Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

0
35

Akwai jita-jitar cewa an kammala gwaji ko kuma ana kan hanya wajen samar da allurar hana haihuwa ga maza. Wannan gaskiya ne cewa ana gudanar da bincike, amma har yanzu babu wata allura da aka amince da ita a duniya domin yin tazarar haihuwa ga maza.

Wasu daga cikin alluran da aka fi duba yiwuwar yin amfani da su, sun haɗa da:

1. Reversible Inhibition of Sperm Under Guidance (RISUG) a Indiya, wacce ta ƙunshi ɗura ruwan magani mai maiƙo a cikin bututun ajiyar maniyyi (injecting gel into vas deferens). Amma har yanzu wannan dabarar ba ta samu amincewa daga hukumomin lafiya na duniya ba.

2. Allurar sinadarin testosterone da progestin wacce take hana samar da ruwa da ‘ya’yan maniyyi. A shekarar 2016, wani bincike na hukumar kula da lafiya ta duniya (World Health Organization – WHO) ya dakatar da yin wannan gwajin saboda zai haifar illolin da suka haɗa da fushi, baƙin ciki, taɓin hankali, da matsalar ƙarancin sha’awa ga maza, illolin da suka fi na alluran tazarar haihuwa na mata muni.

MATAKAN SAMAR DA MAGANI (STAGES OF DRUG DEVELOPMENT)

Domin fahimtar dalilin da yasa ba a samu nasarar fitar da alluran tazarar haihuwa na maza ba, ya kamata a fahimci matakai guda shida waɗanda ake bi kafin a ƙirƙiro magani har ya fita kasuwa:

1. Gwajin yin amfani da maganin a cikin ɗakin gwaje-gwajen kimiyya da dabba (discovery and preclinical lab testing using guinea pigs) – Ana yin sa ne don a fahimci ingancinsa da yadda yake aiki, amma a jikin dabba.

2. Gwaji a mataki na farko (Phase I Trials) – A jikin mutane kaɗan, wato marasa yawa, don tabbatar da ingancinsa a kan lafiyar mutanen.

3. Gwaji a mataki na biyu (Phase II Trials) – Ana yin gwajin ne ga mutane masu buƙata don a duba inganci da illolinsa a jikinsu.

4. Gwaji a mataki na uku (Phase III Trials) – Gwaji mai faɗi ta hanyar ƙara yawan jama’ar da za a yi gwajin a kansu don tantance amfanin maganin da illolinsa a jikinsu.

5. Amincewa daga hukumomin lafiya (Regulatory review and approval) – Hukumomi, kamar NAFDAC a Nigeria ko FDA a America, za su bayar da sanarwar amincewa da maganin a hukumance, domin mutane su cigaba da yin amfani da shi.

6. Bibiya bayan an fara amfani da maganin (Post marketing surveillance) – Don cigaba da sa ido a kan illolinsa.

Yawancin alluran tazarar haihuwa na maza da ake ƙoƙarin ƙirƙirowa suna kasa samun nasarar gwajin ne tun a mataki na biyu ko na uku saboda mummunan sakamakon da suke nunawa ga lafiyar maza, ko rashin daidaiton sakamakon (inconsistent test results).

DALILIN DA YASA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA NA MATA SUKA FI DACEWA DA JIKIN MATAN (REASONS THAT FEMALE INJECTABLE.CONTRACEPTIVES REMAIN MORE SUITABLE)

1. Jikin mace ya fi sauƙin sarrafa sinadaran estrogen da progesterone, saboda tsarin al’ada na halittar jikin mace yana aiki da sinadaran estrogen da progesterone ɗin ne, wanda ake iya kwaikwayon su cikin sauƙi da magunguna. Allurar tazarar haihuwa ta mata tana hana mace yin ovulation cikin sauƙi da aminci, kuma illolinta sun daɗe ana yin nazari a kansu, kuma ana iya sarrafa su.

2. A jikin namiji kuwa, ana samar da miliyoyin ‘ya’yan maniyyi a kullum, waɗanda in har za a yi amfani da allurai na tazarar haihuwa domin rage yawansu, to, hakan yana nufin sai dai a dakatar da samar da su gaba ɗaya, wannan abu ne mai wahala da hatsari.

ILLOLIN DA ZA SU IYA BIYO BAYAN AMFANI DA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA GA NAMIJI (POTENTIAL REGRETS AND CONSEQUENCES OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

Idan aka gaggauta yin amfani da su ba tare da yin cikakken bincike ba, to, ana iya fuskantar matsaloli kamar:

1. Matsalar rashin haihuwa ta dindindin (permanent infertility) – Saboda hana samar da ‘ya’yan maniyyi na dogon lokaci yana iya lalata ƙwayar haihuwa har abada.

2. Taɓarɓarewar hankali da rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (mood disorders and hormonal imbalances) – Hakan yana iya haddasa damuwa, fushi da cututtukan zuciya.

3. Ƙarin hatsari ga dangantakar aure – Mace tana iya ɗaukan cewa an ɗauki matakin hana haihuwa alhali namiji yana fama da illoli ko ya manta. Daga nan sai ciki ya samu ba tare da an shirya masa ba.

Wani bincike da aka wallafa a “The Journal of Clinical Endocrinology & Metabolism” ya nuna cewa yin amfani da sinadaran testosterone da progestin yana iya aikin samar da tazarar haihuwa ga maza, amma yana haddasa hawan jini, lalacewar hanta, da hauhawar kitse (cholesterol).

SHAWARA GA YAN’UWANA MATA

Ya kamata mu kasance cikin shiri da fahimta. Duk da cewa alhakin yin tazarar haihuwa ya rataya ga maza suma, yana da muhimmanci mu san cewa jikin mace ne yafi dacewa da irin waɗannan magunguna, tunda an ɗauki dogon lokaci ana yin nazarin su kuma an riga an tabbatar da ingancinsu.

Idan aka gaggauta yin amfani da alluran tazarar haihuwa na maza ba tare da cikakken bincike da tabbatar da ingancinsu ba, to, duniya za ta yi nadama kamar yadda aka yi da wasu magunguna a tarihi.

Har zuwa lokacin da aka samu cikakken gwaji da tabbatar da ingancinsu, alluran tazarar haihuwa na mata su ne mafi aminci da sahihanci.

Danna nan don karanta Rashin Kawowar Mace A Lokacin Jima’i (ANORGASMIA)

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceIllolin Shaye-Shaye
Labarin na GabaKumburin Mahaifa Mai Sanya Zubar Jini (ENDOMETRITIS)