Cikakken bayanin ciwon sanyi daga likitan Asibitin Murtala Muhammad Special Hospital, Kano. Dr Adam Bala Husaini
Mutane da yawa, musamman mata, suna fama da yawan fitar da ruwa daga al’aurarsu. Wannan fitar ruwan yana iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ko rashin lafiya ba. Mata sun fi yawan samun kansu a wannan yanayi na fitar ruwa daga mafitsararsu fiye da maza. Wannan bayanin da zan yi, zan fi karkata a kan mata.
Yanayin yadda Allah (SWT) ya yi cikin al’aurar mace shi ne, ya kasance a jiƙe (mai danshi-danshi) a kowane lokaci. Ruwan da yake jiƙa a gaban mace yana fitawo ne daga wasu ɓangarori daban-daban da suke cikin gaban nata. Yawan ruwa yana iya ƙaruwa, raguwa ko kuma yana ɗauke gaba ɗaya. Zan yi bayani a kan ƙaruwar ruwa.
Wannan zubar ruwa ana kiransa “vaginal discharge” a likitance. Hausawa suna kiransa da “ciwon sanyi”, wasu kuma suna kiransa da “toilet infection (ma’ana, cutar da ake ɗauka a banɗaki maras tsafta)”. Ya kamata a sani cewa, har yanzu, a likitance, ba a tabbatar da cewa yin amfani da banɗaki marar tsafta yana ɗaya daga cikin hanyar da ake kamuwa da wannan cutar zubar da ruwan ba, amma dai ana zargin hakan, kuma ya kamata a yawaita tsaftace banɗaki.
ME YAKE JANYO YAWAN ZUBAR DA RUWAN
Kamar yadda na faɗa a baya, shi yawan zubar da ruwan zai iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ba.
Abubuwan da suke janyo zubar da ruwa na cuta sun haɗa da:
1. Juna biyu (ciki): Amma fa wani lokacin, juna biyu yana iya janyo zubar ruwa na cuta.
2. Yin amfani da ƙwayoyin tsarin iyali.
3. Lokacin jinin al’ada
Abubuwan da suke janyo zubar ruwa na cuta sun haɗa da:
1. Shan magunguna barkatai, musamman waɗanda ake kira da Antibiotics ko Steroid da sauran su.
2. Cututtuka a jiki kamar Diabetes (ciwon suga), HIV, Cancer da sauransu
3. Juna biyu (ciki): yana iya janyo zubar ruwa na rashin lafiya da kuma wanda ba na rashin lafiya ba.
4. Saduwa da wanda yake ɗauke da cutar: namiji zai iya dauka daga wurin mace, sannan mace ma za ta iya dauka daga wurin namiji
5. Zinace-zinace
6. Yawan wanke cikin gaba da wani sinadari (vaginal douching)
7. Masan tangaran (toilet seats): musamman idan wadda take dauke da cutar ta yi amfani da shi kuma ba ta wanke masan ba. Amma fa har yanzu ba a tabbatar da wannan hanyar ba.
Idan mace tana da, ko kuma, tana aikata ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan, to za ta iya kamuwa da wannan cuta ta zubar da ruwa.
YADDA AKE GANE ZUBAR RUWA NA CUTA
1. Idan ruwan yana da ɗaya daga cikin waɗannan siffofin:
• Ya kasance yana Wari ko ƙarni
• Launinsa ya kasance ruwan ɗorawa (yellow) ko ruwan toka ko kuma kore.
• Yanayinsa ya kasance kamar dusar awara ko kuma kamar zare
2. Kaikayin gaba
3. Jin zafi lokacin saduwa (jima’i)
HANYAR KARIYA DAGA KAMUWA DAGA WANNAN CUTA
1. A daina amfani da magunguna barkatai, ba tare da shawarar likita ba, musamman waɗanda ake kira da antibiotics da kuma steroid.
2. A ƙauracewa zinace-zinace
3. A daina tura ko kuma zura wani abu a cikin gaba (al’aura)
4. Wadda take da cutar, ta je ta nemi magani a asibiti saboda ka da ta shafawa wani ko wata.
KAMMALAWA
Zubar ruwa daga gaban mace yana damun mata kwarai da gaske, amma ba kowanne ba ne yake na cuta ba. Idan na cutar ne kuma, ana iya warkewa idan an sha magani. Kuma har yanzu, a likitance, ba a tabbatar da cewa ana ɗaukar cutar a banɗaki ba.
Allah ya ƙara mana lafiya da zama lafiya da ilmi mai amfani.
Allah shi ne mafi sani.
Za ku iya turawa da tambayarku ta hanyar wajen tura sako dake ƙasan rubutun nan ko kuma danna koren rubutun nan
Dr. Adam Bala Husaini
Murtala Muhammad Spacial Hospital, kano