Sababbin Karin Maganar Hausa

0
58

SALMANU FARISS ADAMU

Sakamakon zagayowar ranar Hausa ta duniya ta shekarar 2025, ga wasu sabbin karin magana:

1. Abin nema ya samu matar Bakano ta haifi buhun kuɗi.

2. Abin nema ya samu matar Basakkwace ta haifi buhun taba.

3. Abin nema ya samu matar Bazazzage ta haifi kunyar doya.

4. Abin nema ya samu matar Ɗangaruwa da cikin tulu.

5. Abin nema ya samu matar Marubuci ta haifi biro.

6. Abin nema ya samu matar Ɗanjarida ta haifi amsa-kuwwa (Speaker)

7. Abin nema ya samu matar liman ta haifi ladan.

8. Abin nema ya samu matar Likita ta haifi allura.

9. Abin nema ya samu matar mai-shayi ta haifi mummuƙi (burodi)

10. Abin nema ya samu matar malami ta haifi alli.

11. Abin nema ya samu matar Bafulatani ta haifi saniya.

12. Abin nema ya samu matar direba ta haifi mota.

13. Darajar sana’a wanzami yake taɓa gemun sarki.

14. Ba kuka na ba, ɗan kishiya ya faɗa rijiya ya mutu.

karanta Isra’i Da Mi’iraji

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceGudunmawar Sarki Abdulazeez Da Birtaniya Wajen Kafa Ƙasar Saudi Arabia
Labarin na GabaIllolin iPhone Ga Tarbiyyar ‘Ya’yanmu