Saƙo Ga Masoyiyata

0
1017

Salam ya ke muradina, Da safe na antayo ƙauna, Na bayyana sirrikan raina, Gare ki ina makwancina, Zo amsa min cikin son rai.

 • Abar sona abar sona,
 • Ya abar ƙauna abar ƙauna,
 • kin zam abar marari a rayina,
 • Yau ga ni da so cikar ƙauna,
 • Cikar buri cikar komai.
 • Gare ki masoyiya tawa,
 • Ki ji ni da zantukan baiwa,
 • Na ƙaunar nan da ba tsiwa,
 • Cikin mararin cikar sowa,
 • Na bayyana baitukan so dai.
 • Idan na gane ki don ƙauna,
 • Na manta abin dake raina,
 • Cikar buri ki zo guna,
 • Ki amshi buƙatuwar raina,
 • Ki share min duhun komai.
 • Ranar wanka Bahaushe de,
 • Ya ce cibi waje buɗe,
 • Nufinsa a wangame buɗe,
 • Kowa ya gano ido buɗe,
 • A san shi a san kalar komai.
 • Kin san so ba a mai yarfe,
 • Ba a ƙyamar tuwon safe,
 • Zoben so ba a sa ƙarfe,
 • Burina na tattaro lefe,
 • Na kai ki garin da ba kome.
 • Kin san so ba a mai kulle,
 • Gararinsa yawa na ‘yan talle,
 • Shuhurarsa a zuciya zille,
 • A ganta a fuska ba kyalle,
 • A san ya zarce duk komai.
 • Idan na taho a motata,
 • Cikin tafiya ta ƙasaita,
 • Idan na gane ki ‘yar auta,
 • Kina tafiya ta ƙasaita,
 • Na manta batu na tuƙin dai.
 • Kalarki daban a mataye,
 • Sunanki daban na ‘yar yaye,
 • Sautinki daban a ƙaraye,
 • A soyayya ana maye,
 • A sonki ko za na yo komai.
 • Naman da ake kira soye,
 • A cakuda kafi zabaye,
 • A sa naman a sa maye,
 • A sa gishiri a yo soye,
 • A so haka duk ake komai.
 • Maimaita aji fa sai dolo,
 • A so kam ba a son gwalo,
 • Ba a kome cikin salo,
 • Jifa kam sai da ɗan qwallo,
 • A so ba a barin komai.
 • Baitin ƙarshe na ce santsi,
 • Ya ɗebi mutum ya yo watsi,
 • Ya farfasa kai ya yo rotsi,
 • A soyayya a bar kutsi,
 • Aure a gare ki ne komai.
 • Ni Nayaya na ce ki dube ni,
 • Ki min kallon da ba raini,
 • Da zai mai she ni ɗan birni,
 • Na sa kaya na sa rawani,
 • Na so domin na zam komai.

       domin samun karanta saƙo ga masoyiyata danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceYadda Ake Sallar Zazzaɓin Rana Da Wata
Labarin na GabaWaƙa A kan Dangina