Mijin Marigayiya Babi Na Bakwai

0
24

khairatu.shehu

Haka Khadeeja ta kwana a asibitin ƙarƙashin kulawar Anti Iyami. Tun dare likita ya gama da ita aka ba ta duk wasu magungunanta, ya sanar da Anti Iyami za a iya tafiya da ita gida. Don haka gari yana wayewa ƙarfe takwas na safe Anti Iyami ta gama aiki za ta tafi gida ta shiga ɗakin da Khadeejan take.

Bayan sun gaisa tace ‘Yanzu akwai inda yake miki ciwo Khadeeja.’ Ta jijjiga kai tace ‘A a, ko ina ya warware, yanzu ma na gama breakfast ɗin da kika aiko min da shi.’ ‘Ok, so ki kirawo Mustapha kice masa zan wuce da ke gida sai mu tafi na kai ki gidan Mommy ɗin.’

Ba ta son ta yi magana da shi sai ta je gidansu don haka cikin sauri tace ‘Ai yanzu na kirawo shi bai ɗauka ba, ina jin yana bacci ko baya kusa da wayar amma na san da ya gani zai kira. Mu wuce kawai tunda tun jiya na gaya masa za mu wuce gidan.’

‘Ohk, to tashi mu tattara kayan mu wuce. Ni ma tun dare na kirawo Mommyn naki na sanar da ita, da safe ma mun yi waya. Na dai ce mata kada ta kirawo ki ne don duk lokacin da na shigo sai na same ki kina bacci, shi yasa nace ta bari idan kin tashi zan kirawo ta ku yi magana.

But ba komai idan mun je za ta ganki tunda mun shirya.’ Nan suka haɗa kayan Khadeejan waɗanda daman ba yawa ne da su ba suka shiga motar Anti Iyami suka kama hanya.

Khadeeja tana zama a mota ta lalubo wayarta ta saka ta a silent ta jefa a jaka don ba ta so Mustapha ya kirawo ta a gaban Anti Iyami domin ba ta san me zai ce ba idan ya ji ta wuce gidan Mommy. Duk inda suka je checkpoint aka tsayar da su da an ga uniform ɗin Anti Iyami kuma ta nuna ID card sai a bar su su wuce, haka har suka isa gidan Mommy.

Tun suna asibitin Anti Iyami ta sanar da Mommy za su taho don haka kafin su isa an ɗorawa Khadeeja ruwan wanka, suna shiga ta wuce ɗakin Mommy inda Azumi mai aikinsu ta sirka mata ruwan a banɗaki. Ba tare da ɓata lokaci ba ta faɗa wanka.

A parlor Mommy suka zauna da Anty Iyami; bayan sun gaisa sun jajantawa juna Mommy tace ‘Ina Mustaphan? Ai na zata tare kuke da shi.’ Ta gyara zama tace ‘Bai zo ba ma yau da safen duk da dai tace ta gaya masa nan za mu huto, amma don Allah ƙawata a duba yarinyar nan.’

Cike da kulawa Mommy tace ‘In sha Allahu kuwa, ke ma kin san ba zan barta haka ba ko akwai wata matsala ne da ta samu ko rashin lafiya.’Ta jijjiga kai ‘Babu fa, kawai dai tace min tana son dawowa gida. Duk dai wasu tambayoyi da zan yi mata na yi ta nuna min babu komai, to amma kin ga akwai yaransa guda huɗu.

Wataƙila hidimar gida da ta yaran ce take mata yawa ga ciki shi yasa ta sume masa. Baccin da ta dinga yi kawai ya tabbatar min da cewa ba ta samun isasshen bacci wallahi, don shi yasa ma na ƙi tashinta ku yi waya. Gaskiya ku bincika, ya nema mata mai aiki ko ya san yanda zai yi da yaransa.’

‘Umm! To kin ga dai idan ma da wata matsala ba ta faɗa ba, koda yake kwanaki tace mai aikinsu ba ta nan a bata aron Nabila amma Baffansu ya ƙi amincewa. Wataƙila saboda babu mai aikin ne abun ya yi mata yawa ga laulayi.’

‘Gaskiya dai ku duba, ko da za ta koma ku bar ta ta huta ta sami natsuwa sannan kuma a ɗaukar mata mai aiki.’ Suka ƙarasa hirarrakinsu daga baya suka yi sallama Anti Iyami ta kama hanya.

Bayan ta fito daga ta tarar da farfesun kaza mai rai da lafiya wanda Mommy ta dafa mata sannan ga shayi mai kauri Azumi ta haɗa mata da burodi a gefe, cikin sauri ta gyara jikinta ta sa kaya sannan ta shimfiɗa dadduma a gaban gado ta miƙe ƙafafu ta zauna ta fara cin abinci.

A nan Mommy ta shigo ta same ta ita ma ta zauna, sai da ta gama cin abinci sanna ta fara yi mata tambayoyi. Ba ta ɓoyewa Mommy komai ba ta sanar da ita halin da ake ciki, ta tabbatar mata cewa idan dai da mai aiki musamman babba wadda ba za ta sa ta surutu ba.

Sai dai ta kasa gaya wa Mommy cewa gaba ɗaya ma ko da da mai aikin ita ji take kamar ma Mustaphan baya ƙaunarta, gani take kamar yanda take zama kullum cikin hidima ya sa ba ta gane kulawarsa a gareta. Don haka ta bar wannan a ranta tana fatan idan an sami mai aiki ya zama suna samun lokaci a tare to za ta fuskanceshi.

Muryar Mommy ce ta katse ta tana cewa ‘To yanzu yaushe zai zo ya ɗaukeki?’ Ta kalle ta suka haɗa ido ta sunkuyar da kai sanna cikin muryar shagwaɓa tace ‘Mommy kin ga yanzu mai aikin ba ta dawo ba, kuma na gaya miki shi ba zai taya ni komai ba kuma ba zai bari yaransa su tayani ba.

Kawai ki bar ni sai bayan sallah ko kuma duk lokacin da mai aikin ta dawo ko aka sami wata.’ Mommy ta jijjiga kai tace ‘Na fahimce ki, amma me kike so na gayawa Baffanku? Shi kuma Mustaphan wane dalili za a ba shi na riƙe ki a nan ɗin. Tunda dai ciki ya fice an riga an wake; kuma ga ki nan kowa yana ganinki ras.’

Ta karyar da kai kamar abin tausayi tace ‘Umma ni dai don Allah ki san yanda za ki yi a bar ni na huta. To bari mu gani. Idan kuma akwai wani abun da Mustaphan yake yi miki wanda kike so a yi masa magan to ki gaya min.’

‘Babu komai tunda ma bai hana a ɗauki mai aikin ba, in sha Allahu da ta dawo ko kika samo min wata zan koma.’ Ta gyara zama ta kafa tagumi ‘Hmm! bari mu ga yanda za mu yi da Baffan naki tukunna.’

Sai da suka gama wannan hirar sanna ta tuna tunda suka shigo ba ta ma nemi wayarta ba, ta san yanzu haka Mustapha yana ta faman kiranta. Cikin sauri ta miƙe ta ɗauko wayarta daga jakarta, ai kuwa tana dubawa taga missed calls ɗinsa har guda goma sha ɗaya.

Tana gani danna masa kira, ko ringing ba ta yi ba ya ɗauka ‘Hello, wai ina kika shiga ne naje asibiti ina ta nemanki? Na rasa mai ba ni tsayayyiyar amsa, sai ce min kawai ake kin tafi da Anti Iyami, na za ta gida za ta kawo ki na dawo gidan kuma baku zo ba. Kin sa ina neman haukacewa na rasa wanda zan kira don ban san me zan ce musu ba.’

‘Subhanallah! Ka yi hakuri Babe, wallahi ka ganni nan ai gidan Mommy ta kawo ni. Na kirawo ka ba ta shiga ba kuma shi ne na jefe wayar a jaka na manta sai yanzu da na fito daga wanka na tuna. Amma shi ne ba ki gaya min ba? Kin san wulaƙancin da aka dinga yi min a checkpoint kuwa?’

Ta tausasa murya ‘Sorry Babe, wallahi laifi na ne don tun a asibitin Anti Iyami tace na kirawo ka sai wayar ta ƙi shiga.’ Ya ɗan saki numfashi ‘To me yasa ba ku taho nan ba ko kuma a jirani na zo? Me ya sa za a kai ki gidan Mommy?’

Ta ɗan yi shiru, shi ma bai yi magana ba yana sauraronta; ta murguɗe baki kamar yana kallonta tace ‘Ai ka san dai idan an haihu ana zuwa wanka gida, may be shi yasa da suka yi waya Mommy tace a kawo ni gida.’

‘To kuma shi ne aka rasa wanda zai gaya min.’ Cikin ƙosawa tace ‘To ba ga shi na gaya maka ba, kuma ai nace maka mantawa na yi.’ Ya ɗan ja numfashi ‘Uhm! To ya jikin naki? Shike nan an gama yi miki alluran?’

‘Na sami sauƙi, ga ragowar magungunana na taho da su daman yawanci na kwana bakwai ne, amma na sami sauƙi. To idan an buɗe gari sai na zo na ɗauke ki, ina ga ranar Saturday za su ɗan buɗe mu, nan da kwana uku kenan.’

‘Uhm, to ka dai zo amma gaskiya sai bayan sallah zan dawo kafin nan na dan huta na gama arba’in tunda ka san shi ma ɓarin ai sai an yi wanka. Ɓarin, gaskiya ban taba ji ba. Ma’u ma fa su biyu tana yin ɓarin amma na biyun babu wanda ma muka gaya wa a nan ta yi zamanta ta cigaba da hidimarta.

Hutawa kawai ta yi na kwana biyu. Idan ka zo dai ma yi maganar.’ Ta tamabye shi yaran ya ba ta su suka gaisa sannan suka yi sallama suka ajiye waya.

Tunda yake bai taɓa ganin son zuciya irin wannan ba, ya za a yi a ɗauke masa mata kuma a ce sai bayan sallah za ta dawo? Kawai saboda ta yi ɓari. Asma’u ma ai ta yi ɓari har sau biyu ma; na farkon shi ne bayan haihuwar Habib, bayan an yi mata wankin ciki a ranar suka dawo gida.

Ko maganar ta je gidansu ma ba a yi ba kawai dai an kawo mata ƙanwarta tunda dama tana da mai aiki. Na biyun kuwa ma bayan haihuwar Nasreen babu wanda suka gaya wa, suna zuwa asibiti aka ce musu ya fice gaba ɗaya ba sai an yi wankin ciki ba aka ba su magunguna suka dawo gida.

Kawai dai ya san ba za ta koma ɗakinsa ba sai bayan kwana arba’in, kuma ba shi da matsala da wannan. Amma su iyayen Khadeeja saboda son zuciya sai akwai su ɗauke ‘yarsu? Kuma ko gaya masa ba za ayi ba.

Haka ya gaji da saƙe-saƙensa ya sake daga wayar ya kirawo Alhaji ya gaya masa, don bai gaya musu cewar a asibiti ma ta kwana ba yana so ya je da safen ya gani tukunna. Shi ma Abban ya nuna rashin jin daɗinsa da aka tafi da ita, musamman da ya gaya masa ba su ma tambaye shi ba suka tafi da ita.

Bayan sun gama waya da Alhaji ya kirawo Ummansu ita ma ya sanar da ita. Suma su Afaf sai da ya yi musu bayani don tunda ya dawo ba su ganshi tare da Khadeeja ba suke ta faman yi masa tambayoyi. Babu yanda za a yi ya iya ɓarin Khadeeja ta zauna a gidansu, ya suke so ya yi?

Ga lockdown an hana mutane fita sannan kuma su ɗauke masa mata. Kwana ukun nan ma da zai yi da yaran bai san ta ina zai fara ba don yana tuna yanda a kwana ɗayan nan suka gama firgita shi; ga gari a kulle balle ya kai su gidan Umma. Gaskiya da an buɗe gari ranar Asabar zai je ya ɗauko ta tunda dai ko shi ya tambaye ta jiki ta ce da sauƙi.

Sai can da yamma dabara ta faɗo masa; ya ɗauki waya ya kirawo Baffan Khadija, bayan sun gaisa ya jajanta masa jikin Khadeejan sannan ya sanar da shi cewa ranar Asabar idan aka buɗe gari zai zo ya ɗauki Khadeejan.

Ba tare da matsala ba kuma Baffan ya amsa masa da hakan ya yi, don haka cikin walwala ya ƙarasa wuninsa. Bayan Ummi ta gama haɗa musu kayan shan ruwa shi da yara ta wuce ta tafi gidansu ta bar su.

Tun bayan dawowar Khadeeja gidan sau ɗaya Baffanta ya shiga ɗakin Mommy ya same ta ya yi mata sannu. Yana zaune a parlor bayan ya dawo daga sallar tarawih Mommy ta shiga ta same shi, ta zauna a gefensa suna kallon labarai a tashar Aljazeera tare. Bayan sun ɗan taɓa hira yace ‘Ɗazu Mustapha ya kirawo ni yana duba Khadeeja, ya ma ce min idan an buɗe gari ranar Asabar zai zo su tafi.’

Ta ɗan gyara zama ‘Ranar Asabar fa kwana uku kenan, haba ai sai ta kwana arba’in. A ah to ai ni na za ta sun gama magana da ita ne a kan hakan.’ Ta jijjiga kai tace ‘Gaskiya dai ba su yi wata magana ba don da kanta tace min tana so ta yi arba’in ɗin. Suna zuwa da na sa ruwan zafi nayi mata wanka ta ji dadin jikinta da kanta tace a bar ta ta yi arba’in ɗin.

Haba, kuma haka za a mayar da ita haihuwar fari babu wani gyara? Sai kace ‘yar tsana.’ ‘To ai na ga ɓari ne ba haihuwa ba.’ ‘To ai Baffan Nabila ɓari ya fi haihuwa wahala sosai ma, sannan kuma na fari ne haka za a ba shi matar ya ma kasa ɗaga mata ƙafa a kwana arba’in ɗin.’

‘To na ga dai ai matarsa ce ko? Ina laifi, kuma ma ai shi ma ba zai ce bai san waɗannan hukunce-hukuncen ba tunda ga yara nan har huɗu an haifa masa.’ Ta sake gyara zama ‘Ku dai yi haƙuri Baffa a bar ta ta yi kwana arba’in ko a ƙalla talatin, kafin nan ta ji daidai a jikinta sai ta koma.’

Ya ɗaga wayarsa ya cigaba da dubawa yana cewa ‘To ai shikenan idan ya zo sai ku yi masa bayani, ni bani da matsala da hakan.’ ‘Yauwa, ai lalacewar zamanin ba ta kai an daina wanka da gyara a haihuwar fari ba. Amma dai idan ya zo sai ka yi masa bayanin idan kana nan tunda ka ga kai ya nema, gara ku cigaba da magana man to man.’

Ya yi dariya yace ‘To babu laifi.’ Ya san halin matarsa da kishi, yanzu haka haushi ta ji shi Mustaphan bai kirawo ta ya duba Khadeejan ba ko a ƙalla ya gaya mata zai tafi da Khadeeja ranar Asabar tunda ya san ita ce za ta shirya Khadeejan amman ya kirawo Baffa. Jimawa kaɗan kuma ta fice ta ba shi waje.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Shida

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Shida
Labarin na GabaDalilan Da Ke Sa Zubar Ruwan Nono Alhalin Babu Ciki Ko Goyo
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.