Buki A Bahaushen Tunani

0
16

Babahabu49

Gabatarwa
Buki wani abu ne da ke cikin tsofaffin al’adun mutane da, da wuya a tantance ranar da aka fara shi. A duniyar da muke ciki yau, babu al’ummar da ba ta da buki, kuma babu al’ummar da ta yi watsi da bukukuwan da ta gada kaka da kakanni.

A ra’ayinmu ɗaliban al’ada, buki ya leƙa duk wata gargajiya, wayewa, da ci gaban mutanen da ke aiwatar da shi. Don haka, cikin hada-hadar buki za a iya ƙyallaro wani abu daga tarihin mutanen da ke aiwatar da shi da kuma dangantakarsu da maƙwabtansu, masoyansu, magabtansu, baƙinsu, da magabantansu da mamaya bayansu. A tarihance, buki Mahdi ne mai dogon zamani. A la’adance, wandon roba ne daidai da kwankwason mutum na kowane zamani.

Kadadar Nazari

Ba dukkanin bukukuwan Bahaushe wannan ‘yar takarda za ta yi nazari ba. Takenta ya yi faɗi, ya yi tsawo, sosai, amma “tunanin Bahaushe” da aka kawo ya ɗan takura mata iyakokin nazarinta. Takardar ta yi garkuwa da “Sallar Gani” a Daura domin ta ƙyallaro Bahaushen tunani a kan buki.

Don haka, manufa ita ce a kalli Bahaushen buki tare da ƙyallaro Bahaushen tunani a kan faruwarsa, dalilansa, yaɗuwarsa da muhimmanci da ke tattare a ciki. Bahaushen tunani za a kalla a ciki, za a yi garkuwa da Sallar Gani a Daura da masarautun da ke mara mata baya domin ci gaba da wanzuwarta.

Ra’in Bincike

Yayin da aka nemi in ce wani abu kan Sallar Gani a Daura, na ga ba makawa sai na bi diddigin tarihin samuwarta. Na so in ji sunanta na fari gabanin ta kasance: “Salla”. Cikin kai da kawo na ga daidaitaccen tafarkin da ya kamata in daidaita wannan ɗan yunƙurin shi ne: “In babu ƙira me ya ci gawai”? Matuƙar maƙera bai ga gawayin da ya ajiye a maƙera ba, zai nemi yaransa da su zo su gaya masa wa ya yi ƙiri wurin?

Dalili kuwa shi ne, gawayi ba a cinsa, dabbobi ba sa ci, a can da ba a sayar da shi, in ba maƙera ba babu mai amfani da gawayi. To! In babu ƙira me ya ci shi? Na danganta wannan batu da cewa, a ko ina aka tarar da ana buki dole da dalili. Babu bukin da ake yi ba ya da tarihi, ba ya da mafari, ba ya da wata fa’ida ko da kuwa ɓoyayya ce.

Da an ga Bahaushe na gudanar da buki a ƙasarsa, babu shakka an yi irin sa gabanin ya yi. Haka kuma, idan an shiga taliyon bincikensa, za a gano a ina ya fito? Matuƙar babu hujja ta al’ada Bahaushe ba zai iya buki ba, dalilina kenan na cewa: “In babu ƙira me ya ci gawayi”? Me ya sa ƙasar Daura da Gumel da Haɗeja kawai ake gudanar da Sallar Gani? In babu ƙira me ya ci gawai?

Dabarun Bincike

Tattare da irin muhimmancin Sallar Gani a wuraren da ake gudanar da ita da tarihin garuruwan da ta yi ƙamari, ba a samu wani gawurtaccen aiki a kanta ba a rubuce da sunan bincike. Tilas na dogara ga bayanan baka da aka tsinta daga Sarakunan Daura, Gumel da Haɗeja ta bakin wasu jami’ai daga masarautunsu.

Haka kuma, na yi amfani da wasu abokan aikina da ɗalibaina na garuruwan da ake gudanar da bukukuwan, da ɗan abin da suka kalato daga bakunan kunne ya girmi kaka. Na sake lalubo taskokin adabin bakan Bahaushe domin kwakkwashe bayanai. Na tattaka da kaina na yi rangadi a Daura domin in ji ta bakin masu abu.

Da yake zamani riga ne, na ga ba a sa wa “Sallar Gani” rigar zamani ba, domin an neme ta ƙaura Wambai a intanet ba ta. Wannan ba ta hana aka sa hular zamani ta amfani da wayoyin hannu domin sadar da muryoyinmu na bincike a wuraren da dugadugan mai bincike ba su wada kai ba. Ta haka aka tsinci abin tsinta aka watsar da na bari.

Fashin Baƙin Fitilun Kalmomi

Taken wannan bincike shi ne: Buki a Bahaushen Tunani: (Duba Cikin Hada-hadar Sallar Gani a Ƙasar Hausa). A Bahushen tunani, buki wani taro ne na gangamin jama’a domin gudanar da wata hidima. Bahaushe shi ne wanda ba ya da wani harshe sai Hausa, ba ya bugun gaba da wata al’ada sai ta gargajiyar Bahaushe. A same shi uba da kaka da kakanni duk Hausawa ne cikon sunna ne makaho da waiwaya.

Tunani shi ne, abubuwan nazari da ke bayyana cikin adabi da harshe da al’adun mai tunanin, kuma su ne tunaninsa ko ya yarda ko ya ƙi, ƙaddara ta riga fata. Duba shi ne, tsura ido ga abin da aka sa gaba a kansa. Sallar Gani ita ce farfajiyar da ake so a duba. An danganta batun da “ƙasar Hausa” dalili kuwa shi ne, Daura ta shahara da Sallar Gani, kuma a Hausance Daura ita ce tushen Hausa, ita ce Hausa, ita ce ƙasar Hausa mai dalili a tarihi da tarihihin Bahaushe.

A tunanin wannan bincike “Sallar Gani” buki ce domin Daurawa da Haɗejawa da Gumawa suna ce da ita: Bukin Sallar Gani”. Ashe kalmar “Buki” wata babbar kafaɗa ce da wannan bincike zai dafa ya miƙe tsaye a gan shi, don haka fayyace ta ya zama dole.

Menene Buki?

A al’adance, gidan kowa ana buki, garin kowa ana buki, ƙasar kowa ana buki, a addinin kowa akwai buki, a matakan rayuwar kowa akwai buki. Samun taron mutane a buki bai da makawa kamar yadda hidimomi da hada-hada cikin cikin kowane buki ya zama suturar ƙawa ga bukin. Ƙamusun Bargery ya fassara buki da cewa:
(a) Feast, e.g, in celebration of a marriage or on naming day

(b) (bikin farar kaza balbela ba gayya ba ce) a relation or intimate friend needs no invitation in a feast

(c) at a feast given by a white hen the buff-backed heron would naturally attend without needing, waiting for, or expecting an invitation…

Fashin baƙin Bargery buki shi ne shagulgulan aure ko suna, kuma buki gayyatar abokan hulɗa da arziki ake yi. Ɗan uwan da bukin ya shafa ba sai an gayyace shi ba domin su ne masu gayyata. A tunanin Ingilishi a fassarar The New International Webster’s Comprehensie Dictionary of the English Language Deluxe Encyclopedic Edition ya ce:
Ceremony n. pl. (nies):

(1) A formal or symbolical act or observance, or a series of them, as on religious and state occasions.

(2) The doing of some formal act in the manner prescribed by authority or usage. The ceremonies at an ordinary inauguration, or coronation.

Da gangan na kawo fassarar “buki” ta Ingilishi domin tabbatar da cewa, buki al’adar duniya ce, ta ‘yan duniya, don a ci duniya, a more duniya. A nan, mun ga cewa buki harkar taro ce, yana kasancewa na al’ada ko addini ko ayyuka na gudanar da hukuma yadda ta shata a yi su. A taƙaice a wurin Bahaushe buki shi ne:

Taron masha’a da assha ko mu ce, taron dariya da gintse fuska. Yadda duk ya ksance akwai hidimomi da hada-hada a ciki. Ba a koyaushe yake gudana ba, amma a koyaushe buƙata ta taso, ko tarihi ya maimaita kansa, za a yi shi. Mai buki da ‘yan uwansa ke buki, wani ba su ba, taron a ci buki ne. buki ba a yin sa sai da mafari, mafarinsa shi ne tarihinsa.

Bukin A Taskar Adabi da Al’ada da Harshe

Al’adun da mutane suka gada kaka da kakanni za a ci karo da su cikin adabinsu da al’adunsu da harshensu. Duk abin da adabin mutane ya kawo, to a je a binciko shi cikin al’adunsu da nahawun harshensu za a ga wurin da salka ke tsatsa. Ga yadda buki ya yi naso a adabinmu:

  • Bukin farar balbela, kaza ba gayyatarta ake ba.
  • In gani a ƙas, an ce wa kare ana buki a gidansu.
  • Ƙudan buki, ba gayyar ku ake ba.
  • Arha matan buki.
  • Ban ci buki ba, buki ya ci ni.
  • Uwar buki, ba ruwanki da ɓarakar zane.
  • Bukin Sa’a ba kyanta ba ne.
  • Bukin Magaji, ba ya hana na Magajiya.
  • Bukin wani kundumi, bukin wani doka.
  • Ba ya bukina, ba na bukinsa.

Waɗannan karuruwan maganganun da zantukan hikima in an bi su daki-daki ba ƙaramin kundin PhD za a rubuta ba. Buki a jinin mutane yake, adabinsu ke fitar da shi a sararin adabi a harare shi. Bukin Bahaushe da na farin ciki, da na baƙin ciki, duk akwai hidimar kyauta a ciki. Malamin Kiɗi Ibrahim Narambaɗa, ya tabbatar mana da haka a waƙar “Ya ɗau girma ko ba a so”

Jagora: Ko way yi buki bai ba ka ba
: In na yi buki ba ka ba shi ba

Yara: Ya san ba ka da laifi ko ƙiris

Gindi: Ko way yi buki bai san da kai ba
: In ka yi buki ba ka ba shi ba

Yara: Ya san ba ka da laifi ko ƙiris

Gindi: Ya ɗau girma ko ba a so
: Maƙi gudu baban ‘yan ruwa

Babu wai, adabi ya tabbatar muna, a cikin buki, akwai ciye-ciye, da tanɗe-tanɗe, da shaye-shaye, da haɗuwar mata da maza da, gudunmuwa ta ‘yan uwa da abokan buki, ga su nan dai. Buki na Sarauta irin su “Sallar Gani” cincirindon talakawa cikin ado da bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, su ne adon Sarki da masarautarsa. Ƙin fitowar talaka a yi da shi, laifi ne na nuna bijirewa, kamar yadda ƙin ba da tasa gudunmuwa ga bukin ‘yan uwa da abokan arziki laifi ne ga dokar buki da sabgar dangi.

Lokutan Buki Da Halayyar Ribantar Su

Hankalin Bahaushe ya zarce tunanin na bayan fage, da dabirtaccen ɗan boko, mai ra’ayin duniyar baƙar fata baya take ga ci gaba. Bahaushe, da ci gabansa, da wayewarsa, aka gan shi, duk ci gaban zamani da ya riske shi, ba a rasa nasonsa da hancin adabinsa ya sunsuno. A kowace hada-hada ta buki Bahaushe na da:

  • Lokacin Buki
  • Wurin Buki
  • Fitar Buki
  • Ribantar Buki

Lokutan Bahaushe na buki uku ne: sassafe tun gabanin hantsi ya dubi ludayi, musamman in bukin ya shafi dafe-dafe, da toye-toye, da soye-soye. Da rana tsaka, bukin da ya shafi maza zalla ake yi musamman bukukuwan da ke buƙatar a ɗebe wa ido kwantsa. Da dare, ana bukukuwan da ke buƙatar sirri ko kuma ba su da nauyin sai a bayyana su da rana. Sallar Gani da rana tsaka ake aiwatar da ita ba ta kunyar idon kowa, kowa na son ganinta.

Wuraren bukin Bahaushe sun haɗa da gidan buki idan bukin ƙarami ne, kuma na ƙaramin gida, ko kuma wanda dole sai a gidan za a yi shi. Akwai dandalin unguwa idan ya shafi mutanen unguwa. Akwai na kasuwa ko maciya, idan abin na gari ne gaba ɗaya. Babban buki gagarumi sai Kan Wuri wanda ya shafi mutanen gari da maƙwabtan garuruwansu irin bukin “Sallar Gani”. Ana gabatar da wasan bukukuwa wuraren ban gaskiya da maƙabarta idan sun shafi mutuwa da addini.

Ga al’adar Bahaushe, fitar Buki ta musamman ce, za a yi wa yara maza da mata kwalliya gwargwadon halin iyayensu. Manyan maza da mata za su sha kwalliya irin ta yara ko fiye da ita. A wasu bukukuwan kuma za a fita da kayan gado na shirin kare martabar magabata. Babu bukin da za a yi fita Bambarakwai a ƙasar Hausa in ba na roƙon ruwa ba ne. Bukukuwan da suka shafi fada da Sarauta manya ne ga Bahaushen tunani, wani ba su ba ƙanana ne. Sallar Gani babba ce ta kowa da kowa sannan na hawa irin na kowace salla.

Ribantar buki na kowa da kowa ne. A tsarin buki, abinci ba sai an saya ba, kowa zai kawo tasa gudunmuwa har sai an kasa cinye na kowa. Masu wasannin gargajiya, da wasannin gwada martabar gado, da magani da buwaya, da ƙwarewa kan kowane irin abu na iya bayyana a dandalin babban buki a ji su, a gan su. Taka rawar gado da za su yi, zai ba da damar a yi musu karin kuɗi da ƙadara, tare da yaba musu, da gode musu, da saka su cikin adabin ƙasar a taskace sunansu a tarihi.

Matakan Bukukuwan Bahaushe

Bukukuwan ƙasar Hausa matakai gare su da al’ada ta kiyaye da su. A farfajiyar nazarin al’adar Buki a ƙasar Hausa, matakan bukukuwa su ne:

  • Bukukuwan Matakan Rayuwa
  • Bukukuwan Tsari da Yaƙi
  • Bukukuwan Buɗi
  • Bukukuwan Dattako
  • Bukukuwan Naɗi
  • Bukin Dubu da Tambarci
  • Bukukuwan Ban Gaskiya
  • Bukukuwan Saukakkun Addinai
  • Bukukuwan Tsafe-tsafe da Siddabaru
  • Bukukuwan Sana’o’i
  • Bukukuwan Kafa Tubalan Harsashe
  • Bukukuwan Askewa (Tuba)
  • Bukukuwan Gayya

Bukukuwan Matakan Rayuwa: Su ne bukukuwan aure, raɗa suna, kaciya da mutuwa da duk wani abu da ya shafe su na buki. Sallar Gani ba ta ciki domin daga baya ta zo.
Bukukuwan Tsaro da Yaƙi: Su ne bukukuwan gwazangwari na zagayowar wata rana da aka ci wata nasarar yaƙi da wani gari ko wata ƙasa. Haka bukukuwan tunawa da mazajen da suka faɗi a wata arangama yaƙi da aka yi da wasu, sai a zaburar da maza su ɗauko fansa, Kabawa da Gobirawa suka shahara da waɗannan. Sallar Gani ta saɓa musu domin ba da makaman gaba ake yin ta ba.

