Afwan yau jikin kamar wani mai laulayi
Haka na yini ta har daren Allah haka na yi
Ban aika ba babu wanda kuma nace ya yi
Shi ai so fa ba abin dama ba ya yi.
Ita waccen tana faɗin ni ce taka ɗai
‘Ƴar dangi na faɗin ba mai min kwaɗai
Abba fa nawa ne ki jini na ni ni kaɗai
Gogan naku ko yana kwance kishingiɗe
Babu fa wanda za ya ce bai son nasa kam
Sai dai in ya zam yana ɓoyewa kurum
Ba a makara idan handset kwai alarm
Babu ruwansa sai ya yo ma ƙara daram.
Maganar gaskiya fa waccen na riƙa sila
Tun da kamar muna ƙanana fa ya ‘ƴan shila
Ba ko hantara bare zancen matsala
Tun ma kan tsayinta ɗinnan fa ya kammala
Haka siddan ki zo ki ce sai min banƙara
Daga haddar izawaƙa kika nufi baƙƙara
Kika bar nan kika wuce ƙarshen saɗɗara
Fazuƙu falan-nazidkum ki yi hattara.
Maganar gaskiya kamata fa ki hanƙura
Tinda gidanku na sani ba mai takura
Ba mai ji kama da kamun da ta kumbura
Ko mai na ci ya beban da ya ke bara.
Kin ga fa ni gidanmu ni ne ɗai salimi
Kar fa ki sa mutan gidajenmu a zullumi
Kar ki bari na dinga jin zafi ba gumi
Sai dai in jikin ga nau to da akwai shimi
Kin ga idan akwai rabo wataƙil za ya zo
Ko duk duniya su taru su yo dandazo
In dai Rabbi ya hana to dai ba ya zo
Ba na son kira a ce min to je ka zo.
Tabbas na sani kina so na Mahira
Kuma ni ma fa da hakan take ya Ɗahira
Amma yanzu kam a ƙyale ni na tsahira
Ɗandagus da shi da Ɗanbello Jira! Jira!!
Afwan ni fa ba na yin ƙusƙus duk dare
In ka ganni kan icen kuka maza ɗare
Ba akuya kana sannan kuma ba kare
Sai ‘ƴa’ƴan fire a mota fal maƙare.
Afwan duk da na sani ba kya jin bari
Mai suna Karima ce aka cewa Kari
Mai son shi a kai shi police bai jin bari
Sai ya je shi dole wata ƙila da ma mari.
Allah ya sani fa ba so ne ba na yi
Da harawa da garera a haɗa da ƙamayi
Duk akuyar da tai ta kushe haka so ta yi
Tattauna shi gunta ko ba ranar ta yi.
Domin ni fa ɗan titis nake sam ba nawi
Ba Li’irab bare a ce mini annahawi
Shi farce yana da aiki ran ƙaiƙayi
Allah dai ya sa abin da ake so na yi.
Abban Marke
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu