Mijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Ɗaya

0
169

Suna daga cikin na farko-farkon dawowa a alhazai. Tun kafin su baro masaukinsu ta gama magana da shi a kan ba za a ɗauko yara ba sai ta yi kwana biyar tana hutawa, don Rukayya ma tace kada a dawo da ita sai bayan sati biyu. Abokinsa ne ya ɗauko su daga airport ya kai su har gida, da yake ya saka Habib ya buɗe gidan an gyara tsaf suka sami ko ina.

Da safe suka sauka don haka kafin su shiga gidan sai da suka yi order ɗin abincin rana. Sai can da yamma bayan sun gama hutawa sannan ya shirya ya wuce gidan Hajia. Nan ya zauna suka yita hira a wajen Hajia. Duk da ya gaya musu ba yau zai tafi da su ba amma Shukra ta kafe a kan ita a ranar take son ta bi su, don haka yace su shirya tare da su zai tafi.

Sai bayan sallar magriba sannan Alhaji ya dawo, bayan sun gaisa suka cigaba da hirarrakinsu. Alhaji yace ‘Yauwa, ya wajen Khadeeja kuwa? Kun yi magana ne? Yace ‘A a ni ban neme ta ba kuma ba zan neme ta ba Allhaji, ita ce fa tace na sake ta kuma na saketan, ta je ta ɗana zaman gidan.’

Alhaji ya ɗan ɓata rai yace ‘Kai! Ba a yi wa mata haka, idan jira kake ta neme ka to ba lallai ta neme ka ba gara ma ka je idan da wani abu ka yi wa iyayenta bayani su yi mata faɗa ka mayar da aurenta. Ya jijjiga kai ‘Alhaji ni ba inda zan je, idan tana son auren nata za ta neme ni tunda ai da kanta ta nemi sakin.’

Haka Alhaji ya saka shi a gaba ya yi ta yi masa nasiha, daga baya ya yi musu sallama ya kwashi yaransa suka wuce. Ba shi kaɗai ba hatta yaran ma sai da suka gane ba ta ji daɗin dawowarsu a ranar ba, haka dai suka gaggaisa suka yi mata sannu zuwa kowa ya shiga harkarsa. Inda Allah ya taimake ta ma shi ne ya siyo musu abincin dare.

Ta riga shi kwanciya saboda gaba ɗaya ba ta ma jin daɗin jikinta, sai da suka gama hira shi da yaransa sanan ya rufe gidan kowa ya tafi ya kwanta. Motsin shigarsa ɗaki shi ya tashe ta daga bacci, sai da ta bari ya gama shirinsa ya kwanta sannan ta gyara kwanciya tace ‘Kai da muka yi da kai ka bar yara sai mun huta shi ne ka taho da su?

Ya gyara kwanciyarsa yace ‘To sun ce za su taho, su ma fa ba daɗin zaman suke ji ba a wani wajen kin san kowanne yaro ya fi son gidansu. Ta kula idan dai a kan yaransa ne ba zai saurare ta ba don haka ba tare da ta ce komai ba ta juya masa baya ta cigaba da baccinta; amma dai ta san tabbas dole ta ɗauki mataki don babu yanda za a yi ta bari ya kori kishiyarta kuma ya mayar da yaransa kishiyarta.

Dole ta ɗauki mataki. Sai da ta yi sati da dawowa sanna ta je gidansu ta taho da Rukayya, don ko ‘yan gidan nasu ma da za su zo musu sannu da zuwa cewa ta yi kada a zo da ita don idan ta zo ba za ta yadda ta koma ba. Bayan ta gama hirarta a gidan ta wuce gidan Anti Wiyya.

Nan suka zauna ta yi mata bayanin ayyukan da aka yi mata, sannan ta ba ta wasu layu guda biyu tace ‘Gasu nan hatimi ne aka rubuta da ayoyin Allah, ki sami waje ki ƙone su ƙurmus sai ki zuba masa tokar a miya. In dai ya sha miyar nan to ba zai sake yi miki musu ba. Wannan aikin bana haufinsa kamar yankan wuƙa ne sai dai idan ba ki aikata ba.

Ta karɓa ta mayar cikin ledarsu ta kulle ta jefa a jaka tana cewa ‘Ai dai kin ce ayoyi ne ko? Tace ‘Wallahi ayoyi ne, ke malamin fa har almajirai gare shi suna karatun allo. Ai idan kin haihu za mu je ki gani da kanki idan har kina da wata matsala. ‘Hmm! Ai dole ma na yi Anti Wiyya, daga dawowarmu ya fara neman ya nuna min iyakata a kan yaransa, ga shi su baka isa ka saka su aikin komai ba sai dai kai ka ƙare a hidimarsu.

Ai yau ɗin nan zan aikata wannan layun kowa ya shiga hankalinsa. Ko nan ma fa da zan taho shi so ya yi na taho da su wai saboda kada na bar su su kaɗai, ki ji don Allah sai kace wasu jarirai. ‘Ya zata ke ma Khadeejan ce. Suka yi dariya gaba ɗaya. Sai gefin magriba sannan ta ɗauko Rukayya suka dawo gidan. Tana zuwa ta ɗora abincin dare inda ta dafa tuwo miyar kuka.

Tsaf ta haɗe tokar layun nan ta juye masa a miya ta juya komai ya shige, ta yi sa’a kuma ya sami tuwon nan ya yi masa cin ƙoshi. A hankali ta fara ganin kyawun aikin da Anti Wiyya ta yi mata. Cikin wata ɗaya da dawowarsu ta tattare kayanta ta koma sama part ɗinshi, ba ta son ta yi maganar part ɗin Khadeeja sai ta bari wata uku ya cika saboda kada ma ta tuna masa ya je ya dawo da ita.

Yanzu ta samu idan suna sama shi da ita ta hana yaran hawa kuma ya kasa yi mata magana. Ta san bai ji daɗi ba don yana nuna mata a fuska amma wannan ba damuwarta ba ce, kuma idan shi ya zauna a ƙasan da zarar ta kirawo shi haka zai tashi ya bi bayanta su koma saman da shi da ita da Rukayya, sauran yaran suna ƙasa.

Sai dare ya yi idan za su kwanta ne suke hawa saman da yake ɗakinsu yana can. Suna hawa sai ta kaɗa su su wuce ɗaki su kwanta. Tun ranar da ta koma gida take lissafi, duk da dai tana jini a lokacin amma dai sai da ta lissafa jini uku, kuma jiya ne ranar da ta fita daga jini na uku bayan rabuwarsu da Mustafa.

Tana zaune a gefen ƙaramin gadonta wanda shi ne dai gadonta tun kafin ta auri Mustapha, ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana tunanin yanda rayuwarta za ta cigaba; tabbas ta ji daɗin rabuwa da Mustapha, ba ta yi nadama ba kuma ba za ta koma ba. Domin ko babu komai yanzu ne ta tabbatar tana cikin nutsuwa.

Duk wani abu na kulawa da Hammad yake buƙata za ta iya yi masa don haka ba zama ta nemi Mustaphan da maganar Hammad ɗin ba saboda ma kada yace ta ba shi yaronsa. Fatan ta ɗaya Allah ya tabbatar mata da alkahiri a cikin rayuwarta ta nan gaba; duk da ba ta tunanin akwai namijin da za ta sake aure.

Ba za ta yarda a sake yi mata yanda Mustapha yai mata ba kuma ba ta fatan ta zama dalilin da zai saka wani namijin ya mayar da matarsa kamar yanda Mustapha ya mayar da ita bayan ya ƙara aure. A hankali ta miƙe ta fito daga ɗakin. Ta ji daɗi da ta sami Baffa da Mommy a parlor suna zaune suna cin abinci. Bayan ta gaishe su ta dubi Baffa tace ‘Baffa ina so a debo min kayana na gidansu Hammad.’

Ya ajiye cokalinsa yace ‘Ikon Allah, bai neme ki ba kenan? ‘Eh Baffa, duk da ma ko ya neme nin ba zan koma ba. Jiya ne na gama iddata ka ga auren ma ya ƙare kenan. ‘Haka ne, Allah ya sa haka ne ya fiye muku alkhairi gaba ɗayanku. Gobe sai ƙaninki ya shirya su je a kwaso miki kayan, ki yi masa bayanin abubuwan da za su kwaso. ‘To Baffa.’

Mommy tace ‘To ya za a yi da Hammad? Ai dai ya kamata a yi magana da Mustaphan ya dinga turo abinda za a kula masa da yaron ko? Tace ‘Eh ba mu dai yi magana da shi ba, amma da bari na yi sai zai shiga makaranta tukunna. Baffa yace ‘A a tun yanzu zai ɗauki nauyin ɗan sa, ni zan neme shi in sha Allahu.’

