Rataye na 2: Waƙar Hana Shan Ƙwaya da Sauran Kayan Maye Ta Marigayi Abdullahi Sani Makarantar Lungu

0
25

khairatu.shehu

Kuma babu ƙarfi wajen mai shan ta ni na faɗi,

Domin jininsa takan tsotse ya bar tafiya.

Bacci kwa in har ya kwanta sai ya kai mako,

Ba wanda zai ce da kai ya gan shi ya juya.

 

Aiki fa ja a gaban mu a taimaka jama’a,

Don alhaki ne wuyan kowanmu kar mu ƙiya

Gyaran ƙasa dole sai an kau da shashanci,

Sannan fa duk ci gaban jama’a ya zam tafiya

 

A ɗau matakin da za a ga babu kwaya sam,

Domin mu tsere ta kaicon rayuwar duniya.

A hukunta mai sha da mai saida ta kar a raba,                                                              Laifinsu ya yi kama da fashi a Nijeriya.

 

Burinmu ya bar cika in har ba mi azama,

Mun kau da ƙwaya ba ƙarshe za mu sha kunya.

Wannan masifar fa ba birni kawai ta tsaya,

Har ƙauyuka ta gama duk ‘yan uwa ku jiya.

 

A wajen manoma akan ce wai da sun sha ta,

Wai sai su kwana suna aiki fa ba gajiya.

In masu neman karatu sunka je gunsu,

Wai sai su ce maganin niyya fa kar ku ƙiya.

 

In ban da ƙarya ina wani maganin niyya,

Da za ya sanya ƙwaƙwalwa har ta zama tawaya

In na tuno lamarin kan ba ni mamaki,

Hanyar da za a bi gyaran nan ya zam tafiya.

 

Ƙwaya takan ɓata dukkan rayuwar jama’a,

In har aka yi sakaci ba a tashi an aniya.

In har ana so ƙasa ta zamo cikin tsari,

Sai an kawar da abin maye da sa tawaya.

 

Wasu sanya ƙwaya suke randa ta kan hanya,

Jama’a ku gane da makircinsu kar ku biya.

Duk ci gabanmu suke nema ya salwanta,

Don tun da farko fa su ba su samu tarbiyya.

 

Kuma har da mata a wannan kar ku ce ƙari,

Da masu aiki da kwaya babu wai ku jiya.

A gidan biki ko ko suna sai a same ta,

A cikin ruwa ko kunun zaƙi da za a biya.

 

Wallahi duk wanda ya ba ɗan uwansa guba,

Ya sani haƙiƙa Ta’ala zai yi sakayya.

Duk mai nufin cutatar da waninsa ya wahala,

Shi zai ga cuta a kansa fa babu wai ku jiya

 

Duk ɗan ƙasa nagari burinsa ai kirki,

Ba za ya so ‘yan uwansa cikin rashin shiriya.

A kiyayi ƙwaya da ganye kar a raɓe su,

In dai da son a ji daɗin rayuwar duniya.

 

In anka ce hankali kuma ya gushe babu,

Ai rayuwa ba ta amfani a nan ku jiya.

Komai muƙamin mutum wa za ya raɓe shi?

Domin kwa ya cusa kansa a surƙuƙi da ƙaya.

 

Na bayyana muku kwayar nan fa cuta ce,

Domin takan hana barci har ido ya tsaya.

In babu barci ko tilas hankali ya gushe,

Domin ƙwaƙwalwar mutum ta ɓaci ta tawaya.

 

Daga nan mutum sai ya hau yawon da ba gaira,

Bare dalilin da za a ji tausayi a biya.

Sai zantuka marasa kai babu gindinsu,

Ƙwaya fa ta fara narkewa a nan ku jiya.

 

Kuma sai ya zauna ba zai wanka bare wanki,

Suma da annakiya sun san gurin ɓuya.

Sai tsince-tsince a bola ko cikin kwatami,

Tsumma a gunsa kwa ya wuce ai ta jayayya.

 

Ai ba batun wani jin daɗi a kan wannan,

Sai jefa kai a tsiya da barin abin kunya.

Wa zai ga wannan ya nuna har yana sha’awa?

Sai dai a nemi tsari da halin maƙi shirya.

 

Domin karanta Rataye Na 1: Waƙar ‘Yar Maye Ta Ahmad Tijjani Gandu danna nan

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceRataye Na 1: Waƙar ‘Yar Maye Ta Ahmad Tijjani Gandu
Labarin na GabaRataye na 3: Waƙar Shan Ƙwaya ta Alhaji Dr Adamu Ɗanmaraya, Jos
Ado Ahmad Gidan Dabino
Shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Najeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni sannan ɗan wasa ne a shirin finafinan Hausa kuma ɗan jarida. Tare da shi aka kafa wasu ƙungoyoyi na marubuta da masu shirya finafinai. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama'a da yake yi a cikin ayyukansa.