khairatu.shehu
Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi suna da illoli masu ɗimbin yawa ga mashayansu. Wasu daga cikin waɗanṇan illoli kan shafi dangin mashayan da ma al’umma baki ɗaya. Masu shan ƙwayoyi ko kayan da suke sa su maye suna fuskantar matsaloli iri-iri. Misalin wasu daga ciki su ne:
- Rashin tsayar da ibada (Bauta wa Allah)
- Gushewar hankali
- Ɗaukar cututtuka
- Shiga mummunan hali
- Mummunar kama
- Aukar da fyaɗe
- Shiga haɗari
- Yin sata
- Yin fashi
- Kura daga makaranta
- Rasa aiki
- Shiga ƙungiyoyin asiri
- Rasa rayuwa
- Yawan haɗura a kan abubuwan hawa
- Mutuwar fuju’a (mutuwar fad-daya)
- Mutuwar aure da sauransu.
In muka ɗauki batun mutuwar aure da shaye-shayen abubuwan sa maye suke haifarwa, za mu tabbatar da hakan babbar illa ce in muka karanta waɗannan labarai guda biyu da suka faru a wasu gidajen ma’aurata:
1. Wata matar aure ce wadda take shaye-shaye amma mijinta bai sani ba, kullum sai ta sha wani magani ta yi ta barci, amma shi mijinta bai gane ba cewa maganin maye ne, kullum ya same ta tana barci sai ta ce ai mura ce ta yi mata babban kamu. In kuma ya ce a kai ta asibiti sai ta ce a a, ai tana samun sauƙi, ko kuma ta ce ai likitoci ne suke cewa mai mura ya dinga samun barci shi ne maganin mura.
Da abu ya yi nisa miji ya ga barci ya ƙi ƙarewa, sai ya fara damuwa. Da dubu ta cika sai wata rana dalili ya kai shi duba ƙarƙashin kujeru, nan fa ya ga tarin maganin mura da tari turmis, a ranar ne ya gane cewa maganin nan ba don mura take sha ba, dọn maye kawai take shan sa.
Da aka matsa bincike sai da aka gano wasu kwalaye da kwalabe a cikin ma’ajiyar tufafinsu. Ana cikin haka kuma sai mai kantin sayar da magani na unguwarsu ya turo a ba shi kuɗin maganin da matar take aikawa tana karɓowa bashi. Wannan shaye-shaye ne sanadiyyar mutuwar auren.
2. Shi kuma wani ango da aka yi masa rufa-rufa ya auri ‘yar maye, kullum gidansa cike da ‘yan mata, kuma abin da ke kawo su shi ne su haɗu da amaryar su yi ta shaye- shayen ƙwayoyi da magungunan mura da tari da kuma tabar wiwi.
Kuma har faɗa ake yi a gidan nasa, wanda haka ya dami maƙobtansa suka gaya masa, shi kuma ya cewa matarsa ba ya son wannan tara ƙawaye da take yi. Kai abu dai ya ƙi daɗi kullum tashin hankali shi da matar, har dai aure ya rabu, an zo kwashe kaya ya ga kwalaben magungunan mura da na tari da kwalayen magunguna sun kai guda ɗari uku.
Bayan haka kuma, wasu daga cikin fasiƙai mata ko maza suna amfani da ire-iren waɗannan magunguna wajen juyar da hankalin ‘yan mata don su yi lalata da su, wato su yi zina da su ko maɗigo, ko masu yin luwaɗi su yi da su, musamman idan sun neme su cikin girma da arziki suka ƙi yarda, to sai su yi amfani da waɗannan magunguna a cikin lemo ko wani abin sha, da zarar sun sha, shi ke nan sai su sami damar yin abin da suke son yi da su.
Don karanta Wasu Wuraren da Aka fi Koyon Shan Kayan Maye danna nan
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu