Kumburin Mahaifa Mai Sanya Zubar Jini (ENDOMETRITIS)

0
9

Endometritis kumburin bangon mahaifa ne (endometrium) wanda yake haddasa zubar jini daga gaban mace. Zai iya kasancewa mai tsanani amma ba ya ɗaukar dogon lokaci (acute). Haka nan zai iya zamowa mai tsanani kuma mai ɗaukar dogon lokaci (chronic). Mafi yawanci ƙwayoyin cutar bacteria ne suke kawo shi, musamman waɗanda suke kama al’aurar mace bayan ta haihu, ko kuma a lokacin da ake yi mata aikin tiyata a mahaifa ko mara.

Bincike ya tabbatar da cewa manyan dalilai masu kawo endometritis su ne:

1. Haihuwa (childbirth): Idan ƙwayoyin cutar bacteria suka shiga cikin mahaifa a lokacin da mace take yin naƙudar haihuwa, to, za su iya haddasa mata matsalar endometritis, musamman idan ta yi doguwar naƙuda (prolonged labour), ko yagewar jakar ruwan mahaifa (amniotic sac rapture), ko yawan duba mata buɗewar farjinta (multiple vaginal examination-VE).

2. Aikin tiyatar cire jariri (caesarian section-CS): Matan da aka yi wa tiyatar CS sun fi kowa hatsarin kamuwa da endometritis, duk da kasancewar kayan aikin da kuma ɗakin tiyatar masu matuƙar tsabta ne. Hakan yana da nasaba da tsanin yawa, naci, da kankantar bacteria ɗin ne.

3. Ayyukan tiyatar da suka shafi farji da marar mace (gynaecological procedures): Waɗannan sun ƙunshi wankin ciki (dilation and evacuation), aikin duba mahaifa (hysteroscopy), ɗaukar wani abu daga cikin mahaifa domin yin awon wata cuta (endometrial biopsy). Ƙwayoyin cutar bacteria za su iya shigar mahaifa a lokacin waɗannan ayyukan.

4. Cututtukan da ake ɗauka a wajen jima’i (sexually transmitted diseases – STDs): Waɗannan sun ƙunshi chlamydia, gonorrhea, staphylococcus, da sauransu. Duk suna iya haifar da endometritis idan suka shiga mahaifa.

ALAMUNSA (SYMPTOMS)

Alamun endometritis su ne:

1. Zubar ruwan da mace ba ta saba gani ba daga gabanta (abnormal vaginal discharge): Ruwan zai iya kasancewa mai wari ko ƙarni, sa’annan mai launin ruwan ƙwai (yellowish) ko ruwan ganye (greenish).

2. Ciwon mara (pelvic pain): Mace mai matsalar endometritis za ta riƙa fuskantar ciwon mara mai tsanani, ko dai mai daɗewa bai bari ba ko kuma mai zuwa ya tafi.

3. Zazzaɓi da jin sanyi (fever and chills): Shi ma zai iya zamowa mai tsanani, sa’annan mai zuwa ya tafi ko mai daɗewa.

4. Jin zafin fitsari ko yawan yin fitsari (dysuria or polyuria): Shi ma zai iya zama mai zuwa ya tafi ko mai daɗewa.

5. Zubar jini mai yawa lokacin al’ada ko rashin tsayayyar al’ada (heavy or irregular menstrual bleeding): Shi ma zai iya zama mai zuwa ya tafi ko kuma mai daɗewa.

TASIRINSA A JIKIN MACE (EFFECTS)

Idan ba a magance endometritis ba, zai iya haifar da:

1. Rashin haihuwa (infertility): Hakan zai faru ne sakamakon raunana da kuma lalata halittun mara na haihuwa.

2. Taruwar ruwan gunya a cikin mara (pelvic absess): Zai iya haifar da gyambo mai tara ruwan gunya a cikin mahaifa.

3. Kumburin dukkan jiki (sepsis): Hakan zai iya faruwa ne sakamakon yaɗuwar ƙwayoyin cuta a dukkan sassan jiki ta hanyar jijiyoyin jini.

HANYOYIN RIGAKAFI (PREVENTION)

Za a iya rigakafin kamuwa da endometritis ta hanyar:

1. Inganta tsabta a lokacin karɓar haihuwa, da lokacin yin tiyatar mahaifa a marar mace, domin kaucewa yaɗuwar ƙwayoyin cuta.

2. Tsabtace kayan ayyukan tiyata yadda ya kamata.

3. Tabbatar da cewa ma’aurata ba su ɗauke da cututtukan da ake ɗauka a wajen jima’i.

MAGANI (TREATMENT)

Hanyar magance endometritis ita ce zuwa asibiti domin likita ya yi aune-aune kuma ya ɗora mace a kan maganin antibiotics da ya dace. Idan abin ya ta’azzara, to, sai an kwantar da ita.

Don karanta Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza danna nan
Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceHalin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)
Labarin na GabaRataye Na 1: Waƙar ‘Yar Maye Ta Ahmad Tijjani Gandu