Kwanci tashi sai da Khadeeja ta kwashe shekaru biyu tana aiki a gidan rediyon nan a matakin internship sannan aka sami gurbi aka ɗauke ta cikakken aiki, aka saka mata albashinta Naira dubu saba’in.
Ba ƙaramin daɗi ta ji ba da samun wannan ci gaban domin tun da ta fara service ya zama wasu hidimomin nata ita take yi wa kanta kamar kayan shafe-shafe, turare wani lokacin ma har da sutura. Ba ta sani ba ko haka yake yi wa Najan ma tunda ita ma tana da albashi ko kuma ita kaɗai yake yi wa hakan.
Sai dai ba ta da lokacin da za ta bincika ko kuma ta tambaya don haka take rayuwarta yanda ta ga za ta iya. Afaf ta shiga Jami’ar Bayero ta Kano inda take karantar Computer Science yayin da Habib yake SS3 yayin da Nasreen take JSS3 ita kuma Shukra tana primary 5.
Zuwa yanzu duk baƙon da ya yi kwana ɗaya a gidan zai gane cewa gidan ya kasu kashi biyu; Shukra da Halifa waɗanda su ‘yan ɗakin Khadeeja ne da kuma Afaf da Nasreen waɗanda su ‘yan ɗakin Naja ne. Ko a wajen tarbiyya ‘ya’yan ɗakin Khadeeja sun fita daban da ‘yayan ɗakin Naja.
Domin ita Khadeeja tarbiyyar take ba su da kulawa saboda Allah kamar yanda take yi wa Hammad, ita kuma Naja hankalinta yana kan yanda za ta ƙwace gida ta mallake maigidan don haka duk abinda zai saka shi farin ciki shi da yaransa shi take yi; ko da kuwa abun ba daidai ba ne.
Lokuta da dama idan ta je wajen malamanta tana samu ta fara juya Mustapha, sai dai abun bai fiya daɗewa ba. Da zarar ta fara samun yanda take so sai kuma ta sake rasa kan maigidan nata. Ta yi iya bakin ƙoƙarinta ganin ta inda za ta samu ta haɗa shi faɗa da Afaf amma ta gagara; saboda son da yake yi wa Afaf ba kaɗan ba ne. Kuma kusan duk wani abu da zai yi to da Afaf yake shawara.
Haka aka yi a farkon shekarar nan da zai canza mota; da kansa yake faɗa Afaf ce ta zaɓar masa motar bayan ita ba ta ma san zai canza motar ba sai da aka kawo motar gidan. Haka kuma aka yi da zai canza fentin gidan; Afaf ce ta zaɓi wanda take so aka yi, sai daga baya matan gidan suka ji labari.
Lokuta da dama Naja ta so su haɗe kai da Khadeeja ko da su samu su ƙwaci Mustapha daga hannun ‘yayan ne, amma ba ta sami haɗin kai ba. Domin har yanzu zaman nasu dai babu yabo babu fallasa. Shi yasa ma Najan take wa Khadeeja kallon ba ta san me take yi ba saboda yanda ta bari yara suke controlling miji.
Ita kuwa Khadeeja ba ta taɓa ɗaukan alaƙarsa da yaransa a matsayin matsalarta ba, matsalarta ɗaya da shi rashin adalcin da yake nuna mata tsakaninta da Naja. Idan dai abun a nuna kulawa ne da ƙauna to Naja yake nunawa, amma idan abu ne wanda za a yi masa hidima shi da yaransa to sai yace a kai wa Khadeeja.
Duk wani ƙoƙari da za ta yi ta ga ya nuna mata so da ƙauna ta yi amma abun ya ci tura; har ta gaji ta zuba masa ido. Lokuta da dama idan ta yi magana sai dai ya dinga ƙoƙarin nuna mata cewa ya fi sonta kuma ya fi trusting ɗinta shi yasa yake saka ta hidimarsa da ta yaransa. Ta gaji da jin wannan tatsuniyar shi yasa ma ta haƙura ta daina ƙorafi; kawai dai duk abinda za ta yi za ta yi, abinda ba za ta yi ba kuma haka za ta zuba masa ido ya ƙaraci barazanarsa amma ba ta yi.
Haka rayuwarsu ta cigaba.——–
Tun kafin ta yaye Hammad al’adarta ta dawo, don haka kai tsaye ta tafi asibiti ta karɓo ƙwayoyin family planning; ko Mustaphan ma ba ta gayawa ba sai da ta karɓo. Ba wai haihuwar ce bata so ba, kawai dai ba ta da tabbas ɗin zaman auren.
Kullum Mustapha nuna mata yake ita ce jakar gida yayin da Naja ita ce matar gida; don haka duk da yana kula da yaransa sosai kuma yana son su amma ba ta jin za ta iya tara masa wasu yaran balle ma a zo inda za ta yi magana a ce ta yi haƙuri ta zauna don yaranta.
Tunda ta karɓi ƙwayar nan ba ta taɓa yin fashi ba kamar yanda likita ya sanar da ita, ko da kuwa ba ita ce da kwana ba haka take shan ƙwayarta. Amma a ‘yan kwanakin nan gaba ɗaya ta rasa gane kan jikin nata; wasu abubuwa take ji kamar na mai laulayi.
A hanyarta ta dawowa daga office ta tsaya a chemist ta siyo pregnacy test strip, har ta zo gida tana fargaba saboda duk wasu alamu na ciki sun gama bayyana a tare da ita. Sai da ta bari ta yi baccin dare sannan ta ɗauki fitsarinta na sassafe ta gwada da shi; kafin sakamakon ya bayyana a jikin ‘yar takardar gaba ɗaya ta gama ruɗewa.
Ko da ta ga layukan guda biyu sun bayyana ba tare da wata matsala ba sai da zuciyarta ta kusan bugawa, ta muttsike ido ta sake kalla amma har yanzu layukan suna nan guda biyu. Haka ta haƙura ta miƙe ta ɗauro alwala sannan ta fito daga banɗakin ta tayar da sallar asuba.
Bayan ta idar da sallar ta zauna a kan daddumar ta yi shiru; ta daga hannu za ta yi addu’a amma ta rasa ta inda za ta soma. Gaba ɗaya ma ba ta san me take ji ba. ‘Alhamdulillah. Ta faɗa a fili kamar me yin raɗa. Haka ta ƙarasa azkar ɗinta sannan ta miƙe ta shiga hidimarta.
Dole ta haƙura ta daina shan ƙwayar family planning ɗin da take sha saboda kada ta je ta cutar da abinda yake cikinta. Sai bayan kwana biyu ta ɗan sami natsuwa sannan ta je asibiti aka sake yi mata gwajin, aka tabbatar mata tana ɗauke da ciki na sati shida. Bayan ta dawo daga asibitin sannan ta sanar da Mustaphan.
Wannan gwajin da ta yi kuma sai ya zama kamar ta kunno laulayin gaba ɗaya. Babu inda yake mata ciwo amma tana fama da kasala sosai sannan kuma ga rashin son cin abinci. Haka dai ta cigaba da lallaɓawa.
Ranar kwananta ne don haka Mustapha a ɗakinta zai kwana. Yaran duk sun kwanta a ɗakinsu yayin da Hammad da Shukra suke kwance a ɗakin baƙinta wajen Hafsa. Yana zaune a gaban mudubinta yana aiki a computer ɗinsa yayinda ita kuma take kwance a kan gado tana game a waya. Ya bar aikin ya juyo yana kallonta ya kirawo sunanta, ta bar game ɗin ta mayar da hankalinta kanshi sannan ta amsa.
Yace ‘Umm! Ina so dama na sanar da ke bana za mu je aikin Hajji da Naja. Da da ke za mu je amma kin ga ke laulayi ya saka ki a gaba don haka na cire sunanki na saka nata sunan. Ta ɗan yi shiru saboda yanda maganar ta zo mata a ba-zata; idan dai ba wai ba ta ga dai-dai ba ma kamar dai ganin da ta yi wa Najan shekaran jiya ta ga kamar ita ma tana ɗauke da yaron ciki; ko da bai fito ba dai amma ita Khadeejan ta ga wasu alamu.
Domin a lokacin har ta ji kunya tana fatan Allah ya sa ba ganewa Najan ta yi ita tana ɗauke da ciki ba ta je ita ma ta yi. Kallon da ya kafe ta da shi ya sa ta yi firgigit ta dawo hayyacinta tana cewa ‘Masha Allahu, Allah ya nuna mana. Amma ai ana zuwa da masu ciki kuma zan iya; in dai an yi niyyar kai ni to a ba ni kujerata zan je.’
Ya yi dariya ‘Haba aikin hajin fa ba wasa ba ne kuma ba a kwance ake yi ba, ko so kike mu je wahala ta sa ki sami miscarriage? Kuma ya za a yi na ɗauke ku mu tafi saudiyya gaba ɗayanmu? Mu bar yaran a wajen wa? Kin san Hajia yanzu ba lafiya ce da ita ba.’ ‘Haka ne, to ai sai Najan ta zauna ni na je tunda ni ka fara yin niyyar biyawa.’
‘To ai na gaya miki ke ga ciki, da a ce ba ki sami ciki yanzun ba da ke za mu je amma ki yi haƙuri sai shekara mai zuwa in Allah ya nuna mana. Ta tashi zaune ta ƙara marairaicewa tace ‘Idan na mutu a haihuwa fa? Ya harare ta yace ‘Ka faɗi alkhairi ko ka yi shuru.’
Ta sunkuyar da kai tana murmushin yaƙe; yayin da ya juya ya cigaba da aikinsa. Ta zame ta koma ta kwanta; tabbas ba kuskure ta yi ba ciki ne da Naja, ko da kuwa bai kai sati shida ba. Kuma tabbas ta san ba ita Mustapha ya yi niyyar biya wa Hajji ba, Najan ya so biyawa. Kawai dai cikin ya zo masa ne a matsayin uzuri da kariya. Ya wanke kansa daga zargi.
A hankali ta zame ta gyara kwanciyarta ta janyo abun rufa ta rufe jikinta sannan ta rufe idonta kamar mai bacci; haka ta kwana zuciyarta tana ƙuna. Me Mustapha ya mayar da ita ne; shikenan idan dai abun ƙaruwa ne ba zai iya sakata a ciki ba sai bayan ya saka Naja amma idan dai wahala ce ita ce a kan gaba? Yanzu yana nufin yace da matarsa zai tafi aikin Hajji; wadda ita ma cikin ne da ita sannan ita kuma ya barta ta kular masa da yara da gida duk da ita ma cikin ne da ita.
Za ta iya wahalar kula da gida amma ba za ta iya wahalar ibada ba kenan? Sai yau ta gane girman rainin da Mustapha ya yi mata da kuma yanda ya ɗauke ta. Tun ranar da Mustapha ya sanar da ita zai tafi Saudiyya da Naja ta so ta je gida wajen Mommy, amma saboda kada abun ya yi kama da za ta yi reporting ɗinsa sai ta haƙura.
Tun dare ta sanar da shi za ta je gida kuma ya ba ta izini, don haka gari yana wayewa da yake ba ita ce da girki ba ta shirya. Hafsa ta kama hannun Hammad suka sauko, suka fice tsakar gida suna jiranta yayin da ita kuma take rufo part ɗinta. Ta saba duk lokacin da za ta fita idan Naja tana nan sai ta leƙa ta sanar da ita ta fita, don haka yau ɗin ma tana saukowa ta shige parlor ɗin Naja.
Tun kafin ta hango fuskokinsu ta ɗauki muryar Yaya Jidda, ba ta yi mamaki ba tunda yanzu sun saba zuwa gidan su wuni a wajen Naja idan ba ta sauko ba babu mai hawa nemanta kuma ko yara ba za a tura a ce ta zo ba. Ta ƙarasa ta zauna a kan hannun kujera ta gaida Yaya Jidda cike da girmamawa sannan suka gaisa da Naja.
Har ta miƙe za ta fice Yaya Jidda ce ‘Sai muka ji abun arziki kuma, Mustapha yace da shi da Naja za su je aikin Hajji. Ta ɗan koma ta zauna tana murmushi tace ‘Eh, haka yace. To Allah ya sa su je a sa’a, muma ‘yan baya Allah ya kirawo mu. ‘Amin ya Allah.’ Ta amsa sannan ta miƙe ta yi musu sallama ta fice.
Har ta je gida abun yana yi mata ciwo a rai; wato har ma ya gayawa ‘yan uwansa da Naja zai tafi Hajji kenan an fara zuwar mata murna ta kuma ana yi mata Allah ya kawo na ‘yan baya. Kuma wannan ganin da ta yi wa Naja ya ƙara tabbatar mata da cewa Najan tana dauke da ciki domin yawu ne a bakinta irin wanda masu ciki suke tarawa.
Tun da ta shiga gidan Mommy ta san da matsala, amma dai ba ta tambaye ta ba saboda bata son ganin kukanta. Ta san yanzu da ta tambaye ta damuwarta sai ta yi kuka mai isarta sannan za ta gaya mata damuwar. Suna zaune a parlor ɗin Mommy bayan sun gama cin abincin rana suna hira yayin da Hammad yake ta kai wa da kawowarsa, Mommy ta dube ta tace ‘Ki bar min Hammad a nan ya kwana biyu ki samu ki ɗan huta, na ga duk kin yi wani zuru-zuru.’
Ta yi gajeran murmushi tace ‘Ga shi nan Mommy an bar miki, idan na shirya sai Ahmad ya mayar da ni gida ya karɓo masa kayansa. Ta yi dariya ‘Dama neman kai ake da shi.’ Jimawa kaɗan tace ‘Momy wai Abbansu ne zai tafi Hajji shi da Naja. Nan da nan fara’arta ta ƙaru, tace ‘Kai ma sha Allahu, Allah ya amsa ibada.’ Ta kalli Khadijan suka haɗu kuma kamar wadda aka tunawa wani abu tace ‘Ah, to ke me yasa ba za a haɗa da ke ba ko kuma a fara kai ki, ko kin yi halin naki ne ya ɓata miki rai kin ce ba kya son kujerar?
Ta sa yatsanta ta goge ƙwallar da ta faɗo a kwarmin idonta, ta kawar da kai sannan tace ‘Haka ya zaɓa ya fara tafiya da ita. Da mamaki ta zaro ido tana tambaya ‘To ke me kika yi masa, tunda dai ai kece babba ke ya kamata ya fara tafiya da ke ko kuma ya tafi da ku dukanku a lokaci guda.’
‘Yace wai ciki ne da ni don haka ba zai tafi da ni ba sai dai ko wata shekarar zuwa lokacin na haihu. Ta kalli cikinta sannan ta kalli fuskarta ‘Ciki? To ai ƙarami ne kuma na ga har yanzu ana zuwa da masu ciki sai dai idan basu da lafiya. Ni ban ma san kina da cikin ba ai. ‘Ni ma bai fi last week na gane ba, ban ma sa rai da shi ba kawai na gan shi.’
Mommy ta dafa hannunta tace ‘To ai shikenan tunda ya zo sai mu ce Allah ya raya, amma dai masu ciki suna zuwa aikin Hajji har yanzu. Ana ta dai cewa za a hana amma ba a hana ɗin ba tukunna. Kawai da yace bai so zuwa da ke ba. Ta sake share ƙwalla tace ‘Tabbas Mommy bai so ba, don ita ma Najan ai ciki ne da ita.
Kawai dai ya zata ban san tana da cikin ba ne shi yasa yake so ya raina min hankali kamar yanda ya saba. Ikon Allah. ’Suka yi shiru na ɗan lokaci; ita ma Mommy abun ya ɗaure mata kai. Duk gidajen da ta sani na mata biyu ko sama to idan irin wannan damar ta samu babba ake fara kai wa. Tabbas abun ya sosa mata rai to amma babu yanda za ta yi.
Ta dafa hannun Khadeejan wadda ita ma ta yi nisa a nata tunanin tace ‘Kuma ba ki gaya masa Najan ma ciki ne da ita ba? Ban gaya masa ba Mommy, kuma ba zan gaya masa ba. Yana sane da abinda yake yi Mommy, tsaf ya san tana da ciki. Ita da take tara yawu idan tana laulayi, kuma ko yau ma da na shiga wajenta da yawun a bakinta.
Kawai dai da ita ya yi niyyar zuwa, ko na gaya masa kuma ba canzawa zai yi ba sai dai kawai ya yi ta kawo hujjoji. ‘Uhm, to ai shikenan. Kin ga dama shi Hajji kiran Allah ne, ke ma in sha Allahu Allah zai kirawo ki nan ba da daɗewa ba ta hanyar da ya so. Kada ki sa wata damuwa a ranki balle ki illata ɗan da yake cikinki.’
Suka yi shiru na ɗan lokaci, jimawa kaɗan ta gyara zama tace ‘Wallahi ni Mommy na ma gaji da auren nasa gaba ɗaya. Tabbas ko shekara nawa zan yi da Mustapha ba zai taɓa canzawa ba, ba zai iya yi min adalci ba. Wataƙila ya daina so na, wataƙila kuma iya son da yake min kenan. Amma dai gaskiya na gaji Mommy.’
Ta dafa hannunta cike da kulawa tace ‘To ai haƙuri za ki yi, dama shi aure ya gaji haka kuma ribar aure ta me haƙuri ce. Ba ki sani ba ko ita abokiyar zaman naki wani abun take yi na biye-biyen malamai, ai duka ana yi. Ta yi murmushin yaƙe tace ‘Ai wallahi babu wani biye-biye Mommy, a hayyacinsa yake yi.
Kawai dai idan hidima za a yi masa to ya fi so ni ya saka ni aiki, idan kuma morewa zai yi da harkar soyayya to wannan ita ta iya. Amma babu wani asiri haka ya tsarawa kansa. Ta sake kama hannunta ta riƙe tana kallon fuskarta tace ‘Ki dai yi haƙurin, in sha Allahu za ki ga ribarsa. Kuma idan dai Hajji ne da izinin Allah ke ma zai kirawo ki.’
‘Uhm.’ Nan suka ɗauki lokaci Mommy tana ba ta baki. Can zuwa yamma ta shirya Ahmad ya mayar da ita gida ta ba rwa Mommy Hammad.
Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Bakwai
Edita@rumasau-kallamu








