Nason Al’adun Baƙi Maƙwabta Na Kusa A Wanzancin Hausawa

0
86

Wannan babi an yi bayani ne a kan nason al’adun baƙi maƙwabta na kusa waɗanda suka haɗa da Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa da sauran ƙananan ƙabilu a kan wanzancin Hausawa. Da farko an fara kawo bayani kan ƙaura da shigowar waɗannan baƙi ƙasar Hausa, daga nan kuma sai aka ci gaba da kawo bayanai dangane da fannonin sana’ar wanzanci waɗanda aka sami nason al’adun waɗannan baƙi a cikinsu.

Shigowar Fulani Ƙasar Hausa

Mazaunin Fulani na farko a Afrika ta Yamma yana a yankin Senegal, amma a yanzu ana samun su a Chadi da Kamaru da Gambia da Sudan da Habasha (Abubakar, 1977:27). A wannan zamani yawan al’ummar Fulani ya fi miliyan shida kuma fiye da rabinsu suna zaune a Arewacin Nijeriya (Johnston, 1970:20). A lokaci mai tsawo da ya gabata al’ummar Fulani ta kasu zuwa kashi uku. Akwai Fulani Mbororore’en da Fulɓe Na’i da Fulɓe Shi’e.

Dangane da shigowar Fulani ƙasar Hausa, a haƙiƙa yana da matuƙar wuya a ce ga takamaiman lokacin da suka fara shigowa wannan ƙasa, amma duk da haka manazarta ƙaura da shigowar baƙi ƙasashe sun yi kintacen wata ƙungiyar Fulani maƙaurata ta shigo ƙasar Hausa a farkon ƙarni na goma sha huɗu (Abubakar, 1977:29). Wannan kuwa ya faru ne sakamakon ƙaura da suka yi daga yankin Senegal zuwa gabas domin neman wuraren kiwo masu kyau.

A farkon ƙarni na goma sha shida akwai al’ummomin Fulani da daman gaske a ko ina cikin ƙasar Hausa. Daga ƙasar Hausa ne wasu Fulani suka yi kudu-maso-gabas har suka kai gewayen kogin Gongola a cikin ƙarni na goma sha bakwai.

A bayanan da aka samu daga Katsina an bayyana cewa kafin kafuwar mulkin Muhammadu Korau a Katsina cikin shekarun 1450 wasu Fulani da ake kira Sissilɓe (Sulluɓawa) sun baro Futa-Toro da niyyar zuwa Masar, amma sai suka tsaya a Katsina (Nadama, 1977:170). Su ne suka kafa garuruwan Kanwa da Ƙusa da Zandam da Bugaje da Shinkafi a kusa da Birnin Katsina (Usman, 1972:191-192).

Wasu Fulanin kuma sun haɗa da Yerimawa da Gallawa (Gallanko’en) da Daɓawa da kuma Dallazawa, dukkan su sun sauka a garuruwan da suke iyakar ƙasar Katsina ta gabas. Yerimawa sun mamaye ƙasar Yamel. Su kuma Gallawa sun zauna a arewacin Yamel suka kafa ƙauyen Kantche a cikin Jamhuriyar Nijar.

Daga nan ne kuma wasu suka matsa gaba suka kafa ƙauyen Daɓawa wanda yake kusa da garin Kaita, wasu kuma zuwa garuruwan Sirika da Gallu, dalilin kiran su da sunan Sirikawa. Daɓawa kuwa sun zauna ne a kan iyakar da, a yanzu ta raba Nijeriya da Jamhuriyar Kanembakashe duk a ƙasar Katsina. Su kuma Dallazawa sun zauna a arewacin wuraren da Yerimawa suka zauna suka kafa ƙauyen Dallaje (Usman, 1972:190-191).

A cikin ƙarni na goma sha takwas Fulanin da ake yi wa laƙabi da Yerobawa waɗanda daga cikinsu ne ake sa ran Malam Na’Alhaji ya fito, suka shigo ƙasar Katsina. Al’ummar Fulani sun fara shiga ƙasar Kano a lokacin mulkin Sarkin Kano Yakubu (1452-1463), kuma sun fara zama a Ɗanbatta da Rano da Sumaila da Kazaure da dai sauran wurare da dama a cikin Kano da kewayenta (Palmer, 1970:106).

Akwai kuma wasu Fulani da suka shigo ƙasar Kano don yin yaƙin jihadi a farkon ƙarni na goma sha tara. Waɗannan Fulani ne suka kafa unguwanni Yola da Danbazau da Galadanci da Daneji duk a cikin Birnin Kano (Baƙo, 1990:73). Torankawa Fulani zuri’ar da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya fito daga cikinta sun sauka a Ƙwanni arewacin ƙasar Zamfara a ƙarƙashin shugabansu Malam Musa Jokollo a cikin shekarun 1450.

A sakamakon ƙaura da shigowar Fulani ƙasar Hausa an sami wata al’umma wadda a yau ake kira Hausa/Fulani. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon cuɗanya da auratayya wadda ake yi a tsakanin waɗannan al’ummomi fiye da dukkan wasu ƙabilu da suke cikin Nijeriya da kuma na maƙwabtanta. Haka kuma ayyukan da masu jihadi suka yi wanda ya haifar da Daular Sakkawato ta ƙara taimakawa wajen samuwar wannan al’umma ta Hausa/Fulani.

Nason Al’adun Fulani a Kan Wanzancin Hausawa

A lokacin da Fulani suka shigo ƙasar Hausa sun riƙa gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali da lumana. Wannan ne ya ba su damar aiwatar da al’adunsu cikin Hausawa ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba. Haka su ma Hausawa da aka tarar a ƙasarsu suna tafiyar da nasu al’adun a kan idanun Fulani. A lokacin da suke yin wasu al’adu kamar bikin aure ko haihuwa da dai sauransu sukan gayyaci juna.

Watau a lokacin da Fulani suke yi sukan gayyaci Hausawa, haka kuma idan Hausawa suna yi sukan gayyaci Fulanin. Wannan dangantaka ta taimaka ƙwarai wajen musayar al’adu da fahimtar juna a tsakanin waɗannan al’ummomi. A sakamakon haka ne aka riƙa samun nason al’adun Fulani cikin al’adun wanzancin Hausawa. Wannan al’amari ya yi babban naso a kan yadda Hausawa suke tafiyar da al’adun wanzanci musamman yadda ake gudanar da aski da gyaran fuska da cire belun-wuya da tsayar da gemu da kaciya da tsagar kwalliya da dai sauran ayyukan wanzanci.

Yanzu za a bi diddigin ire-iren waɗannan ayyuka na wanzanci don gano tasirin da al’adun Fulani suka yi a kansu.

Aski da Gyaran Fuska

Ta fuskar aski da gyaran fuska al’adun Fulani sun yi tasiri a kan wanzanci musamman ire-iren aski da gyaran fuska da ake yi masu. Su dattawan Fulani askin ƙwaryar molo ake yi masu, a wurin gyaran fuska ne aka sami nason al’adunsu a kan wanzanci. Dattawan Fulani suna yin irin gyaran fuska wanda Hausawa suke kira ƙahon barewa.

Gyaran Fuska Ƙahon Barewa

Wannan nau’i na gyaran fuska dattawan Fulani ne ake yi wa irinsa. Ana yin irin wannan gyaran fuska don a aske gashin da yake a wurin fuska da haɓa a lokacin da suma ba ta yi yawan da za a aske ta ba. A wannan lokaci ne sai wanda yake da buƙatar ya je wurin wanzami don a yi masa. A irin wannan gyaran fuska ana gyara gashin da yake wurin goshi a kuma aske dukkan saje tun daga wurin da ya haɗu da sumar kai har zuwa wurin gemu.

Ba a aske gemu sai dai a kwakkwafe shi ya yi siriri da tsawo. A lokacin da aka zo yin irin wannan gyaran fuska, sumar da take wurin goshi ana kwakkwafe ta har a taɓo wadda take a gefen goshin. Ana ɗan shiga ciki yadda wurin zai yi kyau sosai.

Irin wannan aski Hausawa musamman dattawa waɗanda suke yin hulɗoɗi da Fulani ko waɗanda suke zaune a wuri ɗaya da Fulani na kwaikwayon yin irinsa. A yanzu ana samun wasu Hausawa a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara da cikin Jamhuriyar Nijar waɗanda ake yi wa irin wannan gyaran fuska.

Tukkayen Fulani

A lokacin da jariri namiji ya kai kimanin wata biyu zuwa uku da haihuwa ana yi masa tukkaye uku a bisa kansa. Ana yin ɗaya a goshi ɗaya tsakiyar kai ɗayan kuma a ƙeya. Waɗannan tukkaye ba za a aske su ba, sai a ranar da za a yi wa wannan yaro kaciya, wasu ma sukan bar irin waɗannan tukkaye har sai sun girma sosai sun isa aure. Idan suka yi tsawo, sai a riƙa yi masu kitso. Akwai Hausawa waɗanda suke kwaikwayon yi wa ‘ya’yansu ire- iren waɗannan tukkaye, amma su ba sa yi wa ‘ya’yansu kitso.

Zanƙo

Wani nau’in aski irin na Fulani wanda ya yi naso cikin al’adun wanzancin Hausawa shi ne zanƙo. Ana yin zanƙo ta hanyar aske gashin kai na ɓangaren hagu da na dama a bar gashin tsakiyar kai kamar layi tun daga goshi har zuwa ga ƙeya.

Ana yin zanƙo ga yaro namiji ban da mace a aski na biyu bayan askin suna watau askin ya da wanka. A duk lokacin da za a yi wa wannan yaro aski ba a aske wannan zanƙo, sai dai a gyara shi. A al’ada wannan aski na Fulani ne, don kuwa a ƙasar Katsina lokacin da Malam Ummarun Dallaje ya kafa mulkin Fulani a wannan ƙasa zuri’arsa suna yi wa ‘ya’yansu irin wannan aski na zanƙo.

Daga nan ne wasu daga cikin Hausawan ƙasar Katsina suka riƙa kwaikwayon yin irin wannan aski har ya kai matakin sun mayar da shi askin gado wanda suke yi wa ‘ya’yansu.

Domin karanta Yadda Tsayar Da Gemu Yake A Al’adar Fulani danna nan

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU ya wallafa WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Tsayar Da Gemu Yake A Al’adar Fulani
Labarin na GabaShigowar Barebari Ƙasar Hausa
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.