Episode 2
A short story by
Sakina Yazid (Innar su Amal)
Mutanen da suka fara dawowa daga maƙabarta ne suka gan ta, don haka ƙanin mahaifinta ya kama hannunta suka koma gidan tana biye da shi kamar wata marar hankali.
Suna shiga farfajiyar gidan ta turje, ta ƙi ƙarasawa cikin parlor. Nan aka yi wa Ummanta magana inda suka fito ita da Maman Misbahu da ma wasu matan waɗanda suka haɗa da ƙawar Farida, Rabi’a wadda isowarta kenan.
Ummanta ta ƙarasa kusa da ita ta kama hannunta cike da kulawa tace ‘Farida ki dangana mana, Allahn da ya karɓe shi zai ba ki wani. Ki taho mu shiga gida mu zauna. Ta fizge hannunta daga hannun Ummu tace ‘Ba zan shigo ba, ba zan sake shiga gidan nan ba in sha Allah.’
Zuwa lokacin ragowar mazan sun ƙaraso har da Misbahu da babansa da Baban Farida. Suka tsaya suka yi cirko-cirko. Maman Misbahu ta ƙaraso ta dafa kafaɗarta tace ‘Idan ba ta son nan ɗin ai sai ku wuce gida. Ta sa hannu ta ture hannun Maman Misbahu daga jikinta tana mata kallo na ƙyamata.
Ta dubi Umma ta tace ‘Ba zan je gidan ba, wane gidan zan je? Ba kwa buƙata ta ai tunda ba zan sake zama da Misbahu ba. Dole ya sake ni tunda ya kashe min yaro, kin ga kuma kuma ke da Abba ba kwa son bazawara. Don haka ba zan je muku gida ba, in sha Allah daga yau ba za ku sake ganina ba balle na janyo muku abun kunya.’
Duk wanda yake wajen jikinsa ya yi sanyi, kowa ya kasa magana. Maman Misbahu ta daure tace ‘Ki yi haƙuri Farida a zauna a bi abin a hankali. Ta yi murmushi yaƙe ta juya tana fuskantar Maman Misbahun sannan tace ‘Dole ki ce na yi haƙuri tunda ke ɗanki yana raye, amma ni ya kashe min nawa ɗan.
Kuma na san kamar yanda kika saba kariya za ki ba shi, sai dai ina miki albishir da cewa ba zai rayu har abada ba. Za mu tsaya a gaban Allah wanda shi kaɗai zai iya yi mana adalci. Ta juya ta yiwo tattaki ta ƙaraso gaban Misbahu ta tsaya, ta zuba masa ido har sai da ya gaji ya sauke nasa ƙwayar idon.
Kana kallonsa ka san a jigace yake sannan kuma cikin tashin hankali. Ta share ɗigon hawayen da ya gangaro a fuskarta tace ‘Yanzu ka ji daɗi ko Misbahu? Ɗanka, kuma ɗana guda ɗaya ka kashe shi ka huta. Burinka shi ne ka cuzguna min ka saka ni a cikin ƙunci kawai saboda ni na nuna maka soyayya na aure ka. Yanzu ka ga sai ka je ka auri Shahida ka sake rayuwa.
Na san cewa iyayenka za su ba ka kariya kamar yanda suke yi idan ka yi min wulaƙanci na kai ƙara, kuma na san duk taron mutanen nan da suke kallonmu ba za su iya yi min adalci ba tunda suma duka sun yarda da cewa duk abinda namiji ya yi ado ne; mace ita ce take laifi. Sai dai ina so ka sani daga rana irin ta yau duk lokacin da na yi sujuda sai na kai ƙararka wajen Allah; Allah ya yi maka abinda ka yi min kuma Allah ya saka mana ni da ɗana da ka kashe.’
Ya runtse ido saboda yanda kalmar ka kashe ɗana take sukansa a zuciya. Yana matuƙar son Adnan, ya za a yi a ce shi ya kashe shi. Har yanzu ma ƙoƙari yake ya yarda cewa Adnan ɗin suka kai maƙabarta suka binne. Ta yi murmushi sannan ta cigaba ‘Ina jiran ka aiko min takardar saki na zuwa gobe. Ban san hukuncin da zan ɗauka ba amma tabbas duniyar nan ba za ta ɗauke mu ba ni da kai idan dai ka bari na sake ganinka ba tare da ka sake ni ba.
Na tsane ka, bana fatan na sake ganinka a rayuwata. Ina fatan Allah ya hana ka farin ciki kamar yanda ka hana ni da kai da duk wanda yake goya maka baya. Ta matsa daga gabansa ta nufi waje; Ummanta ta bi bayanta da gudu ta sha gabanta tace ‘Ina za ki Farida, ki bari na ɗauko jaka ta mu tafi gida.’
Ta kalleta tana share hawaye tana cewa ‘Ban san inda zanbi ba, amma wallahi ba za ni gidanku ba balle na janyo muku abun kunya a ce ‘ƴarku ta ƙi zaman aure. Na san dai ko gidan marayu na je za a karɓe ni a ba ni wajen da zan zauna na ƙarasa rayuwata wadda ina ji a jikina ba ta da yawa.’
Ta raɓa ta gefen Umman ta wuce ta nufi gate. Umma ta tsaya a nan tana share hawaye ba tare da ta san abin yi ba. Gaɓa ɗaya mutanen da suke wajen duk an kasa motsi, kowa binta yake da kallo ana share hawaye. Rabi’a ce ta fito daga cikin matan nan tana riƙe da jakarta cikin hanzari ta ƙarasa ta dafa Farida; wadda ta kusa gate ta baya.
Ta juya ta kalleta yayinda Rabi’an ta kama hannuwan Farida ta riƙe tana cewa ‘Ki zo mu je gidana Farida, don Allah ki zo mu tafi. Babu wanda zan bari ya ganki, kin ga gobe ma za mu wuce Abuja ba za su sake ganinki ba.’
Ta kalli hannuwansu waɗanda suke a haɗe, cikin hawaye tace ‘Ba ki yi fushi da ni ba Rabi; ke da aka saka ni na daina kula ki saboda kada ki aure min miji kuma yanzu ba kya tsoron na biki gidanki, gidan mijinki? Ki bar ni kawai na shiga duniya Rabi, na gaji da kowa wallahi.’
Ta jinjina hannuwansu tace ‘Ba zaki shiga duniya ba Farida, ai ni ba ki gaji da gani na ba ko? Shiru ta yi ta kasa ba ta amsa, don haka ta ja hannunta suka fice daga farfajiyar gidan kowa yana kallon su.
ƘARSHE….
EPILOGUE
Mata da yawa suna zaune a gidajen aurensu cikin cin zarafi da ƙunci ba lallai duka ba. Wasu zagi ne da rashin girmamawa da kuma sauran nau’o’i na emotional abuse.
Iyayensu ne ya kamata su ba su kariya a irin wannan lokacin to amma haƙuri kawai suke ba su; suna kuma mayar da su cikin halin da yake firgita nutsuwarsu. A mafi yawancin lokuta ma idan iyayen suka saka baki aka zauna da mijin matsalar za ta warware, sai dai idan iyayen ba su jajirce ba. To amma ba za a ko gwada ba. Haka ake zuba musu ido suna rayuwa cikin ƙunci – alone, sad and depressed.
Iyayensu ba za su taimaka musu ba.
Al’umma ba za su taimaka musu ba.
But idan depression ya yi musu yawa har ya janyo suka aikata wani abu na assha a lokacin ne za ka san every single member of the society yana kallon su; domin kuwa za a yi assembly a tsine musu albarka.
Ban sani ba, ba mu san depression ɗin ba ne ko kuma ba mu yarda yana iya saka mutum ya cutar da kansa ba ko ya cutar da wani. Da sun yi magana sai mu ce su yi haƙuri. Su fita daga harkar mijin su yi zaman ‘ƴa’ƴa. Idan sun matsa mu ce ƙaddararsu kenan.
Haka za su ƙare rayuwarsu cikin damuwa. Babu abinda ban ji ba from real people
“Mamaki nake idan na ga mutane suna walwala, su ba su san a cikin matsala ake ba ne?”
“Mahaifina yace kada na kashe aurena na ba shi kunya, na yi zamana.”
“Mahaifiyata tace ban isa na janyo mata magana a tsakanin kishiyoyi ba, babu me bazawara ba za a fara a kanta ba.”
“Na rasa yanda zan yi da shi Anti, duk wanda na gayawa sai a ce na yi haƙuri. An ma rasa me yi masa ko da nasiha ne. To har tsawon yaushe ne zan yi haƙurin? Sai na mutu? Shikenan daga na yi aure nayi sallama da jin daɗi har sai na koma ga Allah?”
Waɗannan maganganun fa real people ne suke faɗa, very young women; all less than 30.
Are we alright? Is this fair? Idan muka cigaba da bari ‘ƴa’ƴanmu da ƴan uwansu suna azabtuwa a dalilin aure tabbas ba mu yi wa aure adalci ba kuma ba mu yi wa musulunci adalci ba.
Ina mafita?
Innar su Amal.
Karanta Baɗi Ba Rai Kashi Na Ɗaya
Edita@rumasau-kallamu









