Ma’anar Damokuraɗiyya

0
22

Ita dai damokuraɗiyya ana ganin cewa gwamnati ce wadda mutane suka zaɓe ta. Wannan ita ce fasasara mai sauƙi, amma wasu suna ƙalubalantar wannan. kuma su yanke hukunci ba tare da an tilasta musu ba. 

Mutane za su yi zaɓe, su yi abin a cikin lumana, kuma kowacce ƙasa da irin nau’in gwamnatin da ta ɗauka na tafiyar da gwamnati mai adalci ko da ba a yi zaɓe ba. Bisa haka ne ma mutane irin su Muhammad Gaddafi yake ganin shi damokuraɗiyya yake yi saboda ya ba wa al’ummarsa duk irin abinda suke bukata, shi ma damokuraɗiyya ce. Kamar ƙasar Rasha da suke yi abubuwansu mai inganci, su ma suna ganin damokuraɗiyya ce. Ita damokuraɗiyya ta banbanta da yanayin da mutane suka ɗauki kansu. 

Misali kamar mutanen China, suna ganin ƙasarsu ma tana bin damokuraɗiyya duk da cewa ba zaɓe suke yi ba da za a ce duk gari mutum ɗaya a zaɓe shi, a a sai dai ‘yan jami’yya ne  kawai suke yin zaɓe tare da bin ƙa’idoji na tabbatar da tsarin gwamnati, saboda China sun fi shekara dubu uku (3000) sun yi gwamnati mai inganci, wadda kafin a ɗauke ka aiki, sai ka nuna ƙwarewa (meritocracy), sun daɗe suna irin waɗannan abubuwan tarihi da ya ba su damarsu fito da tsarin da zai amfane su. 

Saboda haka a ko ina za ka ga mutane suna da irin nasu tsarin na damokuraɗiyya ta yadda za su aiwatar da ita. Tun da haka kenan za a ce irin damokuraɗiyyarsu ba za ta zama irin ta ƙasashen turawa ba. A zaɓi shugaban ƙasa, da gwamna da ‘yan majalisa. In dai aka samu gwamnati mai inganci, mai adalci, mai kulawa da haƙƙin jama’a, shi kenan su wasu suna ganin cewa wannan damokuraɗiyya ce.

Saboda haka, amana ce idan aka ɗauketa aka auna ta za a ga cewa wasu mutane ne suke damfarar jama’a su juya akalar gwamnati, duk da kana zaɓe amma ba ka da tasiri sai wasu mutane ƙayyadaddu da suke da kuɗi da ɗaurin gindi na wasu ƙungiyoyi, kamar yadda yake yanzu a Amurka take fuskantar barazanar yahudawa (Zionists) sun karɓe ƙasar sai yadda suke so, saboda suna da yadda za su yi, ba ka da damar cewa komai saboda suna da kuɗi da jaridu da abubuwa da za su iya hanaka samun wannan zaɓe, tun da ba kowa zai tsaya a zaɓe shi ya ci ba, sai ace damokuraɗiyya ce.

Kuma akwai yawancin mutane da suke ganin cewa damokuraɗiyyar nan turawa ne suka ƙirƙireta kuma ya saɓa da tsarin musulunci. To amma shi fa tsarin musulunci nan ya danganta da wanda yake magana, misali, musulmin ƙasar India kimanin mutum miliyan ɗari biyu (200 miliyan) fiye da yawan musulmin ƙasashen Afirka, babu inda ya fi su yawan musulmi a duniya sai ƙasar Indonesia. 

  Shi wannan musulmin sai ya ce maka shi ya fi son tsarin damokuraɗiyya, saboda idan ba tsarin damokuraɗiyya ba, babu yadda zai iya gudanar da addininsa na musulunci. Saboda haka a ba wa kowa ‘yancin ya gudanar da addininsa yadda yake so shi musulmin India yake buƙata.  

Amma kuma idan ka je ƙasar da musulmi ke da rinjaye, za su  ce mu a bar mu mu yi tsarin musulunci mu ɗabbaka shari’a, domin shi ne  zai yi mana dai-dai da yadda muke so. Don haka,  a nan an samu bambanci da damokuraɗiyya da yadda za a yi aiki da ita.

Damokuraɗiyya kamar riga ce ko mota da za ka yi amfani da ita, ba lallai sai an bi tsarin yadda turawa suka kawo ba. Su turawan sun kawo wannan tsarin (liberal democracy) ne da a zo a yi zaɓe kuma duka abin da mutane suke so shi za ayi, kenan babu haƙƙin Allah. Tun da farko Kent ne ya zo da tsarin wayar da kai a kan babu Allah (enlightment) da suka ce kada mutum ya yarda da abin da ba ya ganinsa. 

Tun daga nan turawa suka daina tunanin Allah cikin al’amuransu saboda waccan aƙidar ta (Enlightment philosophy). Allah da suke bauta masa shin “son zuciyarsu”, duk abin da zai tabbatar musu  da wannan son zuciyar da jin daɗi. Shi kuwa musulmi ai ba za su yarda da wannan ba. 

 Idan ka ba da zaɓi za a yi wannan, a misali ƙasar Misra, idan  ka zo ka ce za a yi damokuraɗiyya a yi zaɓe, mutanen Ikhwan su ne za su ci zaɓen, saboda haka turawa ba za su yarda a yi damokuraɗiyya a Egypt ba. Sun fi son a dinga mulki irin na soja ko sarakuna (mulukiyya) , wanda da wannan za su yi amfani su juya mutane yadda suke so. 

Amma idan aka ce za ayi damokuraɗiyya to, tsari irin na Ikhwan ne zai tabbata. Musulmi da ‘yan ideology sun fito sun ce wai ‘yan Ikhwan ba mutanen kirki ba ne, saboda haka a nan za ka zaɓi Musulmi ‘yan Ikhwan ne ko maƙiya addinin Allah irin su Sise. Sai ka ga shugabannin larabawa suna goyon bayan Sise sun ƙi su goyi bayan Ikhwan, waɗanda za su tabbatar da adalci, su ba da dama a yi addinin gaskiya. Amma sai su goyi bayan Zionists don biyewa son zuciya, kawai.

Ita damokuraɗiyya ba ya danganta da yadda ka ɗauketa, wanne tsari ka shigo da shi don ka tabbatar. Shi yasa ƙasar China da suka fi kowaɗanne mutane yawa, sun tafiyar da damokuraɗiyyarsu a kan tsari na tafiya da gwamnati mai kyau, kuma za a dauki mutane waɗanda suke da inganci su yi aiki. 

Yanzu shi shugaban ƙasar China sai da ya yi shekara 30 yana aiki, tun daga kan matsayin Kansila ya fara, sai sun tabbatar da kai kwararre ne kafin ya zo kan shugaban ƙasa. To ka ga China da suka zo da ‘yan gurguzu (communist) ɗinsu dole ne ka ba su wannan matsayi na damokuraɗiyya, idan aka zo za a yi aiki ko na makaranta ne ko asibiti ko kwashe shara, sai sun fito da abubuwa an tambayi mutane domin a ji ra’ayinsu tare da bin diddigi a kan aiki. 

Shi yasa masana ilimin kimiyyar siyasa suke cewa, ba za a ce China ba ta bin tsarin damokuraɗiyya ba, domin kowanne aikin gwamnati sai an tabbatar da ingancinsa, kuma sai an tambayi ra’ayin jama’a amma ba haka ba ne a ƙasar Amurka, ba ruwansu da wannan, kawai idan an yi zaɓe bayan shekara hudu an kori wannan an kawo wannan haka dai. To amma su China a tsarin damokuraɗiyyarsu da manufarsu shi ne ta yaya tattalin arziƙinsu zai juya ƙasar. Shi ya sa daga 1978 zuwa yanzu mutum sama da miliyan 500 sun fitar da su daga talauci. 

 Wane abu ne za su fito da shi da za su taimakawa mutane. Shi ya sa su a wurinsu duk wanda ya ce tsarinta ba ingantacce ba ne ya yaudari kansa. Domin sun ɗora sha’anin al’adunsu da tarihinsu. 

Da wannan za mu fahimci cewa ita damokuraɗiyya nan da ake magana ba tsarin da za a ce don kana da gwamnati da aka yi zaɓe wai ka yi damokuraɗiyya, haka ne  ka yi demokuraɗiyya, amma akwai abubuwa da yawa da suka shafi wannan. Kamar irin abin  da yake faruwa a Indiya, ga shi nan Indiyan tun 1940 suka samu ‘yancin kai ba a taɓa gwamnatin soja ba, amma yanzu indiya ta lalace, saboda ‘yan Hindu masu aƙidar bambancin addini, waɗanda su ne mafi yawa suke tsangwamar musulmi saboda ƙiyayya. 

Idan zaɓe ne , to an yi zaɓe a Indiya, kuma abin da suke so masu rinjaye (majority) su kashe mara rinjaye (minority). Wannan bai shigo cikin tsarin damokuraɗiyya ba, domin yadda aka ce, amma ana amfani da dangwalen masu rinjaye domin a cutar da marasa rinjaye (musulmi). Ya nuna cewa Indiya duk maganar da suka yin a damokuraɗiyya ba haka ba ne. 

Bisa wannan, idan za ka yi maganar damokuraɗiyya, sai ka yi bibiya, menene ya shafi rayuwar al’umma, an samu ci gaba ko ba a samu ci gaba ba?

Domin karanta tarihin damokuraɗiyya a Najeriya danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Sabulun Wanka Da Wanki
Dr. Ibrahim Ado Kurawa
An haife ni, a ranar 10 ga Agusta, 1963, a Kano. Na yi karatu a fannoni daban-daban, tun daga kimiyyar halittu har zuwa karatun Larabci da ilimin addinin Musulunci. Na wallafa littattafai da takardu masu yawa kan tarihi, siyasa, da al'adu, wanda hakan ya ba ni damar samun kima a duniya, har ma na zama ɗaya daga cikin masu zama a Rockefeller Villa Serbelloni a Italiya.