Labari Mai Taken Fansar Hawayen Kakana

0
6

15/5/2025. ADADIN KALMOMI:2876

Gidan mu na gado yana tsakiyar badalar garin mu, shahararru ne a sanaʼar sarrafa fata wacce aka fi sani da dukanci. A wata sharariyar unguwa da ke zagaye da kasuwanni. Kasuwanci da kiwo shi ne alʼfaharin mu, kamar kowanne gidan bahaushe kakana malam Gambo yana da mata biyu Hauwaʼu ita ce amarya Rakiya uwar gida. Amarya ‘ƴa’ƴanta biyu duk mata, uwar gida ‘ƴa’ƴanta uku maza biyu mace ɗaya.

Kakana shaharren badukku ne duk garin mu kowa ya san shi kuma duk wanda ya iya aikin dukanci a garin mu, gurin sa ya koya, masauratar garin na alfari da irin aikin sa, duk wani aikin fata da ake amfani da shi gidan sarauta tun daga kan takalmin sarki har kaya ƙwalliyar dawakai na fata kaka na ne da tawagarsa suke yin sa, lallai ya shahara kuma yana fidda su kunya a harkar dukanci.

Kakanmu ya aurar da ‘ƴa’ƴansa mata ukun Lami, Hausu da Amina sai baban mu Auwalu da yayansa Sani, su ma duk da iyalan su wan babana ‘ƴa’ƴansa biyu duk mata Hadiza sai Rakiya da ta ci sunan kakarmu muna ce mata uwa, baban kuma duk maza ne Habu sunana ɗan uwana Muhammadu shi ne babba, kullum suna tare da ƙoƙarin koya mana sanar dukanci. A zauren gidan sa  yake aiwatar da aikin sa.

Ƙwatsam!! Wata rana sai ga wata alʼumma haye kan ababan hawan su wasu dokuna, ƙurar su ta tokare sararin samaʼu, makaman su suna sheƙe da walƙiya a sama cikin duhun ƙurar da suka tayar, suna tafe cikin azama da ƙwarin gwiwa, kaɗe-kaɗe na tashi, wasu daga cikin tawagar mata da maza suna rawa cikin nishaɗi da burgewa da shaye shaye lallai wannan tawagar akwai abinda ta taka.

Sun nufo garinmu, wasu irin mutane ne kafta-kafta masu zagayyayir fuska idanuwan su kamar an nitsawa sakwara yatsa da gajeren hanci kalar fatar su jajur kamar ƙosai, suna sanye da tufafin da aka yi da fatar dabbobi mai gashi gashi haka takalman su yake, kuma duk girman mutum rigar sa ba ta huce cibiya haka ɗankamfan da ke ƙugunsu bai huce ƙwawrun su kowannen su goyen da mashi a bayan  riƙe da garkuwa na kan doki da ƙafa adadin su yana da yawan ba zai harsasu ba.

A kwai ƙananu garuwa da wannan tawaga ba ta bari sun kai labari, tuni sun murkushe  tare da kama bayi. Duk garin da su ka dunfara sai wani ba shi ba, domin ɗaurin butar malam duk inda suka ƙaddamarwa sukan kwashi dukiya da bayi, su afka masa wuta ba za su bar gurin ba sai sun ga kiyashi a gurin ba ya numfashi, bukkokin sun zama toka bishiyu sun zama gawayi, gonaki sun zama toka, sun tabbatar koʼina ya zama fili.

Duk garin da suka hara basa shiga sai da dare, su ya-da zango a bayan gari su tura ‘ƴan leƙen asiri, su gane musu girman; yawan jamaʼar; ƙarfin masarautar, don sanin shirin da za su yi, duk wannan abun suna yi ne cikin ƙanƙani lokaci, salo da ƙwarewa. Inda suka hara garin mu, don babbar cibiyar kasuwancin kuma daular mulkin mu yake, duk garuruwan da sukai fatali da su a hanya gudun kar su haɗu su kawowa garin mu ɗaukin in sun kai musu hari duk salo ne na yaƙi.

Waɗannan maharan duk da ba su san komai a kan garin mu ba, amma ba shi ne zuwan su na farko ba domin na gaya muka garin mu babban gari ne dalilai da dama suna kawo alʼummu misali: yawon buɗe ido muna da daɗaɗɗiyar alʼada ta gargajiya masu ban shaʼawa, gine-ginenmu wanda ba a koʼina ake ganin sa ba, tsarin zamantakewar mu bukukuwan alʼadu na suna da na aure, tsarin sarautarsu da ƙwarewarsu a kasuwanci.

Wannan dalilin ya kawo waccan alʼumma garin mu dan ƙulla harkar kasuwanci mai ƙarfi tun ana harkar ban gishiri in ba ka manda. Alʼumma sun riƙe su da amana  zuciya ɗaya, duk da sun san tarihin su a gurin malam da suka addinin musulunci, mutanen mayaudara azzalima masu butulci ga Allah subhanahu  wata’ala. Wanne tudu wane gangare suka zo mana da halin su na asali suka yi ƙwanton ɓauna suka san sirri mu.

Suka nufato mu da niyyar yaƙi,  suka shigo mu da ƙarfin tuwo domin sun san ƙarfin masarautar mu ba za ta ciyu da sauƙi ba, sun san zurfin tunani mayaƙa da ƙarfin  ƙwarewarasu a yaƙi. Abun da suka fi mu shi ne ilimin suna da makamai na zamani masu aiki da naʼura, an kai ruwa rana, an yi karan batta uwar barai da mayaƙan mu.

Kowanne gari suka hara cikin awanni sun kai shi ƙasa, amma garinmu sai da aka yi fafatawar kwana biyu ba tsagaitawa, har sun fara sarewa duk da sun yi wa mutan gari laga-laga sun ɓarnata dukiyoyin, ba wani ragowar ƙarfi a waje mutane da yawa an kama su wasu an kashe su, wasu an raunata su ba su da kataɓus dan suna da yawa kuma suna da makaman zamani.

Mu kuwa ba yawan jamaʼar, baƙi ne masu zuwa kasuwanci ko ci-rani tunda labarin rashin zaman lafiya fara yaɗuwa sai kowa ya ja jiki, duk da haka aka ci gaba sai da suka sa da karun suka zagaye garin. A wunin ƙarshe suka kaiwa masarautar hari cikin saʼa suka kutsa kai cikin gidan mai ɗinbin tarihi suka banƙara iya ɓanƙarawa suka kama tare da kashe manyan dakarun sarki,  wanda da su ne sarki yake jin shi sarki ne, suka yi wani salon ta ƙarƙashin ƙasa suka cimma iyalan sarki.

Daga nan suka ci lagon yaƙi suka yi fatali da alʼadun da gadon  iyaye da masarauta da dukiyoyin. Wannan ta hura wutar gaba da ƙin jinin mayaƙa a zukata. Sun shiga da yaƙi na cin zalin da wulaƙanta sarakunan mu da zubar musu da ƙima sun karɓe mulkin da ƙarfin tsiya. Sun karɓi masaurata suka sa dakaru a gidan don  tsare sarki da iyalan sa da kuma manyan masarautar na tsahon ƙwanaki.

Suka Afkawa lalitar gari da ma shirin su kenan. Masarautar garin duk yankin ita ce babba da ake gudanar da harkokin kasuwanci, duk wasu alʼummu garinmu ne karafkar. A haka aka cigaba da rayuwa a garin sun samar da dokoki da irin yadda suke so mulki ya gudana. Amma ba su sami yadda suke so ga talakawa sai da su ka biyo da sarakuna. Sarakuna ba su da kataɓus sai yadda suka dama haka ake sha.

Hakan ‘ƴan mulkin mallaka suka ringa yin amfani da su domin zalinci. Sun ɗorawa talakawa haraji da jangali duk wani mai gidan ya dangata da ƙarfin samun sa, kowanne me unguwa ko mai gari zai karɓa a hannun talakawan sa, (jangali ko haraji kuɗi ne ko kadara da masu mulki kan karɓa a gurin talakawa). Kuma ba ruwan su da za ka iya ko ba za ka iya ba su dai buƙatar su ta biya.

