Buzaye mutane ne waɗanda suke zaune rukuni-rukuni a cikin Hamadar Sahara da kuma a yankin Sahel da yake cikin Afrika ta Yamma.
Buzaye sun kasu zuwa manyan rukunoni uku kamar haka; akwai na Tassili-ni-Ajjar da na Ahaggar da kuma na Adrar-n-Ifoghas (Labaran, 1975:1). Al’ummar Buzaye suna zaune a bisa tsarin zamantakewar rukunoni. Kowane rukuni yana tafiyar da harkokinsu a ƙarƙashin wasu shugabanni.
Akwai Amanokal waɗanda su ne dattawa masu bayar da shawara kan dukkan abin da ya shafi al’ummarsu. Imajeghen su ne mayaƙa kuma suna ƙarƙashin ikon Imghad waɗanda su ‘ya’ya aka haife su. Akwai kuma “Ineslemen”waɗanda su suke yin sasanci da alƙalanci da tafiyar da harkokin addinin Musulunci a tsakanin Buzaye.
Daga nan, sai Enadan watau baƙaƙen maƙera da Ikanawan masu ginin tukwane, daga ƙarshe sai baƙaƙen bayi da ake kira Iklan, idan suka sami ‘yanci ana kiran su da sunan Iderfan. Baƙaƙen Buzaye sun fi jajaye yawa (Hammani, 1975:194).
Ko da yake mafi yawancin Buzaye makiyaya ne waɗanda suke yawace-yawace domin neman wuraren da za su yi kiwon dabbobinsu, waɗanda suka haɗa da raƙuma da awaki da tumaki da dawaki da jakuna da sauransu, amma wasu daga cikinsu kamar Enadan da Ikanawan da Iklan suna zaune a garuruwa irin su Agades wanda a yanzu shi ne babban birninsu da kuma Arlit da Tchivozum da Iferouom da Ingel da Adeɓbissinat da Tchimia da Tabelot da Aoudaɓas da Elmiki da Egadawel da Dabaga da dai sauransu (Hira da AHSAMA, 20/5/2005).
Bayan kiwon dabbobi Buzaye suna yin noma da ‘yan aikace- aikacen ƙodago don samun kuɗin ɓatarwa kuma suna yin kasuwanci. Daga cikin abubuwan da suke nomawa akwai dabino da kayan marmari. Akwai tsohuwar dangantaka tsakanin Buzaye da Hausawa wadda ita ce ta taimaka wajen shigowar Buzaye ƙasar Hausa.
An bayyana cewa sakamakon mamayewar da Larabawa suka yi ko’ina cikin ƙasar Buzaye, an tilasta wa wasu daga cikinsu yin ƙaura suka yiwo kudu har zuwa cikin ƙasar Hausa. Haka kuma shigowar Turawan Faranshi cikin ƙasar Buzaye wadda ta haifar da zanga-zangar da Buzaye suka yi daga shekarar 1916 zuwa 1918 ta ƙara taimakawa wajen yin ƙaurar Buzaye suka yi kudu har zuwa cikin ƙasar Hausa (Labaran, 1975:1).
Bayan wannan an bayyana cewa dangantakar jini da al’adu da kasuwanci sun ƙara taimakawa wajen shigowar Buzaye ƙasar Hausa. Kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka na Faranshi da na Ingilishi a ƙasashen Sudan ta tsakiya, wasu al’ummomi haɗe suke da juna a ƙarƙashin sarki ɗaya. Zuwan Turawa da kuma ƙirƙiro iyakokin zamani ya raba al’umma ɗaya zuwa ƙasashe biyu.
A iya ganin haka a tsakanin Maraɗi da Katsina da kuma tsakanin Tchibiri da Zamfara, inda Maraɗi da Tchibiri suka faɗa cikin Jamhuriyar Nijar, Katsina da Zamfara aka bar su cikin Tarayyar Nijeriya. Waɗannan al’ummomi waɗanda suke cikin ƙasar Hausa sun yi iyaka da ƙasashen Buzaye, wannan maƙwabtaka ta ƙara taimakawa wajen yin cuɗanya a tsakaninsu wadda ta haifar da auratayya. Ta haka ne aka sami shigar al’adun Buzaye cikin al’adun Hausawa, haka kuma aka sami shigar al’adun Hausawa cikin na Buzaye.
