Daga Cikin Addu’o’in Roƙon Ruwa

0
31

“Allaahummasƙinaa gaisan mugiisan marii’an marii’a, naafi’an gaira dhaarrin, aajilan gaira aajilin”.
{Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama mai yaye tsanani, mai daɗi, mai ni’ima, mai amfani ba mai cutarwa ba, da gaggawa ba da jinkiri ba}.
“Allaahumma agisnaa, “Allaahumma agisnaa, “Allaahumma agisnaa”.
{Ya Allah! Ka yi mana agaji (da ruwan sama). Ya Allah! Ka yi mana agaji. Ya Allah! Ka yi mana agaji}.
“Allaahummasƙi ibaadaka wabahaa’imaka, wanshur rahmataka wa ahyi baladakal mayyiti”.
{Ya Allah! Ka shayar da bayinka, da dabbobinka; kuma ka yaɗa Rahamarka, ka rayar da ƙeƙasasshiyar ƙasarka}.

Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a A Yayin Da Ruwan Sama Yake Sauka danna nan.

Wannan bayanin an ciro sh ine daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunnah wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAddu’a A Yayin Da Ake Iska
Labarin na GabaAddu’a Bayan An Gama Cin Abinci
Suna na Isa Uba Chamo masanin na'ura mai kwakwalwa da ilimin addini da harshen Hausa da kuma ilimin halaiyar dan adam, kuma nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe