Mijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Biyu

0
118

Ba a fi sati ɗaya da kwashe kayan Khadeeja ba Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya sake fentin saman aka gyara ta kwashe kayanta ta koma. Yaran kuma gaba ɗaya ta tattaro su ta dawo da su ƙasa tare da masu aikinta guda biyu. Ɗakinta da parlor ɗinta nan ta mayar ɗakinsu Afaf, suna ji suna gani babu yanda suka iya.

Shi kanshi Mustapha abun bai yi masa daɗi ba amma ya kasa magana; yana matuƙar mamakin abinda yasa ba ya iya hana Naja abinda take so a ‘yan kwanakin nan. Cikinta yana cika wata tara ta sake haifar ‘yarta mace, haka ta dage ta shirya taron suna fiye ma da wanda ta shirya a haihuwar Rukayya. Aka sakawa yarinyar suna Maryam.

Washegarin suna su Anti Wiyya da sauran dangi suka soye naman suna suka gyara komai, sannan suka tafi suka bar Anti Wiyya ita kaɗai wadda za ta ƙara kwana biyu saboda taya ta jego. Tana zaune a parlor ɗin sama Anti Wiyya ta shigo da sallama, bayan ta amsa ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita sannan tace ‘Wannan mai wankin naki gaskiya ya iya wulaƙanci, sai da ya fuskanci ana taro sannan ya gudu.

Ni dai wallahi ko kayan sakawa gobe ba ni da su duk sun yi datti, ga shi duk jikina ciwo yake balle na zage na wanke kuma ‘yar aikinki ma dai ta fi ni gajiya. ‘Ai mai wankin nan ya yi wa kansa, in sha Allahu gobe Abban Rukayya zai samo mana wani mai wankin kowa ya huta.’ Ta faɗa tana gyara zama.

Anti Wiyya tace ‘Don ma dai ‘yayanki ba sa moruwa ne in banda haka ga Habib can a ƙasa yana wanki ai da ko kala ɗaya ne ya wanke min. Ta gyara zama ‘Au ai ban san ma yana gidan ba kwaso kayan duka bari na kirawo shi zai wanke miki yanzu. Ba tare da ɓata lokaci ba ta juya ta koma ƙasa inda ta kwaso kayan nata yayin da ita kuma Naja ta ƙwalawa Afaf kira ta saka ta ta turo Habib.

Kusan a lokaci guda suka isa parlor ɗin, shi ya tsaya daga a bakin ƙofa yayin da ita kuma ta ƙarasa ta zube kayan a gaban Naja. Yana daga tsaye a bakin ƙofa yace ‘Anti ga ni.’ Tace ‘Mai wanki ya kwana biyu ba ya zuwa, ka kwashi kayan nan ka wankewa Anti. Ya kalli kayan ya kalle ta yanda take muzurai; ba wai ba ta saba yi masa hakan ba ne, ta riga ta saba musamman tun bayan da Khadeeja ta bar gidan.

Kawai dai ya kan yi mata abinda zai iya wanda ba zai yi ba kuma ya bar mata kayanta. Ya sake kallon kayan yace ‘Ah ku bar shi dai yanzu zan fita sai na samo muku wanda zai wanke ku biya shi. Har ya juya ya fara tafiya tace ‘Kana nufin ba za ka wanke ba ko me.’ Ya dan dawo ya kalle ta ya kalli kayan, har ya buɗe baki zai yi magana kuma sai ya fasa, ya fice ya barta nan a zaune da kayan.

A fusace ta miƙe tana huci, kafin ta yi magana Anti Wiyya tace ‘Ai na gaya miki waɗannan yaran ba sa moruwa. ‘Ni ka tafi ka bari ina magana ko Habib? Saboda ka ga ni ba uwarka ba ce kuma ba khadeeja ba ce ko? Saboda ba a isa a saka aiki ka yi ba ko? To wallahi bari Abban naku ya dawo, sai dai ko ni ko kai a gidan nan don idan dai ba zan more ka ba sai dai ka bar gidan wallahi.’

Wiyya tace ‘Ah to, yaron da bana jin ya haura sha takwas ya dinga yi miki irin wannan rainin, wannan nan da ‘yan shekaru ai sai ya kai miki duka. ‘Wallahi bari ubanshi ya dawo, dole ya bar min gidan nan idan ba haka ba ni na bar masa gidan. Idan ma Khadeejan ce take zuga shi ta janyo masa. Haka Wiyya ta sakata a gaba ta ƙara zuge ta kafin ya dawo.

Ana idar da sallar Magriba ya shiga gidan, Habib ne ya buɗe masa gate tare da Baba maigadi ya yi masa sannu da zuwa sai dai bai raka shi har cikin gidan ba. Kamar yanda ya saba a parlor ɗin ƙasa ya sami yaran suna zaune suna kallon TV, bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce sama.

Da da ne Nasreen da Shukra sai sun raka shi har ɗakinsa, sai dai yanzu saboda yanda Naja take yawan korarsu tana nuna musu su dinga tsayawa a ƙasa ya sa sun haƙura, haka ya haye shi kaɗai zuciyarsa babu daɗi; saboda shi ma yana kewar wannan rakiyar. A ɗakinsa ya same ta tana ta cika tana batsewa, domin ko sannu da zuwa haka ta yi masa tana ta faman zumɓura baki.

Bayan ya amsa yace ‘Me ya faru ne naga kina ta wani ɓata rai? Ta sake haɗe rai sannan tace ‘Ya za a yi a gidan nan a ce ban isa na saka Habib aiki ya yi ba? A gaban kowa zan ce Habib ya yi aiki amma kai tsaye ya ce min ba zai yi ba? Ai ba haka yake yi wa Maman Hammad ba, ko da yake na ji suna cewa yana zuwa wajenta ban sani ba ko ita ce take zuga shi ya dinga yi min rashin kunya.’

Ya ajiye jakarsa ya zauna a kan kujerar gaba mudubi ya fara cire takalmansa yana cewa ‘Kada ki saka Khadeeja a cikin wannan maganar, da za ta sa wani ya yi miki rashin kunya da tun tana nan za ta saka su. Habib ɗin me kika ce ya yi ya ƙi yi? ‘Wankin kayansa yake yi shi ne na kirawo shi na ba shi kayan Anti Wiyya kala ɗaya nace ya taimaka ya wanke mata amma yaron nan ya ƙi, kuma yana kallo mai wankin namu ya gudu.

Ita ce ta ke ta fama kula da gidan kayanta duk sun yi datti amma a gabanta Habib ya ce ba zai wanke mata kala ɗaya ba don wulaƙanci don ya nuna mata ban isa ba. Ya miƙe ya cire kayansa yana cewa ‘Ki ɗauko kayan idan na fito zan ba shi ya wanke in ya so zan gayawa Baba Maigadi ya zagaya nan makarantar almajirai ya samo yaro a wajen malaminsu wanda zai dinga zuwa yana wankin.’

Kafin tace wani abu ya shige banɗaki. Ta zumɓura baki ta ja tsaki don ba haka ta so ba, so take a yi masifa ta sami damar da za a ce Habib ya bar gidan. In ya so sai ta san yanda za ta yi da Afaf, tana gamawa da waɗannan biyun ta san gidan ya zama nata, musamman da yake Shukra ita matsoraciya ce duk yanda ma aka juya ta haka take yi.

Jimawa kaɗan ya fito ya sake kaya sannan ya wuce ya zauna a dining table ya fara cin abinci. Yana cikin cin abincin ya ɗauki waya ya kirawo Habib, ba tare da ɓata lokaci ba ya hawo ya same shi. ‘Abba gani.’ Ya faɗa yana tsaye daga gefe. Ya ajiye cokalin da yake hannunsa sannan yace ‘Habib me yasa Antinka ta saka ka wanki ka ƙi yi?’

Yace ‘Abba ba ƙin yi na yi ba, wankin ne da yawa kuma nace gobe zan samo musu yaro ya wanke a biya shi. ‘Kala ɗayan ne da yawa? Kayan ma da ba nawa ba ne.’ Ta faɗa tana wasu muzurai. Yace ‘Ni dai kayan da aka ba ni za su kai kamar kala biyar ko fiye, ban sani ba ko ba su aka nuna maka ba.’

Abbansu yace ‘Ka ga Malam, ba na son wani ƙarin bayani. An ce kaya kala ɗaya ne kuma gobe ake so a yi amfani da su. Ka je a ba ka kayan ka wanke yanzu in ba so kake ranka ya ɓaci ba, kuma daga yau ba na son a saka ka aiki ka dinga ƙin yi. Ba zan ɗauki taurin kai da rashin kunya ba. Ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa, ya juya ya fice.

Ya dubi Najan yace ‘Ki je ki ce mata ta ba shi kayan ya wanke. Ta tashi ta fice. Yana zaune a tsakar gida wajen Baba maigadi Shukra ta je ta kirawo shi. Yana shigowa ya ci karo da wankin a zube a bakin ƙofa; tabbas wankin sun fi kala biyar. Yana shiga cikin parlor ɗin kafin ya yi magana Naja da take tsaye tace ‘Gasu nan ka je ka wanke, kuma wallahi idan ba su fita ba sakewa za ka yi har sai sun fita.’

Ta juya ta haye sama ta bar su a nan shi da ƙannensa. Ya juya ya dawo ya tsaya a kan wankin yana ƙare musu kallo yana tunani; tabbas ba zai yi wankin nan ba, ko da kuwa kala ɗayan ta bayar kamar yanda tace. Kuma yanda ya ga a gaban Abban tace kala ɗaya ne kuma ta ɗauko kaya da yawa haka ta ba shi ya san ta shirya wata maƙarƙashiyar.

Ya san ba lallai Abbanshi ya saurare shi ba saboda tana gabansa tana tsara masa zance, kuma ya san idan har ya yi wannan wankin to ta sami damar da za ta mayar da shi ɗan aikin gida kuma ba zai yi ba. Haka ya kewaye ya fice ya bar wankin a nan inda ta ajiye su. Suna sama ita da maigidan suna ta hirarsu cikin kwanciyar hankali, sai waje ƙarfe tara sannan Anti Wiyya ta fito daga ɗakin baƙi ta ga wankin.

Ta yi matuƙar mamaki musamman da ta tambayi Afaf ta tabbatar mata Habib ɗin ya fice bai ɗauki wankin ba. Nan ta koma ɗaki ta kirawo Naja a waya wadda ta sauko, ta nuna mata wankin sannan ta yi mata bayanin cewa a nan ya fice ya bar su.Yaran suna kallo ta tsuguna ta tsince kayan ta bar kala ɗaya da hijab guda ɗaya sannan Anti Wiyyan ta koma ɗaki ita kuma ta haye sama.

Jimawa kaɗan Mustapha ya sauko yana tambayar Afaf ina ƙaninta. ‘Abba ban ganshi ba, ficewa kawai ya yi ba tare da yace komai ba.’ Ta ba shi amsa. A fusace ya murɗa ƙofar ɗakin Habib ɗin ya shiga yana kiransa, sai dai ga mamakinsa Habib ɗin ba ya cikin ɗakin. Ya fice wajen Baba Maigadi inda ya tabbatar masa bai san inda Habib yake ba, ya ƙara da cewa ‘Bana jin ma fita ya yi, don tun da aka ce ya zo kana kiransa ban sake ganin gilmawarsa ba.

Sai dai ko da ina sallah ne ya fice ban sani ba. Ya koma cikin gidan ba tare da yace komai ba. Yana shiga parlor ɗin ya dubi kayan yace ‘Nasreen zo ki kwashi kayan nan ki mayar mata, yayan naki zai zo ya same ni. Ya haye saman inda ya tarar da Naja a zaune a parlor ita da Rukayya, ya sami waje ya zauna sannan ya ɗauki wayarsa ya dannawa Habib kira.

