Rabiu Musa Adam
Malam Imam Ahmad da sauran malaman sunan sun rawaito daga Abi Darda` (RA) ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: “Lallai Malamai magada Annabawa ne, Su Annabawa ba su bar dinari ko dirhami ba, sai dai sun bar ilimi. Wanda ya yi riƙo da shi lallai ya yi riƙo da rabo babba”
A cikin wannan rubutun duk inda aka faɗi malami ko malamai ana nufin malamin addinin musulunci wanda aka yarda da iliminsa da kuma tsoron Allahan sa. Irin waɗannan malaman su ne magada Annabawa, saboda suna yaɗa shiriya ga mutane (Wanda aiki ne annabawa). Ko kuma don su (malamai) suna ɗauke da wani abu (ilimi) wanda yake daga wurin Allah wanda aka samu ta hanyar Annabawa. Duk ɓangare biyun sun cancanci girmamawa.
Malanta wata hanya ce da ta ƙunshi kyautata niyya, tsoron Allah, gwagwarmaya, haƙuri, jajircewa, ladabi da girmama wanda ake neman ilimi wurinsa, dan neman sanin abinda ya shafi addini, wanda ya ke ɗaukan lokaci mai tsawo. Duk mai neman ilimi yana ba da lokacinsa ne gaba ɗaya, ya lizimci malami, ya jajirce, tare da yi wa malami ladabi, da haƙuri ga duk abinda zai iya bijirowa ta ɓangaren malamin ko ta ɓangaren karatun ko yau da gobe.
Duk wanda ya bi wannan hanyar, bayan wani lokaci ana sa ran ya sami wani abu na ilimi, har ma ya amsa sunan malami. Sanin kowa ne shi ilimi ba a daina nemansa kuma ba a iya ƙure samunsa. Sai dai mutum ya yi iya yinsa kawai. Sannan ba kawai don mutum ya sami ilimi shi ke nan ba, sai an cigaba da bincike, karatu da nazarce nazarce.
A ƙarni na Sha-shida (16) a Arewacin ƙasar nan, Jami`ar Gobarau da kuma `yandoto ta Katsina sun zamo wurare da suka tara masana a kowani fanni na ilimi wanda manyan malamai daga duk faɗin nahiyar Afrika da ma wasu wuraren suke zuwa dan neman ilimi da ilimantarwa.
Bayan jihadin Babban Malami, Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo, cikin jama`ar Shehun malamin, manyan malamai irin su ƙaninsa, Abdullahi Ibn Muhammad Ibn Fodiyo (Abdullahin Gwandu), Malam Mustapha (Ɗan Tafa), Waziri Ɗan Laima da kuma irinsu ɗan Shehu Usman bin Fodiyo wato Muhammad Bello da ƙanwarsa Nana Asma`u da ɗanta Abdulkadir Ɗan Tafa da sauran manyan malamai sun yi ta ba da gudunmawa wurin karantar da mutane, rubuce rubucen littatafi da ƙasidu na ilimin addini, lugga da sauransu.
Duk lokacin da aka sami tarin malamai a wuri, ko a lokaci ɗaya, sau da yawa akan sami wata mas`ala ta addini wadda za a iya samun saɓani a tsakanin malamai. Wannan yana faruwa ne sakamakon yawan bincike a kan mas`aloli na addidni daban daban da malamai su ke yi. Sabani ba wani abu ba ne da zai sa a ta-da jijiyar wuya ko a ɗau makami, tun da su masu ilimi ne, toh a ilmance ake komai ta hanyar rubuce rubucen ƙasidu, littattafai da wasiku da fitar da fatawa.
MISALAI GUDA UKU KAƊAI DAGA MAGABATA.
Misali na farko shi ne: Lokacin da Turawan mulkin mallaka suka shigo yankin Arewa, Sarakunan mu na musulunci sun ƙi miƙa wuya, kamar yadda turawan suka nema. Da yawa sun zaɓi su yaƙi waɗannan turawan.
Sarkin Muslumi Attahiru I da sanyin safiyar ranar 15 Maris 1903 bayan an gwabza tsakanin jama`arsa da turawa na kimanin sa`o`i biyu, sai ya fahimci yaƙi da turawan nan babu nasara, saboda a ƙalla an kashe mutane kusan 100 cikin mutanen sa, a ɓangaren turawa ko mutum guda ba a kashe ba, saboda bindigogi na zamani da suke amfani da su a wancan lokacin.
Ganin haka, ya yanke shawarar yin hijira zuwa gabas, bayan ya yi shawara da wasu daga cikin muƙarrabansa. A ranar 27 Yuli, 1903 aka yi yaƙin ƙarshe a wani gari da ake kira Burmi ranar Juma`a Sarkin Musulmi Attahiru I da kusan mutane 600 suka yi shahada a cikin masallacin juma`a. Wannan jajircewa da Sarkin musulmi da yayi, ɗaya daga cikin sojojin taurawan Ingila William Wallace ya tabbatar da haka.
Ba tarihin Sarkin Musulmi Attahiru I zan bayar ba, amma ana cikin wannan taƙaddama bayan fitar Sarkin musumi daga birnin Sakkwato ranar 21 Maris, 1903 aka zaɓi Muhammad Ibn Ali Ibn Bello (Attahiru II) a matsayin sarkin Musulmi. A wannan lokacin Wazirin Sokoto Muhammadu Buhari ya nemi fatawa a wurin Alkalin Gwandu Ahmad Bin Sa`id kan maslaha ga musulmi; A miƙa wuya wa turawa, ko a ci gaba da yaƙarsu ko a yi hijira? Wanda wasu suna ganin ba bu wata maslaha da ta wuce a miƙa wuya wa turawa kawai.
Wannan fatawa ta a miƙa wuya ta samu karɓuwa sosai musamman dalilin takardar da Wazirin Sokoto Muhammadu Buhari ya yi “Risalatil Wazir Ila Ahlil Ilmi Wat Tadabbur” ta yadda suka yi amfani da ilimin usul wurin bayanin hukuncin abinda ya kamata shugabannin musulmi su yi na miƙa wuya da yarda da turawan mulkin mallaka. Akwai waɗanda suka saɓa musu a ra`ayi suma da hujjojinsu, amma cikin rubuce rubuce na ilimi kowa ya fito da hujjarsa, ba hayaniya ko zage –zage da cin mutunci.
Misali na biyu: Shi ne Lokacin da aka sami taƙaddama kan saka karatun Qur`ani a gidan rediyo a 1955 zuwa 1960 wanda Sheikh Ibrahim Nyass ya ba da fatawar ya halatta a sa karatun Qur`ani a gidan rediyo, shi kuma Sarkin Zazzau Malam Jafaru Ɗan Isyaku ya ba da fatawa sɓanin haka.
Dukkansu (Sheikh Ibrahim Nyass da Sarkin Zazzau Malam Jafaru Dan Isyaku) kowa ya yi amfani da ilimi mai zurfi na Usulul Fiqh da hujjoji masu ƙarfi wurin bayanin hukuncin wannan mas`ala. Sheikh Ibrahim Nyass ya ba da fatawarsa ne sakamakon tambaya da wasu daga cikin malaman Kano suka yi masa. Sarkin Zazzau Malam Jafaru Ɗan Isyaku ya ba da nasa fatawar ne sakamakon tambayar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi I ya tura masa duk da cewa shi ma Sarkin Kano Malam Muhammadu Sasusi I babban malami ne.
Abin sha`awa a nan shi ne Shiekh Ibrahim Nyass har wani littafi ya yi wanda aka buga shi a shekaran 1956 a ƙasar Masar mai suna “Alhujja albaligha fi kawn Idha`at alQur`an fir radiyo Sa`igha”. Wannan mas`alar ita ma haka aka ƙarƙareta ta hanyar ilimi ba hayaniya da harigido.
Misali na uku, a ƙarni na 19, an sami taƙaddama a kan Sadalu da Qabalu a sallah, wannan taƙaddama ta samo asali ne saboda bayyana da yaɗuwar tajdidin ɗarikar Tijjaniya da Sheikh Ibrahim Nyass ya kawo wanda kafin zuwan wannan tajdidi, ɗarikar Ƙadiriyya ita ce aka fi sani kuma ta fi daɗewa a ƙasar Hausa tun bayan jihadi.
Malaman ɗarikar Kadiriyya sun tafi a kan sadalu cikin sallah. Sheikh Ibrahim Nyass da wasu malamai a Kano suka zo suka warware wancan fahimta ta sadalu da hujjoji. Wannan ya sa `yan Kadiriyya suke ganin `yan Tijjaniya sun zo da wani sabon abu har aka riƙa kiran `yan Tijjaniya masu bin wannan fatawar da “`Yan Ƙabalu”
Shehunan malamai irin su Malam Muhammadu Salga (r. 1938), Malam Tijjani Usman Zagon Barebari (r.1970), Malam Shehu Maihula (r1988) da sauransu sun yi rubuce rubuce dan tabbatar da ingancin yin ƙabalu a sallah. A ɗayan ɓangaren na Qadiriyya wanda Malam Nasiru Kabara ya ke jagoranta sun yi na su rubuce rubuce kan ingancin yin sadalu a sallah.
A nan ma wani abin sha`awa, shi ne duk rubuce rubuce na ilimi aka rinƙa yi, har yau waɗannan rubuce-rubuce suna nan. An sami irin wannan taƙaddama ta faru a sokoto har Malam Abubakar Atiku Gwandu (r. 1913) ya rubuta wani littafi mai Irshad al-ikhwan ila bayan hukm as-salat bis-sadlu wa al-kablu.
A kwai misalai masu yawa kan taƙaddama ko saɓani da ake samu tsakanin malamai tun tuni, amma abin zai birge ka idan ka kalli hanyar da ake bi wurin bayyana ra`ayi da hujjoji da fito da komai fili, hanya ce ta rubuce rubuce na ilimi, ba soki burutsu da hauragiya da shirme ba. Kuma malamai su suke kayansu ba kowani kare da doki ba. Hargowa da hayaniya da shiga fagen ilimi daga ko wani kare da doki ya samu asali ne dalilin yaɗuwar hanyoyin sada zumunta.
Wanda shi ne za mu tattauna a rubutu na gaba.
Rabiu Musa Adam
Whatsapp: 08039290267
September 12, 2025
Karanta Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga
Edita@rumasau-kallamu