Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Shida

0
4

Tana jiyo motsin shigowar Mustapha gidan amma ba ta yi zaton zai tafi da sauri ba, don haka ma ta jira sai da ta gama abinda take yi tunda ta jiyo shi da Baffa a tsakar gida. Sai dai ga mamakinta ko da ta fito Baffa ta tarar shi kaɗai, yana shirin shigewa mota ta yi sauri ta karasa.

Tace ‘Na ji kamar kai da Mustapha ne, ko har ya tafi ne? Ya tsaya yana riƙe da murfin mota yana cewa ‘Shi ne, matar tasa ce ta fara gwada masa tutsun nata shi ne ya taho kawo ƙara da sassafe. Ikon Allah, Khadija Iya-rigima. Me ta yi kuma?’

Nan ya ba ta labari kamar yanda Mustapha ya ba shi, ya ƙara da ‘Na ce su zo bayan Magriba don ita ma yanzu zan kirawo ta na sanar da ita kada ta yi taurin kai, kin san hali. Ta yi dariya ‘To Allah ya kai mu, ai an auna arziƙi ma da aka ɗauki lokaci haka ba ta fara rigimar ba. Suka yi dariya ta yi masa a dawo lafiya ya wuce sannan ta koma ciki.

Sai da yamma ta yi sannan ta kirawo Khadeeja a waya, bayan sun gaisa tace ‘Me ya haɗoki da Mustapha ne ya kawo ƙararki da sassafe ne? Ta yi dariya sannan ta ba ta labari, bayan ta gama ji tace ‘Ikon Allah, to neman mata Mustaphan yake yi kenan ko kuwa dai aure yake nema?’

‘Ni ma ban sani ba Mommy, amma dai ko ma menene ai da akwai cin fuska a ce ina yawo a taxi ita kuma tana yawo a motar mijina; at least ya bari ta aure shi sai ya ba ta wannan ikon. Kuma sannan idan ita ce za ta dinga yi masa hidimar yaransa ai sai ta karɓa gaba ɗaya ni kuma na huta gaba ɗaya.’

Mommy tace ‘Um! Da wannan, amma dai ki bari a bi abun a hankali. Saura kuma idan kun zo ki yi shiru ki ƙi yi wa Baffa bayani ya yanke miki hukunci in ma ya ga dama yace ki ba wa Mustaphan haƙuri. Ta yi ‘yar dariya ‘Ba zan yi shiru ba Mommy. Suka yi sallama suka ajiye wayar.

Sai dab da magriba ya dawo gidan, ya yi mamaki da ya jiyo Rashida da Afaf a kitchen suna ƙoƙarin dafa abincin dare; a tunaninsa tunda ya san Baffa ya gaya mata yana nemansu ya kamata a ce ta shiga hankalinta. Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce ɗakinta; ƙofarta a rufe take, ya saka mukullinsa ya ji har yanzu ba ta cire mukullin ba don haka ya daure ya ƙwanƙwasa.

Sai da ta gama yauƙinta sannan ta buɗe ta rige hannun kofar ta matsa ya shige. Ya so ya zare mukullin kofar to amma sai ya ga idan ya zare ai duk da haka ba lallai ta dinga fita daga ɗakin ba balle ma ta dinga yin hidimar da ta saba; tunda dai wulaƙanci ne kawai ta shirya za ta yi.Don haka ya bi bayanta suka shige ɗakin, tun kafin ta gama zama a inda ta tashi yace ‘Baffa ya gaya miki mu je yana nemanmu ko?’

Cikin halin ko in kula tace ‘Ƙarfe nawa za mu je? Ya so a ce ta ba shi dama su yi magana su kashe wannan rigimar in ya so ya kirawo Baffa yace masa sun shirya amma sai dai ga alama ta fi so su je wajen Baffan. Yace ‘Da na dawo daga masallaci sai mu je.’

Ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya saurari amsarta ba. Ta bi bayansa da harara tana dariya; wato shi uban ‘yan son kai har yanzu bai ga laifinsa ba don haka ita yake tsammani ta ba shi haƙuri kenan. Tabbas yau sai ta ƙure wannan son zuciyar na Mustapha duk da har yanzu wata zuciyar tana gaya mata kada ta je ta yi wa mijinta tonon asiri a wajen iyayenta.

Yana dawowa daga masallaci ya same ta a shirye, ko zama bai yi ba suka sallami yara suka fice daga gidan. Suna shiga gidan suka sami Mommy wadda ta ba su umarni su ƙarasa parlor ɗin baƙi domin Baffa yana can yana jiransu. Yana zaune a kan kujera 3-seater don haka Mustapha ya zauna daga gefen damansa jikin 2-seater ita kuma Khadija ta koma ɗaya gefen jikin single seater ta zauna.

Bayan Baffa ya amsa gaisuwarsu ya dubi Khadeeja yace ‘Dije, me ya haɗa ki da maigidanki ne kika daina kula shi shi da yaransa? Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace ‘Baffa ba daina kula su na yi ba. Kafin Baffa yace wani abu Mommy ta shigo da sallama Nabila tana biye da ita ɗauke da tray wanda aka jera ruwa da lemo a kai, don haka Baffa ya tsaya ya amsa sallamarta.

Ta nunawa Nabila inda za ta ajiye tray ɗin daga kusa da Mustapha, ta ajiye ta gaida Mustaphan sannan ta miƙe ta fice daga parlor ɗin ita kuma Mommy ta kara ta zauna a kan kujerar da Khadija take zaune a ƙasanta. Ya juya ya gaida Mommy, bayan ta amsa Baffa ya sake duban Khadeeja yace ‘Ya aka yi Dije ina saurarenki.’

Tace ‘Baffa ba daina kula su na yi ba fa. To ai ya ce kusan kwana uku kenan ba kya kula kowa sai dai kawai ki kulle kanki a ɗaki kin bar yara da mai aiki sannan kuma gari yana wayewa sai ki fice ki tafi makaranta. Kawai saboda ya tura sakatariyarsa ta je makarantar yara kun haɗu.’

Ta faki ido ta share ƙwalla; ya riga ya ba wa Baffa kanun labaran don haka duk yanda take son ta kare mutuncinsa ba zai yiwu ba domin ita ma dole ta kare kanta a wajen mahaifinta. Ta gyara zama tace ‘Wallahi Baffa ina bakin ƙoƙarina wajen kula da gidan da yaran, kuma babu laifi duk mun sami fahimtar juna da yaran gaba ɗaya.

Duk wata hidimarsu ni nake yi, kuma ni ce nake ɗauko su daga makaranta ranar da ba na nan kuma sai mai-aikina ta ɗauko su. To shi ne ranar Monday suka yi open day a makaranta; ni ce na saba zuwar musu don haka tun weekend suka gaya min, shi kuma na manta ba mu yi maganar ba.

Don haka gari na wayewa da na shirya zan tafi school sai na tsaya makarantarsu. Shi ne sai na ga har ya tura sakatariyarsa ta je musu. Baffa ya yi dariya yace ‘To ai babu komai Dije, wataƙila don ba ku yi maganar ba ne kuma kin ga ita ɗin ai sakatariyarsa ce zai iya saka ta wannan aikin duk da dai personal ne.’

‘Ni Baffa ba zuwanta ne ya ɓata min rai ba…’ nan ta ba shi labarin yanda ta ga sakatariyar a motar Mustapha ɗin da kuma yanda tunda ta aure shi sau ɗaya ya taɓa kai ta makaranta a motarsa da kuma yanda ko ta shirya ba ya yarda ya fita da ita. Da kuma yana wasu lokutan tana tsaye a bakin titi yake dawowa daga kai su; ba ta sani ba ko yana ganinta amma ita dai tana ganinsa.

Baffa ya kalli Mustaphan ya kalli Mommy sannan ya kalli Mustapha wanda ya yi tsamo-tsamo don bai za ta Khadija za ta kawo wannan maganar ba; shi da ya ga ta daina damuwa ya rage mata hanya ma ya zata ta haƙura gaba ɗaya don haka bai san tana jin haushinsa a kan wannan ba.

Yace ‘Ikon Allah, yanzu a ce a ki ragewa mutum hanya sai ka ce wani wanda ake jin haushi? Ko dai akwai wata matsalar ne Mustapha?’ Nan da nan ya fara gyara zama kansa a ƙasa cikin rawar murya yace ‘Babu wata matsala, em… dama yawancin lokutan ne ai ba ta shiryawa da wuri su kuma yaran idan 7:30am ta yi rufe musu gate za a yi.

Umm.. shi yasa dole muke tafiya, kuma wasu lokutan ma idan na kai su gidan nake dawowa sai daga baya nake fita. Tace ‘Baffa ai ko ya dawo zai fita idan nace ya rage min hanya sai ya san abinda zai faɗa wanda zai sa ba zai tafi da ni ba don haka ma tun tuni na daina tambayarsa.’

Suka ɗan yi shiru na ɗan lokaci Mustapha yana ta ƙoƙarin haɗa ido da ita yayin da ita kuma take ta ƙoƙarin kauce masa don ko gefen da yake ba ta kalla ba. Baffa yace ‘Shikenan abinda ya saka ki fushin ko akwai wani abun?’ Kana jin muryarsa kuma ka kalli fuskarsa za ka san ransa ya sosu matuƙa, domin karsashi da rahar da ya fara wannan tattaunawar da su duka babu.

Har ta gyaɗa kai Mommy ta zungure ta da kafa, ta dago suka haɗa ido. Ta sunkuyar da kanta tace Baffa ita sakatariyar tasa kuma na tambaye shi menene a tsakaninsu; idan ma aurenta zai yi ai sai ya gaya min ba wai kawai na dinga ganinta a motarsa ba tana yawo a gari ni ina yawo a tasi.

Saboda ni dai yanda na ga ta nuna alaƙarsu ta fi ƙarfin ta office kawai, don yaran ma duk sun santa ni kaɗai ce a gida na fara ganinta ranar. Baffa ya mayar da idonsa kan Mustapha wanda ya yi sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa, ji yake kamar ya zura da gudu don bai taɓa zata Khadeeja za ta kawo waɗannan maganganun a gaban Baffa ba.

Suka yi shiru na ɗan lokaci kowa yana sauraron abinda Mustaphan zai ce, shi kuma ya sunkuyar da kai ya yi shiru kamar wanda ruwa ya ci. Mommy ce ta gaji da shirun ta yi gyaran murya tace ‘Uhm, ai gara ka gaya mata idan auren sakatariyar za ka yi ka ga tunda dai na san cewa ta san ka kai ka ƙara auren.’

Ya gyara zama yana shafa ƙeya yace ‘A a ba ma shi ba ne, kawai dai da na aiketan ne to kuma ana ɗan wahalar mota shi ne na ce ta je a motata tunda ta iya tuƙi. ’Jimawa kaɗan Baffa yace ‘Allah ya sauwaƙe. ’Mommy tace ‘Amin dai.

Suka sake yin shiru na ɗan lokaci, sannan Baffa ya kirawo sunan Khadeeja, ta amsa ta dube shi suka haɗa ido sannan yace ‘Ki yi hakuri Dije, kin ji. Ta gyada kai shi kuma ya ɗan numfasa sannan ya cigaba ‘Ki yi hakuri ki bi mijinki, kin ji bayanin da yayi. Kuma idan ma yace zai auri waccan yarinyar wannan bai kamata ya zama matsala ba tunda dai kin san duka wani namiji mijin mace huɗu ne.

Ki yi haƙuri ki cigaba da hidimarki kamar yanda kika saba, kin ji. Batun kai wa makaranta kuma kin ga shi ‘yayansa yake zubawa a mota yake kai su a makaranta kuma tabbas haka ya kamata uba nagari ya kasance, don haka idan kika gama shirya masa nashi yaran ke ma ki shirya ki yi min waya sai na zo na kai ki tunda dai ke ma ‘yata ce; kai ki makaranta kuma ba baƙon abu ba ne a wajena.’

Ya gyara zama ya ɗago kai a razane ‘A a Baffa a yi haƙuri ai ba sai an yi haka ba, in sha Allahu za mu dinga tafiya ma. Dama ai ba ta gaya min ne shiryawa kawai take tace ta tafi. Kada ka damu, zan dinga zuwa ina kai ta wannan aikina ne.’ Baffa ya ba shi amsa rai a ɓace.

‘A yi haƙuri Baffa, in sha Allahu ba za sake ba, ni ɗin ma zan dinga kai ta. A yi haƙuri.’ Mommy tace ‘Ke kuma ki yi haƙuri da yaranki tunda su ba su yi miki komai ba, ki kula da su ku zauna lafiya. Shi ma kuma kin ji bayaninsa, ki je ku yi zamanku lafiya kamar yanda kuka saba saboda Allah. Ita rayuwar aure haƙuri ce, ku dinga haƙuri da juna.

Kuma nan gaba ko wata matsala ta taso muku ku yi ƙoƙari ku kashe ta a tsakaninku. Toh.’ Ta amsa cikin sanyin murya. Jimawa kaɗan suka yi wa Baffa da Mommy sallama suka fice; Khadeeja ta so shiga cikin gidan wajen Nabeela amma Mommy tace kada ta shiga ta bar shi yana jira idan ta shirya ta dawo su yi hirar.

Tunda suka shiga motar bai ce komai ba sai muzurai kawai yake, don haka ita ma zuciyarta wasai take. Ta ji daɗin yanda Baffa ya nunawa Mustapha cewa ita ma da gatanta; duk da dai har yanzu tana jin cewa ba za ta ɗorawa kanta jiransa ya kai ta makaranta ba balle ta ɗorawa kanta damuwa.

Suna shiga gidan ta wuce ɗakinta shi ma ya wuce nashi ɗakin. Sai da ta yi sallah sannan ta fito wajen yaran; zuwa lokacin Shukra har ta riga ta yi bacci. Bayan ta tabbatar sun ci abinci ta wuce kitchen, ta kirawo Rashida tana tambayarta me suka dafa da daddare. Ta gaya mata indomie suka dafa saboda haka Afaf tace, ta nuna mata indomie ɗin da ta saka a flask ta ajiyewa Abbansu.

Ta riga ta san ba ya son indomie, musamman idan ta fara sanyi kuma ita ma yunwa take ji ba ta son cin indomie mai sanyi. Don haka Rashida ta taya ta ta gyara busasshen kifi ta dafa musu jollof sphageti mai rai da lafiya. Nan da nan gidan ya ɗauki ƙamshi; zuwa loakacin yaran duk sun kwanta.

Ta jera abincin a dining table sannan ta haɗa masa shayi mai kayan ƙamshi irin wanda yake so sanna ta wuce ɗakinsa ta tura ƙofa ta shiga. Saura kaɗan ta yi dariya saboda ganin yanda ɗakin ya yi kaca-kaca; ga ƙura ga kaya da tarkacensa ko ina. A ranta tace mutum sai kace kuturu, ya sa hannu ya gyara makwancinsa kawai ya gagare shi.

Ta ɗan yi gyaran murya tace ‘Ga abinci can na saka a dining,’ Dama tunanin abincin yake don yunwa yake ji sosai; ya riga ya san indomie suka dafa tunda jiya ma ita suka dafa don haka ya riga ya fara tunanin yanda zai yi sai kuma tace masa ga abinci. Ya dube ta ya ɗan sassauta fuskarsa yace ‘Yanzu zan fito.’

Ba tare da ta ba shi amsa ba ta juya ta fice, ya bi bayanta da kallo yana murmushin yaƙe. Ya rasa daɗi zai ji ta ba shi abinci wanda hakan yake nuna za ta cigaba da hidimarta; ko kuwa haushinta zai ji saboda yanda ta yaga shi a gaban Baffanta. Haka dai ya taso ya fito, babu kowa a parlor ɗin don haka ya zauna ya ci abincinsa ya ƙoshi; irin ƙoshin da ya kwana biyu bai yi ba.

Sai da ya gama cin abincinsa ya huta sannan daga baya ya je ya kullo gidan ya shiga ɗakinsa; har ya kwanta kuma ya tashi ya bi bayan Khadeeja. Ya kula idan ya biye mata ba za ta neme shi ba, ko ba komai kuma yana so su yi magana ya ƙara kwantar mata da hankali game da maganar Naja don ba yanzu yake so ta sani ba. Sannan kuma yana so ya nuna mata rashin jin dadinsa game da yanda ta je ta kunyata shi a gaban Baffa.

Duk yanda yaso ta taso su koma ɗakinsa su kwana kamar yanda ya saba bai samu ba, daga haka ya gane idan ya fiye takura mata zata sake ɗauke musu wuta; don haka sai ya haƙura ya zubar da duk maganganun da ya taho da niyyar gaya mata. Ya haƙura suka kwana a nan ɗakin nata tunda tace ta fara bacci ba ta son canza ɗaki.

Tun asuba ta tashi kamar yanda ta saba, nan da nan ta shiga hidima da yara da taimakon Rashida. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba da ya dawo daga masallaci sallar asuba ya jiyo ta a kitchen, don haka cike da walwala ya wuce ɗaki ya koma bacci kamar yanda ya saba.

Ƙarfe bakwai na safe yana fitowa kowa ya shirya yayin da Khadeeja take kai wa da kawowa tana jera masa nasa abincin a dininga table. Bayan ya amsa gaisuwar yaran yace ‘To kowa ya ɗauki kayansa mu wuce ko? Nan da nan suka miƙe suka fara ficewa. Ya dubi Khadeeja wadda take fitowa daga kitchen yace ‘Ba ki shirya ba ke, ko sai an jima za ki tafi?’

Da murmushi tace ‘No, yau ba mu da lecture ba zan je ba. ‘Ok.’ Ta yi musu a dawo lafiya suka wuce. Bayan ya dawo haka ya yi ta tambayarta idan ta san za ta je makaranta ta gaya masa ya jira ta ya tafi da ita ya kai ta; sai da ta tabbatar masa ba za ta fita ba sannan ya fita ya tafi office.

Washegari ranar Juma’a ce; kamar yanda ya saba yana kwance a ɗaki bayan ya dawo daga masallaci yana rage bacci kafin a gama shirya yara ya kai su makaranta. Wayar Khadeeja ce take ta faman ringing a ɗakin tana katse masa bacci, baya son tashi don haka ya yi tsaki ya gyara kwanciyarsa.

Sai dai wayar da ta tsinke sai a sake bugowa; to waye ma yake kiranta da wannan safiyar bayan ko wayewa garin bai gama yi ba? Wayar tana fara ringing a karo na uku ya mirgina ya miƙa hannu ya ɗauko wayar daga kan durowar gefen gado. Ya kallin screen ɗin inda sunan wanda yake kiran ya bayyana “Baffa” ya karanta a fili yana wattsakewa.

To me yasa Baffan Khadeeja yake kiranta yanzu? Allah ya sa dai ba wani abun ne ya faru a gidan nasu ba. Nan da nan ya sauko daga kan gadon ɗauke da wayar ya nufo kitchen inda Khadeejan take faman zubawa yara abinci suna tsaye kowa yana karɓar nasa. Ya miƙa mata wayar wadda take ringing yana cewa ‘Ki amsa Baffa ne yake ta kiranki kin baro wayar a ɗaki.’

Tana karɓa ta amsa ta kara a kunnenta; yana tsaye yana kallonta yana tsoron kada a ce wani abu ne ya faru a gidan nasu. Bayan sun gama gaisawa da Baffan tace ‘A a Baffa, ina nan ne muna shirin makaranta ni da yara.’

Daga ɗaya ɓangaren Baffa yace ‘Ƙarfe nawa ne lecture ɗin naki Dije? ’Tace ‘Karfe takwas. Idan nazo 7:30am ai kin gama shiryawa ko? ‘Eh Baffa. ‘To ki shirya idan na ƙaraso zan yi miki waya ki fito na kaiki makarantar sai na wuce office. ’Cike da girmamawa kamar wadda za ta tsuguna a wajen tace ‘To Baffa na gode, Allah ya ƙara lafiya.’

Ta ajiye wayar bayan ya amsa, kafin ta yi wani abu Mustapha yace ‘Lafiya ƙalau dai naga Baffa yana kiranki da safe. Ta miƙawa Habib shayinsa da ta haɗa masa tana cewa ‘Uhm zai zo ya kai ni school ne shi ne yake tambayata ƙarfe nawa zai zo. Habib ya karɓi shayinsa ya fice yayin da Mustaphan ya matsa kusa da ita cike da kulawa da damuwa yana cewa ‘Makaranta kuma?

Ba nace zan dinga kai ki ba? Yanzu ke saboda rashin tausayi sai ki taso shi da wannan safiyar kawai don ya kai ki makaranta? Ke abu ba zai wuce a wajenki ba? Ta juya cikin halin ko in kula tana cewa ‘Shi ne ya karɓi timetable ɗina yace zai dinga zuwa yana kai ni ko? Ai a gabanka ya faɗa.’

‘Kuma a gabanki na ba shi haƙuri ai; wannan wanne kalar abin kunya ne ina nan kuma ina da abin hawa amma za ki taso Baffa ya zo ya kai ki makarnta don Allah? Dariyace take son ta ƙwace mata saboda yanda duk ya muzanta kamar ma Baffa yana tsaye yana kallonsa. Kafin ta ba shi amsa ya ɗauki wayar tata ya dannawa Baffa kira ya miƙa mata waya yana cewa ‘ki gaya masa zan kai ki ba sai kin yi min wulaƙanci ba.’

Kafin ta yi magana har Baffan ya ɗauka, don haka ta kara a kunnenta tace ‘Um Baffa ka bari ma Abban Afaf zai kai ni makarantar. ’Yace ‘Ah, kin tabbata dai ko? ‘Eh Baffa, ga su ma tare za mu fita gaba ɗaya shiryawa muke.’

Ya zare wayar daga hannunta kafin ta sake magana ya kara a kunnensa cike da girmamawa yace ‘Baffa za mu tafi tare in sha Allahu, zan dinga kai ta. A yi haƙuri. Yace ‘To, to babu laifi. Allah ya yi muku albarka. Ya ajiye wayar yana harararta yana cewa ‘Yanzu zan je na shirya, ke ma ki shirya sai mu fita gaba ɗaya ko kuma idan na kai su sai na dawo kafin nan kin ƙarasa sai mu wuce.’

Tace ‘Um, ka ga babu komai fa, za ku iya tafiya ma sai na wuce kawai ba sai na gayawa Baffan ba.’ Ya kakkafe ta da ido yana harararta har sai da ta sunkuyar da nata idanun, ya juya yana cewa ‘Ki shirya nace. ’Ya fice ya bar ta a nan. Ta yi dariya ta cigaba da aikinta.

Ba ta da zaɓi haka ta shirya suka fita tare, kuma daga wannan lokacin ya zama ko da wanne lokaci zata makaranta haka yake barin abinda yake yi ya zo ya kai ta. Sai dai idan ta gama abinda take yi kawai sai ta hawo motar haya ta dawo.

Karanta  Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Biyar

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Biyar
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.