Ba ƙaramin mamaki ya yi ba da ya ji wayar Habib ɗin a kashe, sai dai ya yi tunanin kashe wayar Habib ɗin ya yi don ya san ba shi da gaskiya. Don haka sai kawai ya sauko ya sanar da Baba Maigadi cewa idan Habib ya shigo gidan ya yi masa waya. Tun yana sa ran shigowar Habib har abun ya fara ba shi tsoro; yaran duk sun tafi sun kwanta har sha biyun dare ta yi amma Habib bai shigo gidan ba, ga shi sai kiran wayarsa ake yi a kashe.

Yana son ya kirawo Hajia ko Habib ɗin ya je can amma kuma ba ya son ya ɗaga musu hankali. To ina Habib zai shiga? A karo na babu iyaka motsin shigarsa ɗakin ne ya farkar da ita daga bacci, ta gyarawa Baby Maryam kwanciyarta sannan ta dube shi tace ‘Wai bai dawo ba. A jigace yace ‘Eh, wallahi har abun ya fara ba ni tsoro. To ina Habib zai tafi?

Ina ma ya sani a garin nan shi da ba wani yawo yake ba? Tace ‘Ya za ka ce ina ya sani yaron da yake level 1, kuma yake tafiya makaranta da kansa. Ai yanzu ba kamar da ba ne, tsaf ya san ko ina. To ina zai tafi a wannan daren? Ga shi Baba Maigadi ma yace ko fitarsa bai gani ba kuma gidan nan babu inda ba mu duba ba baya nan.’

Tace ‘To ka dai yi hakuri ka zo ka kwanta tunda ka ga yanzu ɗayan dare ta kusa, zuwa wayewar gari sai a nemo shi a ba shi haƙuri a gaya masa ya bar wankin. ‘Mtseww! Wai kin san me kike faɗa kuwa? Na zo na kwanta saboda ke kin kwanta ko? Ya sake jan tsaki sannan ya fice daga ɗakin ya rufe mata ƙofar da ƙarfi, rufe ƙofar da sai da ya farkar mata da Baby daga barci.

Ta juya a fusace tana gunguni ta ɗauki yarinyarta ta saka mata nono. Yanda ya ga rana haka ya ga dare, yana zaune a parlor shi kaɗai. Sai dai idan bacci ya ɗauke shi ya yi firgigit ya farka, ya sake buga lambar Habib amma a kashe. Yana fara jin kiran sallar asuba ya kirawo Alhaji ya sanar da shi ba a ga Habib ba.

A shirye ya fice masallaci, bayan an idar da sallar asuba ya sanar da su ɓacewar habib. Yana dawowa gidan ya ɗauki mukullin motarsa ya fice ya nufi gidan Hajia. Su ma a tsaye ya same su cikin tashin hankali, nan suka zauna suna jira gari ya ƙara wayewa su je police station su sanar. Suna zaune a parlor ɗin Alhaji cikin tashin hankali Hajia ta dubi Mustapha tace ‘Kuma ka tuntubi kakanninsa, can gidan su Ma’u da ma ita Khadeejan ko wajensu ya tafi?’

Ya gyara zama yana cewa ‘Khadeeja dai na tambaye ta ita ma ba ta ganshi ba, amma gidan mama ma ni na manta da su. Bari na kirawo su na ji. Kafin ya gama laluben lambar suka jiyo bugun ƙofa, gaba ɗayansu suka nufi ƙofar saboda Alhaji ya ba da sanarwa a masallaci ya yi zaton ko an sami wani labari ne. Ga mamakinsu Kawu Auwal ne wato ƙanin Ma’u tare da Habib ɗin.

Suna haɗa ido Mustapha ya kai masa duka yana cewa ‘Shi ne za ka fice ba tare da ka gayawa mutane ba saboda raini ko? Alhaji yace ‘Ka bar shi mana ya zauna ya yi bayani.’ Suka ƙarasa cikin gidan suka zauna a parlor ɗin Alhaji. Bayan sun gaggaisa Kawu Auwalu yace ‘Wallahi ni ma da asuba Mama ta kirawo ni tace na zo na dawo da shi, ita ma ta yi zaton an san yana gidan shi yasa ma ba ta nemi kowa ba.

