- Ƙaunar ku ce ta jiƙa7 ni
- Sai ta mantar ni tunani
- Kuskuren nan da nake yi Ku sani ku kuka sa ni
- Tun da in nai muku laifi Ba wanda za ya kwaɓe ni.
- Sai da Allah ya nufe ni Rannan na samu sukuni.
- Zuciyata ta matsa min Waƙe nake jin za ni.
- Musa da Gambo da Shehu Waɗanda Arrahamani.
- Ya ba su ni’imominSa Masu bamban a kamanni.
- Jami’a Gambo ya samu Shehu ko angon Ƙarni.
- Musa ya yi amarya Tun a can wasu makonni.
- Zuciya ba ta da laifi Murna za ta taya ni.
- Baban Mujahidu Shehu Fitila haskaka birni.
- Dauriyarka ta Koyarwa Ita ke sa ni yaƙini.
- Bayanka za ta yi haske Ta sha gaban zamani.
- Baban mujahidu ɗana Tsaya na ba ka bayani.
- Ka kira ɗanka Mujahid Wallahi ka birge ni.
- Tun da kai ma a jihadi Kake in an yi tunani.
- Koda yaushe burinka Kowa ya san addini.
- Kullum ba ka da hutun Jigila ƙauye da birni.
- Malam Musa ango To, sai ka gafarce ni.
- Don ba ka so a yabe ka Ni ko yabon yau za ni.
- Inda ina kannewa A yau biki ya zuga ni.
- Kowa yana shagalinsa Ni ko ina ta tunani.
- Da ma fatan Malam Ya auri mai addini.
- Wadda ta san Larabci Da ilmin zamani.
- Gwana idan ta kawaita Zaƙaƙura a bayani.
- Allah gwani mai kyauta Ya ba wa liman rawani.
- Ya tabbatar da mafarki Ƙuruƙuru a yaƙini.
- Angwanci da amarci Sauƙi mai kashe rauni.
- Ya zumunci makusanci Mai maganin saƙonni.
- Cikinka babu takaici In dai da so a tsakani.
- Wani haske na filasha Ya tsai da ni a tunani.
- Da na farka na ga ango Gami da shi da sa’anni.
- Kowa yana shagalinsa Ba wanda ke alhini.
- Farin ciki ya rufe ni Sai na sabunta tunani.
- Ga su malam Musa nan Masu halin ladani.
- Kullum kiran da suke yi A zo gurin imani.
- Wadda ta auri irin su Ta ci ribar zamani.
- Za ta rayu cikin ni’ima A ƙarqashin Ƙur’ani.
- Ba ita babu fasadi Na Bature Majanuni.
- Mai kilisai da katifa; Ai ya huce karauni.
- Malam ina daɗa murna Allah ya ba ku sukuni.
- Da so da ƙaunar juna Su ƙara inganta gini.
- Ya ba ku ‘ya’ya nagari Jigajigan addini.
- Malam Gambo Lawan, ko Sibawaihin Zamani.
- Dole ne in masa murna Ta masoyi da amini.
- Yau farin ran da nake ji Ya fi ƙarfin na yi muni.
- Tun da dai Gambo ya dace Ya adon ta da kyan launi.
- Ilmi ne kwaɗayinsa Shugaban kowane ƙarni.
- Ai ko ya samu taraƙƙi”8 Ya haye ƙolin tsauni.
- Allah ya ba mu najahi Mu ja gaban zamani.
- Ya azurta mu da ilmi Gami da kyan imani.
Domin karanta cikekken littafin Danna nan