Za a yanka maka lokaci, ka nema idan ba ka samu ba za a kai ka gidan mai gari ko hakimi su yanke ma ka hukunci, ko ƙari kan abinda za ka biya a da, ko yari a haka  mutum ya zama bawa a kan rashin biyan haraji ko jangali. Gari ya zama ba daɗi sun kassara ƙwarjinin da tattalin arzikinsa. Wannan dalilin yasa alʼumma yin hijara daga mahaifar su zuwa ƙasashe maƙota don samun ƙwanciyar hankali, wasu dalilin su ke nan na barin garuruwan su.

Daga nan cinikin bayi ya samu ƙafar kafuwa wanda mu ba mu san shi ba, suka ringa kama mutane su na fitar da su ƙasashen su  domin bautar da su aikin da injina ne ya kamata su yi, amma saboda zalinci, kuma duk wanda suka kama su kafitar da shi ya tafi kenan, an raba shi da iyalan sa da ‘ƴan uwansa kai uwa uba har da addininsa.

A wannan lokacin addinin bai kama jiki da zuciya ba babu cikakken ilimin. Abu mafi muni da sa ɗacin zuciya shi ne yadda ake ɗaure mutane a matsayin bayi ko dabba aka yi wa an zalince ta, sarƙa ce za a sa a ƙafafuwansu a jera a layi a ɗora musu ƙaton icce a kafaɗunsu sannan abi kafaɗun su a zarga sarƙa ta wuyan su a ɗaure su katamau, sannan a tura su a gurin da in ka kirawo shi kabari ka yi daidai.

Haƙiƙa alʼummar sun sha wuya a hannun azzalimai ‘ƴan mulkin mallaka sun yi wa kakkanin mu da iyayen cin zarafi da ƙetare iyakar mutunta. Wannan ta kaurara ƙin jini da ƙyamar su a zukatan alʼumma. Kaka na ya ce “Idan mu ka gano waɗannan mutanen  yayin rangandin su, mukan gudu ne don ɓuya kamar mun gano mayunwacin zaki domin ba su da imani ko tausayi in suka ga mutum lafiyayye shi kenan sun ga nama, don za su ɗauke shi a matsayin bawa, in sun yi masa da ƙauna su bar shi a tare da su ya ringayi mu su hidmar gida.

In kuma ba haka ba su saka cikin wanda za su kai su can ƙasashen don yin aikin bauta musamman noma,”.Wannan na ɗaya daga cikin dalilin mutanen Afrika yin tsagu a fuska  in za su ɗauki bawa sai sun ga wanda ba wani lahani a wannan ɓangaren sun samu sauƙi, hakan yasa za ka ga kowacce ƙabila da irin nata tsagun na fuska. Haka suka ringa yi wa lamarin rayuwar ɗiban karan mahaukaciya, bayan sun gama kankane komai sun samu abinda ya kawosu.

Sai suka fara tunani koyawa  mutanen mu yarensu da kuma irin ilimin su, suka daina kamen bayi, sannan suka rage zalinci da cikin zarafi. Hankula sun fara ƙwanciya an fara komawa harkoki, baƙi ma sun fara leƙowa sun samu labarin an daina tashin hankali da kamen Bayi.

Kamar kowane mai sanaʼar hannu shi ma ya koma bakin aiki ya je kasuwa ya sisiyo duk kayan da yake buƙata a harkar dukancin sa, mun gyara ko ina ni da ɗan uwana an fito da kayan aiki kamar kullum abokan aikin sa sun hallara, mutum uku ne sai babana da ɗan uwa sa, idan an haɗa lissafin su mutun shida ke aiwatar da aikin samar da takalma da kayan fata irin su gafaƙa; bulala; kayan adon doki; kuben mashi da wuƙaƙe girma girma dai dai ɓukata.

Soron gidan mu babbar masanaʼanta ce mai zaman kanta, baƙi na gida da na waje haka ake zuwa don siyan kayan da muke samarwa, mu aikin mu ba ya huce aike don siyo abubuwa da kuma aiken cikin gida ko taimakawa baƙi ɗaukan kayan da suka siya, ba ma nisa da gida muna kusa, kullum ta Allah abun da yake faruwa ke nan sanaʼar iyayen da kakkani mu ke nan duk a cikin ta aka haife mu  kuma aka koya mana hatta iyayen mu mata sanaʼar su kenan.

Amma su sun fi manna kaya ƙyallin da ɗinka Rumi jikin takalmi ko kayan adon doki. Duk gari ya ɗauka ƴan mulkin mallaka za su fara koyar da jamaʼa ilimin da suka zo da shi , kakan mu “yace ilimin da ba na Allah ba!, Allah kar ka nuna min wannan rana lallai da wannan rana gara mutuwa ta, mai za a yi da ilimin taurin kai da bujirewa Allah”.

Wata rana bayan sallar asuba a masallaci, dama a nan mai unguwa kan sanar da mutane saƙo, haka yau bayan shafa adduʼa mai unguwa ya tashi don isar da saƙon yace “Bayan sallama irin ta addinin musulunci, a jiya mun yi taro da sarakuna da hakimai sun ba mu saƙo zuwa gare ku, sun ce a gaishe ku kuma a sanar da ku shirye-shiryen ya kankama kan fara koyar da yaran mu da manyan ilimin ‘ƴan mulkin mallaka.

Kuma dole ne a kan kowanne yaro da yake faɗin garin nan kuma sun ce in kunne ya ji, jiki ya tsira, ya ɗora da cewa tuni aka fara sa ‘ƴa’ƴan masu mulkin gargaji, awo na gaba ‘ƴa’ƴan talakawa za a ɗora, “cikin ɗan lokaci masallaci ya ɗau hayaniya masu aʼuziyya suna yi tare da neman ɗaukin Allah, domin babban balaʼi ya dumfaro ba mai iya masa sai Allah haka kowa ya ja jiki zuwa gida ba kuzari.

Hantsi na ɗagawa duk mun fito gurin sanaʼa kowa ya fara aikin sa kamar kullum, tuni baƙin sun fara zuwa siyan kayayyaki, sai ga saƙo daga fada cewa sarki yana umartar kakana da ya ba da sunayen mu ni da ɗan uwana ƙarshen wata za a kai mu makaranta, da jin wannan saƙo kaka na yana zaune sai ya miƙe sai kuma ya tuna saƙon daga inda yake sai ya zauna cikin tashin hankali ya amsa da to kuma ya ce “a cewa sarki godiya yake”

Ko da ‘ƴan saƙo suka tafi kakana buta ya ɗauka ya zagaya bayi, can ya dawo bai iya cewa kowa komai ba sai um sai um um haka wunin ranar kowa na zauren nan rai ba dadi, lokacin tashi kowa ya kama gabansa, a ƙaʼidar sa ba ya shiga gida sai ya yi sallar isha amma a ranar gida ya shiga don yana ta zaryar banɗaki. Ta ɓangare na ni abun ya yi min daɗi domin na harsaso sauyin rayuwa a tare da wannan ilimin da za a kai mu muddin ka yi amfani da shi yadda ya dace, na tabbarwa raina sai na yi ko da kuwa ba ya so, na saƙa hakan.

Kowa ya ga kakan mu ya san yana cikin tashin hankali ko mai da zancen ake yakan ce yau na ga ranar haihuwar ‘ƴa’ƴa mata, ga ‘ƴa’ƴan Auwalu suna ɗakinsu na godewa Allah amma ‘ƴa’ƴan Sani, za su ja min magana kai tur!!! da wannan ranar takaici, haka dai muka ci gaba da murginawa da daɗi ba daɗi har Allah ya kawo mu ƙarshen wata, saura ƙwana ki biyu tafiyar mu aka ƙara turowa kakana cewa ya shirya mu jibi za a zo a tafi da mu.

