Ciwan Hanta {Hepatitis}

0
46

Shi dai ciwon hanta:- Wasu kwayoyin cutar virus ne ke shiga cikin hanta ta hanyar jini su kawo irin wannan ciwo.

Akwai Nau’insu Har Kusan Kala Shida:
  • Akwai ajin  A 
  • Akwai  B 
  • Akwai  C 
  • Da  D 
  • Da  E 
  • Da kuma  F. 

Amma an fi ganin nau’i uku na farko wato A, B, da C,a cikin wadannan ukun ma an fi ganin nau’in ko ajin B,wanda kuma shi ne ya fi yi wa hanta illa.,ya kamata a san banda wadannan rukunin kwayoyin cuta akwai sauran abubuwan da suke kashe hanta, kamar barasa da burkutu da shan miyagun ƙwayoyi da shan wasu guba irin waɗanda mahaka kuza suke samu kamar gubar ƙarafuna irinsu dalma da sauransu.

Idan kunaso ku karanta Larurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za’a Magance ku danna nan

Rukunin B&C

Nau’in da za muyi magana akai sune wadanda ƙwayoyin cutar rukunin B da C ke kawowa, hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa hanyoyin da ake daukar wadannan kwayoyin cuta masu nakasa hanta kusan hanyoyi daya ne da ake daukar cutar ƙanjamau,ayanzu haka an fi samun mace-mace daga cututtukan hepatitis fiye da mace-macen cutar ƙanjamau saboda ba a samun magungunan ciwon hantar ba kamar yadda aka samar da na ƙanjamau ba,haka nan kuma saboda faɗakarwa da ake ta yi a kan ciwon na ƙanjamau din ana mantawa da na hepatitis,domin a yanzu mutane fiye da miliyan 1.5 ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hantar, amma masu ƙanjamau wajen miliyan 1.3 ke mutuwa a duk shekara. 

Haka kuma kusan kowa ya san cutar ƙanjamau amma da yawa ba su san ciwon kumburin hanta ba,shi ya sa da yawa mutane idan za su yi aure sai dai a yi gwajin ƙanjamau kawai ba a hadawa da na hepatitis,yawanci a wurin gwajin ba da jini kawai akan gano mutum yana dauke da cutar ba tunda sai ta yi shekara da shekaru mutum bai ma san yana dauke da kwayar cutar ba.

Hanyoyin da ake daukar kwayoyin sune 
  • Yayin saduwa daga mai dauke da kwayar zuwa wanda bai dauke da ita.
  • Sai kuma ta hanyar ƙarin jinin da ba a yi wa gwajin tantance ƙwayar cutar ba.
  • Sai kuma ta hanyar amfani da kayan kaifin da ba su da tsabta,kamar askar wanzamin da ba a gasa ba,amfani da rezar da mai ciwon ya yi amfani da ita,ko amfani da allurar da aka yi wa wani,maimakon sabuwa.
  • Sai ta hanyar cin abinci da cokali daya tare da mai cutar,ko ya gwaguiyi abu da baki ya baka kaima ka ɗora
  • Wata hanyar kuma ta daukar ciwon a yara ita ce ta wurin uwa mai ƙwayar cutar, yayin haihuwa ko yayin shayarwa.

Da yake ƙwayoyin cutar shiga cikin hanta suke ta yi barcinsu,da yawa masu dauke da ƙwayoyin ba sa jin wasu alamu tsawon shekaru sai ranar da suka farka suka fara cin hantar sa’annan alamu za su bayyana,wannan na faruwa ne kawai a kashi daya 1% cikin hudu na waɗanda ke dauke da ƙwayar,sauran kashi ukun ba za su taba nuna wata alama ba duk tsawon rayuwarsu,shi ya sa aka fi cewa masu dauke da ƙwayar su ƙwantar da hankalinsu domin zai wahala su nuna alamun,amma a wannan tsakanin ne masu ciwon ke yada ta musamman ga abokan zama na aure da kuma ’ya’yansu.

Domin karanta bayani akan Toshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki Danna nan

Alamomin Ciwon Hanta
  • Yawan zazzabi
  • Yawan ciwon ciki bangaren dama
  • Yawan tashin zuciya da rashin son cin abinci 
  • Yawan kasala
  • Idan tai tsamari akan iya ganin kumburi a fuska da ƙafafu
  • Yawan samun shawara,wato kadawar ido zuwa ruwan dorawa da sauran alamu da mutum zai ji dai cewa ba lafiya ba.

A daidai wannan lokaci ne dole a dauki matakin kashe ƙwayoyin cutar domin kada su nakasar da hantar gaba-daya,wanda babban abin da suke kawowa shi ne motsewar hanta ko ciwon daji na hanta,magunguna da alluran da ake amfani dasu aci karfin kwayoyin cutar kafin su kai ga illa suna da matukar tsada sosai,shi yasa mukan ce riga-kafi yafi magani.

Hanyoyin Kariya
  • Kamewa har sai an yi aure,masu auren ma su rike matansu kawai.
  • Tabbatar da an yi gwajin cutar ga wadanda suke shirin aure,da nuna wa juna takardar shaida kafin a daura auren. 
  • Tabbatarwa cewa jinin da za a kara wa mutum an gwada shi a asibiti an tabbatar ba ya dauke da kwayoyin cutar 
  • A wurin awon mata masu juna biyu ana auna wannan ciwon,idan an samu mace mai ƙwayar cutar ana daukar duk matakan da suka kamata wajen kare abin da take dauke da shi. 
  • A yanzu akwai alluran riga-kafin kamuwa daga wadannan ƙwayoyin wadanda aka sa a rika yi wa yara da zarar an haife su,sa’annan a watanni na biyu da na uku,akasin ƙwayar ƙanjamau wadda har yanzu ba a gano allurar riga-kafinta ba.
  • Ba yara kawai ba,har manya wadanda ke cikin hadarin kamuwa za a iya yi wa allurar riga-kafin,wadannan sun hada da ma’aikatan lafiya,musamman masu aiki a dakin gwajin jini,mata masu zaman kansu da mutanen da ke aiki cikin damara,a ma’aurata wadanda daya ke da kwayar cutar amma daya ba shi da shi,shi wanda ba ya dauke da kwayar cutar sai a yi masa riga-kafi.ana samun wadannan allurai a asibitocin da mata ke zuwa awo. 
  • A tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko a kona su da wutar lighter ko a wanke su da sinadarin bleach kafin a yi wa mutum amfani da su,sai dai idan sabuwa ce daga ledarta aka bare a gaban mutum,haka ma sirinji da reza,a rika tabbatarwa sababbi fil aka bare kafin amfani da su. 
  • Zuwa cibiyoyin gwaji na kyauta don sanin matsayin mutum na taimaka wa rage yada ciwon.

Domin karanta bayani akan Sanƙaran Bakin Mahaifa (Cervical cancer) Danna nan 

labarin da ya wuceSanƙaran Bakin Mahaifa (Cervical cancer)
Labarin na GabaMinene Fibroid? {Ƙarnin Mahaifa } Da Kuma Abubuwan Da Suke Kawosa