Abubuwan Dake Sa Wa Miji Ya Zamo Mafi Soyuwa A Wajen Matarsa

0
79

Ya zama wajibi ga maza su zamo masu kyawawan halaye da ɗabi’u. su yi nazarin litattafai da suke magana a kan aure domin su koyi yadda za su yi mu’amala da matansu.

Mace na jin daɗi kwarai, idan ta ga mijinta na nuna mata soyayyaarsa. Hakan na sa wa mace da dinga jin cewar lallai ta more miji. Don haka duk abin da miji ke so cikin hanzari za ta dinga yi. Da yawa ana samun mace ta yi ta nuna wa mai neman aurenta soyayya. Amma da an yi aure ta ga shi ya daina nuna mata ƙauna kamar da can.

Kuma har ta gano ba shi da kyawawan halaye da ɗabi’u. To daga nan ne sai ta dinga jin rayuwarta fa ta shiga ruɗani. Sai ƙiyayya ta fara shigarta, yana da kyau ka dinga sabunta soyayyarku.Ta bin hanyoyi daban-daban.

Domin karanta Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Danna nan 

Annabi Alaihissalam yakan ɗauki ƙashi da A’isha (R.A) ta ci, sai ya ci.Yakan sa bakinsa ta daidai inda ta sa bakinta. Hikimar hakan shi ne, nuna mata yadda yake kaunarta. Don haka ma ba ya ƙyamar komai nata.

Namiji ya zama mai kulawa da ibadarsa.

Ya zama wajibi ya kula da ibadarsa. Kuma ya tsaya ya jajirce don ganin matarsa na yin duk abin da Allah ya ɗora mata. Haka ma zai jajirce don ƴaƴansa su zama masu kulawa da addini. Wannan ma babban abu ne da ke ƙara wa mutum daraja ainun a wajen matarsa. Kuma cika umarnin Allah ne hakan. Domin Allah ya ce:

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku karewa kanku da iyalanku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kanta akwai waɗansu mala’iku masu kauri, masu ƙarfi. Basa saɓa wa Allah ga abin da ya umarce su, kuma suna aikata abin da ake umarnin su.(Tahreem:6)

A wani Hadisi kuma Annabi ya yi addu’a ga duk mai ta da iyalansa su yi sallah ne. Annabi (S,A,W) ya ce: “Allah ya jiƙan namijin da zai tashi cikin dare, ya tayar da matarsa don su yi sallah, ta ƙi tashi saboda barci, sai ya shafa mata ruwa a fuska har ta tashi suka yi sallah”

(Abu Dawud)

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceAbubuwan Dake Rage Ƙaunar Miji Gurin Matarsa
Labarin na GabaYadda Mace Ke Yin Bincike Da Kanta A Kan Manema Auranta