Wani al’amari wanda ya ƙara taimakawa wajen shigowar Buzaye ƙasar Hausa shi ne yaƙin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wanda ya gudana a tsakanin shekarun 1804 zuwa 1809. A wannan yaƙi wasu Buzaye sun taimaka wa rundunar Shehu Ɗanfodiyo, wasu kuma suka taimaka wa sarakunan Gobir. An bayyana cewa Buzaye waɗanda ake kira Kel Geres da Itesan suna zaune a cikin ƙasar Hausa tun lokaci mai tsawo da ya gabata.
A saboda haka sun ɗauka yawan rundunonin Gobirawa na da ƙarfi sosai wanda za su iya cinye rundunar Shehu Ɗanfodiyo da yaƙi. Wannan ne ya sa suka bayar da goyon bayansu ga Sarakunan Gobir. Amma Buzaye Ineslemen da magoya bayansu sun yi mubayi’a ga rundunar Shehu Ɗanfodiyo, kuma suka shiga aka yaƙi Gobirawa tare da su (Hammani, 1975:197,198).
A Kano an bayyana cewa Buzaye ne daga Agades suka kafa unguwar Agadasawa a cikin Birnin Kano tun lokaci mai tsawo da ya gabata. An ƙara da bayyana cewa tsakanin shekarar 1916 zuwa 1919 Buzaye kimanin dubu talatin (30,000) suka yi ƙaura daga ƙasarsu suka shigo ƙasar Hausa. Waɗannan Buzaye sun baro ƙasarsu ne suka zauna a garuruwa da ƙauyukan cikin ƙasar Hausa.
Wannan kuwa ya faru ne sakamakon zanga-zanga da tawayen da suka yi wa Turawan Mulkin Mallaka na Faranshi. Mafi yawa daga cikin ire-iren waɗannan Buzaye sun zaɓi su zauna a garin Kano da ƙauyukan da suke kusa da ita fiye da sauran garuruwan ƙasar Hausa kamar Zariya da Katsina da dai sauransu. Wannan kuwa ya faru ne saboda Kano ta fi sauran waɗannan garuruwa samun wuraren yin aikace-aikacen samun kuɗi, kuma a Kano akwai ‘yan uwa da abokan arziki waɗanda suke zaune a nan shekaru da dama da suka gabata.
Waɗannan Buzaye suna zaune a wurare daban-daban cikin Birnin Kano musamman wuraren da suke da kamfanoni da gidajen attajirai waɗanda ake ɗaukar su aikin gadi, kuma suna sayar da shayi. Amma aikin gadi shi ne babban aikin da aka san mafi yawancin Buzaye da suka shigo ƙasar Hausa suke yi domin samun kuɗi (Baƙo, 1990: 138,140). Dangane da shigowar Buzaye ƙasar Katsina an sami bayanin da ya nuna sun shigo wannan ƙasa tun fiye da shekaru ɗari biyu da suka wuce. Waɗanda suka shigo suna da yawan gaske kuma a ƙasar Mani suka fara sauka.
Daga can ne wasu suka ƙara yin kudu waɗanda a yanzu ana samun zuri’arsu a garuruwan da suke kusa da Katsina kamar Kaita da Jibiya da Mashi da Dutsi da Kankiya da Rimi da Charanci da Kusada da Ingawa da Musawa da Safana da Kurfi da Dutsin-ma da Batsari da kuma cikin Birnin Katsina da ƙauyukan da suke ƙarƙashin mulkin waɗannan garuruwa (Hira da MGƊ, a garin Mani, a ranar 14/7/2005).
Ire – iren waɗannan Buzaye sun kasu zuwa kashi-kashi kamar haka; akwai masu tsagar ɗunkin huɗu da tukarci da makitanawa waɗanda su bayin Buzayen Tassawa ne. Wasu Buzayen sun shigo ƙasar Hausa ne a sakamakon kasuwancin da ya gudana tsakaninsu da mutanen ƙasar Hausa. Bayanai sun nuna tun kafin ƙarni na goma sha tara akwai hulɗar kasuwanci wadda aka gudanar ta hanyoyin kasuwanci waɗanda suka biyo cikin ƙasashen Buzaye.
Daga nan suka ratsa ta cikin hamadar Sahara zuwa wasu sassan ƙasar Hausa da kewaye. A lokacin da ake gudanar da wannan kasuwanci Buzayen da suke shigowa ƙasar Hausa suna safarar kayayyaki daga ƙasarsu waɗanda suka haɗa da dabbobi da dabino da kanwa da balma da manda da kayan hawan dawaki irin su sirdi da linzami da mashinfiɗan sirdi da kayan ado da dai sauransu. Bayan sun sayar suna sayen kayayyaki daga ƙasar Hausa don kai wa kasuwannin ƙasarsu.
Ire – iren kayayyakin da suke saye daga kasuwannin ƙasar Hausa sun haɗa da abinci kamar gero da dawa, suna kuma sayen suturu irin waɗanda aka saƙa a ƙasar Hausa da baba da shunin gadi da auduga da dai sauransu.
Haka su ma Hausawa suna yin safarar kayayyaki daga ƙasar Hausa zuwa ƙasar Buzaye, kuma suna sawo kayayyaki daga wannan ƙasa zuwa ƙasar Hausa. Ta irin wannan kasuwanci ne wasu Buzaye suka yi zamansu a wasu garuruwa na ƙasar Hausa kamar Kano da Katsina da Zamfara da Gobir da kuma ƙauyukan waɗannan garuruwa (Labaran, 1975:11 – 15).
Dalilin kasuwanci da wasu hulɗoɗi wasu Hausawa sun yi ƙaura daga ƙasar Hausa zuwa ƙasar Buzaye, kuma suna zaune a can shekaru da dama da suka wuce. Tsakanin Buzayen da suka shigo ƙasar Hausa da kuma Hausawan da suka shiga ƙasar Buzaye an sami dangantaka mai inganci wadda ta haifar da musayar al’adu da auratayya a tsakaninsu.
A nan al’adun Buzaye waɗanda suka shafi aure da haihuwa da mutuwa sun shiga kuma suka yi naso cikin al’adun Hausawa. Haka nan ma irin wannan ta auku ga al’adun Buzaye. Wani babban al’amari da ya faru a sakamakon wannan cuɗanya shi ne, Buzayen da suka shigo ƙasar Hausa shekaru aru-aru da suka wuce, kuma suka yi zamansu cikin ƙasar Hausa sun rikiɗe sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’adu, amma wannan al’amari bai shafi Hausawan da suka koma ƙasar Buzaye ba. Don kuwa ba su yada harshensu da adabinsu da al’adunsu ba.
Nason Al’adun Buzaye A Kan Wanzancin Hausawa
A wurin Buzaye ana gadon wani ɓangare na sana’ar wanzanci, haka kuma akwai sashen da ba sai an gada ba kowa yana iya yi. Waɗanda suka gaji yin sana’ar wanzanci su ne ake kira da sunan “aghachaou”, kuma su ne suke yin ayyuka irin su cire belun-wuya da kaciya da tsagar gado da ta kwalliya. Amma sauran ayyuka musamman aski kowa yana iya koyo ya riƙa ba dole sai wanda ya gada ba. Dangane da wannan bincike an gano akwai wasu al’adun Buzaye waɗanda suka yi naso cikin wanzancin Hausawa a waɗannan fannoni.
Cire Belun-wuya
A al’adar Buzaye a lokacin da aka cire wa jariri ko yaro belun-wuya, sai a jiƙa kanwa da ruwa a ɗiga wa wannan jariri ko yaron ruwan don maganin tsayar da jini da kuma saurin warkewar wurin da aka yi yankan. Haka kuma wanda aka cire wa belun zai sami sauƙin zafi da ciwo a cikin maƙogaronsa inda aka cire belun (AHSAMA, Jamhuriyar Nijar, a ranar 20 ga watan Mayu 2005).
Wannan al’ada ta yi naso sosai a wurin Hausawa, don kuwa a wannan zamani a mafi yawancin sassan ƙasar Hausa idan aka cire wa jariri ko yaro belun-wuya, sai wanzamin ya umurci iyayen yaron da su jiƙa kanwa da ruwa a ba wannan jariri ko yaron ruwan ya sha domin maganin tsayar da jini da saurin warkewa da kuma sauƙin zafi da tsananin ciwo a cikin maƙogaro kamar yadda Buzaye suke amfani da shi (Hira da MASASKM, a fadar Sarkin Katsinan Maraɗi, Jamhuriyar Nijar, a ranar 2 ga watan Maris, 1998) .
Aski Da Ladar Da Ake Biya
A lokacin da aka haifi jariri, a al’adar Buzaye ana iya yi masa aski a kowace rana ake so, ba dole sai an keɓe wata takamaimar rana ba. Mafi yawancin lokaci Buzaye sun fi yi wa jariransu aski kafin ranar suna watau kwana biyu ko uku ko huɗu da haihuwa. Haka kuma a al’adarsu ba wanzaman gado ne suke yin irin wannan aski ba, baƙaƙen maƙera waɗanda su abokan wasan Buzaye ne suke yin irin wannan aski.
Idan suka gama aski ba a biyan su da wasu kuɗi, suna ɗibar nama ne daga dabbar suna wadda aka yanka, sannan kuma ana ƙara masu da abinci (Hira da AAASA, Jamhuriyar Nijar, a ranar 20 ga watan Mayu, 2005).
Irin wannan al’ada ta yi naso a cikin wanzancin Hausawa, don kuwa a wannan zamani akwai wasu Hausawa waɗanda ke yi wa jariran da aka haifa aski kwana biyu ko uku ko huɗu da haihuwarsu. Ire-iren waɗanda suke koyi da irin wannan al’ada ba sa bari sai ranar suna su yi wa jariransu aski.Haka kuma wajen biyan ladar askin suna biyan wanzamin da ya yi askin da abinci da naman dabbar suna kamar yadda Buzaye suke yi.
Wannan al’ada ta yi tasiri a kan wanzanci saboda wanzaman Hausawa da suke yi wa ‘yan’uwansu waɗanda suka yi koyi da wannan al’ada ta saɓa yadda ake yin wannan sana’a a ƙasar Hausa a inda ba a yi wa jariri askin suna sai ranar suna ko bayan an yi suna (Hira da MGƊASASƘ, a fadar Mai Martaba Sarkin Ƙwanni-Birnin Ƙwanni, Jamhuriyar Nijar, a ranar 3 ga watan Maris 1998).
Nason Al’adun Buzaye A Kan Tsagar Gado
Akwai wasu Hausawa waɗanda saboda wasu dalilai suke barin tsagarsu ta gado su ɗauki irin ta Buzaye. Misali, a ƙasar Katsina akwai wasu daga cikin mutanen wannan ƙasa waɗanda suka bar yin tsagar gado irin ta Katsinawa watau bille suka ɗauki irin ta Buzaye. Wannan kuwa ya faru ne saboda irin muzantawa da ƙyama da wasu Hausawa suke nuna wa masu irin wannan tsaga ta Katsinanci.
Saboda hulɗa wadda take tsakanin ire-iren waɗannan Katsinawa da Buzaye, sai suka riƙa kwaikwayon yin tsagarsu a matsayin wadda suka gada. A nan ma wannan al’ada ta Buzaye ta yi naso a kan sana’ar wanzanci saboda wanzaman Hausawa ne suke yi wa waɗannan Hausawa irin tsagar Buzaye, ba wanzaman Buzaye ne suke shigowa ƙasar Hausa don yin ire-iren waɗannan tsaga ta Buzaye.
Nason Al’adun Buzaye Kan Aski
Al’ummar Buzaye na yi wa ‘ya’yansu tukku a ƙeya wanda ba sa aske shi sai lokacin da wannan yaro ya yi girma sosai ya isa aure. Irin wannan al’ada ya yi tasiri a kan wasu Hausawa musamman waɗanda suke zaune a ƙasar Buzaye da kuma wasu sassan ƙasar Hausa waɗanda suke maƙwabtaka da ƙasar Buzaye irin su Katsina da Daura da Maraɗi da Ƙwanni da Kano da Zamfara.
Wannan kuwa ya faru ne saboda a wannan zamani akwai wasu Hausawa waɗanda suke yi wa ‘ya’yansu irin wannan tukku a matsayin na gado (Hira da MGƊASASƘ, a Birnin Ƙwanni da kuma MASASKM, dukkansu a Jamhuriyar Nijar a ranakun 3 da 4 ga watan Maris 1998).
Nason al’adun Buzaye a irin wannan aski ya fito ne saboda wanzaman Hausawa ne suke yi wa Hausawa waɗanda suka yi kwaikwayon yin irin wannan nau’i na aski ba wanzaman Buzaye ne suke shigowa ƙasar Hausa su yi wa Hausawa ba.
Karanta Shigowar Barebari Ƙasar Hausa
Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU ya wallafa WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA
MAYU 2009/JUMADA ULA 1430
Edita@rumasau-kallamu