Ciwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo

0
64

Ciwo ne sakamakon harbin ƙwayar cuta musamman bairos da bakteriya,harbin ƙwayar cutar na faruwa ne idan ƙwayar cutar ta samu kafar shiga yatsa bayan fatar yatsa ko farce sun samu rauni,miki,yanka,tsaga ko kurjewa.

Alamun Ciwon Sun Haɗa Da:
  • Ciwo,zogi,raɗaɗi da ƙaiƙayi.
  • Kumburi,kumewa tare da bayyanar ja a fatar yatsan.
  • Ɗurar ruwa ko jan ruwa.
  • Fitar ruwa ko fitar ɗiwa.

Da zarar an ji waɗannan alamu a garzaya domin ganin likita,sai dai wani abin lura shi ne bayan ciwon ya warke sai kuma gaɓoɓin yatsan su ƙale ko su ƙage ko kuma su riƙe,saboda haka,idan aka yi buris da yatsan sai ya nakasa.

Da zarar ciwon yatsan ya warke likitan fisiyo zai taimaka wajen dawo da aikin gaɓoɓin yatsan domin kada ya nakasa,idan aka yi buris da yatsan har aka bari jijiyoyin tantanin yatsan suka gama riƙewa hakan na iya tilasta yin tiyata domin sakin jijiyoyin tantanin,domin kauce wa nakasar yatsa  bayan wannan ciwo,tuntuɓi likitan fisiyo da wuri.

Domin karanta Alamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu Danna nan

labarin da ya wuceAlamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu
Labarin na GabaNau’in Jinkiri Guda Uku Da Suke Sabbaba Mace-macen Mata Masu Naƙuda a Nigeria