Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Ɗaya

0
33

Cike da ɗoki ya shiga ɗakin amaryarsa riƙe da ledarsa ta kayan ciye-ciye; tana zaune a can a ƙuryar gado. Ko da a ce ta amsa sallamarsa to shi dai bai ji ba, amma ya riga ya san yanda amare suke. Har inda take ya ƙarasa ya same ta bayan ya ajiye ledar hannunsa a kan mudubi.

Ga mamakinsa bayan ya ɗaga fuskarta kuka take yi sosai da hawaye kamar wadda aka yi wa auren dole, don haka nan take ya shiga aikin lallashi. Sai da suka kusan minti talatin sanna ya samu ta goge hawayen ta saurare shi. ‘Wai me ya faru ne kike ta faman kuka haka sai kace wadda aka yi wa auren dole?’

Ta ɓalla masa harara ta ɗauke kai sannan tace ‘Ni da ka kawo na zaɓi ɗakin da nake so a sama kusa da naka ɗakin shi ne za a kawo ni a ajiye ni a nan, ka sa ina nema na yi musu da masu kawo ni. Ya yi murmushin yaƙe ya sake kamo hannunta wanda ta riga ta fizge yana cewa ‘Haba ke kuwa? Ai na zata da suka zo kafi sun gaya miki.’

Ta zumɓura baki ‘Ni babu wanda ya gaya min, sai da aka kawo ni kawai na ga an ajiye ni a ƙofar gida kamar wata wadda ba a so zuwanta ba. Nan ya shiga faman ba ta haƙuri da bayani tana faman fizgewa har dai ya samu ta sauko. Ta kalle shi tace ‘Amma gaskiya ni fa ba zan zauna a nan ba, matarka da yaranka da kai kuna sama.

Kenan fa duk ranar da ba kwana na ba ni kaɗai ce a ƙasa bakin ƙofa. Gaskiya wannan tsarin bai yi min ba, ko dai a ba ni sama ko kuma gaskiya ka nema min wani gidan. Wannan ai duk wanda ma ya zo ya san matsayina. Ya ƙara matsawa ya janyo ta jikinsa ‘Kin ga, kada wannan ya dame ki. Ko da ban kama wani gidan ba za ki iya komawa saman in ya so ko ni sai na dawo ƙasan ku kuma gaba ɗaya ku yi zamanku a saman.’

‘Ni dai ba haka nace ba, amma gaskiya ka cika min alƙawari don ba zan yarda wata tana sama ni ina ƙasa ba. Haka ya yi ta lallaɓa ta har ya samu ta amince masa. Ya tattara musu kayansu suka wuce sama ɗakinsa wanda da farko ta so ta ƙi zuwa, sai kuma ta tuna gara ita ma ta hau saman ta ga yanda Khadeejan za ta yi.

Da yake dama Hammad bai saba barinta baccin safe ba yau ɗin ma tun wajen 6am ya tashe su, ba ta buɗe ɗakin ba sai da ta yi wanka shi ma ta shirya shi. Ta riga ta ji motsinsu tun dare don haka ta san a ɗakin Mustaphan suka kwana. Tana fitowa ta taso Hafsa suka shiga kitchen.

Ya siyo burodi kamar yanda ya saba duk dare, don haka nan da nan ta soyawa kowa ƙwai ta haɗa kayan shayi tsaf ta ba wa hafsa ta sauko da shi ƙasa. Kafin ƙarfe takwas ta jera komai da suke buƙata ita da yara na breakfast a parlor ɗin ƙasa. Tana shirin hawowa bene Hafsa ta biyo ta da wayarta ta miƙa mata tana ringing. Tana dubawa ta ga Baffa ne.

Bayan sun gaisa ya ƙara yi mata nasiha sanna yace mata nan da awa ɗaya Nabeela ta shirya Ahmad zai zo ya ɗauke ta.Ba ta ji wata damuwa ba saboda dama ta san halin Baffa, ba tare da ɓata lokaci ba ta taso Nabila ta sanar da ita. Nan da nan ta haɗa kayanta don ko wanka cewa ta yi idan ta je gida ta yi abunta, haka ma breakfast cewa ta yi idan ta je gida ta ci kosai don tabbatar yau Lahadi ƙosai Mommy ta yi.

Wajen 9am suna zaune a dining table ita da yara in banda Afaf wadda ba ta tashi ba ko kuma ba ta fito daga ɗakinsu ba. Breakfast suke yi suna ta hirarrakinsu Shukra sai labari take ba su suna dariya gaba ɗaya. Da sallama ya sauko daga benen ya ƙarasa gaban table ɗin yana cewa ‘Ina can ina nemanki a ɗakinki ashe kina nan ke da yara kuna ta jin daɗinku.’

Ta yi murmushi ta kawar da kai. Ita da yaran duka suka gaishe shi, bayan ya amsa ya dube ta yace ‘Idan kun gama cin abincin ki zo ki ba ni nawa breakfast ɗin ni da ƙanwarki. Ta yi murmushin yaƙe tace ‘Da yake mu ma bread da shayi muka sha ba wani abu ba,  amma dama na ga bread ɗin da yawa ka siyo ga shi can mun bar muku guda ɗaya ka ɗauka ka haye muku da shi.

Ko a nan za ku yi breakfast ɗin? Ya kalle ta da ɗan mamaki ya cije leɓe don ba ya son ya ja zancen a gaban yara yace ‘Um, idan kin gama dai kya hawo da shi.’ ‘Ok.’ Ta amsa cigaba da cin abincinta. Sai da suka gama cin abincinsu tsaf sannan ta ɗauki bread ɗin ta haye sama, tana shiga babu kowa a parlor ɗin don haka ta ƙarasa kan dining table ta ajiye bread ɗin ta shige ɗakinta.

Kamar tare suka shiga ɗakin don ko zama ba ta yi ba ya shigo ya tura ƙofar, yana daga tsaye a jikin kofar yace ‘Wai ya na ganki a nan ina breakfast ɗin namu ni da ƙanwarki? Ta ƙarasa ta zauna a kan gadon ta jingine ta miƙe ƙafarta tana cewa ‘Oh, ga bread ɗin can na ajiye muku ai ko akwai wani abun ne?’

Da mamaki yace ‘Ai na zata za ki ɗan dafa wani abu ko don saboda ganin ga baƙuwa kin kwana da ita a gidan. Ba ta san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, haka kawai maganar tashi sai ta ba ta dariya musamman da ta kalle shi kuma yana cewa wai “kin kwana da baƙuwa”

Ta ɗan gintse tana ƙoƙarin saita fuskarta sanna tace ‘Na kawana da baƙuwa ko ka kwana da ita? Tea and bread muka ci fa kuma ga shi can na ajiye mata ita baƙuwar tawa, ina ga kamar ai dafa ruwan zafi bai kamata ya zama matsala ba ga wanda aka ba wa burodi ko? Ya ɓata rai saboda kwata-kwata bai zata haka ba; a iya saninsa sai sun kwana bakwai da amarya Khadeeja tana yi musu girki sannan sai a raba kwana amma ga shi tana nema ta kawo masa raini.

‘Ba fa na son raini Khadeeja, duk wanda ya ƙara aure matarsa ta gidan ita ce take yi wa amarya girki har sai ta kwana bakwai amma zan zo ina miki magana kina min wani zancen banza. Ai ko bazawara na aura kin san ya kamata ki yi mata abinci na kwana uku balle budurwa. Ta kalle shi ta kawar da kai; babu yanda za a yi ta yi wa Naja girki sai dai duk abinda zai yi ya yi; ta tsani Naja ta tsani jin sunanta.

Wataƙila da a ce ya biyo ta hanyar da ta dace wajen sanar da ita zai ƙara aure da wadda zai aura da haushin da take ji bai kai haka ba, amma gaskiya babu abinda zai sa ta yi wa wata Naja girki. Ya auro matarsa ya gama more kwanan amarci sanna ita kuma bayan bacci da ba ta yi cikin nutsuwa ba kuma ita yake so ta tashi da sassafe ta haɗa musu breakfast na warware gajiya, bata taɓa ganin rainin hankali irin wannan ba.

Ta ɓata rai sannan tace ‘Ba a biya mana wannan hadisin ba a islamiyya. Mamaki ya kama shi ya buɗe baki amma ya rasa abinda zai gaya mata. Yana kallo ta zame ta gyara kwanciyarta ta juya masa baya. Bai shirya da wannan mahaukacin taurin kan nata ba wanda idan ta fara shi sai duk garin kowa ya ji.

Ya ɗan tausa muryarsa yace Bana son wasa Khadeeja, don Allah ki tashi ki samarwa yarinyar nan abinci. Next week ai za ku raba girkin kowa ta dinga yin nata, amma for now ki tashi ki ba mu breakfast. Ta sake gyara kwanciya ba tare da tace masa komai ba. Ya kalli kasa yana jijjiga kai don ya san ta gama magana; takaici ya kama shi.

To yanzu ya za a yi tana amarya ya ba ta bread ruwan zafin ma a ce sai ta dafa. Haka ya fice daga ɗakin yana wasi-wasi. Yana ficewa ta juyo ta harari ƙofar kamar yana wajen ta ja dogon tsaki tace ‘Ɗan rainin hankali!’

Yana shiga ya tarar da ita ta fito daga wanka tana shiryawa. Tun kafin ya gama shiga ɗakin tace ‘Allah ya sa dai an gama abinci don wallahi yunwa nake ji kamar an min sata a ciki. ‘Akwai dai bread, sai dai idan kin fito ki dafa ruwan zafi da ƙwai haka sai mu karya.’

Da mamaki ta kalle shi tana cewa ‘Ruwan zafin ma sai na dafa? Yau ne fa kwanana na farko a gidan, haba! Kitchen ɗin ma ban san inda yake ba. Cikin damuwa yace ‘To ko order za a yiwo? ‘Ni ban gane ba, wai ita matar gidan ba ta girki ne? Ya ƙarasa kusa da ita yana ƙoƙarin kama dogon gashinta da take tajewa yana cewa ‘Ki bar wannan maganar, ki zo mu je na nuna miki kitchen ɗinki sai ki samar mana ruwan zafi mu karya.

Idan kuma akwai inda za ki iya yiwo mana order a kawo nan da awa ɗaya haka to sai na tura kuɗin. Ta jijjiga kai ‘Gaskiya babu, sai dai ko na rana don wallahi kwana bakwai ɗin nan sai na yi su ba tare da na ɗora tukunya ba. Don ni abinda na sani matar gida ko ‘yar gwal ce idan aka yi amarya ita take girki kafin a zauna a raba.

Haka ya yi ta ba ta haƙuri yana lallaɓa ta, daga ƙarshe ta shirya suka sauko parlor ɗinta ta dafa musu ruwan zafi sanna ya ɗebo ƙwai ta soya musu. Wajen 12pm ya haɗa su a parlor ɗinsa ya yi musu introduction; ita Naja amarya sai muzurai take yi tana wata yanga, ita kuwa khadeeja cike da walwala ta yi mata maraba suka gaisa babu laifi.

Ya sanar da su idan an kwana bakwai za su raba kwana kowacce kwana biyu. Ba ƙaramin mamakin Khadeeja ta yi ba, ko da yake wannan ba baƙon abu ba ne a wajensa. Ta yi masa rashin kunya mintuna kaɗan kuma ta koma kamar ba ita ba. Shi yasa a lokuta da dama yake kasa fassara ta.

Ganin walwalarta ya saka ya sa rai cewa za ta yi abincin rana da su, amma gudun kada a kuma ya sa ya bi ta don ya tabbatar. Sai dai ta tabbatar masa da cewa ta riga ta dafa abincin rana tun da safe kuma nasu ne ita da yara, sauce ne kawai a fridge za ta ɗumama ta haɗa musu salad su ci. Ko amsa bai ba ta ba ya fice ya bar ta a ɗakin, ta bi bayansa da harara tana dariya.

Don haka da rana ta yi sai kawai ya yiwo order ɗin abinci aka kawo musu har gida, haka ya kirawo yaransa gaba ɗaya suka haɗu da Naja suka ci suka ƙoshi. Ita kuma Khadeeja ko damunta abun bai yi ba, ta ci abincinta ta zuba wa Hafsu sannan ta bayar da ragowar. A haka aka ƙarasa wannan amarcin. Kullum Khadeeja za ta dafa abincinta shi kuma zai yiwo order su ci su ƙoshi tare da amarya da yaransa. Babu wanda ya taɓa yiwa Khadeeja tayi ita kuma ba ta taɓa tambayarsa nata kason ba.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWasu Kayan Sana’ar Saƙa
Labarin na GabaMajin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Biyu
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.