Shigowar Ƙananan Ƙabilu Ƙasar Hausa

0
36

Sauran Ƙabilu

Bayan waɗannan al’ummomi da aka yi bayani kan shigowarsu ƙasar Hausa akwai wasu ƙananan ƙabilu waɗanda suke maƙwabtaka da suka shigo. Misali, a kudancin Jihar Kaduna akwai ire-iren waɗannan ƙananan ƙabilu waɗanda suka haɗa da Katab da Morwa da Kaje da Kagoro da Jaba da Kaningkon da Ninzam da Ayu da Kadara da Gwari da Gwandara da Kagoma da sauransu.

Akwai wasu kuma a yankin Filato waɗanda suka haɗa da Birom da Angas da Ganawuri da Sayawa da sauransu. A jihohin Bauchi da Gwambe akwai wasu ƙananan ƙabilun kamar Gerawa da Terawa da Jerumawa da Ganjuwa da Denawa da Kanakuru da Tangale da Waja da dai sauransu. A ƙasar Hausa ta yamma akwai wasu ƙananan ƙabilun da suke zaune a yankin Yawuri da Kwantagora waɗanda suka haɗa da Dakarkari da Kambari da Kamuku da dai sauransu.

Shigowar Ƙananan Ƙabilu Ƙasar Hausa

Akwai daɗaɗɗiyar dangantaka a tsakanin Hausawa da waɗannan ƙananan ƙabilu masu maƙwabtaka da ƙasar Hausa. Mafi yawa daga cikin waɗannan ƙananan ƙabilu sun zauna a ƙarƙashin mulkin sarakunan ƙasar Hausa waɗanda suke maƙwabtaka da su. Misali, ƙabilun da suke kudancin jihar Kaduna sun zauna a ƙarƙashin mulkin Sarkin Zazzau tun cikin ƙarni na goma sha takwas, wanda shi ya sa a yanzu ake kiran su da sunan ƙabilun kudancin Zariya (Adeleye, 1975:593).

Ta wannan hanya ce al’ummomin waɗannan ƙananan ƙabilu suka riƙa hulɗoɗi da Hausawa. Ta hanyar waɗannan hulɗoɗi mafi yawa daga cikin al’ummomin waɗannan ƙabilu da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa koyon harshen Hausa wanda ya zama harshe na biyu gare su bayan harshen da suka gada.

Haka kuma harshen Hausa ya zama harshen da kowa da kowa daga cikin su yake amfani da shi wajen sadarwa da kasuwanci da addini da sauran ma’amalolin rayuwa na yau da kullum a tsakaninsu da sauran al’ummomin da suke cikin ƙasar Hausa da kuma waɗanda suke maƙwabtaka da su. A sakamakon wannan dangantaka ne, a yanzu harshen Hausa yake ƙoƙarin mamaye waɗannan ƙananan harsuna da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa.

Idan muka juya kan shigowar al’ummomin waɗannan ƙananan ƙabilu cikin ƙasar Hausa, za a ga mafi yawancinsu sun shigo a cikin ƙarni na ashirin. Wannan kuwa ya faru ne a sakamakon kafuwar mulkin mallaka wanda ya haɗa waɗannan al’ummomi wuri ɗaya a ƙasa ɗaya.

Kamar yadda wasu daga cikin waɗannan al’ummomi suka shigo cikin ƙasar Hausa, akwai wasu Hausawa da suka yi ƙaura daga ƙasar Hausa suka shiga ƙasashensu. Misali, a sakamakon samun kuza da kwaranda a ƙasashen da suke kudancin Zariya da yankin Filato tun cikin shekarun 1920, an sami Hausawa waɗanda suka yi ƙaura daga Kano da Katsina da Zariya da Sakkwato suka koma waɗannan ƙasashe.

A wuraren da suke zaune sun riƙa yin hulɗa da al’ummomin wuraren, wannan ya sa sun auri mata ‘yan ƙasar suka mayar da su Hausawa (Hira da GMW, a garin Godo- Godo da kuma MIM, a garin Kafanchan, a ranar 24/8/2004).

Nason Al’adun Sauran Baƙi Kan Wanzancin Hausawa

Sauran baƙi a nan ana nufin ƙananan ƙabilu waɗanda suke maƙwabtaka da Hausawa daga kudu da kudu-maso-gabas da kuma kudu-maso-yamma da ƙasar Hausa. Dangane da wannan bincike an duba ƙabilun Dakarkari da na kudancin jihar Kaduna da kuma ƙabilar Tera a jihar Gwambe.

A nazarin da aka gudanar a waɗannan ƙabilu an fahimci nauyin al’adunsu cikin wanzanci ba shi da yawa. Wannan kuwa ya faru ne saboda yadda al’adun Hausawa suka taushe al’adunsu ta yadda a wannan zamani wasu daga cikin al’adunsu sun fara ɓacewa na Hausawa na maye gurbinsu. Amma duk da haka ga ɗan abin da aka samu.

Magungunan da Wanzamai Suka Samo Daga Wurin Dakarkari

Hausawa sun sami wasu magunguna daga wurin Dakarkari mazauna ƙasar Zuru a cikin Jihar Kebbi. Ire-iren waɗannan magunguna sun haɗa da na ƙarin ƙarfin azzakari. A wannan magani ana samo sauyoyin wani icce da ake kira jan yaro, sai a taho da su gida a sanya aska ko wuƙa a kankare su sosai.

Daga nan sai a ɗebo gero daidai gwargwadon wanda idan an yi kunu da shi mutum zai iya shanye shi, sai a sanya wannan bayan sauyoyin jan yaro da aka ɗebo a cikin tukunya a tafasa a dama kunun salala. Wannan kunu ne mutum zai yi ta sha sannu a hankali zai ji azzakarinsa ya yi ƙarfi sosai.

Wani magani da Hausawa suka samu daga Dakarkari shi ne, na nuna buwaya. Ana samun ƙanzon tuwo da aka yi a gidan wanda zai yi amfani da maganin, sai a ɗebo sassaƙen iccen gamji a daka shi.

Daga nan sai a haɗa garin wannan magani da ƙanzon tuwo a sa a ruwa a cakuɗa su a yi mulmule uku, za a riƙa cin mulmule ɗaya a kullum har zuwa kwana uku. Idan aka yi haka mutum zai buwaya a duk duk wurin da yake. Idan aka yi kuskure aka ci sau huɗu, to mutumin zai zama maye (AGMSAZ, 21/5/2005).

Magungunan da Wanzamai Suka Samu Daga Wurin Terawa

Tera wata ƙabila ce wadda ake samu a wuraren da suka haɗa da garuruwan Gwani ta gabas da Gwani ta Yamma a Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba a Jihar Gwambe. Al’ummar Tera tana tafiyar da al’adun wanzanci kamar yadda Hausawa suke tafiyar da nasu. Wannan dalili ya sa aka sami kamanci da bambanci dangane da yadda suke tafiyar da wannan sana’a a tsakaninsu.

Haka kuma akwai fahimtar juna a tsakaninsu wadda ta haifar da musayar al’adu. A saboda wannan dalili ne wanzaman Hausawa suka sami maganin ƙurajen aski daga wurin Terawa.

A lokacin da aka yi wa mutum aski don maganin ƙurajen aski, sai ya sami buri na hura-hura wadda ‘yan mata suke talla, ya shafa a wurin da aka yi masa aski. A duk lokacin da aka yi masa aski idan ya shafa wannan gari ƙurajen aski ba za su fito masa ba (MYHW, 13/8/1998).

A taƙaice kamar yadda aka gani wannan babi an yi bayani ne kan nason da al’adun baƙi na kusa waɗanda suka haɗa da Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa da ƙananan suka yi a kan wanzanci.

An duba rawar da al’adun waɗannan baƙi suka taka wajen kawo wasu sauye-sauye dangane da yadda Hausawa suke gudanar da al’adunsu waɗanda suka shafi aski da cire belun-wuya da na mata da kaciya da tsaga da kuma magungunan gargajiya.

Karanta Nason Al’adun Yarabawa A Kan Wanzancin Hausawa

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU ya wallafa WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceZubar Da Ruwa A Farko Da Kuma Ƙarshen Juna Biyu
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.