Sai ɗazu bayan sallar asuba Antinsa Khadeeja ta kirawo ta tana cigiyarsa. Shi ne ta kirawo ni tace na kawo shi nan na yi bayani. Alhaji ya yi masa godiya sannan ya dubu Habib yace ‘Mutumina ya haka kuma? Me suka yi maka a gidan da za ka bi dare ka gudu? Kuma madadin ka zo ka gaya min sai ka tafi ka ɗagawa Mama hankali.’

A nan ne ya sami dama ya gayawa Alhaji abinda ya faru, sannan ya sanar da shi irin zaman da ake yi a gidan. Hajia tace ‘Dama Aminan Jidda ta faɗa, tace wancan zuwan da suka yi gidan ba su ma ga Najan ba. Kamar yaran suna ƙasa su da mai aiki suna rayuwarsu ita kuma tana sama ita da nata yaran, kuma yanda ya faɗa haka Aminan ta faɗa tace shi kanshi Mustaphan yaran ba sa ganinshi sai dai idan ya sauko.’

Shi ma Auwalu ya tabbatar musu da cewa duk waɗannan maganganu yaran sun daɗe da yi wa Mama bayani, sai dai da yake ta ɗauka ba huruminta ba ne shi yasa ma ba ta ce komai ba. Amma dai gaskiya da akwai matsala, tunda ai da ba a taɓa samun matsala irin wannan ba. ‘Haka ne, in sha Allahu za a duba kuma a ɗauki mataki.’ Alhaji ya faɗa.

Suka ƙarasa tattaunawa Auwalu ya yi musu sallama ya tafi. Shi ma Mustapha ya miƙe ya sa Habib a gaba don su tafi, sai dai shi Habib ɗin ya nuna ba zai koma don ya fi so ya zauna a nan wajen Hajia. Alhaji ne ya saka shi a gaba da nasiha yana nuna masa gara ya zauna saboda ƙannensa, kada ya tafi ya barsu su kuma bai san me zai faru da su ba.

Sai wajen ƙarfe tara sannan Hajia ta shirya suka kama hanya tare da Habib ɗin da Mustapha suka koma gidan. A cikin tashin hankali suka sami yaran, Nasreen da Shukra suna sanye da uniform ɗinsu; don sai da suka fara shirin makaranta sannan Naja ta sauko ta sanar da su ba za su makaranta ba Habib ya ɓata Abbansu kuma ya tafi nemansa.

Babu wanda ya ji shigowarsu gidan saboda Mustapha a waje ya ajiye motarsa saboda Hajia tace yanzu za ta fito ya mayar da ita. Da sallama suka shiga parlor ɗin, Nasreen ce da Shukra suna zaune a parlor ɗin da flask ɗin shayi a gabansu da ƙaton bread. Sai dai sun kasa shan shayin sun yi tsuru-tsuru. Da gudu suka miƙe, Shukra ta faɗa jikin Habib tana dariya yayin da Nasreen ta matsa kusa da Hajia. Suka ƙarasa ciki suka zauna.

Hajia tace ‘Ina Afaf? Nasreen tace ‘Tana ɗakinmu. ‘Antin fa da Rukayya? Nasreen ce ta sake sunkuyar da kai tace ‘Ba su sauko ba. Hajia tace ‘To ki je ki kirawo min ita ki ce ta zo. Shukra tace ‘Yanzu fa ta leƙo kuma tace kada wanda ya hau mata sama ya dame ta, ko menene a jira sai ta sauko. Hajia ta jijjiga kai, ta kalli Mustapha.

Ya ɗan diririce sannan yace ‘Hajia tasowa za ki yi mu je saman ai. Ba tare da wani musu ba ta miƙe ta tasa Nasreen da Shukra a gaba tana biye da su yayin da Mustapha da Habib suke biye da ita. Anti Wiyya ce a zaune a kan kafet da kwanuka a gabanta suna cin abinci ita da Rukayya, yayin da Naja take zaune a kan kujera tana cin nata abincin suna hira.

Da yake kicin a buɗe yake ana hango mai aikinta da goyon baby tana goge-goge. Shukra ce ta fara shiga tana surutu don haka a fusace Anti Wiyya tace ‘To sarkin tsurku, ba cewa aka yi ku zauna a ƙasan ba shi ne kika shigo kina….’ A lokaci guda kuma Naja tace ‘Ai sai na yi maganin wannan yar… Sallamar Hajia ce ta katse musu zantukan, ta ƙarasa ciki yayin da Shukra ta zagaye ta koma bayan Abbanta.

Suka ƙarasa ciki suka zauna yayin da Naja da Wiyya suka diririce. Naja ta yi wuf ta miƙe ta kwashi kwanukanta tana cewa ‘Bari na wanko hannu.’ Ta nufi kicin cikin sauri. Ita ma Wiyya ta kwashi nata kwanukan ta miƙe tana cewa ‘Sannu da zuwa Hajia, bari na kawo miki abinci. Rukayya tace ‘Anti ban ƙoshi da naman ba.’ Ba ta ko saurare ta ba ta wuce kichin yayin da ita kuma ta tashi ta bi bayanta da sauri.

Sai dai duk saurinsu kowa ya riga ya ga abinda yake cikin kwanukan nasu; farfesun kaji ne wanda suke haɗawa da burodi da shayi suna ci. Bayan sun zauna Hajia ta dubi Mustapha sannan ta dubi Nasreen tace ‘Nas ku ina naku naman na ga kuna cin gayan burodin. Ta yi darya tace ‘Ba a bamu ba, dama kullum abincin sama daban da na ƙasa har gara ma idan Abban yana nan.’

Hajia ta sake kallo shi tace ‘Allah ya sauwaƙe. Naja ce ta dawo parlor ɗin ta zauna a kan kafet ta gaida Hajia, bayan ta amsa ta dubi Nasreen tace ‘Je ki kicin ki taya Anti Wiyya ta ɗauko wa su Hajia abinci. Hajia ta ɗaga hannu tace ‘Ki ce ta bar shi, ku bar shi ma, abincin da na ga bai isa an raba da yara ba ai ba zai isa har a ba wa baƙo ba. Ni na ci abincina ku bar shi na ƙoshi.’

‘A a Hajia ai akwai, su ma hawowa ne ba su yi ba nake jira Jummai ta gama wanke-wanke ta miƙa musu. ‘To me za su shigo su yi, su da za ki yi maganinsu. Ai sai dai kawai a cigaba da addua kada a wayi gari kin koro su daga gidan kamar yanda kika koro ɗan uwansu cikin dare.’ Hajia ta ba ta amsa.

‘Wallahi Hajia babu wanda ya koro shi. ‘Allah ne kawai zai gane gaskiya, amma dai ke ki ji tsoron Allah. Kin ba ni kunya, wallahi kin ba ni kunya! Ban taɓa zaton haka daga gareki ba. Gaba ɗaya mun zata zuwanki gidan nan zai sa yaran nan su sami kulawa ta musamman ashe ba haka ba ne. Ke da ‘yauwarki da ‘yayanki kuna sama kuna cin kaji yaran suna ƙasa suna fama da burodi.

Kuma ma har sharaɗi aka kafa musu cewa kada su hawo su dame ki. Kamar dai ba gidan ubansu ba. Suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Hajia ce ta karya shirun ta dubi Mustapha tace ‘Kai dai ba ka kyauta ba, yanzu rayuwar da kuke yi kenan? Su waɗannan da uwarsu ta mutu kun bar su a ƙasa kuna sama kuna jin dadi. To ka ji tsoron Allah. Ke ma kuma ki ji tsoron Allah.

Bana jin sun taɓa ganin haka a wajen Khadeeja, ashe dama jira kike ku kore ta daga gidan ki cuzgunawa marayun Allah. Ta sunkuyar da kai kamar wadda za ta dungura. Habib yace ‘Ai tunda suka dawo daga Saudiyya aka hana su hawowa nan, ɗakinsu ma da komai nasu ya koma ƙasa.’

Hajia ta dubi Mustapha duba na takaici har sai da ya sunkuyar da kansa cike da kunya. Ta miƙe tana cewa ‘Ai shikenan, amma tabbas ba zan bar wannan zaluncin ba. Kuma ko da kin ga kamar kin yi nasara to Allah yana kallonku gaban ɗaya. Yaran su ma suka miƙe, Hajia ta dubi Mustapha wanda kunya ta hana shi miƙewa tace ‘Za ka samu ka mayar da ni gida ko sai ta ba ka izini?’

Ya miƙe kamar wanda aka tsikara. Naja tace ‘Don Allah Hajia ki yi haƙuri. Wallahi ba haka abubuwan suke ba rashin fahimta kawai aka samu wallahi ana kula da su. Ta dube ta tace ‘Allah ya sa, ai ni ma haka nake so. Sai dai kowa yayi don Allah ai ya sani ko, Allah kuma yana sane. Ta wuce yaran da Mustapha suka bi ta a baya suka fice.

Har suka isa gida tana faman caccakar Mustapha a kan yanayin da ta gani a gidansa kuma tana tuna masa girman haƙƙin yaran nan a wuyansa da shi da matarsa. Ba shi da abinda zai gaya mata sai haƙuri kawai yake ba ta; shi ma ba ya jin daɗin yanda gidan ya koma tun bayan rabuwarsa da Khadeeja. Ba da son ranshi ba ta mayar da yara ƙasa kuma wannan raba abincin ya sha yin magana a kai.

Amma ta iya abun ganin ido ne kawai, idan yana nan sai ta yi kamar komai normal amma da zarar ya fita sai ta tsawatarwa yaran kowa ya shiga hankalinsa. Abinci kuwa dama idan dai ba a gidan zai ci ba tabbas abincin da ake dafawa a sama daban kuma abincin da take ba wa mai aiki ta dafawa yaran daban ne. Duk wani daɗi a sama suke ci ita da yaranta da ‘yan uwanta su kansu yaran har sun saba.

Ga shi ta hana su kula ubansu sosai, domin in dai yana saman nan ba ta barinsu su ganshi. Har sun gaji da yanda take musu sun haƙura sun ma daina cewa suna son magana da shi. Haka ya ƙarasa gidan ya ajiye Hajia a bakin gate ya dawo saboda ba ya son ya shiga ciki saboda ya san ba zai ji da daɗi ba a wajen Alhaji.

Suna fita Anti Wiyya ta fito daga kitchen jiki a sanyaye, ta zauna kusa da Naja ta kama haɓa tana cewa ‘Ikon Allah, kin ji mutane ko? Ko motsin shigowarsu ba mu ji ba sai kace shiri. Ta taɓe baki ‘Hmmn! Su suka sani. Dama tafiya ya yi ya kai rahoto shi yasa ya bi dare su kuma ba su yi tunanin su kirawo mutane su sanar cewa ya isa can ba saboda sun shirya tsiya. A kansu zata ƙare in sha Allahu.’

Ta miƙe kamar an tsikare ta tana cewa ‘Bari ki gani na haɗa kayana na bar gidan nan kafin ya dawo ya kore ni da kansa. ‘Haba Anti, saura sati biyu dama fa ki tafi tunda kin ce ba za ki yi min arba’in ba. Ki yi zamanki babu abinda zai yi.’ Ta faɗa tana gyara zama. Wallahi tafiya zan yi, da wanne idon zan kalle shi ya riga ya gama raina ni. Ina nan ina yagar kaza na bar masa yara suna fama da gayan burodi.’

Ta marairaice ‘Anti idan kika tafi ma in ya dawo ai sai yace ba ni da gaskiya. Ta nufo ƙasa don haɗa kayanta tana cewa ‘Ku kwashe ƙalau amma ni da mijinki ba za mu sake haɗuwa ba in sha Allahu, ko a kwararo balle ma a gidansa. Tana ji tana gani Anti Wiyya ta fice ta bar mata gidan. Ba ta daɗe da fita ba Mustapha ya dawo.

Yana shiga parlor ɗin ƙasa ya tarar da Afaf ta fito tana shan baƙin shayi da burodi yayinda sauran yaran suke zaune suna kallon TV. Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya ƙarasa ya zauna a kusa da Shukra, ya kalli kofin shayin Afaf wanda ta ajiye a kusa da ita tana ƙoƙarin sake yago burodi. Yace ‘Ya kike shan baƙin shayi Yaya?’

Tace ‘Um, babu madara a nan dama idan na yi canjin kuɗin makaranta ne nake siyo mana kuma yanzu ka ga ina hutu shi yasa ba ni da kuɗi. Takaici ya cika shi, yanzu da ransa da lafiyarsa madarar shayi a ce sai Afaf ta tara kuɗin makarantar da yake ba ta ta siya sannan za su sha. To wai ina kansa ya shiga hakan take faruwa a gidansa? Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin Khadeeja ta hana yaranshi wani abu da ya siyo ba, sai dai ma ya san lokutan da take sayen abu da kuɗinta su ci ita da yaran.

To wai yaushe ma Khadeeja ta bar gidan? Ba a fi wata takwas ba fa da rabuwarsa da Khadeeja amma gidan duk ya zama haka? Ita da take zama cin abinci a tsakiyar yaran balle a ce ta ɓoye wani abu ta hana su. Ya bi fuskar yaran da kallo gaba ɗayansu babu wadda take da cikakkiyar walwala, tabbas yanzu ne za su ji nauyin maraicinsu.

Shi kanshi sai ya ji ƙwalla tana neman kwace masa, sai da ya yi da gaske sannan ya mayar da ƙwallar. Ya dubi Nasreen yace ‘Nas ɗauko min kofi ni ma na sha shayin.’ Ta tashi ta shiga nan kichin ɗin ƙasan ta ɗauko masa tsohon kofin tangaran ta kawo masa da sugar a ‘yar roba. Ya kalli kofin duk ya dafe ya dubi Nasreen ɗin da ta ajiye kofin yace ‘Ki je sama ki dauko min wani kofin mai kyau.’

Tace ‘Abba Anti Naja fa tace kada mu hau kuma wallahi idan na hau zagina za ta yi in na yi magana tace na mata rashin kunya, sai dai ko yaya Afaf ta je ta ɗauko. Haka ya karɓi kofin ba don ya so ba ya haɗa banƙin shayi ya sha tare da ragowar burodin da suke ci. Sai da ya gama sannan ya tashi ya haye sama domin ya shiryo ya fita aiki.

Ta ji dawowarsa tunda ya shigo da motarsa, sai dai da ta ji shiru ta saka rai ya tsaya a wajen yaransa don ya ƙara jin abubuwan da za su gaya masa a game da ita. Don haka a parlor ya same ta tana ta cika tana batsewa ita a dole kada ya yi mata faɗa. A gajiye yake sannan ba shi da karsashin hayaniya da ita, don haka ko inda take bai kalla ba ya shige ɗaki ya fara shirinsa.

A shirye tsaf ya fito ɗauke da jakarsa, tana nan zaune a inda ya bar ta. Ya ɗauke kai ya nufi ƙofa bayan ya amsa a dawo lafiyar da Rukayya ta yi masa. Ta miƙe ta nufo shi fuska babu walwala tana cewa ‘Ga abincinka can za ka fita ba ka yi breakfast ɗin ba. Ya kalle ta a fusace ba tare da ya daina tafiya ba yace ‘Abincin da kike hana yarana? Ni na ƙoshi ki kirawo ragowar ‘yan uwanki ku cinye.’

Ta buɗe baki za ta yi magana sai dai kafin ta ce wani abu ya ci rabin ƙafar benen, tana nan tsaye kamar za ta haɗiyi zuciya ta jiyo ficewar motarsa daga gidan. Dole ita ma ta shirya ta fice ta tafi wajen aiki domin a hakan ma ta san sai an harare ta tunda ta makara.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Ɗaya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Ɗaya
Labarin na GabaWasu Laƙanin Sunayen Hausawa A Al’adun Gargajiya 3
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.