Me Ke Kawo Warin Jiki?

0
43

Shin za ka iya gane shekarun mutum a yayin da yake zaune a gefenka ta hanyar warin jikinsa? Zai iya yiwuwa mutum yana sanye da turare, amma duk da haka za ka iya gano shekarunsa ta hanyar warin jiki. Ta hanyar bincike, an gano yadda ake gano hakan.

Shi dai warin jiki ya bambanta tsakanin kowane mutum. Amma kuma yana sauyawa yayin da mutum ke girma. Wannan na faruwa ne ba kawai saboda muhallin da mutum ke zama ba, har ma da yadda yake cuɗanya da al’umma.

Lokacin da mutum ke ƙarami, warin jikinsa ba ya fitowa sosai saboda rashin aikin gaɓoɓin da ke fitar da zufa yadda ya kamata da kuma ƙarancin ƙananan halittu da ke rayuwa a fatar mutum.

Amma duk da haka, iyaye na iya tantance warin jikin ‘ƴa’ƴansu ƙanana. Wannan warin jiki na ƙara danƙon soyayya da ƙauna tsakanin iyaye da ƴaƴansu. Kuma hakan na rage damuwa ga iyaye, yayin da suke ƙoƙarin sanya yaran nasu farin ciki, domin warin jikin ƙananan yara na da jan hankali sosai.

Sai dai kuma masu jegon da kan yi fama da damuwa sanadiyyar haihuwa, ba su iya tantance warin jikin jariransu. A lokacin balaga, warin jikin mutum kan sauya lokaci zuwa lokaci.

Wannan na faruwa ne sanadiyyar sinadaran da jiki ke fitarwa waɗanda ke haɓɓaka gaɓoɓin saduwa, waɗanda su kuma ke haɓɓaka aikin ɓangaren fatar jiki da ke samar da zufa da kuma maiƙo. Yawancin waɗannan gaɓoɓi na samar da ruwa da kuma gishiri.

Sinadaran Apocrine, masu samar da maiƙo da zufa na fitar da wani wari, wanda ya sha bamban ga kowane mutum. Sinadaran su ne ke samar da maiƙon da ke sanya fatar kai da ta jiki laushi. Sai dai a lokacin da suka cakuɗa da ƙananan ƙwayoyin halittu, sai su riƙa fitar da warin jiki da zai iya damun mu.

Yayin da yaran da ke tasowa ke fitar da wani wari, warin kan canza a lokacin da suka balaga, kuma warinsu na asali kan ɓace, wanda hakan ke sanyawa warin ya sha bamban da wanda iyayensu suka sani tun asali.

Danna nan don karanta gwargwadon shayarwarki gwargwadon kariyarki

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceHani Akan Yin Duba 2
Labarin na GabaKafar Sadarwar Zamani, Amfani Da Ƙalubalenta