khairatu.shehu
Akwai matsaloli masu yawa game da shan miyagun ƙwayoyi, kuma yana yin tasiri sosai a rayuwar mashayan musamman ta fannin lafiya.
Masu shaye-shaye suna haɗuwa da waɗannan cututtuka masu alaƙa da illolin da waɗannan sinadarai sukan yi wa jiki in an sha ba tare da ƙa’ida ba sakamakon abubuwan da suke sha masu sa maye:
- Matsanancin ciwon kai
- Matsanancin ciwon ciki
- Matsanancin ciwon ƙirji
- Ciwon hanta
- Ciwon ƙoda
- Ciwon saifa
- Ciwon huhu
- Ciwon zuciya (kalbu)
- Ciwon daji (cancer)
- Ciwon hawan jini
- Shafar jaririn da ke cikin mace mai ciki
- Rashin gani
- Rashin jin ɗanɗano a baki
- Rashin cin abinci
- Rashin natsuwa
- Rashin tsafta
- Yawan tunani
- Yawan jin tsoro
- Yawan kasala
- Yawan ramewa
- Tsotsewar jikin mutum
- Saurin kamuwa da Tarin fuka (tuberculosis wato TB)
- Taɓuwar ƙwaƙwalwa
- Saurin kamuwa da “cutar Sida (AIDS), sakamakon munanan ɗabi̇’un da shaye-shaye kan haifar ta hanyar jima’i ko allura.
Sannan kuma a cikin rayuwar masu shaye-shaye akwai waɗannan abubuwa da suke cin karo da su wato aikata mugayen laifuka waɗanda suka haɗa da:
- Sata
- Fashi da makami
- Karuwanci
- Kisan kai
- Rataye kai
- Damfara
- Ha’inci
- Ƙarya
- Yawan faɗace-faɗace
- Yawan mutuwar aure
- Rashin kulawa da tarbiyyar yara
- Rashin zuwa makaranta
- Rasa aikin da ake yi
- Rashin cika alƙawari
- Rashin tsayar da ibada a kan lokaci
- Zama alaƙaƙai a cikin al’umma
- Zaman daba
- Shiga ƙungiyoyin asiri.
Duk matashiyar da ta zama ma’abociyar shaye-shayen kayan maye tana tattare da fuskantar matsalolin rayuwa da kuma zamantakewarta cikin jama’a, kuma za ta ci gaba da fuskantar waɗannan abubuwa matuƙar ba ta daina ba:
Mace in tana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da wuya ta zama tana da abokai na ƙwarai. Matashiya mai shaye-shaye idan ta haifi ‘ya’ya da wuya ta ba su tarbiyya mai kyau. Kuma ire-iren waɗannan matasa in suka zama shugabannin al’umma mai zai faru ga waɗannan al’umma musamma wannan lokaci na mulkin damokaraɗiyya?
Matashiya, mai shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ba a bari saurayi na kirki ya zo neman auren ta. Kamar yadda ya faru ga wata budurwa ‘yar shekara ashirin da biyu a duniya, wadda ta gama karatu ba tare da kyakkyawan sakamako ba.
Ƙawayenta wasu duk sun ci gaba da karatu wasu sun yi aure, amma ita tana nan a gida kuma haɗuwa da mugayen abokai suka koya mata shaye-shaye, wani saurayi ya gan ta suka yi maganar aure har an buga katin gayyata aka zagaya aka kai wa saurayin labarin cewa wadda zai aura ‘yar maye ce, daga nan ya ce a ba shi kayansa ya fasa.
Domin karanta Zaurancen ‘Yan Maye danna nan
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu