Duk da an ce samuwa da ginuwa na adabin jama’a ko yayi ya tusgo ne daga ƙasar Ingila, amma ba a ƙasar Ingila irin wannan rayuwar adabin kasuwa ko yayi ya samu gindin zama ba kawai, a can Jamus a cikin ƙarni na 18 da na 19, an sami irin wannan adabi da ake wa laƙabi da Kitsch.
A cikin harshen Jamusanci ko Yiddish, kalmar Kitsch na nufin duk wani aikin adabi ko zane da bai da tagomashi ga masu mulki ko tajirai ko ya kasance lami ko kwashe-kwashen ayyukan wasu da aka yi a baya, (Wikipidia.org).
Adabin Kitsch ya soma watayawa sosai da sosai a ƙasar Jamus a ƙarni na 19, musamman a kasuwannin birnin Munich a tsakanin 1860 zuwa 1870, inda ake kiran duk wani aikin adabi da ke da arha ko na yayi ko mai karɓuwa a tsakanin al’ummar da aka yi domin su ko yake ja a cikin kasuwar sayar da ayyukan adabi da sunan na Kitsch.
Shi wannan adabin na Kitsch ba wai na talakawa ba ne kaɗai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kuɗin sayen irin waɗannan ayyuka, amma ƙarfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafaɗa-kafaɗa da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na ƙwarai.
Duk da cewa Kitsch ya samu karɓuwa a tsakanin jama’a, duk da haka bai wuce adabin kasuwa ko yayi ba ga sauran jama’a, musamman masu sarauta da tajirai, domin kuwa ba a yi aikin da kyau ba ko kuma takardun da aka zayyana hoton ko buga aikin adabin sun kasance na banza, ba su da aminci.
Ke nan adabin Kitsch bai wuce adabin Jamus da bai da mazaunin ƙwarai ba a tsakanin masu mulki da tajirai ko kuma yana magana kan abubuwan da ba su ne aka sa gaba ba a tsakanin al’ummar, ko kuma dai gwanjon adabi ne ko adabi ne da ke kwaikwayon wani adabi, ba tunani ko ƙirƙirar wanda ya samar da shi ba ne ko da kuwa ya samu karɓuwa tsakanin wasu gungun mutane, (Cuddon, 1999).
Saboda haka kamar yadda muka gani a baya, Kitsch wani nau`in adabi ne da ya wanzu a ƙasar Jamus wanda yake nufin duk wani aiki na zane ko aikin adabi wanda masu mulki ko masu kuɗi ba su yi na`am da shi ba. An samar da wannan adabi ne mai suna Kitsch domin a mai da martani ko ya yi jayayya da ayyukan adabi da aka samar a ƙarni na 18 da na 19 wanda yake ana masa kallo na masu mulkin ƙasaita da fitattun masu kuɗi ne.
Shi dai wannan salon adabin yana da matuƙar alaƙa da adabin da ke tashe ko kuma na yayi, ba wani abu ya sa aka kira shi da haka ba kuwa sai ganin cewa aikin da aka yi na zanen ko aikin adabin ba a yi shi yadda za a iya cewa ya ginu ko tsaru ba.
Ke nan adabin Kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kuɗi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da waɗanda suka yi fice ba, duk da haka su ma waɗanda suka yi ficen, ganin ƙarko ko kuma yanayin da wannan adabi ya fita da yadda mutane ke rububinsa ya sanya suka fara saye da karanta shi.
Za mu iya cewa adabin Kitsch ya kasance na talaka ne kawai domin ganin fasalin yadda aka samar da shi ba mai aminci ba ne, ma’ana kayan da aka yi aiki da su wurin samar da waɗannan zane ko ayyukan adabin ba su da inganci, kuma an samar da su ne ganin cewa waɗanda suke sayen shi ba su iya sayen manyan ayyukan adabi, wato wannan yana da sauƙin kuɗi ga masu sayen shi, kusan kowa zai iya sa kuɗi ya saye shi.