Tashin hankalin kakana ya ƙara taʼazzara, nan ya ƙara surar buta yay bayi wannan karan bai fito zaure ba cikin gida ya shiga ya sanarwa da iyayen mu mata, a ƙwana a tashi rana ta zo sai ga ɗan saƙo daga fada a tafi da mu, kakana tun yana daurewa sai da ƙwalla ta fito masa cikin hanzari yay cikin gida haka muka bi bayan sa, ni cikin zumuɗi na haɗo kayana amma muhammadu lamarinsa ba yabo ba fallasa.

Aka tisa ƙeyar mu sai makaranta. Bayan tafiyar mu aka ba mu labari ranar ba a yi aikin dukanci ba kakana ya ƙule cikin gida ba wanda yake zuwa inda yake, haka rana ta biyu ma ba a yi aikin ba amma a wannan ranar tabarma aka fito da ita waje kakanmu ya lallaɓa ya fito aka yi ta yi masa jaje, duk wanda yace Alhaji Gambo ashe abun da ya faru kenan, ya  ce” ee haka ƙaddara ta samu amma Allah ka gani ba a son raina ba Allah kar ka kama ni da wannan laifin”

Sai ya fashe da kuka, haka ya dinga kuka kamar ɗan yaye kusan ƙwana uku aka jera kakan mu yana karɓar jaje. A hankali aiki ya dawo daidai amma dai ya rage walwala kullum yana neman gafarar Allah. Ko hutu muka zo kaka ya dinga ja mana kunne mu kula da abinda ake koya mana gudun kar a koya mana kafurci, yace ku kula da sallah.

A haka muka yi ƙarama da babbar makaranta matakai uku nan haka muka yi matakin farko da na biyu shekara shida shida matakin ƙarshe ne muka yi shekara huɗu kuma duk hukuma ce ta ɗau nauyin karatun mu. Wani hutu da muka dawo wanda shi ne in mun koma za mu yi jarabawar fita, muka zo muka tarar da kakanmu cikin jinya rai a hannun Allah, a wannan jinyar Allah yay masa rasuwa mun ji baƙin cikin rashin sa domin mutum ne jajurtacce a lamarin iyalin sa, bayan share makoki muka koma makaranta iyayen mu suka ci gaba da jan ragamar masanaʼantar mu ta dukanci.

Alhamdulillah yau na zama cikakken maʼaikaci ƙarƙashin hukumar kula da lafiyar alʼumma bai ɗaya a matsayin likita, bayan gwagwarmayar makaranta ni da ɗan uwa na muhammadu inda shi kuma ya zama babban ɗan jarida a garin mu. Rayuwar mu ta yi kyau. Allah ba ya barin wani don wani, na so yau a ce kakanmu yana raye duk dangi suna alfahari da ba mu bauɗe a kan tafarki madaidaici da kaka yake tsoro ba, lallai Allah ya karbi adduʼar sa.

Masu mulkin mallaka sun bar mana gari sun danƙa ragamar komai a hannu ‘ƴan gari, Amma ba su tafi ba sai da suka ga ilimin su ya karɓu a garin mu har ana tafiyar da harkokin ci gaba na rayuwa, kuma suna ci gaba da karɓar jangali da haraji a hannun shuganinmu kuma harkar mulkin har yanzu su ke gudanar da ita a fakaice, masu mulkin gargajiya na jagorantar wani ɓangaren.

Na ci alwashin bunƙasa masanaʼantar kaka na ta zama ta zamani, a santa ko ina a duniya, na ci alwashi gina gidansa da irin ginin zamani duk da ba ya raye iyalansa sa mora. Na ci alwashin hawayen kakana ba zai tafi a banza ba, lallai karatuna gaba ɗaya fansar hawayen kaka na ne.

Karanta Labari Mai Taken Wata Sabuwa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceLabari Mai Taken Wata Sabuwa
Labarin na GabaTatsuniyar Cin Kasuwar Sama
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.