Ko wane ɗa ba shi da burin da ya wuce ya samu iyaye masu ba shi kulawa, kama daga tarbiya, ilimi, ci da sha ke har ma da tarairaya da ɗaukar dukkan wata ɗawainiyya tasu, har zuwa lokacin da za su girma suma su zama wasu su taimaki iyayen su har ma da sauran Al’umma, amma ni ban samu wannan damar ba Khadija, sabo da….
Dai dai wannan lokacin ne malam Hadi ya shigo cikin fushi daret ɗaki ya nufa kasancewa dama wasu lokutan bai fiye yin sallama ba musamman in yana cikin fushi.
“Barira! Barira!!” “Na am baba”
Wace kalar shashasha ce ke ina ta kira amma kamar banza yana magana iyeeh? “Ka yi haƙuri baba wallahi ban ji ba ne amma insha Allah ba za a kuma ba. ” Barira ta faɗa cikin ladabi. Wani irin kallo ya yi mata tare da faɗin
“ina babar taki ?” “Ta je tayo awo ne saboda garin mu ya ƙare” “Ta dai tafi gantalinta ta ne kawai” Ba tare da sake ce masa komai ba Barira ta yi zugum tana kallon sa zuciyarta kuwa kawai tafasa take tare da karanta mata munanan wasiƙu.
Washe gari da safe Bashir ya shirya da nufin tafiya makaranta ya yi sallama da Lami wadda ta kasance mahaifiya a gunsu, kafin ya nufi ɗakin mahaifin tuni kunnuwan sa suka cika da kiran sunan sa da mahaifin ke ƙwalawa, tuni ya nufi ɗakin yana isa ya tsaya a bakin ƙofa tare da yin sallama.
“Fitowa kake son na yi dan uwaka? Rasa kunya ɓeran tanka..” Cikin fushi Bashir ya shiga ɗakin tare da faɗin “ga ni” Malam? Hadi ya ɗaga kai tare da faɗin “ina za ka ka ratayo jaka kamar wani wanzami..? Malam je ka ka cire kayan nan mu tafi kasuwa yau ina da aiki sosai a kasuwa”
Bashir ya miƙe cikin fushi ya yi waje yana faɗar ƙananan maganganu. Minti goma Malam Hadi ya fito yana neman Bashir, Barira da ke tankaɗen gari ta yi saurin risinawa tare da faɗin “baba ai Bashir ya tafi makaranta..”
“Makarantar banza da ta wofi, wato gani bawanku ko? In je in nemo muku ku ci ko? To wallahi yau in bai zo kasuwa ba sai na saɓa masa kuma ko sisi ba zan ba ku ba, yaran banza marasa albarka”
Kallon sa kawai Barira ta yi domin wannan baƙin cikin ya daɗe da yin tsatsa a cikin zuciyarta, baba Lami kuwa fitowa ta yi cikin fushi domin ita kanta abun ya kai ta maƙura, suna haɗa ido ya yi wani tsaki tare da wurgi da robar da ke kusa da shi ɗauke da busashshen ƙanzo.
“Malam gaskiya na gaji da tambaɗar mun da ‘ya’ya da kake yi, a ce kullum maƙota sai sun ji mu,” “To su ji mana ko rashin kunya za ki yi mun” “Babu rashin kunya amma dai ka sani duk mutumin da bai san haƙƙin iyalinsa a kansa ba to ya shiga matsala, duk yaran mu babu mai ilimi babu wanda ka sa a makaranta, sai wanda maƙota suka dubi Allah suka dubi Annabi suka saka su, ba ka damu da cinsu ba, shansu, sittira, zama da su ka ji damuwarsu, babu kuɗin sabulu babu na kitso babu kalaman kwantar da hankali, cefane ma sai ka yi gorin sa.
To ka sani wannan haƙƙin ka ne da Allah ya ɗora maka, amma duk mijin da ke zagin matarsa ko aibata ta a gaban ‘ya’yan ta to bai nemi haɗa zuriya ɗayyiba ba haka ita ma matar, amma kullum kai ne Allah ya isa, lalatattu, marasa ilimi, Malam ta ya yaro zai ji ƙanka har ma ya taimake ka, ko wasu yara suna bukatar kulawar iyaye da ƙwarin gwiwa musamman yara mata amma malam…”
“Ya isa lami kin gama rashin kunyar taki da kika koyawa ‘ya’yan ki ?” Malam Hadi ya yi tsaki tare da ficewa waje, Barira kuwa tuni hawaye sun wanke fuskarta. “Allah ka shiga lamuran gidan mu ka chanza halin dukkan wani miji mai irin halin baba Hadi…
Wannan bayani an ciro shi ne daga maƙala mai taken TSATSAR ZUCIYA wadda Ismail Usman Abubakar @Dr. Hisham ya wallafa, wadda aka gabatar a Taron Ranar Marubuta Ta Duniya na ranar (31/12/2025) a Dutsen Jihar Jigawa.
Danna nan don karanta Yadda Manufar Rayuwarka Take
Edita@rumasau-kallamu