Mommy tace ‘Haka ne kam, ba sai daga baya ba a zo ana sa toka sa katsi. Suka ƙarasa hirarrakinsu sanna Khadeeja ta yi musu sallama ta tafi office. A mota suke tafe yana tuƙa su, zai sauke Naja a wajen aikinta sannan ya wuce. Wayarsa ce ta fara ringing, kusan a lokaci guda suka kalli screen ɗin wayar “Babe” shi ne sunan da ya yi saving lambar Khadeeja da shi tun kafin aurensu kuma rabuwarsu ma ba ta saka ya goge ba.

To me ya mantar da shi Khadeeja ma da bai ko da kirawo ta a waya ba tun bayan dawowarsa daga aikin Hajji? Ko da yake ba mantawa ya yi ba jira yake ta kirawo shi ta ba shi hakuri idan ba haka ba ma ya ƙyale ta ta ɗanɗana zawarcin daga baya ya koma a sake ɗaura musu aure idan ta gane shayi ruwa ne. To menene take kiransa yanzun?

Ko har zawarcin ya ishe ta ne? Wataƙila kuma ta ga tana daf da gama idda ne bai neme ta ba shi ne ita take nemansa ya zo a daidaita. Ya ɗauki wayar ya amsa sannan ya kara a kunnensa a daidai lokacin da ya kaucewa haɗa ido da Naja wadda take ta faman bin shi da kallo saboda ta san lambar wacece ya yi saving da sunan Babe.

Babu wata alamar nadama ko kuma damuwa a muryarta, cike da walwalarta suka gaisa kamar babu wani abu na rashin daɗi da ya taɓa haɗa su. Bayan sun gaisa tace ‘Na gama idda jiya, so in sha Allahu idan babu damuwa gobe zan turo Ahmada za su zo su ɗebar min kaya na. kayan da suke bedroom ɗin kawai za a ɗauka tunda dama duk na sabon gida ne ka saka.

Amma akwai food flasks ɗina a kitchen guda uku da kuma tea flask da za su haɗo min da su shikenan. Ina fatan babu wata damuwa. Sai da ya buɗe baki da niyyar ba ta amsa sannan ya gane yawun bakinsa ya riga ya ƙafe, ya kifta ido ya ɗan lalubo yawun bakin nasa sannan ya kalli Naja wadda take ta faman binsa da kallo kamar wata mayunwaciyar kura a yayin da ta hango nama yace ‘Ehhm, babu matsala. Um kin gama idda kenan?’

‘Eh, na gama jini uku a jiya. Idan ma an haɗa da jinin ɓarin da na yi jini huɗu kenan duka da shi kwana biyu ya yi ya ɗauke tun kafin sakin. ‘Oh haka ne, Allah ya kai mu, sai sun zo ɗin.’ Ya amsa. Da yake ranar aiki ce za su zo da wuri domin su same ka a gidan in sha Allahu.’ Ta faɗa sannan ta yi masa sallama ta ajiye wayarta.

Ya mayar da tashi wayar ya ajiye a inda ya ɗauka ya mayar da hankalinsa ga hanya. Naja wadda take ta kallonsa tana jiran ya ba ta labarin abinda aka faɗa wayar ta gaji da kallonsa kuma bai yi alamar zai yi magana ba tace ‘Maman Hammad ce? A gajarce yace ‘Eh.’ Ba iya wannan amsar take son ji ba don haka tace ‘Wai menene?’

Cikin yanayi na ƙosawa yace ‘Ta gama idda ne take so gobe da safe za a zo a kwasar mata kayanta. Ta gyara zama ta ɓata rai tana cewa ‘Ai na zata furnitures ɗin naka ne? A fusace yace ‘Eh, iya nata za a kwasar mata ai ko akwai naki a ciki ne kuma. Ta taɓe baki tace ‘A a, me ya yi zafi.’

Daga haka har suka ƙarasa ya sauke ta babu wanda ya sake magana. Duk yanda ya so ya mayar da hankali a kan aikinsa hakan bai samu ba; zai iya cewa ba ya nadamar rabuwa da Khadeeja amma tabbas yau da ta gaya masa ta gama idda jikinsa ya yi sanyi. Zai yi kewarta, kuma ya ma ji a jikinsa kamar a gutsure wata tsoka daga jikinsa.

Bai ma taɓa tunanin zai yi kewar Khadeeja haka ba amma ga shi kayanta kawai aka ce za a kwasa amma ya ji babu daɗi. Bai daɗe da shiga office ɗin ba ya lalubo wayarsa ya danna mata kira, kamar ɗazu yanzu ma muryarta cike take da walwala. Sosai ya kasa kunne yana ƙoƙarin ko gano wata alama ta damuwa a muryarta amma ji yake kamar ma an ƙarawa muryarta zaƙi.

Bayan ta amsa sallamarsa tace ‘Um ka yi mantuwa ne? Kamar wanda aka farkar daga barci yace ‘No. Umm! Hammad fa? Ya kamata ya dawo cikin ‘yan uwanasa ai ko? A nutse tace ‘Eh haka ne, amma ka ga bai ƙarasa shekaru huɗu ba ma. Ina ganin nan da zuwa ya gama primary in sha Allahu sai ya dawo cikin ‘yan uwansa tunda tabbas ni na san kula da yaro akwai wahala, musamman da yake ka ga Antinsu ba zama take ba tana aikinta.

Ina ganin ka bar min shi duk wani abu da yake buƙata in sha Allahu zan sanar maka, idan ya iya kula da kansa sai ya dawo gida. So yake ya ce mata hakan ba zai yiwu ba ko don ma ya ɓata mata rai, amma ya kasa. Tabbas yana son ganin yaronsa a kusa da shi cikin ‘yanuwansa amma kuma idan ya karɓe shi ba ya jin Naja za ta iya haɗawa da shi ta riƙe, don yanzun ma kullum cikin ƙorafi take a kan yara suna gajiyar da ita.

Gara ma ya bari ta riƙe shi in Allah ya yi da ragowar zaman sa koma tare. ‘Um haka ne, to babu damuwa. Sai goben kenan. ‘Ok, Allah ya kai mu goben. Ba ta taɓa tsammanin Mustapha zai bar mata Hammad da sauƙi ba, don haka ma da ya yi saurin amincewa da maganarta sai ta ji wani daɗi marar misaltuwa; domin ta hango wahalar da zai sha idan ya koma gidan; zama zai yi kamar maraya.

Tunda su Shukra su huɗu ne, Rukayya kuma uwarta tana gidan sai shi kaɗai wanda ba shi da uwa ba shi da ɗan uwa a gidan. A hankali ta mayar da wayar tata ta ajiye a kan teburinta. Ta sunkuyar da kanta ta share ƙwallar da ta taru a kwarmin idonta sannan ta zuba fuskarta a tafukan hannunta; ta tuno lokacin da suna soyayya da Mustapha kafin suyi aure. Wai ina soyayyar nan ta tafi ne?

Ya barta ita kaɗai tana ta dakon soyayyarsa har tsawon shekaru takwas? Tabbas ta sha wahala a gidan Mustapha; ba wai wahalar jiki ba don wahalar jiki ta san abinda ta yi bai wuce abinda matar aure za ta yi ba. Sai dai wahalar zuciya da ta sha; kulawa da tausaya tare da ƙauna da zuciyarta take buƙata daga wajen Mustapha su ne ba ta samu ba.

Ko su ɗin ma ta haƙra da su tana zama haka tunda ko babu komai tana kallonsa a matsayin mijinta kuma suna kwana tare. Amma daga lokacin da ya auro wata kuma ya ke ba ta kulawa da ƙauna wanda ita ya kasa ba ta daga lokacin ta yanke ƙauna daga zaman gidan Mustapha.

Ba za ta ce ba ta jin zafin rabuwa da shi ba domin tabbas ta san ko babu ƙauna akwai sabo, amma tabbas ba za ta sake komawa gidan Mustapha ba. Domin ta yi sujjada ta roƙi Allah kada ya sake haɗa ta zaman aure da Mustapha. Da farko ta fara jin haushnsa amma daga baya sai ta ga jin haushin babu wani amfani; ko babu komai dole ta yi wa Hammad kara ta girmama mahaifinsa.

Ta sake share ƙwallar da ta taru a kwarmin idonta, ta kalli ruwan hawayen da ta lakata a hannun nata; to kukan me take a halin yanzu? Ta zata ta gama kuka a kan Mustapha. Ta yi murmushi ta sake goge ƙwallarta; ta san ba za ta iya goge Mustapha daga cikin tarihin rayuwarta ba amma tabbas ba ta fatan sake rayuwa irin wadda ta yi a gidansa. Ta goge fuskarta ta fice ta nufi cikin studio inda za ta gabatar da labarai.

Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Talatin

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTarihin Dr. Magaji Ahmad Gaya (PhD)
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Biyu
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.