Bukukuwan Buɗi: Buɗar Dawa, Buɗar Hurumin Kogi ko tabki na su. Sallar Gani ta ban girma da ban gaskiya da tuna baya ce.
Bukukuwan Dattako: Bukin Aza Gemu, Bukin Kai Bante ga amare mata. Ana bukin aza geme daga shekaru 30-40, kai bante kuwa da amarya ta tare gobe da safe mata za su yi.

Bukin Naɗi: Naɗin Sarautar ƙasa, Sarautar gado ta sana’a ko Sarautun girshi, Sallar Gani babba ce ba a sakaɗa naɗin kowace Sarauta ranar da gudanar da ita.
Bukin Dubu da Tambarci: Sai manomi ya kai babban goje zai noma dami dubu na hatsi ko masaki dubu da tsabar shinkafa ko wake da sauransu. Ana yi musu buki na musamman da tamburan yaƙi. A gona ake fara bukin in an dawo gida a yi ban gajiya.

Bukin Ban Gaskiya: Ban gaskiya shi ne bukukuwan Girka da Bori da Kan gida.
Bukukuwan Addini: Salloli, Musulunci babba da ƙarama, Hajji, Jumu’a, Saukar Karatun Alƙur’ani, Maulidi, buɗa masallaci da gangamin wa’azin ɗariƙu da ƙungiyoyi.
Bukukuwan Tsafe-Tsafe da Siddabaru: Shan Kubewa ga Kabawa, Shan Gumba ga Rundawa, Cin Tama na Maƙera, Kafin Gari, da cin Sabu ga ‘yan bori.

Bukukuwan Sana’o’i: Cin Tama na maƙera, Hawan Ƙaho na Rundawa, Ɗaurin Ruwa na Masunta da Ɗaurin Daji na mafarauta.
Bukin Kafa Tubalin Harsashe: Bukin kafa kasuwa, kafa gari, buɗa wata babbar hanya, kafa wata sabuwar Sarauta.

Bukin Askewa: Bukin aske zanƙon dambe, cire tukkuwar kokuwa, aske gemun wasa, cire ƙanƙarun maita, tuba da sata ko fashi.
Bukin Gayya: Gayyar Sarakuci, Gayyar rashin lafiya, Gayyar Masallaci, Gayyar gyara wani muhimmin abu a gari, ƙasa, ko unguwa.

Ina Sallar Gani ta Faɗo Daga Cikin Waɗannan?

Waɗannan bukukuwan sun game ilahirin ƙasar Hausa, jiya da yau. Dukkanin ƙasashen da ke karɓa sunan ƙasar Hausa, Gobir, Kano, Kabi, Zazzau, Katsina, Maraɗi, Damagaram, da sauransu duk ana aiwatar da su, amma a Daura da Haɗeja da Gumel kawai Sallar Gani ta yi suna.

Masu bincike sun ce, ana yin bukukuwan Sallar Gani a Daura tun gabanin bayyanar addinin Musulunci. Da Musulunci ya zo, ya samu karɓuwa da bazuwa, ta sake zani ta kutso ciki da rigar Maulidi. Silalin wannan tarihi ya sa za mu ce, “Sallar Gani” tana daga cikin: Bukukuwan Tsaro da Yaƙi da Bukukuwan Addini

Kasancewar Daura tsohon garin tarihi, wannan bukin an daɗe ana yin sa. Idan aka dubi sigar da ake gudanar da shi, buki ne da ke da alaƙa da tanadin yaƙe-yaƙe da tsaron ƙasa. Da aka ga amfaninsa bayan da yaƙe-yaƙe suka kau, aka riƙe shi wani matakin tsaro ta fuskar sadar da zumuncin da ke cikinsa.

Bayan da Musulunci ya zo, ba a sauya masa siga ba, saboda sanin muhimancinsa aka sakaɗo hidimar Mauludi ciki. A halin yanzu, ni ina ganin “Sallar Gani” tana da wani matsayi da za a kira “Bukin Sada Zumunci”. A koyaushe aka hau ta, za a tuna baya domin sake gyara zama a yau, a san yadda za a tunakari gobe.

Sunan Sallar Gani

Idan Bahaushe ya ji an ce: “Salla” addinin Musulunci zai fara zo masa a tunaninsa. Ni kaina, shekaru da yawa a baya, da na ji sunan bukin “Sallar Gani” a Daura haka na yi zato. Yayin da na je Maraɗi wani bincike (2000), na tunkari Maraɗawa na samu bayani a kanta.

A bukukuwan da Jamhuriyyar Nijar ke yi na zagayowar shekararsu ta samun ‘yancin kai, na samu halartar tarukansu na ƙara wa juna sani cikin bukukuwan da suke yi shekara-shekara a jihar Maraɗi da Dosso da Damagaram, kowanne daga cikin ‘yan siyasarsu da ‘yan bokonsu da walilan tsaronsu da dukkanin Hausawan ƙasar da Arawa da Zabarmawa da Dandawa da Buzaye da Fulaninsu da sauransu suna yi wa bukin suna da “Salla”.

A wajensu, duk wani buki da za a yi, a fito a yi kwalliya, manyan gari da masu gari su fito da jama’arsu, sunansa “Sallah”. Ban yi musu ba domin za a ji Hausawan duniya na cewa:

  • Yau take salla
  • Salla mai yawan ƙawa
  • Kukan zakara buki “Gobe Salla a yanke manya, a bar ƙanana”
  • Buki ba naka ba ka bi; ‘yan kaji da yanka

Idan muka dubi wurin da ƙasar Daura take, da dangantaka da kusancinsu da Jamhuriyyar Nijar, da kuma dangantakar tsagarsu ta gado “dogaye biyu a haɓa” irin ta Arawan Nijar, da Arawan Nijeriya, da Gubawan Jamhuriyyar Benin, za mu ce, buki na da suna biyu a wajensu: Buki da “Salla”.

Wataƙila saboda irin tasirin da Musulunci ya yi a Daura suka zaɓi amfani da kalmar “Salla” da ke da makusanciyar dangantaka da Musulunci suka yi watsi da kalmar “buki” da ke da nason gargajiya a ruhin ma’anar ta. A kan wannan tunani ta zama “Sallar Gani” ba “Bukin Gani” ba.

Fashin Baƙin Kalmar Gani

Daga cikin Sallar Gani, kalmar “Gani” na son a waiwaye ta. A furuci, Daurawa da Haɗejawa da Gumalawa da maƙwabtansu suna furta kalmar da sautin /gaa/ da dogon wasali da /ni/ da gajeren wasali. A rubutun aruli, kalmar za ta kasance /gaani/. A lura, kalmar gaɓa biyu gare ta takan ɗauki ma’anoni kamar haka:

Ganii: abin da mutum ke kallo ƙuru-ƙuru
Ga nii: wanda aka kira ya karɓa kira, kuma ya zo, zai ce: “gaa ni na zo”
Gaanii: ɗebe kifin da aka kama a haƙo na kalli ko mamari ko undurutu. Haka kuma, haƙo zuma a raminta ko burtumin da aka haƙa ta duk “gaanii” ne.

Waɗannan kalmomi uku su suka fi kusantar ma’anar kalmar da ke cikin “Sallar Gani”. Daga cikinsu na zaɓi kalmar “gaa nii, mai ma’anar gaa ni naa zoo”. Yayin gudanar da Sallar Sarakuna da Magajiyoyi kan taru, Sarki ya kai gaisuwa ga Magajiya ya ce: “Gaa ni na zo gaisuwa”.

Idan muka dubi yawancin kirari da maganganun da zabiyoyi ke yi wa Sarki a lokacin Sallar Gani za mu yi kirdadon wata Bahaushiyar kalma wai ita “guunii” mai jam’i “gunaagunii”. Guuni wata maganar zuci ce da baki ke furtawa da wani nishi daga cikin bakin, wanda zai hana mai sauraro gane abubuwan da ake faɗa har sai ya ce: “Wane gunaguni ne ake yi”?

Duk wanda ya halarci dandalin zabiyoyin da ke yi wa masarautar Daura jinjina zai tabbata maka daga su matan da ke yi, sai Sarki, da mutanen fada ke iya kama ma’anonin abubuwan da suke faɗa. Ganin irin gurbin mata a tarihin masarautar Daura musamman Sarauniya Daurama, da wasu masana tarihi ke ganin tun fil azal Sarautun mata ke akwai ƙasar Hausa daga baya maza suka ƙwace. Wataƙila, can gabanin Musulunci “Buki/Taron Guunii” yake saboda mata ke sarauta, mata ke zabiya, mata ne Magajiya.

A hasashe na biyu na dubi yanayin mutanen da ke zaune “Daura”. Tun fil azal, akwai Larabawa, akwai Barebari, akwai Arawa, da Arewawa, da sauran nau’o’in Hausawa da Buzaye. Tunani da tarihin Bayajidda ya sa na yi tunanin kalmar Balarabiya ce, musamman idan aka lura da irin adabin Larabci da yadda waƙa da waƙoƙin mata suka yi tasiri a ciki.

