Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya 1st August 2025

0
26

Aminu Bashir

Huɗubar 07/02/1447H 01/08/2025M

Mai huɗuba: Sheikh Dr. Yasir Ibn Rashid Addausari

Mai fassara: Malam Salisu Alhaji Abdullahi

Huɗuba ta farko:
Dukkan yabo tabbata ga Allah, Wanda Ya koyar da alƙalami. Ya koyar da mutum abin da bai sani ba. Muna gode Masa bisa ni’imominSa masu bibiyar juna, da baiwarwakinSa waɗanda ba a iya ƙirga su ko a ƙididdige su. Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, Ya kewaye dukkan komai da iliminSa, kuma Ya sanya iyaka ga kowane abu.

Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, mafi alherin wanda ya bi tafarkin shiriya, kuma ya gargaɗi al’umma game da bin hanyoyin halaka.
Tsira da amincin Ubangijina su tabbata a gare shi, da Alayensa da Sahabbansa ma’abota hankula, da Tabi’ai da waɗanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah matuƙar tsoronSa, kuma ku hararo kulawarSa gare ku a sarari da yayin ganawa, kuma kada rayuwar duniya ta ruɗe ku.

Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: (To, amma duk wanda ya yi ɗagawa () Kuma ya fifita rayuwar duniya () To lallai wutar Jahimu ita ce makoma () Kuma duk wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Ubangijinsa, kuma ya hana zuciya bin abin da take so () To lallai Aljanna ita ce makoma).

Ya ku mutane:
A zamanin nan namu, bil’adama na fuskantar cigaba na ban mamaki ta fuskar rayuwa, da bunƙasa ta musamman a fagage na fasaha da na’urori masu ƙwaƙwalwa, da kafafen sadarwa na dijital, da su ne sadarwa ta sauƙaƙa, kuma nesa ta zo kusa, kuma aka taƙaita lokuta, kuma aka aiwatar da ayyuka, aka kuma inganta hidindimu, kuma aka sauƙaƙa isa ga ilimi ta kafafen zamani, don haka, sai fasahar zamani ta zama wani ɓangare da ba zai iya rabuwa da rayuwarmu ba.

Kuma idan al’ummu suna yin gasa a fagen fasaha, to lallai ƙasarmu mai albarka ta bambanta da hangen nesanta, kuma ta yi fice a matakan da ta ɗauka, sai ta zama jagora a wannan fanni, tana ribatar fannin fasaha kuma tana amfani da ita wurin hidimtawa al’umma da ɗan’adam, har ta zama abin kwaikwayo da ake yabawa kuma ake koyi da ita a cikin wani yanayi mai ban sha’awa da ke tabbatar da matsayinta a mataki na duniya a fannonin fasahohin zamani masu zurfi.

Kuma haƙiƙa ƙasarmu ta tabbatar da cewa cigaba ba ya cin karo da ɗabi’u na ƙwarai, kuma ba ya saɓa wa al’adu, bari-dai, yana gina su ne kuma yana dogaro da su, sai ƙasar ta daukaka ba tare da ta manta da tushenta ba, kuma ta cigaba ba tare da ta yi watsi da tabbatattun al’adunta ba.

Madalla da wannan a matsayin wata ni’ima daga Ubangiji, kuma kyauta daga Allah, wadda take wajabta yabo da godiya, don haka, dukkan yabo ya tabbata ga Allah da Ya hore mana waɗannan hanyoyi, kuma Ya buɗe mana kofofin alheri da sauƙi, kuma Ya datar da jagororimmu shiryayyu zuwa ga amfani da su da kuma inganta su.

Ya ku bayin Allah
Kuma idan har wannan ni’ima na daga cikin manyan ni’imomi, kuma na daga alamomin samun rinjaye a wannan zamani, to lallai ita ni’ima idan aka sanya ta a inda bai dace ba, sai ta koma azaba da bala’i.

Kuma a yayin da fasahar zamani take rasa alƙiblarta, kuma aka rasa wayewar addini tattare da masu amfani da ita, to a wannan lokaci sai na’urori su koma tarko, hanyoyin kuma su koma ababen da suke zamarwa, daga nan ne wata cuta da aka jarrabi wasu mutane da ita ta bayyana, duk da bambancin shekarunsu da wayewarsu da jinsinsu, wannan kuwa ita ce cutar ɗamfaruwar zuciya da kafafen sadarwa na zamani, da nutsewa a cikin duniyar yanar gizo da ba ta da iyaka, har ma a wajen wasu wayoyi suka sauya daga kasancewarsu hanyoyin sada zumunci zuwa hanyoyin kaɗaici da yanke alaƙa.

Sai ka ga mutum cikin jama’a tamkar gangar jiki ne da babu zuciya da hankali a tare da shi; yana kai-komo tsakanin kafafen sadarwa, yana shiga manhajoji sai shafukan yanar gizo su riƙa fizgar sa, kuma yana kallon bidiyoyi masu yawa, bai ma san abin da yake nema ba, kuma bai samu wani abu mai amfani ba.

Wannan wata fitina ce mai hallakarwa, mutum yana rayuwa a cikinta cikin ruɗani ba tare da wasu manufofi ba; kamar ƙaramin kwale-kwale ne a tsakiyar teku ba tare da na’urar gane hanya ko abin tuƙa shi ba, kuma kamar matafiya ne wanda bai isa inda zai je ba kuma ga shi ya halakar da abar hawansa. Tir da shekaru da ke wucewa kamar gajimare, kuma suke ƙarewa ba tare da wani guzuri don ranar hisabi ba.

An karɓo daga Ibn Abbas Allah ya ƙara musu yarda ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Akwai wasu ni’imomi guda biyu da ake yi wa yawancin mutane kamunga a cikinsu, su ne lafiya da lokaci). Bukhari ne ya rawaito shi.
Ibnul-Ƙayyim Allah Ya masa rahama ya ce: “ɓata lokaci ya fi tsanani fiye da mutuwa; domin mutuwa tana raba ka ne da duniya, amma ɓata lokaci yana raba ka ne da Allah da kuma rabauta a lahira”

Ya ku Musulmi:
Lallai zuciya idan ba a shagaltar da ita da ayyukan ɗa’a ba, to sai ta shagaltu da saɓo, musamman ma a wannan zamanin na kafafen sadarwa na zamani, da yawan bibiyar hotuna da labaran yau da kullum, da ƙawata shafuka, sai ka ga mutum ya nutse cikin ruɗanin da ba shi da ƙarshe, da burace-burace waɗanda ba sa ƙarewa, kuma abin da ya fi wannan muni shi ne wanda yake rayuwarsa cikin bibiyar rayuwar wasu kuma yake ɓata lokutansa, kuma yake sa ido a rayuwar mutane amma yake manta tasa rayuwar.

Kuma haƙiƙa lallai gargaɗi ya zo daga shari’a game da irin wannan shagaltuwa abar zargi, kuma ɗabi’a mai guba, wadda ke lalata wa mutum addininsa, kuma ta ɓata masa lokacinsa. An karɓo daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Yana daga cikin alamomin kyawun Musuluncin mutum, barin abin da bai shafe shi ba” Tirmizi ne ya rawaito shi.

Kuma Abubakar Allah ya ƙara masa yarda ya ce: “Lallai wasu mutane sun sadaukar da rayuwarsu ga wasunsu, kuma sun manta da kawunansu, saboda haka, ina hana ku ku zamto kamar su”.

Kuma ya kamata a sani, ya ku bayin Allah, cewa: Lallai kafafen sada zumunta na zamani a mafi yawan lokuta sun zama matattarar rayuwa ta ƙarya, kuma wajen gasa marar amfani, sai cutar hassada da ƙiyayya ta shiga zukatan wasu, kuma fushi da ƙin juna ya yi naso a zukatansu, sai godiya da yabo ga Allah bisa nani’imominSa da baiwarwakinSa su yi ƙaranci.

Kuma daga cikin sharrori da masifu akwai shafukan ƙarya na bogi da ke fesa gubarsu cikin al’umma, kuma suke yaɗa fitintinu da ƙarairayi, suna ƙirƙirar maganganu da jita-jita, kuma suna fatawowi na ƙarya da sunan malunta, a cikin wasu shirye-shirye da aka ɗau nauyinsu, da kuma ɓatanci da ake yi da gangan, waɗanda ba sa la’akari da addini ko kyakkyawar ɗabi’a.

Abin mamaki baya ƙarewa game da wanda ke bibiyar irin waɗannan shafuka ba tare da tantancewa ba, yana gaggauta yaɗa abin da suka wallafa ba tare da jinkiri ba, kuma ba tare da komawa ga majiyoyin hukuma da amintattun tashoshi ba.
Allah Maɗaukaki Ya ce:

(Ya ku waɗanda kuka yi imani! Idan wani fasiki ya zo muku da wani labari, to ku yi bincike, don kada ku cuci mutane cikin rashin sani, sai ku wayi gari kuna masu nadama game da abin da kuka aikata)

Ya ku mutane,
Kuma akwai wata fitina da ke lalata zukata a lokutan kaɗaici, lokacin da mutum ya ke keɓancewa da wayarsa a wuraren da babu kowa, sai ya keta alfarmar addini, yana kallon haramtattun abubuwa, yana raina umarnin Allah, ba ya damuwa da abin da Allah Ya hana, yana mai manta irin cututtuka da annoba da irin waɗannan abubuwan kallo ke jawowa, da keta mutunci, da ɓata shekaru da lokuta, da kuma salwantar da kyawawan ayyuka.

An karɓo daga Sauban Allah Ya ƙara masa yarda, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Lallai ina sane da wasu mutane daga cikin al’ummata, za su zo a ranar alkiyama da kyawawan ayyuka masu girma kamar manyan duwatsun garin tihama farare, amma sai Allah Ya mayar da su ƙura abar sheƙewa)

Sauban ya ce: Ya Manzon Allah, ka siffanta mana su, ka fito mana da su fili mana, saboda kada ya zama muna cikinsu alhali ba mu sani ba, sai ya ce: (Lallai su ‘yan’uwanku ne kuma daga cikin danginku, kuma suna ibada a wani sashe na dare kamar yadda kuke yi, sai dai su wasu irin mutane ne waɗanda idan suka keɓe da dokokin Allah sai su keta su) Ibn Majah ne ya rawaito shi.

Ya ku bayin Allah, Allah Ya mana albarka cikin Alƙur’ani mai girma, kuma Ya amfanar da mu abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima, ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu, don haka ku nemi gafaraSa, lallai Shi Mai yawan gafara ne da jinƙai.

Huɗuba Ta Biyu

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya shiryar da mu zuwa ga hanyar samun rabo, kuma Ya nusantar da mu zuwa ga hanyar tsira, kuma Ya saukar da haske da rahama a cikin littafinSa, kuma Ya sanya shiriya da hikima a cikin sunnar AnnabinSa, kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba shi abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, tsira da aminci da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa da Sahabbansa da wanda ya bi tafarkinsa zuwa ranar ƙarshe.

Bayan haka, Ya ku ‘yan’uwa Muminai!
Lallai daga cikin mafiya girman ni’imomin Allah akwai cewa mutum ya faɗaku game da tasgaronsa kafin ƙurewar lokaci, kuma ya lura da zuciyarsa kafin rufi ya mamaye ta, sau dayawa muna buƙatuwa ga maganin wannan alaƙa mai cutarwar a wannan duniya ta dijital da fasaha, hakan zai kasance ne ta hanyar ɗaga kafa, wanda da shi ne za mu daƙile guguwar amfani da waɗannan na’urori, ba wai don mu ƙaurace wa rayuwa ba, bari dai, sai don mu sabunta daidaito game da tasgaro da aka samu a rayuwarmu.

Ibnul Jauziy ya ce: Ban taɓa ganin abin da ya fi amfani ga zuciya ba, fiye da ƙauracewar da mutum zai gano aibobinsa kuma ya riƙa nazari cikin makomar al’amuransa).

Ya ku bayin Allah!
Lallai addininmu addini ne na tsaka-tsaki da daidaito, don haka, ku ware wa ibada lokaci, haka rai ma a ba shi nasa kason, kuma iyalai ma a ba su rabonsu, haƙiƙa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gaskata maganar Salman ga Abu Darda’i Allah Ya ƙara musu yarda cewa: (Lallai Ubangijinka Yana da hakki a kanka, kuma kai kanka kana da hakki a kanka, kuma iyalanka suna da hakki a kanka, don haka ka ba wa duk wani ma’abocin hakki hakkinsa) Bukhari ne ya rawaito shi.

Kuma ku sani Allah Ya muku rahama cewa: Lallai fasaha ni’ima ce mai girma idan aka fuskantar da ita zuwa ga alheri kuma aka dabaibaye ta da dabaibayin shari’a da hikima, don haka ita ba tsagwaron sharri ba ce, kuma ba abar ƙyama ba ce a asalinta, bari dai, ita kamar takobi ne mai kaifi biyu, saboda haka ka zamto wanda yake amfani ba wanda ake amfani da shi ba, kuma na’urarka ta kasance hadima ba shugaba ba, kuma gada zuwa ga ɗa’a ba ramin da zai kai ka zuwa ga saɓo ba, kuma ta kasance tsani na samun ilimi da fahimta ba filin wasa na son zuciya da jahilci ba.

Saboda haka ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah, kuma ku yi riƙo da sabbuban tsira, kuma ku riƙa tunawa koda yaushe cewa lallai za a tsayar da ku a gaban Ubangijinku, kuma za a tambaye ku game da gaɓɓanku, haƙiƙa Allah Mai girma da ɗaukaka Ya ce: (Lallai ji da gani da kuma tunani, duk waɗannan sun zama abin tambaya ne game da su).

Don haka, ku ribaci shekarunku kuma ku mori lokutanku, domin duk wanda yaƙininsa ya gaskata, to zai yi da gaske kuma zai yi ƙoƙari, kuma duk wanda burinsa ya taƙaita, to zai yi guziri da tanadi, ya zo cikin Sahihu Muslim daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ka yi kwaɗayi kan abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah kada ka yi ƙasa a gwiwa).

Ya ku bayin Allah,
Wannan kenan,
Kuma ku yi salati da sallama ga wanda aka aiko shi da hikima da kuma shiriya, mafi alheri cikin halittu kuma mafi darajar wanda ya taka ƙasa, kamar yadda Ubangijinku Mai girma da ɗaukaka Ya umurce ku da hakan cewa: (Lallai Allah da Mala’ikunSa suna yi wa Annabi salati, ya ku waɗanda kuka yi imani, ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa).

Ya Allah Ka yi salati ga Annabi Muhammad Manzo amintacce, da Alayen Annabi Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga Annabi Ibrahim da Alayen Annabi Ibrahim cikin talikai, lallai Kai Abin yabo ne Mai girma, kuma Ka yi albarka ga Annabi Muhammad da Alayen Annabi Muhammad kamar yadda Ka yi albarka ga Annabi Ibrahim da Alayen Annabi Ibrahim cikin talikai lallai Kai Abin yabo ne Mai girma.

Ya Allah Ka yarda da Halifofi huɗu shiryayyu, jagorori masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, ya Allah Ka yarda da Sahabbai baki-ɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, Ka haɗa da mu cikin baiwarKa da karamcinka da kyautatawarKa ya Mafi karamcin masu karamci.
Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmi, Ka kare shingen addini, Ka sanya wannan ƙasa ta kasance mai aminci da lumana da yalwa, tare da sauran ƙasashen Musulmi ya Ubangijin talikai.

Ya Allah muna roƙon Ka dace da gamonkatar ga shugabanmu kuma majiɓincin al’amarinmu hadimin Masallatai biyu masu alfarma da magajinsa amintacce, kuma Ka saka musu da mafi alherin sakamako game da ƙasa da mutane da Musulunci da Musulmi. Ya Allah Ka taimaki jami’an tsaronmu da sojojinmu a kan iyakoki, Ka kare su da kariyarKa, Ka jiɓince su da kulawarKa ya Ubangijin talikai.

Ya Allah Ka yaye damuwar waɗanda suke cikin damuwa, Ka kwaranye baƙin cikin masu baƙin ciki, Ka biya bashin waɗanda ake bi bashi, Ka warkar da marasa lafiyarmu da na sauran Musulmi. Ya Allah Ka jiƙan mamatanmu da na sauran Musulmi, Ka taimaki masu rauna daga cikin Musulmi a kowane wuri, da kuma ƙasar Falasɗinu, ya Allah Ka ba su waraka daga dukkan damuwa, da mafita daga dukkan ƙunci, da kuɓuta daga dukkan bala’i, ya Allah Ka warkar da masu rauninsu, Ka tsare jinanensu, Ka tabbatar da zukatansu, ya Allah Ka kare Masallacin Ƙudus, Ka sanya shi ya zamto mai ɗaukaka da buwaya har zuwa ranar Alƙiyama.

Ya ku bayin Allah
Lallai Allah Yana umurni da yin adalci da kyautatawa da kuma bai wa makusanta taimako, kuma Yana hana alfasha da mummunan aiki da zalunci, Yana gargaɗin ku don ku wa’azantu, don haka ku ambaci Allah Maɗaukaki mai girma, Shi ma Zai ambace ku, kuma ambaton Allah shi ne abin da ya fi girma, kuma Allah yana sane da abin da kuke aikatawa.

Don karanta Yadda Falalar Karanta Ayatul Kursiyyi Ya Ke danna nan

Edita@rumasau-kallamu

 

labarin da ya wuceFarfajiyar Ƙasar Hausa Jiya Da Yau
Labarin na GabaHanyoyin Zamantakewar Hausawa