Allah bisa hikimarsa kan yi duk abin da ya so ya ɗaukaka yasasshe ya sakko da wanda al’amarinsa ke bisa. Wanda kuma wannan na cikin abubuwan da Allah maɗaukaki ya keɓanta da su da yake nuna buwaya da iko akan komai.
Kafin yaren Larabci ya sami ɗaukakar samun kansa a matsayin yaren addinin musulunci wasu yaruka da dama sun samu wannan ɗaukaka wanda yake nuna cewa ba kansa farau ba, kuma ba kansa za a ga wasan sallah ba.
Ba ina maganar su sauran yarukan sai sun zama sun taɓa zama yaren da musulunci ya yi amfani da su ba ne a a, magana ake ta wannan yaren ya taɓa zama na addini? Addinan nan kuwa ko da na gargajiya ne, domin aikin da addinai ke yi wa yare kusan duk iri ɗaya ne da ba ya gaza taimakawa wajen wanzar da shi ta hanyar sanya shi a ayyukan ibada da rubuce-rubuce da shi domin koya ko koyar da wannan addini.
Balarabe ya yi amfani da damarsa ya tallata yarensa da wasu daga cikin al’adunsa ta hanyar musulunci a inda ya shiga ya fita har sai da ya girmama yaren nasa a idon mabiya addinin musulunci ta nuna cewa kamar shi da yarensa wasu abubuwa ne da suke da matsayi daban a gurin Allah ta’ala da ba kowanne yare da al’ummarsa ne suke da wannan matsayi ba, wannan zai bayyana ƙarara ne ga wanda yake da masaniyar abubuwan da suka faru a daulolin da larabawa suka kafa da sunan daulolin Musulunci bayan lokacin Habibi (saw) da sahabbansa ya wuce.
Ala sabilil misali ka ɗauko tsari da yanda aka bi aka mulki mutane a lokacin mulkin Banu Umayyah. Duk wanda yake nazartar tarihin waɗannan dauloli ba ta ɓangaren addini ba kawai ya san yanda Banu Umayyah suka dawo da wasu daga cikin ɗabi’un jahiliyya na fifita duk balarabe akan waninsa wannan kuwa ko da sahabi ne, tuna da tsarin MAWALI da suke da shi mana, bayan kuma Larabawa sun san cewa Habibi (saw) ya faɗa cewa “Babu banbanci tsakanin Balarabe da waninsa sai wanda ya fi wani tsoron Allah” Ka san abin da ya faru har shugaba (saw) ya faɗi wannan hadisi?
Balarabe ya ɗauka ɗaukar yarensa a yi amfani da shi a matsayin yaren addini kamar wani abu ne da babu yanda aka iya dole sai haka ya faru, musamman yanda yake ganin cewa wai yarensa na cike da abubuwa gagararru da da yawa ko ma dukka sauran yaruka ba su da su, ya manta da cewa Allah ta’ala ba shi da yare, domin addinin dai da suka ƙi a farko dole ta sa suka ƙarɓa daga baya, yanzu kuma suka ɗauka gadon gidansu ne shi ne ya bai wa yaren nasu wannan girma da ɗaukaka.
Sun manta da cewa da Allah ya ga dama sai ya ƙaddara Shugaba (saw) ya fito Bahabashe kamar yadda wasu Annabawa suka kasance, ko Banufe ko kuma ma Bahaushe wanda zai sa a sauƙar da Littafi maɗaukaki da Nufanci ko da Inyamuranci, yanda kuma kake ganin Larabci da girma yanzu haka shi ma yarenka da kake rainawa zai zama haka a wajenka da Allah ya ƙaddara hakan.
Daga cikin abubuwan da Balarabe ya yi har da samar da hadisan da da yawan malamai suka ra’afanta shi da ke nuna falalar Balarabe da Larabci, ban ce dukansu ƙirƙirarru ba ne kamar yanda masana ba su faɗa ba amma kusan da yawansu akwai lauje cikin naɗi a yanda suka fito. Domin wasu daga cikinsu babu abin da suke nuni sai wariyar launi da fifita wasu bisa wasu ba kuma da tsoron Allah da Al-qur’ani yace shi ne ma’aunin fifiko ba, a a bari kawai dai dan sun kasance Larabawa.
Balarabe musamman na yau a rashin wayo da gidadancinsa ya ɗauka musulunci ma shi ne ya masa rana, ka kula mana ka ga yanda ya ɗauka musulunci gado ne ya yi da dole ya zama shi ne shugaba ko abin koyi in dai a abin da ya shafi addinin ne, ka gwada yin mu’amala da Balarabe na yanzu ka ga yanda abin zai kasance.
Abin da nake son na faɗa shi ne Larabci ya cancanci girmamawa tabbas ko dan wani hadisi da ban san tabbacin sahihancinsa ba (Domin ni ba ɗalibin hadisi ba ne) da yake cewa Habibi (saw) ya ce ina son Larabci domin abu uku, kasancewa ta Balarabe, yaren ‘ƴan Aljanna Larabci ne kuma Al-qur’ani ma balarabe ne.
Amma tabbas addini ne ya bai wa Larabci dukkan matsayi, duk da kuwa masu yaren na ganin akasin haka, wanda mu a ƙasar Hausa shaida ne cewa saboda ganin Musulunci da muke wa Larabci har baƙaƙensa ba ma bari su ke yawo a ƙasa, balle kuma wasu kalmomin cikinsa ko jimloli, kamar yanda zaurukan ɗaukar karatunmu ake koyar da abubuwan da tunda da larabci aka rubuta su sunansu ilimi amma da da wani yaren ne to sunansu shisshigi da taimakawa ɓarna ta ci gaba.
Domin karanta larabci da yanda ya shigo ƙasar Hausa danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu