Lefe A Auren Hausawa

0
73

Sakina Muhammad Yazid

Lefe wani kaya ne da ango yake ba wa amaryarsa a lokacin aure. Kyauta ce ta alfarma da soyayya wadda ta haɗa da sutura, takalma, kayan ƙarau, kayan bacci, kayan kwalliya, turaruka da sauransu.

A shekarun baya sutura ce kala ɗaya ko biyu da takalmi da ‘ƴan ragowar kayan amfani na mata ake zubawa a cikin mazubi; wanda shi mazubin ake kira lefe. Sai mata dattijai a dangin ango su ɗauka a haɗa da kayan amfani kamar su lalle, hatsi da sauransu; su kai gidansu amarya. Daga can gidan su amaryar ma iyayenta mata ne za su karɓi kayan.

Amma a yanzu abun ya canza; wataƙila saboda cakuɗuwar al’adu da kuma shigowar baƙi ƙasar Hausa. A yanzu saitin akwatuna ake cikawa da kaya. Saitin akwati yana iya kamawa daga mai biyu har zuwa mai guda shida. Iya yalwar arziƙin ango da danginsa da kuma gatan amarya iya yawan akwatunan da ake mata.

Kama daga saitin akwati ɗaya har zuwa sama da goma ana yi. Kowanne nau’i na sutura ana ware musu akwatunansu; turamen zani, mayafai, kayan bacci, takalma da jakunkuna, kayan ƙarau, kayan kwalliya wasu lokutan ma harda abaya da kuma kayan turawa waɗanda ake kira ƙananan kaya; kowanne da akwatin su.

Bayan akwatunan kuma sai a haɗa da goro da alawa, lalle, gero, shinkafa da kuma sukari; wasu a buhunhuna suke sakawa wasu kuma a ƙananun mazubi.

Ranar da aka saka za a kai lefe sai dattijai mata daga dangin ango su ɗauka su kai. A nan za a yi musu tarba ta girma, idan suka tashi tafiya kuma sai a ba su tukwici wanda ya haɗa da kuɗi da kuma kayan ciye-ciye da lemuka wasu har da ruwan roba.

A shekarun baya mata ne suke kai lefen kuma mata ne a dangin amarya suke karɓa, sai dai a yanzu maza ma suna kai wa kuma maza su karɓa. Malamai da shuwagabanni suna ta kiraye-kiraye a kan a daina yin wannan al’adar ta lefe, amma har yanzu ba su yi nasara ba.

Wataƙila saboda yanda Hausawa suke alfahari da wannan al’adar ko kuma saboda yanda wasu matan bayan aure mazansu ba sa sake saya musu wata sutura bayan ta lefen.

Danna nan don karanta Rabe-raben Auren Hausawa

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

 

 

 

labarin da ya wuceBirkicewar Sashen Da Ke Sarrafa Ƙwaƙwalwa
Labarin na GabaNasiha A Kan Rayuwa
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.