Sanƙaran Bakin Mahaifa (Cervical cancer)

1
80

Sanƙarar bakin mahaifa (cervical cancer) kamar sauran nau’o’in ciwon daji,tana girma da hayayyafar ƙwayoyin halitta sama da na al’adarsu,iya yaɗuwa tare da nakasa sauran sassan jiki.

Kamar yanda sunanta yake,tana farawa ne daga dan bututun da ya sada mahaifa da gaban mace wanda ake kira ‘cervix’ a nasarance.

Menene Yake Haddasa  Ta?

Ana danganta ciwon daji dai da juyewar ƙwayoyin halitta (mutation),mafi yawa tana samo asali ne daga kamuwa da kwayar virus da ake kira (human papillomavirus) (HPV),wanda yake yaɗuwa ta hanyar saduwa,saidai kamuwa da wannan virus baya nufin tabbatuwar samunta,domin jiki yana iya kakkaɓe wannan virus cikin shekaru biyu.

 Alamominta

Da yawan mata basu gane suna ɗauke da ita har sai tai aure,idan ma alamun sun bayyana, sukan yi kama da al’ada, larurorin mafitsara (infection kamar yadda mata suka fi faɗa).

Ba Kowane Ciwon Ƙirji Bane Ulcer Danna nan domin karanta cikekken dalili

 Daga Cikinsu Akwai
  • Zubar jini daga gaba; bayan saduwa,tsakanin al’ada,ko bayan daina al’ada.
  • Zubar ruwa mai launi da wari daga gaba saɓanin na al’ada.
  • Ciwon ƙwanƙwaso
  • karuwar yin fitsari da jin zafi yayin fitsarin.
Abubuwan  Dake Da Tasiri Wajen Yiwuwar Faruwarta
  • Jima’i barkatai: yana kara yiwuwar kamuwa da wannan kwayar virus ɗin wato HPV.
  • Fara saduwa a kananun shekaru: yana kara yiwuwar kamuwa da HPV
  • Wasu larurorin dake yaɗuwa ta saduwa: Ƙanjamau,sifilis,gwanoriya
  • Raunin garkuwar jiki
  • Shan sigari
  • Amfani da magungunan hana zubewar ciki: 

bincike ya nuna waɗanda iyayensu mata suka taɓa amfani da maganin hana zubar ciki mai suna ‘Diethylstilbestrol’ a can shekarun baya (1950…); suna da yiwuwar samun sankarar bakin mahaifa

Sharawa a gaugauta  zuwa ganin likita dazarar anji wanɗannan  alamun dan samun agajin gaggawa

Domin karanta bayani akan Sanƙaran Nono Wato {Breast Cancer} Danna nan 

labarin da ya wuceSanƙaran Nono Wato {Breast Cancer}
Labarin na GabaCiwan Hanta {Hepatitis}

SHARHI ƊAYA