Wannan ya sa ake danganta adabin Kitsch (Wikipedia.org) da duk wani aikin adabi ko zane da aka samar maras kyau, wanda zai iya biya wa mai saye da buƙatarsa, ma’ana zai kashe masa ƙishirwa daga abin da yake so ya gani ko ya karanta, musamman cikin wata sabuwar kama ko siffa, a ayyukan adabin wanda aka kwaikwaya daga wanda ya gabace shi ko suke rayuwa tare.
Wannan ne ya sa irin wannan tsari ko fasali ya sha suka daga masana, fitattun daga cikin su kuwa su ne; Gabriel Thuller wanda ya goyi bayan wannan adabi na Kitsch bai dace da zamanin ba, domin ba gwanaye ke yin sa ba. Haka kuma wani fitaccen masani a fannin zane Georg Wilhelm Friedrich Hegel ya jaddada cewa zane-zanen wannan zamani yana da alaƙa da wani yanayi na lokacin da aka samar da shi, ba abin damuwa ba ne, in dai ya samu karɓuwa daga masu karatu.
Adabin Kasuwa Na Larabawa
Shi ma adabin Larabci kamar sauran ya sha kwaramniya har zuwa lokacin da aka samar da na zamani wanda yake da alaƙa da na Yammacin Dauri (Neo-Classical) wanda ya nemi ya canza fasalin adabin Larabci gaba ɗaya, wato wanda za a ce ya samo kayan aikinsa daga wanda ya gabata, kamar su Maqamatul Hariri da Alfu Laylah.
Saboda haka su waɗannan na zamanin sai ya kasance sun koma ko dai suna samo kayan gininsu daga waɗannan ko kuma suna juyar aikin marubuta adabin Yammacin Dauri ne kai tsaye, suna mai da su na Larabci.
Marubuta da dama a ƙasashen Siriya da Lebanon da Egypt sun samar da ayyukansu na adabi daga Maqama, fitattun daga cikinsu akwai Al-Muwayhili da littafinsa na The Hadith of Issa ibn Hisham a zamanin mulkin Ismail a Egypt, wanda wannan littafin shi ne za a iya cewa ya haifar da wani sabon zango a adabin Larabci.
Wannan yanayi shi ya ba marubucin nan ɗan ƙasar Lebanon,Goergy Zeidan, wanda kirista ne da ya yi hijira zuwa ƙasar Misira, bayan zanga-zangar da aka yi a Damaskus a 1860 damar fitar da basirarsa a fili sosai.
An dai fara buga labarin Ziedan a farkon ƙarni na 18 a cikin jaridar ƙasar Misira, wato Al-Hilal. Ba wani abu ya sa aka kira ayyukan waɗannan mutane na yayi ko na kasuwa ba sai ganin cewa su ne ayyukan da mutane suka fi sha`awa, saboda irin yadda aka samar da su da harshen da kalmomin da aka yi amfani da su da kuma yadda aka tsara su, sai kuma ficen da marubutan suka yi. Sauran waɗanda suka kasance a cikin wannan tsarin sun haɗa da Khalil Gibran da Mikha`il Na`ima.
Amma dai masana da dama na adabin Larabci sun bayyana cewa an fi ganin Littafin Zaynab na Muhammad Husayn Haykal da Adraa Denshawi na Muhammad Tahir Haqqi da kasancewa ayyukan adabi na farko a wannan ƙarni masu kama da ayyukan adabin jama’a ko kasuwa, fiye da waɗancan da muka ambata a baya. (dubi ƙarin bayani a Arabic Literature daga Wikipidia: The free encyclopedia).
Daga nazarin da aka gudanar an fahimci litattafan adabin yayi ko na jama’a na Larabci sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy inda ya siffanta rayuwar iyali.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Don karanta Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila danna nan
Edita@rumasau-kallamu