Sana’ar Wanzanci Da Sauye-sauyen Zamani Jiya Da Yau (Shimfiɗa)

0
19

Wannan babi ya yi bayani kan hasashe da bagiren wannan bincike da manufarsa da ƙunshiyarsa da kuma dabaru da hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan wannan nazari da wuraren da aka samo su.

1.1 Hasashe da Bagiren Bincike

Hasashe na kai tsaye da aka kalla a kan wannan bincike ya haɗa da:

  • Nazarin wanzanci a wajen Hausawa don gano tsantsar al’adun wanzanci ba tare da sun sami wata gurɓata ba.
  • Gano nauyin sauye-sauyen zamani da suka yi kaka-gida a wanzancin Hausawa tare da fito da yanayin rawar da al’adun wasu al’ummu suka taka a wannan sana’a ta wanzanci. Shin sauye-sauyen zamani sun taimaka wajen bunƙasa wanzanci ko kuwa sun taimaka wajen dankwafe shi?
  • Shin wanzanci da al’adun da suke zagaye da shi suna nan da kadarinsu har a wannan lokaci da muke ciki?

Muhimmin hurumi na wannan bincike shi ne sana’ar wanzanci a ƙasar Hausa tare da duba yadda sauye-sauyen zamani suka shiga cikin wanzancin Hausawa daga al’ummomin Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa. Sannan kuma da abubuwan da Hausawa suka samu na wanzanci daga al’ummar Larabawa da Turawa.

Akwai wasu ayyuka da aka fara yi a kan wanzancin Hausawa da suka haɗa da Musa (1983) da Suleman (1990) da Sallau (2000). Shi wannan ɗoriya ne a kan abubuwan da aka fara tattarawa tare da shigo da wani sabon bincike inda aka duba sauye-sauyen zamani waɗanda wanzancin Hausawa ya ci karo da su daga al’adun wasu al’ummomi.

Wannan bincike an karkasa shi yadda zai shafi manyan garuruwan ƙasar Hausa da kuma wasu sassa da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa na kusa da na nesa. Garuruwan da wannan nazari ya duba su ne kamar haka:

(i) Rukuni na ɗaya ya ƙunshi garuruwan ƙasar Hausa a arewacin Nijeriya waɗanda suka haɗa da Argungu da Birnin-Kabi da Daura da Gusau da Kano da Katsina da Sakkwato da Yawuri da Zariya.

(ii) Rukuni na biyu ya ƙunshi garuruwan da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa ta kusa ko ta nesa a Nijeriya waɗanda suka haɗa da Bauchi da Bida da Ibadan da Ilori da Jos da Kaduna da Kafanchan da Kagoro da Lafiyar-Barebari da Maiduguri da Kwantagora da Minna da Gwambe da Potiskum da Shagamu da Keffi da Yola da Wase da Lagos da Wamba da Zuru.

(iii) Rukuni na uku ya ƙunshi garuruwan da suke cikin Jamhuriyar Nijar waɗanda suka haɗa da Maraɗi da Tassawa da Agades da Birnin-Ƙwanni da Yamai.

 1.2 Manufar Wannan Bincike

Kafin shiga bayani a kan manufar wannan bincike yana da matuƙar muhimmanci a san ma’anar kalmar manufa. A ƙamus na Turanci (Hornby, 2000:804) an fassara kalmar manufa ‘objective’ a “matsayin wani abu ko buri da ake son cimma”. Abin nufi a nan shi ne, manufa na nufin tsara wasu hikimomi don samun biyan buƙata kan abin da aka sa gaba. Misali, babbar manufar duk wani malamin makaranta ita ce, bayan ya kammala darasinsa ɗaliban da yake koyarwa su fahimci abubuwan da ya koya masu.

Idan muka juyo kan manufar wannan bincike za a ga bisa la’akari da ayyukan da mutane suka yi na rayuwar yau da kullum an fahimci kowane mutum yana da manufar da take cikin ransa da yake son ya cim mata. Masana da manazarta sun gabatar da ayyuka gwargwado kan al’adun Hausawa.

Yawanci a waɗannan nazarce-nazarce an fi mayar da hankali kan fito da abubuwan da suka danganci al’adun aure da haihuwa da mutuwa da nazarin addinin gargajiya waɗanda suka shafi sihirce-sihirce da tsubbace-tsubbacen Hausawa. Bisa dukkan alamu ba a gudanar da wani bincike mai zurfi kan sana’o’in gargajiya na Hausawa ba, in ban da aikin Sharifai (1990) shi ma wanda ya yi game da kirari da take na sana’o’in Hausawa na gargajiya da kuma na Sallau (2000) wanda ya yi game da sana’ar wanzanci.

Haka kuma ire-iren waɗannan ayyukan ba a faye duba rawar da sauye-sauyen zamani suka taka a wajen bunƙasa sana’o’in gargajiya na Hausawa ko daƙushe su ba. Saboda haka babbar manufar wannan bincike ita ce nazarin ƙaura da shigowar baƙi da tasirin al’adunsu a kan wanzancin Hausawa. Amma a rarrabe, wannan bincike ya fuskanci waɗannan abubuwa kamar haka:

(i) Ƙaura da shigowar baƙi ƙasar Hausa tun daga farkon ƙarni na goma sha huɗu zuwa yau.

(ii) Matsayin sana’ar wanzanci a idon Hausawa da kuma maƙwabtan Hausawa na kusa waɗanda suka haɗa da Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa da sauran ƙananan ƙabilun sassan kudancin jihar Kaduna da wasu sassan jihohin Bauci da Gwambe da Filato da Nasarawa da Neja. Sai kuma maƙwabtan Hausawa na nesa waɗanda suka haɗa da Larabawa da Turawa.

(iii) Sauye-sauyen zamani irin waɗanda al’adun maƙwabtan Hausawa na kusa da na nesa suka yi a kan sana’ar wanzanci.

1.3 Ƙunshiyar Bincike

Wannan bincike ya ƙunshi babi shida. An fara da yin shimfiɗa a inda aka bayyana hasashen wannan bincike da wuraren da aka samo bayanan da aka yi amfani da su wajen gabatar da wannan nazari.

Sannan kuma aka yi bitar ayyukan da suka gabata waɗanda suka taimaka wajen sanin wuraren da wannan bincike ya sa gaba. Bayan haka an yi waiwaye kan ƙasar Hausa da ɓunƙasarta da yadda baƙi suka shigo da dalilan shigowarsu da garuruwan da suka zauna. An kuma yi bayani dangane da tasirin addinin Musulunci kan wasu al’adun Hausawa waɗanda suka shafi dabbar suna da askin ranar suna da al’adun kaciya da kaciyar mata, da sauran wasu ayyuka da wanzamai suke yi a ƙasar Hausa.

An ci gaba da kawo bayanan da suka danganci wasu al’adun Turawa cikin sana’ar wanzanci waɗanda suka haɗa da aski da kaciya da cire haƙori da gudummuwar ba da jini da matakan da ake bi don kula da mai ciki da iren-iren hanyoyin da ake bi don tanadin abin da aka haifa da kuma irin yadda magungunan Turawa suka yi tasiri a kan ire-iren waɗanda wanzamai suke bayarwa.

Daga ƙarshe an kawo bayani kan nason da al’adun wasu baƙi waɗanda suke zaune a cikin ƙasar Hausa da kuma na wasu al’ummomi maƙwabta waɗanda Hausawa suke zaune a cikin ƙasashensu suka yi a kan wanzanci.

1.4 Dabarun Aiwatar da Bincike

A wajen aiwatar da wannan aiki an bi wasu dabaru da hanyoyi don gabatar da shi waɗanda suka haɗa da:

(i) Hanyar nazarin zaune inda aka bi ɗakunan ajiye littattafai da kundaye digiri na uku da na biyu da na ɗaya da littattafai na ɗab’i aka karanta waɗannan ayyuka aka taƙaita su. Daga cikin ɗakunan karatun da aka ziyarta akwai na Jami’ar Bayero ta Kano da na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta Sakkwato da na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da Jami’ar Maiduguri da Babbar Kwalejin Ilimi ta Abdullahi Augie ta Argungu da Babbar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya a Kwantagora da Babbar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya a Zariya da Babbar Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna a Gidan-Waya Kafanchan. Haka kuma an ziyarci ɗakunan karatu na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman a Katsina da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna.

(ii) Hanyar ziyartar ɗakunan ajiye kayan tarihi na jihohi waɗanda suka haɗa da Hukumomin Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu na Jihohin Kano da Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kabi da Neja da Nasarawa da Kaduna da Yobe da Borno da Adamawa da Bauci da kuma Gwambe. An kuma ziyarci Hukumar Adana Kayan Tarihi ta Ƙasa da take Kaduna. Haka kuma an ziyarci Cibiyar Binciken Tarihin Arewacin Nijeriya wadda take ƙarƙashin Sashen Koyar da Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. An kuma ziyarci Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya ta Jami’ar Bayero Kano da kuma Cibiyar Al’adun Gargajiya ta Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

(iii) Hanyar amfani da takardun tambayoyi da aka rubuta da harshen Hausa waɗanda aka rarraba wa wasu Hausawa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa da wasu garuruwan da suke maƙwabtaka da wannan ƙasa. Akwai kuma wadda aka rubuta da harshen Turanci aka rarraba wa musamman waɗanda ba Hausawa ba mazauna ƙasar Hausa da maƙwabtanta. An rarraba waɗannan takardu ga maza da mata, matasa da dattawa.

iɓ) Hanyar yin hira da mutane daban-daban musamman wanzamai su kansu da ungozomomi da masana da manazarta da sauran jama’a waɗanda suka bayar da ra’ayoyinsu. Haka kuma an zauna cikin waɗannan wanzamai aka yi nazarin yadda suke aiwatar da aikace-aikacen wanzanci, musamman a garuruwan da ba a ƙasar Hausa ba.

An gudanar da waɗannan hirarraki a garuruwan:

Akwanga da Arugungu da Bauchi da Bida da Birnin-Kabi da Birnin-Ƙwanni da Damagaram da Damaturu da Daura da Gusau da Gwambe da Ibadan da Ilori da Jega da Jos da Kaduna da Kafanchan da Kagoro da Katsina da Keffi da Koko da Kwantagora da Lafiyar-Barebari da Lagos da Maiduguri da Manchok daMaraɗi da Minna da Potiskum da Sakkwato da Tassawa da Wase da Yamai da Yawuri da Yola da Zariya da Zuru.

A taƙaice kamar yadda aka gani wannan babi na share fage ne don kuwa bayanan da suke cikinsa an yi su ne inda aka fito da hasashen binciken da manufofinsa da abubuwan da nazarin ya ƙunsa da kuma dabarun da aka yi amfani da su wajen tattara bayan da suka haifar da wannan kundi.

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundi mai taken SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU: NA BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU

KUNDIN BINCIKE WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI, SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

 MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

 

 

labarin da ya wuceKammalawa A Cikin Bincike Mai Taken Adabin Kasuwar Kano
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.