Wanda ya karanci tarihin Daular Banu Umayyad da Abbassid ba zai musanta hasashen ba. A Larabci, waƙa ana ce da ita “alginaa’u” mawaƙi “almuganni”. Wataƙila ‘yan waƙoƙin da matan ke yi ya zama sanadiyyar kiran bukin “Bukin Gaanii” wasali “i” na “n” ya zamo dogo /nii/ ya zamo “bukin zabiyoyi”. Hasashe na uku shi ne, sunan mata na Hausa “Gana”. A garuruwan Hausawa a can da, ana sa wa ɗiya mata suna “Gana” yana da kyau a ɗan nazarce shi.

Bitar “Sunan Daura”

Daura ita ce tushen Hausa. Masarautar Daura kaɗai ce daga cikin masarautun ƙasar Hausa da ke da ikon ba da Sarautar Hausa. Sunan Daura babba ne a tarihi domin tarihin Bahaushe a ko’ina yake ba ya kammaluwa in ba a kawo Daura a ciki ba. Idan muka ɗora kalmar Daura cikin kalmomin Hausa za mu ga akwai:

Daura: Sunan garin da muke zance a kai
Daura: Kalma ce mai nuna, “kusa ga”: Gidan nasa na daura da gidan Sarki
Dauri: Ma’ana a da ko a da can da nisa.
Daura: A lugar Larabci kalmar taro ko matattara ko haɗuwa ta musamman. Ɗaliban ilmi da suka yi karatu a ƙasashen Larabawa sukan haɗa ɗalibai wurare daban-daban don yi musu bita a wuri ɗaya da sunan “daura”.
Daure: Ƙoƙarin cijewa da ƙin nuna gazawa da ƙin raki.

Ba mu samu tabbacin wanda ya raɗa wa Daura suna ba, amma idan muka yi duba cikin ma’anonin kalmomin /Dauraa/ da muka gabatas kalmar “daura” da “dauri” sun fi kusa da juna kuma su ne, makusantan sunan garin. Kalmar “daura” ta Larabci zuwan Bayajidda Daura ya kore ta.

Masu tarihin Daura, sun tabbatar da cewa, Balaraben Iraƙi ne kuma ya taras da Sarauniya Daurama na mulki har ta aure shi. Wannan ya nuna tun Larabawa ba su zo Daura ba sunan garin Daura yake Daura. Haka kuma nan suka tarar da garin Daura ba su suka sare shi ba.

Kwakkwahe Batu Kan Kalmomin “Salla”, “Gani” da “Daura”

Kalmar “Salla” sabuwar kalma ce ta sadu da Hausawa bayan da addinin Musulunci ya zauna da gindinsa a ƙasa da zuciyar masu ƙasa. Kalmar ta tabbatar da akwai wata gabaninta, wadda ba wata ba ce face “buki”. Buki ita ce kalmar da wani addini bai yi naso cikinta ba.

Gani a daidaiciyar ma’ana ta al’adar Daurawa ita ce daga: “ga ni na zo” takan fito bakin wanda aka kira ko aka gayyato ko kuma ya zo karan kansa amma da wata magana ta daban. Kalmar Daura Bahaushen suna ne da Daurawa suka ƙago abinsu. Gabanin yau 2019, Bukin Gani a Daura yake. Da addini ya mamaye masarauta ya koma Sallar Gani a ƙasar Daura. Wannan sunan shi ne ke ci har yau ta koma Sallar Gani a ƙasar Hausa.

Tsarin Sallar Gani a Daura

Tarihin Sallar Gani ba zai kammala ba sai an waiwayi tarihi da tarihihin Garin Daura. A tarihance, Daura babbar ƙasa ce da manyan garuruwa da yawa ke ƙarƙashinta. A tarihin zuwan Bayajidda, an tabbatar da zuwansa Daura da matarsa da yaronta. Bugu da ƙari, tarihin ya nuna ko zamanin zuwansa Daura babbar masarauta ce ƙarƙashin Sarauniya Daurama.

Ya tarar da Daura ta bunƙasa har da babbar rijiyar shan ruwa “Kusugu”. A tarihin, an yi saɓani kan zancen macijin da aka tarar a cikinta a kan matsayinsa. Tsohuwa “Ayana da ya tarar ta ɗan ɓulguta masa matsayin macijin a Daura ta wancan lokaci. Da ya kashe maciji, sai auratayya ta shiga. Cikin auratayya aka samu ‘ya’yan da suka kafa Hausa Bakwai da Banza Bakwai, wanda a yanzu ake yi wa sunan: Yannai Bakwai da ƙannai Bakwai.

An ce, a kowace shekara Yannai Bakwai da Ƙannai Bakwai sukan baro masarautunsu zuwa Daura su kwana, cikin dare za su kwana ana bitar nasarorin da aka ci, da cikas da aka samu, da yadda za a fuskance su. Taron za a kwana zaune ana karatun abubuwan cikin dare, da safiya ta waye a shirya ‘yan bukukuwan ban kwana da kilisar sadar da zumunci.

Daga nan Bukin Gani a Daura ya soma har ya sarƙu da addini ya sauya masa suna zuwa “Sallar Gani”. Babu tabbacin ranar da aka fara yin ta, da Basaraken da ya fara mai da ita buki. Abin sani shi ne, ƙasar Daura da Gummel da Haɗejiya sun fi ba abin muhimanci fiye da kowace ƙasa ta ƙasar Hausa.

A Daura, Sallar Gani, Salla ce ta tunawa da Sarakunan da aka yi mata. Babbar ɗiyar Sarki ita ake naɗawa Magajiya. A ranar Sallar Sarki zai je gaishe ta da shi da hakimansa, amma kowannensu ba zai saka alkyabba ba a ranar, amma ita Magajiya za ta saka. Sarki tare da jama’ar za su kai gaisuwa, Sarki zai gaya mata: “Gani ni na zo”. Hakiman Magajiyar Daura duk ‘yan tsatson Sarauta ne irin su:

  • Yarkuut
  • Gabsai
  • Dangawa
  • Saraki
  • Gizir-Gizir
  • Hamata
  • Jamata
  • Yambamu
  • Saudamat
  • Tawata
  • Mai Babban Ɗaki

Muhimmancin Sallar Gani da Tasirinta

Sallar Gani ƙasaitacciyar buki ce da ta cika dukkanin sharuɗan buki na al’ada guda huɗu (4). Duk wurin da sunanta ya kai, daga Daura ya fito, kuma a Daura aka san shi. Daga cikin muhimmancinta akwai:

  • Haɗin kan masarautun ƙasar Hausa gaba ɗaya Yannai bakwai da ƙannai bakwai.
  • Adana tarihi da al’adun ƙasar Hausa na Sarauta da masu mara wa na Sarauta baya.
  • Sake jaddada cewa, Daura ita ce tushen Hausa domin Hausawa su yi bugun gaba da ita.
  • Adana tarihin Sarautun mata na gargajiya na Magajiya da ɗiya mata ke yi.
  • Fito da ɗawainiyar mata a fagen adabi na Zabaya da Maguɗiya da suka soma mutuwa a yanzu.
  • Hawan daba, da riƙe martabarsa, da koyon sukuwa da dawaki na artabo da tsaro.
  • Sarƙuwar Sallar Gani da Mauludi wani sabon salo ne na ƙara adana Sallar Gani da jaddada ta.

Sakamakon Bincike

Sallar Gani tsohuwar al’ada ce da kowa ya tashi ya tarar da ita a Daura. Rashin samun Sarkin da ya fara ta a zamaninsa, ya nuna tun gabanin bunƙasar Sarautu a ƙasar Hausa ake gudanar da ita. Ga ɗan abin da bincike ya ƙyallaro akwai:

  • Tabbacin cewa, tun gabanin Musulunci ake yin ta, da addini ya zo aka cigaba har aka sako shi ciki.
  • Asalin bukin Sarautun mata ne gargajiya ya assasa shi ya wanzu har zuwa ga Daurama zuwa yau.
  • Ƙasar Daura Sallar Gani ta tsira, a ko ina aka gan ta balaguro ta je.
  • Asalin Sallar Gani kwana biyu ne yini ɗaya. Da dare Sarakuna ke tattaunawa da rana a yi hawa a watse.
  • Duk da muhimmancin Sallar Gani, da tsawon shekarunta, a ƙasar Daura kawai ake aiwatar da ita.

Shawarwari

Tsawon ƙarnukan da aka ɗauka ana yin abu ɗaya a Daura da sunan Sallar Gani, ya kamata a ƙirƙiro wasu abubuwa kamar:

  • Tsereniyar sukuwar dawaki, da fitar da zakara na kowace shekara, tare da kyautar kofi da kuɗi da ƙadara, da sunan ɗaya daga cikin Sarakunan Daura.
  • Samar da sahihin tarihin Daura, tare da ƙara sabunta shi kowace shekara, ana raba wa Daurawa da Sarakunan ƙasar Hausa.
  • A yi tunanin kafa gidauniya ta Sallar Gani, wadda za a tanadi kuɗin da za a gina makaranta da asibiti da filin motsa jiki na mata zalla, domin tunawa da sarautun mata da hidimominsu a gargajiyance.
  • Kowace shekara a riƙa gabatar da shahararriyar ƙasida ta fannonin ilmi daban-daban, da za a gayyato masana ƙwararru su rubuta bisa ga wani abu muhimmi na shekarar a kuma riƙa ba laccar suna “Daurama” a wallafa a raba wa jama’a.
  • A samu gagarumin gidan rediyo ko talabijin a buɗa a yi masa suna “Daurama” dukkan ma’aikatansu su kasance mata, kuma shirye-shiryensu ya shafi mata kawai.

Naɗewa

Ilmi ba kayan gidan kowa ba ne, wanda duk ya nemo shi, ya samo shi, ya zama kayan gidansu. Nagartattun al’adunmu da muke yi wa riƙon sakainar kashi su suka dabirta tarihin mu da irin gudunmuwar da ya bayar har aka kai ga harsashen kafa wannan asa tamu mai suna Nijeriya.

Na yarda cewa, da wasa ake gaya wa wawa gaskiya, cikin bukukuwanmu na gargajiya nan za a tsinci tarihinmu da sana’o’inmuu da hikimomi da basirun da ke ciki domin amfanar da jama’armu. Harsashen kafa Bukin Sallar Gani shi ne samun haɗin kan masarautu da masu sarauta maza da mata, da tuni da juyayin fitar mulki ga hannun mata zuwa ga maza.

Wannan shi ya sa Sarki da kansa ke zuwa ga babbar ‘yarsa Magajiya da sauran ‘ya’yan Sarauta mata waɗanda ba sa hawa karagar mulki kuma abin da suka haifa ba zai hau ba don ɗan mace ne. Cikin hikima, an girmama su an kyautata musu, kuma ƙasa ta zauna lafiya.

MANAZARTA

Adamu, M. (1977) “Towards the Definition of Hausa Culture in African Context” paper presented at Centre for Nigerian Cultural Studies, Zaria: Ahmadu Bello University.
Ahmed, S. B. (1990) “Tsarin Sarautar Gargajiya a Haɗeja”, kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Balbasatu, I. (2009) “Gudummuwar Mata ga Havaka Rubutaccen Adabi”, kundin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bargery, G. P. (1993) A Hausa-English Dictioanary and Eglish Hausa Vocabulary (2nd ed.) Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Barker, C. (2012) Cultural Studies: Theory and Practice (4th ed.) London: Sage Publications.
Bichi, A. Y. (2011) “Bayajidda Legend in the 21st Century: A Reassessment”, in Yalwa, L. D. et al., (ed.) Studies in Hausa Language, Literature and Culture, Kano: Bayero University.
Bunza, A. M. (2006) Gadon Fexe Al’ada, Lagos: Ibrash Islamic Publications.
Bunza, A. M. (2009) Narambaɗa, Lagos: Ibrash Islamic Publications.
Daura, H. K. (2016). “Kirarin Saraki a Bakin Mata: Nazarin Zabiyanci a Ƙasar Hausa”, kundin PhD, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Gama, A. M. (2012) “Tasirin Siyasa a Masarautun Gargajiya Musamman a Makarantun Sakkwato da Katsina da Kano da Daura Daga 1960-2000” kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Hauwa, R. D. (2005): Sarautar Mai Babban Ɗaki a Fadar Kano”, kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Hitti, P. K. (1961) History of the Arabs, London: Macmillan Company Limited.
Ibrahim, A. (1991) Alhaji Muhammadu Bashar: A Biography, Katsina: Himma Press Limited.
Ibrahim, M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Bahaushe ta Gargajiya”, kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Koforowola, E. O. (1982) “Hausa Performing Art and the The Emirs Court”, PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Mack, B. B. (2004) Muslim Women Sing: Hausa Popular Song, Blomington and Indianapolis: Indiana University Press.
Magaji, A. (2002) “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-Yanayensu a Ƙasar Katsina”, kundin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Maimuna, L. D. (1987) “Fadar Daura”, kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Nuruddeen, M. (1982) “Sallar Gani a Daura”, kundin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Ramlatu, J. D. (2012) “Sarautun Ƙasar Daura da Muhimmancinsu ga Al’umma” cikin Champion of Hausa Cikin Hausa, Amfani, A.H. da Wasu (ed) Zaria: Jamhuriyar Ahmadu Bello.
Saulawa, A. M. (2001) “Origin of the Hausa States Revisited” in Degel Journal, Faculty of Arts and Islamic Studies, Sokoto: Usmanu, Ɗanfodiyo University.
Shafa’atu, M. T. (2013) “Kirarin Mata a Ƙasar Sakkwato”, kundin MA, Sokoto: Usmanu Danfodiyo.
Smith, M. G. (1978) The Affairs of Daura, London: University of Califonia Press.
The New International Webster’s Comprehensive Dictionary of the English Language Deluxe Encyclopedic Edition (1996).
Tsiga, I. A. (1978) “Sarauniya Daurama”, takarda, taron Ƙungiyar Hausa, Kano: Jami’ar Bayero.
Turai, U. M. Y. (1983) “Binta Zabiya da Waƙoƙinta”, kundin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Wakili, H. (2005) Turawa a Ƙasar Haɗeja, Kano: Benchmark Publishers Limited.

Mutanen Da Aka Tattauna Da Su

Sarkin Tarihin Daura Alhaji Muhammadu Lawan.
Dr. Halima Kabir Daura, Dept. of African Languages and Culture, ABU Zaria.
Malam Bala Safana Federal Government College Daura.
Dr. Bashir Sallau Sarkin Aska Safana, Dept. of Nigerian Language Umaru Musa Yar’aduwa University, Katsina.
Dr. Yakubu Aliyu Gobir Dept. of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University Sokoto.
Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad Head Hausa Unit, Dept. of Languages, Sule Lamiɗo University Kafin Hausa.

Danna nan don karanata Bikin Kamun Kifi 

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceƘagaggun Labaran Hausa Na Zamani
Labarin na GabaFasalin Ƙagaggun Labaran Hausa A Zamanin Zuwan Turawa