kashi 100 |
Kamar yadda muka gani a sama, mafi yawan masu karanta waɗannan litattafan da suka amsa tambayoyin neman bayani shekarunsu sun kama daga shekara 21 zuwa shekara 40. Sai kashi ɗaya waɗanda shekarunsu suka kama daga shekara 41 zuwa shekara 60. sai sauran da shekarunsu ya kama daga 1 zuwa ashirin.
Jadawali Na Biyu: Bayanai Dangane Da Addini
Addini | Waɗanda suka maido | Adadi |
Musulunci | 350 | Kashi 100 |
Kiristanci | 0 | 0 |
Jimilla | 350 | Kashi 100 |
Haka kuma an dubi addinan waɗanda suka maido bayanan daga waɗanda suke karanta waɗannan litattafan. Su kuma kashi 100 cikin ɗari dukkan su musulmi ne. Wannan shi ma bai zama abin mamaki ba, musamman ganin cewa yawancin garuruwan da aka rarraba takardun na musulmi ne.
Jadawali Na Uku: Bayanai Dangane Da Ƙabila
Ƙabila | Waɗanda suka maido | Adadi |
Hausa/ fulani | 350 | Kashi 100 |
Sauran Ƙabilu | – | Kashi 0 |
Jimilla | 350 | Kashi 100 |
Daga takardun da muka samu karɓa na neman bayanai mun fahimci cewa mafi yawan waɗanda suka yi mana bayanan Hausawa da Fulani ne, domin kamar yadda ya zo a teburi na uku, kashi ɗari na daga masu karanta litattafan Hausawa da Fulanin ne. Wannan ko bai rasa nasaba da cewa Hausawa da Fulani ke zaune inda aka rarraba waɗannan takardun neman bayanai.
Sannnan kamar yadda ya zo a teburi na huɗu a ƙasa, mai nuna matakin ilimin waɗanda suka amsa tambayoyin namu, mun ga cewa matakin ilminsu bai yi zurfi ba, domin sun kama daga matakin sakandare, mai kashi 27 cikin 100 ne, zuwa matakin karatun difloma ko NCE, ko kuma wata babbar shedar karatu, masu kashi 70 cikin 100. Sai dai akwai waɗanda suka yi digiri masu rabin kashi da kuma waɗanda suka yaƙi jahilci masu kashi ɗaya. Sai kuma masu ilmin addini kurum, masu kashi ɗaya su ma.
Jadawali Na Huɗu: Bayanai Dangane Da Matakin Ilimi
Matakin ilimi | Waɗanda suka maido | Adadi |
Ilimin addini | 14 | Rabin kashi |
Ilimin sakandire | 120 | Kashi 27.1 |
N.c.e/difloma | 148 | Kashi 70 |
Digiri | 10 | Rabin kashi |
Yaƙi da jahilci | 58 | Kashi 1 |
Jimilla | 350 | Kashi 100 |
Dangane da garuruwan da waɗanda suka amsa tambayoyin suka fito, wannan binciken ya nuna cewa Katsina (da kashi 40) da Kano (da kashi 34), nan ne aka samu yawancin amsar tambayoyin bayanan da aka nema. Katsina dai ba abin mamaki ba ne, domin mai binciken a nan yake da zama, ke nan ana iya samun takardun neman bayanin da suka dawo masu yawa a nan. Kano dama can ake sayar da litattafan, saboda haka ba abin mamaki ba ne don an samu amsar tambayoyi da dama daga can. Haka akwai sauran sassan garuruwan da aka dawo da amsoshi kamar yadda yake a teburi na ƙasa.
Jadawali Na Biyar: Bayanai Dangane Da Gari
Gari | Waɗanda suka maido | Adadi |
Katsina | 142 | Kashi 40 |
Kano | 92 | Kashi 34 |
Gumel | 2 | Rabin kashi |
Sokoto | 40 | Kashi 10 |
Bauci | 2 | Rabin kashi |
Gombe | 2 | Rabin kashi |
Zariya | 25 | Kashi 5 |
Kaduna | 45 | Kashi 10 |
Jimilla | 350 | 100 |
Jadawali Na Shida: Bayanai Dangane Da Jinsi
Jinsi | Waɗanda suka maido | Adadi |
Namiji | 112 | Kashi 30 |
Mace | 178 | Kashi 65 |
Ba jinsi | 60 | Kashi 5 |
Jimilla | 350 | Kashi 100 |
Dangane da jinsin waɗanda suka mayar da takardu kuwa, daga binciken da aka gudanar a teburi na 6, ya nuna cewa kashi 65 daga cikin waɗanda suka mayar da bayanai mata ne, sai mai bi musu, maza, masu kashi 30. Akwai kuma waɗanda ba su bayyana jinsinsu ba.
Jadawali Na Bakwai: Bayanai Dangane Da Sunan Adabin Kasuwar Kano
Shekara | Waɗanda suka maido | Adadi |
1-20 | 20 | Kashi 1 |
21-40 | 320 | Kashi 98 |
41-60 | 10 | Kashi 1 |
Jimilla | 350 | Kashi 100% |
Daga binciken da aka yi sama da kashi 98 sun san da ana kiran waɗananan littattafan da littattafan soyayya ko kuma Adabin Kasuwar Kano, ƙalilan ne daga ciki ba su sani ba, su ma kuma ɗin daga abin da aka kalato, rashin sanin nasu ba ya rasa nasaba da cewar ko dai ba su mai da hankali ba ne ko kuma suna yin karatun ne ba tare da sanin ana kiran su da wani suna ba, face Hadisan Kano da suka ce suna jin ana kiran su da shi.
Yawancin waɗanda suka san da sunan littattafan Littattafan Soyayya ko Adabin Kasuwar Kano, matasa ne masu shekara 21 zuwa 40 kamar yadda yake a teburin na bakwai. Mafi rinjaye daga masu karatun da suka san da waɗannan sunaye da ake kiran waɗannan littattafai da su suna karanta littatafan domin. kusan kashi 70 na waɗanda aka nemi bayanansu, suna karanta litattafan musamman matasa, kamar yadda muka gani a teburi na uku.
Sai dai wasu daga cikin waɗannan kashi ɗin suna ganin cewa sunan da ake kiran waɗannan littattafai da shi bai dace da shi ba. Kusan kamar kashi uku na daga wannan kason suna ganin bai dace a rinƙa kiransu da Adabin Kasuwar Kano ba, sai dai a kira su da litattafan soyayya ko kuma a canza masu wani suna daban.
Jadawali Na Takwas: Bayanai Kan Inda Ake Sayen Litattafan
Inda ake sayen litattafan | Waɗanda suka maido | Adadi |
Kasuwa | 345 | Kashi 99.9 |
Kantunan saida litattafai | 5 | ½ |
Jimilla | 350 | Kashi 100 |
Sannan dangane da kuɗaɗen da ake sayen littattafan ma bayanai sun zo daidai, domin akasarin amsoshin da aka maido sun nuna kuɗin littattafan sun kama daga Naira 40 zuwa Naira 200.
Dangane da maganar ba da hayar waɗannan littattafan, su ma ɗin kusan kaso 80 cikin 100 na waɗanda suka amsa tambayoyin sun tabbatar da cewa sun san ana ba da hayar waɗannan littattafai. Kashi kamar ishirin ne ba su sani ba, su ma ɗin wataƙila don sayen littattafan kawai suke yi, ba su mai da hankali ga lura da cewar ana ba da hayar ba.
Jadawali Na Tara: Bayanai Dangane Da Ko Ana Ƙaruwa Da Karatun Litattafan.
Sama da kashi 85 cikin 100 da suka amsa tambayoyin sun nuna ba su ƙaruwa da komai daga karanta waɗannan littattafan, suka ci gaba da cewar suna karanta litattfan ne kawai ko dai don rashin abin yi ne ko kuma don nishaɗi. Kaso kamar 15 cikin 100 su ne suka ce suna ƙaruwa da saƙonnin littattafan, kuma daga cikinsu mafi yawanci mata ne suka ce suna ƙaruwar da ko dai zaman aure ko kuma soyayya ko mallake miji da dai sauransu.
Sannan kuma ko a maganar darussan da ke cikin litattafan maganar ba ta canza zane ba, saboda abin da aka zaƙulo, masu karatun sun nuna cewa sun fi sha’awar daga na soyayya, sai zamantakewar aure ko rayuwar jama’a da dai sauransu. Ga dai yadda fasalin yake a teburi na ƙasa.
Ana ƙaruwa da karatun litattafan
|
Waɗanda suka maido | Adadi |
Eh | 15 | 15 |
A a | 335 | 85 |
Jimilla | 350 | Kashi 100 |
Dangane da masu sana’ar ta ko dai rubuta litattafan ko kuma buga su, su ma babu abin da suke cewa da ya wuce sun shiga harkar ne don bunƙasa adabi, sai kuma don neman kuɗi. Wasu sun nuna cewar lallai harkar akwai riba, amma wasu sun nuna cewa babu wata riba sai dai a yi don bunƙasar adabin kawai. Haka kuma kan maganar matsalolin da suke fuskanta wajen rubutun, maganar kuɗi ita ce gaba, sai kuma kayan aiki na ɗab’i da sauransu.
Bayanai Dangane Da Sauran Tambayoyin Bincike
Dangane da tambayar da aka yi na a kawo sunayen wasu daga cikin litattafan da aka karanta, mafi yawanci sun yi ƙoƙarin kawo waɗanda suka karanta ɗin na ainihi, wasu kuma suna haɗawa har da litattafai irin su Ruwan Bagaja da Shehu Umar da sauransu, wanda ya ƙara tabbatar da cewa ba duka suke iya bambancewa tsakanin abin da ake kira Adabin Kasuwa da gangariyar adabin ba.
Sannan kuma bayanai sun nuna cewa kusan kashi 99.9 na daga cikin takardun da aka maido amsar kan inda ake sayen litattafan sun nuna cewa nan a kasuwa ne, domin kuwa abin da ake faɗa daga amsoshin yawanci suna nuna cewa daga kasuwa ko dai ta Kurmi a Kano, ko kuma ta Abubakar Rimi a Kanon, ko bakin Bata a Kanon, ko kuma Kasuwar Bacci a Kaduna ko kuma kasuwar `Yarkutungu a Katsina ko babbar kasuwar Sakkwato, a Sakkwato ko kuma shagunan sai da littattafai da finafinan Hausa a waɗannan garuruwan da aka gudanar da binciken.
Kashi ƙalilan ne kawai suka ce sukan sayi wasu daga cikin littattafan a shagunan sai da litattafai na zamani. Amma fa a kula, ko su ɗin littattafan da sukan ce sun saya, suna daga cikin tsofaffin litattafn Hausa ne kamar su Ruwan Bagaja da Shehu Umar da Iliya Ɗanmaiƙarfi da sauran litattafan da suka fito a wancan zangon.
Saboda haka daga abin da muka gani daga waɗanda suka amsa tambayoyin namu, kusan dukkan litattafan nan da ake wa laƙabi da litattafan Adabin Kasuwar Kano, ana sayen su ne a kasuwanni ko shagunan sai da finafinan Hausa da littattafan, kamar dai yadda ya zo a teburi na takwas.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Danna nan ka karanta Nazarin Rayuwar Adabin Kasuwar Kano
Edita@rumasau-kallamu