khairatu.shehu
‘Hey Babe.’ Ta faɗa tana wani rangwaɗa kai tare da juya ƙwayar idonta kamar dai ga Babe ɗin a gabanta tana kallonsa. ‘Mai kyau, ya kike?’ Ya faɗa daga ɗaya ɓangaren. ‘Lafiya. Yanzu nake dawowa daga school gashi nan na kusa shiga gida.’
‘Oh, ni ma yanzu na mayar da su Afaf gida wajen Hajiya. Mun je shopping ne and I bought a few things for you nake so na kawo miki later. Is that ok? ‘Yes Babe, kai ma ka san ina nan idan dai kai ne kake son ganina. Ya yarana? Hope suna lafiya?’
‘Alhamdulillah ga su nan. I just can’t wait to have you so we can all live in one place na huta da visiting yarana.’ ‘Aww! Kada ka damu, very soon in sha Allah. We will talk more about it idan ka zo in sha Allah don yanzu zan shiga gida ka san Mommy ta hanani waya a kan hanya.’
Ya yi ‘yar dariya yace ‘Kuma fa haka ne, to sai mun haɗu.’ Suka yi sallama suka ajiye wayar. Da sallama ta shiga gidan tana ta fara’a kamar wadda aka yi wa wani babban albishir. Babu kowa a parlor ɗin sai Mommy tana shirin tashi ta shiga sallar Magriba. Bayan ta amsa sallamarta tace ‘Yau kuma haka kike tafe kina tallan macleans?’
‘Kai Mommy! I’m just Happy.’ Ta faɗa tana dariya. Ta wuce ɗakinsu yayin da Mommy ta shige nata ɗakin. Tana sane da yanda take tafiya tana murmushi ɗin kuma tana jin daɗin hakan. Idan dai a kan Mustapha ne fiye da haka ma za ta yi. Muryarsa kawai take buƙatar ji ta shiga farin cikin da ba ya misaltuwa. Wata bakwai da suka wuce suka haɗu, amma saboda yanda ya iya soyayya da tarairaya ya shiga zuciyarta kamar wanda suka yi shekaru a tare.
Da ya sami yanda yake so ma da tuni an ɗaura musu aure don shi a shirye ya zo, ita ce take ɗan dakatar da shi don tana so ta gama level 1 kafin a yi mata auren. Sai dai a daren jiya Baffanta ya sanar da ita cewa ta gaya masa ya turo maganar aurensu. Ta jefa Jakarta a kan gadonsu wadda ta faɗa kan ƙanwarta Nabila. Nabila ta make jakar ta ja tsaki tace ‘A a, must you be stubborn?’
Tayi dariya tana cewa ‘A tashi dai a yi sallah.’ Ta matsa gaban wardrobe ta fara kokarin cire kayan jikinta.
Kamar yanda ya yi mata alƙawari ana idar da sallar isha’i ya iso gidan nasu. A tsakar gida suka zauna inda ta saka musu kujerun roba a rumfar mota, ta ajiye ƙaramin tebur a tsakanin kujerun wanda ta ɗora ruwa da lemon roba masu sanyi a kai.
Bayan sun gaisa suka ɗan taɓa hira, hirar da a mafi yawancin lokuta ita ce take yi shi bin ta kawai yake da kallo yana murmushi yana ba ta gajerun amsoshi. Mustapha kenan; haka yake kamar wani basarake, komai nasa a hankali sannan kuma bisa tsari. Wannan ya sa yake ƙara burge ta.
Ta ɗauki ruwan robar da ta ajiye ta buɗe ta miƙa masa tana cewa ‘Ko ruwan ba ka sha ba Yallabai.’ Ya yi murmushi yayin da ya karɓi ruwan yana cewa ‘Kuma kin san ƙishirwan nake ji ba, don tun daga gida muke waya da su Afaf har na zo nan suna ta surutu duk sun gajiyar da ni.’
‘Kai haba, surutun na su nawa yake?’ Ta faɗa tana dariya. Suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin da ya tashi tafiya wajen ƙarfe tara. Sai da ta raka shi bakin motarsa kafin ta yi masa sallama sannan tace ‘Baffana yace na gaya maka mutanen gidanku za su iya zuwa maganar aurenmu ranar Asabar mai zuwa.’
Take fara’ar sa ta ƙara faɗi, ya dube ta kamar ya rungume ta yana ta murmushin da ita ma yake saka ta murmushi. Yace ‘Allah Khadeeja! Kai amma na ji daɗi wallahi, in sha Allah ranar Asabar ɗin kuwa za su zo da kuɗin aure da sadaki gaba ɗaya.’ Ta yi dariya ‘Kai garaje, saurin me kake?’
‘To ai na kula ba kya tausayina, so kike ki yi ta ja min rai kina bari na sauro yana cinye ni saboda zance.’ ya faɗa da murya kamar ta mai shagwaɓa. Ta yi dariya ‘To kwanan nan za ka huta in sha Allah.’ Suka yi sallama cike da farin ciki bayan ta sanar da shi gidan kakanta inda nan ne za su je maganar auren nata.
Cikin walwala yake tuƙin lokaci zuwa lokaci yana yi wa kansa murmushin jin daɗi saboda wannan labarin da Khadeeja ta sanar da shi. Watansu bakwai kacal da haɗuwa amma ya nutsu da hankalin yarinyar kuma ya yaba da tarbiyyar gidansu, ya tabbatar za ta kular masa da su Afaf kuma za ta tsaya a kan tarbiyyarsu ba tare da wata mugunta ba.
Wata takwas kenan da rasuwar matarsa Asma’u, wadda ita ce ta haifa masa yara huɗu; Afaf mai shekaru goma sha ɗaya, Habib mai shekaru tara, Nasreen mai shekaru shida sai Shukra mai shekaru uku. Ba wani rashin lafiya ta yi ba, haka kawai da daddare tace kanta yana ciwo don haka a gaba ya saka ta sai da ta sha ƙwayar Panadol sannan ta kwanta; sai dai da yake kwananta sun ƙare haka aka wayi gari sai gawarta. Ya yi matuƙar baƙin cikin rasuwar Ma’u kuma ya ji tausayin kansa da yaransa, gaba ɗaya rayuwarsa ta tsaya saboda rashin Ma’u.
Tunda aka kwana uku da rasuwar Asma’u mahaifiyarta ta tattara yaran ta tafi da su gida aka cigaba da kula da su. Can yake zuwa kullum ya ɗauke su ya kai su makaranta idan an tashi ya mayar da su. Ana kula da su sosai kuma suma suna jin daɗin zaman gidan sai dai shi ya fi so ya rayu tare da yaransa.
Da farko ya so ya kwashe su ya kai su gidan yayarsa; tunda mahaifiyarsa ta tsufa da yawa ba za su sami kulawa ba a wajenta. Amma sai mahaifiyar Ma’u tace ba za ta bayar da yaran ba. Sun so su sami matsala domin da kwashe su ya yi ba tare da izininta ba ya mayar da su gidan Yayar tasa, sai da manya suka shiga cikin maganar aka yi yarjejeniya a kan idan ya yi aure zai je ya ɗebi yaransa. Don haka ba ƙaramin daɗi ya ji ba da Khadija tace an ba shi izini ya turo.
Ya riga ya sanarwa Khadija idan ta tare zai dawo da yaransa kuma tayi na’am da hakan. Shi yasa ma wasu lokutan yake kwaso su ya kai mata su har suka saba sosai. Ya yi mata bayanin irin ƙaunar da yake musu da kuma yanda yake so ta dinga kula da su kamar ita ta haife su; kuma ta yi na’am da hakan. Don ko a yanzun ma tana ƙoƙari wajen hidimarsu da jansu a jiki ga kyaututtuka, gashi wata ran da kanta take masa waya ya kawo mata su.
Duk da ya riga ya je gidan mahaifinsa da safe amma a daren ma haka ya koma cike da farin ciki ya sanar da mahaifinsa cewa iyayen Khadija sun ba shi damar ya turo. Mahaifinsa yana zaune a kan kafet a dakinsa ya dube shi bayan ya gama sanar da shi inda za a kai kuɗin yace ‘Shikenan rigimar yara ta ƙare ko, ga amarya ga yaranka sai ka sami natsuwa.’
Ya yi dariya ya sunkuyar da kai. Daga baya ya yi musu sallama ya wuce gidansa cike da farin ciki.
Karanta Yadda Ake Lefe A Auren Hausawa
Edita@rumasau-kallamu